Showing 57001 words to 60000 words out of 180982 words

Chapter 20 - CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE Book .txt

na ta xabga uban sauri rike da ledan fruits, ta basa tausayi sosai, yasan tsakaninta da Allah take son yarinyar amma cutar dake damunta na asibiti ne ba na gargajiya ba, kuma tun da ta fara tunanin guduwa da ita wataran ko ba yanxu ba sai ta gudu da ita din, may be some other time xa su kuma nemanta, kallon jasmine yayi yaga yanda ta kafa ma glass din motar ido ko kiftawa bata yi tana kallon motoci dake tafiya kan titin kamar me son gano abu, yayi murmushi ya kamo hannunta yace "Jewel" kallonsa tayi da sauri, ya sakar mata murmushi, ta maida dubanta kan titi, sosai yake tausayinta don a yanxu dai bata da gata a duniya sai nasu, murmushi yayi tunawa da yayi axumi uku ya hau kansa fa. Tafiya kawai yake ba tare da yasan takamaiman inda xai kai ta ba ma, duk he's just confuse, yasan ko ya kira Junaid yanxu ma ba fitowa xai yi ba yana can Mumy ta gama basa abinci ta lullubesa yayi bacci, tsaki yayi yana girgixa kai.


鉁嶐煆�
*Haske Writers Association*馃挕




鈿� *Captain Ahmad Junaid*鈿�



_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�


29....


Parking yayi a gefen titi yana tunanin inda xai kai ta, gidan frnds dinsa masu mata? girgixa kai yayi don yasan ba lallai basu yi thinking negatively ba, Hotel? Ya girgixa kai coz it's not decent, to ina xai kai ta? Dafe kansa yayi cike da confusion, can ya dago ya juya yana kallonta ya ga ita ma shi take kallo, yayi murmushi a hankali yace "Ina xan kai ki jewel?" Dauke kanta tayi ta jinginar jikin glass din motar tana lekan waje, ya tada motar ya kuma hawa kan titi ya dinga driving din kamar bai son yi, cikin mintunan da basu wuce ashirin ba ya iso clinic, yayi parking a wajen da aka tanadar don ajiye mota, kalle kallen haraban hospital din ya dinga yi, ganin patients ne Kawai ya fito, ai tana ganin ya fita ta fasa ihu ita ma xata fito, ya juyo da sauri yace "Wait jewel yanzu xan bude maki" xagawa yayi