Showing 51001 words to 54000 words out of 180982 words
Chapter 18 - CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE Book .txt
wayoyinsa gaba daya, shi ma Junaid ya fita harkarsa bai kuma bin ta kansa ba, matsalarsa daya yanda Jasmine taki cin komai, gashi da ganinta xaka san abu na damunta, duk taki sakin jiki, though in yaje gidan da yamma ta kan je ta kwanta gefensa ko ta xauna kusa da shi, amma duk yanda xai yi da ita ta ci abinci bata ci, sai dai k'adan shi ma da kyar, in ya takurata tayi masa ihu, bini bini xaka ga ta kalli kofa ko taje can ta tsaya kamar dai tana jiran wani, on the third day Mama jummai ta dawo ya sallami nurse din, yasan yanxun xata fara cin abincin tunda ga mama jummai kila dama don bata saba da nurse din bane amma sai yaga otherwise don yi ma tayi kamar bata taba ganin mama jumman ba, ta kuma ki cin abincin still, da mama jummai ta tambaye Junaid El-Ameen ce mata yayi, yayi tafiya ne, duk abinda mama jummai tasan tana so sai da ta yi ta bata duk taki sai ketchup da take ta sha, duk baiwar Allahn ta rame. Yau Junaid na barin gun aiki ya nufi gidansu Faisal, yayi sa'an shi ma dawowan shi daga aiki kenan, Faisal yayi mamakin ganinsa barin da yaga ko canja uniform din jikinsa bai yi ba. Junaid ya xauna bayan sun gaisa yace "Ina son muyi wata magana da kai ne frnd" Faisal ya maida hankalinsa sosai yace "Am ol ears" Junaid ya shafa kai a nutse ya soma basa labarin mahaukaciyar tun daga farkon haduwarsa da ita, Faisal ya kwalalo ido yana kallonsa baki bude, har Junaid ya kai karshen labarin yana murmushi, Faisal ya sauke ajiyar xuciya yana gyada kai yace "Babban magana, but El-ameen bai kyauta ba, kuma ni ban ga abun fushi a nan ba, sabon da tayi da shi ne ya hanata sakin jiki da bata ganinsa, shiyasa take kin cin abinci!" Junaid ya tabe baki yace "Yanxu dai you are a Doctor, so nake plss ka gaya min yanda xaman psychiatry yake, is it advisable in kai ta can babu matsala?" Faisal ya kuma sauke wani ajiyar xuciyar yace "Gaskiya ina ga na gida kamar yanda El-ameen ke mata ya fi, kuma gashi har ta saba da shi samun lafiyarta ba lallai ya dau lokaci ba, yanxu dai kar ka damu xan je in same sa, nasan..." Junaid yace "No! no bana bukatan sa kuma, he shud hold on to his medication, idan taje psychiatry din suma xata saba da su" murmushi Faisal yayi, Junaid ya mike yace "Plss ka binkitar min psychiatryn da ka ga is ohk... I might come back later ko kuma in kira ka. Don yanxu Mumy xata fara kirana its almost six o'clock" Faisal ya bi sa da kallo har ya fita sannan ya shafa kai yace "Lallai Junaid da El-ameen, mahaukaciya kuma???" Mikewa yayi shi ma ya dau makullin motarsa ya fita xuwa gidansu El-ameen din, Ummi ce da Sumayya xaune parlor, ya gaida Ummi, ta amsa da fara'a tana tambayarsa mutan gida yace "Duk Suna lafiya Ummi, El-ameen na nan kuwa" tace "Ehh yana daki" dakinsa ya nufa ya tura kofar ya shiga da sallama, Ummi ta kalli Sumayya tace "Ki kai masa drink, ki tambayesa ko xai ci abinci" mikewa tayi ta nufi kitchen, kwance faisal ya sami El-Ameen da laptop a gefensa sai dai wayarsa yake dannawa, El-Ameen ya mike xaune ganinsa, Faisal yana murmushi ya karaso ya xauna gefensa yace "Yane the great Dr Ahmad El-ameen" El-ameen yayi murmushi shi ma ya mike xaune yace "Daga ina haka da yamma?" Faisal na kallon fuskarsa ganin yanda manyan idanuwansa suka fito yace "You look pale, are you ohk?" El-ameen ya lashe lebbensa yace "Stress ne frnd, ya aikin?" Faisal yace "Alhmdllh, Ya captain naka...." Dai dai sanda Sumayya ke kokarin shigowa dakin da faranti me dauke da drink da ruwa jin an ambaci Junaid ta tabe baki ta tsaya jikin kofar, El-ameen yace "Yana gidansu!" Faisal yayi dariya yace "Kuna nan har yanxu kamar 'yan biyu abun ku" El-ameen yayi murmushi yace "Sure!" Faisal yace "Uhmm!" El-ameen na kallonsa yace "Ya aka yi?" Faisal yayi murmushi yana girgixa kai yace "Bana tunanin akwai abinda ya isa ya hada ka da Captain..." Sumayya ta gyara tsayuwa da kyau ta baxa kunnuwa, El-ameen yace "Ban fahimta ba" Faisal yace "Daxu ya xo ya sameni ya kuma ban labarin baiwar Allahn da ku ke kokarin ganin kun ceto rayuwarta daga....." El-ameen ya katse sa yace "No! Da yake kokarin ganin ya ceto rayuwarta dai" Faisal yayi murmushi yace "Haba Dr, bayanin da Captain yayi min is not enough ace kayi fushi haka, kuma naga kun saba haka a tsakanin ku, kar ka manta lada ba kadan ba xaka samu idan yarinyar nan ta dawo hankalinta" El-ameen yace "No ni bn yi fushi ba faisal, just dat nayi quit ne, ya nemi wani likitan ko ya kai ta psychiatry..." Faisal yace "No pls, kar kace haka Dr, ba don Junaid xaka yi ba don Allah xaka yi...." El-ameen yayi murmushi yana girgixa kai yace "You know what?" Faisal ya girgixa kai, yace "Wllh wllh ban yi kuma, I've quit, he shud take her to the psychiatry, ka dai ji rantsuwar musulmi na maka, but babu damuwa xai iya ci gaba da amfani da gidana" Sumayya dake jikin kofa har lokacin duk tayi confuse ta rasa gane kan maganar, to wace yarinya suke magana a kai, yanke shawaran kiran Suhaima tayi tasan xata bata labari, El-ameen ya mike yace "kaga am going to clinic yanxu faisal" faisal ya sauke ajiyar xuciya yace "Ban ji dadin rantsuwar da kayi ba El-ameen, don Allah xaka yi ba don Junaid ba" El-ameen ya koma ya xauna yace "Look faisal, kullum! I mean everyday, karfe bakwae na safe baya karasawa nake barin gida in tafi gun yarinyar don akwai injections din da nake mata a lokacin, before leaving kuma sai na tabbatar tayi breakfast dat's around to eight, ina barin gidan xan kuma dawowa nan gida inyi wanka in shirya inyi breakfast snn in tafi clinic, a can clinic duk abinda nake da xaran sha daya da rabi yayi xan bari koma meye kuwa in tafi gun yarinyar don bata drugs dinta, in tilasta ta taci abinci sannan in kuma komawa clinic, duk abinda nake Karfe uku da rabi xan bari in kuma komawa gun yarinyar don bata drugs, sannan in sake komawa asibiti, Karfe bakwai da rabi a gidana yake min don a wannan lokacin ma tana da injections, baxan kuma bar gidan ba sai after ten don kafin ta kwanta Akwae drugs da xata sha, kasan sau nawa Junaid ke xuwa gidan?" Faisal yayi shiru yana kallonsa, El-ameen yace "Sau daya! shi ma sai da yamma ko kuma after magrib, kuma da ya xo xaka yi tunanin tsikararsa ake a gidan da kayi magana yace maka Mumy, ni ne ban san dadin tawa Mumyn ba, kasan matsalar da nake fuskanta yanxu gun parent dina kan yarinyar nan kuwa? yace ko biyar ban taba kashe mata ba I agree kuma dat is as a result of yana nuna shi me kudine, baya bukatan assistant din kowa, kasan dai yanda yake abubuwansa na girman kai, ni kuma kallonsa kawai nake don in kudin account dinsa sun yi wuta wllh basu wuce million uku ba in ma sun kai, kuma medication din hauka ba karamin kudi mutum xai kashe ba, yau da gobe yana cire dubu Dari dubu hamsin dubu dari biyu, dole kudin xai yi kasa, at dat time ko waye ubansa dole xai ce min i shud help ni kuma hakan nake jira dama, don kai kanka kasan waye ni idan baka tambayeni ba wllh baxan baka ba, in ko ka tambaya ko last card dina ne xan baka, kuma yace inyi excluding kai na a wa enda suka taimaketa a rayuwa tuni nayi hakan, don haka ka rakasa ya kaita psychiatry kawai frnd"
*Haske Writers Association*
鈿� *Captain Ahmad Junaid*鈿�
_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�
26.....
Mikewa faisal yayi ya d'aga kafada ya nufi kofa, da sauri Sumayya ta bar jikin kofar ta shige dakinta rike da farantin jin takunsa, faisal yayi ma Ummi dake parlor har lokacin sallama ya fita daga gidan, El-ameen ya koma ya kwanta tare da lumshe idonsa. Suhaima ce ta shigo parlor rike da waya tana kallon Hajiyarsu tace "Hajiyarmu yanxu sumayya ta kira ni...." Da sauri ta kalli khadija da ke kwance parlon sai kawai ta juya ta koma daki, Hajiya ta mike ta bi bayanta, khadija ta tabe baki ta ci gaba da danna wayarta. Junaid na kwance parlon Mumy that same day, idonsa lumshe kamar me bacci kamar wanda ya tuna abu ya mike xaune yana kallon wayarsa ya dauka yayi dialing number bugu uku aka d'aga, bayan sakwanni 20 jin ba ace komai ba daya bangaren yace "Uhn how you?" Jin an ki cewa komai still, yace "sai in kashe wayata ne" kamar xata yi kuka tace "Toh ina ruwana ni nace ka kira" murmushi yayi yace "Ohk, sai anjima" da sauri tace "Noo Ya Ahmad don Allah ka xo ka dauke ni, gida nake son dawowa" yace "Anki, xaman ki a can ya fi maki, sai kiyi ta neman fitina da Jawahir!" Katse wayar yayi ya ajiye yana murmushi, can ya mike ya fita ya koma part dinsa don tun da ya dawo daga gun faisal yake kwance parlon Mumy ko uniform bai cire ba, yana bedroom ya fito daga wanka yana shiryawa yaji an murda kofar parlor, juyawa yayi yana kallon kofar dakin har aka bude, faisal ya shigo da sallama, Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Glad you came" faisal ya karaso ya zauna gefen gado yace "ka jira har El-ameen ya sauko Captain, yayi sama da yawa, beside ni ban...." Da sauri Junaid yace "Xuwa kayi ka samesa?" Faisal ya d'aga masa gira, Junaid yace "Ohhh shit! Why? Meyasa xaka min haka, why did you go faisal, gaskiya ka bata min rai, who's he da yake tunanin without him Allah baxai bata lafiya ba, shi din banxa, bana bukatansa a lamari na kuma, bana bukata...." Faisal yayi murmushi yana girgixa kai yace "Haka kawai in sa baki daga karshe in ji kunya, da dai ban san ku bane, duk ku yi ku gama" Junaid yayi tsaki ya ci gaba da shirin sa, yana gamawa ya juya yana kallon faisal yace "Ka sama min psychiatry din ne frnd?" Faisal yace "Psychiatry me kyau sai Abeokuta or Lagos, but I will advice you to take haka to na Abeokutan ya fi, Neuro Psychiatric hospital Aro" Junaid yace "Har Ogun state? No plss samo min a nan north" faisal yace "Toh ai na can yafi komai ne, ga qualified neurologist..." Junaid ya xauna gefen gadon yace "Abeokuta kuma? Or kasan me I shud just look for a private neurologist for her...." Faisal yayi murmushi yace "That's money frnd, hospital ya fi!" Junaid yayi shiru, sai kuma ya shafa kansa a hankali yace "Allah xai rufa asiri, just get me a qualify one" faisal yace "ohkk dats not a problem, duk dai yanda ta yiwu in na gidan in na hospital," Junaid ya gyada kai yace "Toh shikenan" faisal yace "Sai da abu ya kwabe maku sannan xa a wani xo a sameni.... Ni kallonku kawai nake kai da El," Junaid yayi murmushi ya mike yace "Kaga xan kai mata fruits can gidan yanxu, muje part din mumy sai inyi kamar rakaka xan yi" faisal yayi dariya yace "Plss do and get ur freedom captain! You are getting old fa Mumys boy!" Junaid yace "Uhum kaga in tafiya xaka yi ka taso mu tafi!" Mikewa faisal yayi ya bi bayansa yana dariya, suka nufi part din Mumy, faisal yayi mata sallama, Junaid na shafa kai yace "Mumy bari in rakasa!" Mumy tace "Toh sai ka dawo" fita suka yi faisal na dariya, Suhaima dake tsaye bakin tap ta bi su da kallo tana tunanin xancen da Sumayya ta mata a waya, ajiyar xuciya ta sauke tana tunanin ta ina xata fara binciken da Hajiya ta sa ta, wai Mahaukaciya, tab, har Allah Allah take washegari yayi! Suna fita gidan Junaid ya kalli faisal yace "Kaga ban fito da mota ba, da taka xa mu je can gidan daga can sai ka ga Mahaukaciyar," faisal ya buda ido yace "Da take neman hada aminai biyu ba!" Junaid ya tabe baki yace "No bata hada mu ba, frndship din ne ya xo karshe dama" dariya kawai faisal yake, Junaid ya karbi makullin hannunsa ya shiga motar ya tada. A hanya suka siya fruits sannan suka kama hanyar gidan El-ameen, mama na sharan parlon suka shigo, ta mike tana masu sannu da xuwa, Junaid sai kalle kallen inda xai ganta yake, mama jummai ta lura da hakan ta nuna masa gefensu tace "Ga ta can" juyawa yayi ya ganta xaune ta jingina da bango ta d'an dukar da kai alamar bacci take, xai yi magana Mama jummai tace "Babu yanda banyi da ita ta bar wajen nan ba ta ki, kuma ta ki kwanciya, ni dai na rasa gane kan baiwar Allahn nan, ko abinci taki ci, dama Aminu kadai yasan kanta, rashin cin abincin nan ba karamin daga min hankali yake ba, toh ko dai bata da lafiya ne" Junaid ya tabe baki bai ce komai ba, faisal kuwa kallonta kawai yake, duk da ba ganin fuskarta yake ba, Junaid ya kallesa sannan ya karasa kusa da ita ya duka kamar me rada yanda bbu wanda xai ji sa a hankali yace "Jasmine!" D'ago kanta tayi da sauri ta bude ido tana kallonsa, a hankali faisal ya dinga komawa baya yana kallonta ko kiftawa bai yi har ya isa jikin kofa bai sani ba, kalle kalle kawai take sai kuma ta mike tana kallon kofar jin alamar mutum, da sauri ta nufi kofar Junaid ya bi ta da kallo, tana isa bakin kofar ta tsaya tana kallon faisal, still yayi a wajen ko kwakkwaran motsi bai yi, har lokacin idonsa na cikin nata, juyawa tayi a hankali ta dawo kusa da Junaid ta xube gabansa ta xauna, kallo daya xaka mata ka ga ramar da tayi, mama jummai ta fara dariya tace "Wayyo, ca take Aminu ne baiwar Allah, to ko don bata ganinsa yasa taki sakin jiki ne? Kasan fa ko mara hankali dole ya gane me kyautata masa" Junaid ya lumshe ido ya bude ya ajiye mata ledan fruits din hannunsa ya bude, kallon fruits din kawai take, a hankali ya 6alli ayaba guda daya a bunch dinsa ya mika mata, karba tayi tana ta kallon ayabar kamar me son gano abu, can dai ta sa hannu a hankali ta shiga cire peel din yanda ta ga El-ameen na mata, Junaid dai kallonta kawai yake, tana gama cirewa ta mika masa, ya karba ya kai mata baki ta ki ci, duk yanda yayi da ita kin ci tayi ta kwanta nan wajen, Mama jummai tace "Wai yaushe Ahmad din xai dawo ne, ina jin fa yarinyar nan sabon da tayi da shi yasa ta ki sake jiki rashin ganinsa, tausayi take ban wallahi" mikewa Junaid yayi bai ce komai ba, ya nufi kofa, faisal dake wajen har lokacin yana kallonta ya basa hanya ya fice, sannan shi ma ya juya ya bi bayansa, xama Junaid yayi a balcony ya fito da wayarsa yana jujjuyawa, faisal ya sauke ajiyar xuciya yace "Me ka fahimta game da reaction din yarinyar...." Tsaki Junaid yayi yace "kaga Kawai na yanke shawarar tafiya da ita Abeokutan, xai fi! Maganar ta saba da wannan ta saba da wancan bai taso ba yanxu" faisal dai kallonsa kawai yake, Mikewa yayi yace "Xan koma gida kafin....." Faisal ya katse sa yace "Haba Captain kana jin ance tun safe bata ci komai ba sai kace xaka tafi, ko da milk ne ka siyo a gwada bata mana" Junaid yace "Yea! But I don't want my mum to start calling me, bayan bakin gate kadai nace xan raka ka, do me a favour by buying the milk and bringing it to them, ga Atm card dina" kallonsa kawai faisal ke yi, har ya fiddo card din ya mika masa, can ya girgixa kai yace "Nima yanxu Mumyna xata kira ni" Junaid yace "Ohk then! Let me send the gate keeper!" Daga haka ya nufi gun mai gadi, faisal ya girgixa Kai ya koma parlon, ai tana jin an tura kofa ta mike da sauri, faisal ya rungume hannayensa yace "Poor you!" Komawa tayi a hankali ta xauna. Ya juya ya fita daga parlon wani tausayinta na shigarsa, anya ba asiri bane wannan, ban da haka me yayi mata xafi haka har ya kai ta ga hauka at her young age!" Ko da ya fita har Junaid yayi masa gaba da motarsa, tsaki kawai yayi ya nufi titi don hawa tricycle, ko waye bai son uwarsa???
Washegari Junaid na office ya kira faisal, bayan sun gaisa yace "Plss frnd make arrangement for me ko xuwa gobe ko jibi sai a tafi da ita can din, ta flight" faisal yace "Who's going der with her?" Junaid yace "Yea xan ce ma Mumy an min transfer din sati daya xuwa lag, kaga kafin sati dayan duk xa ayi abubuwan da ya kamata, bari dai xan xo idan na bar gun aiki sai muyi magana" faisal ya tabe baki yace "Ohk," sannan ya katse wayar. El-ameen ne xaune office ya hade kai da table, ya ji an bude kofar office din, dagowa yayi da sauri don ganin waye, sanin ya gaya ma nurses din ya gama attending ma patients for that day, ganin faisal ne ya kalli agogo yaga uku ya gota, faisal ya karaso yace "What's the problem El?" El-ameen ya shafa kansa tare da lumshe ido yace "Bacci!"
鉁嶐煆�
*Haske Writers Association*馃挕
Thanks all for the prayer Allah bar xumunci.
鈿� *Captain Ahmad Junaid*鈿�
_Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�
27.....
Faisal yace "Uhn wai bacci!" Kallonsa kawai El-Ameen yake da lumsassun idonsa, faisal ya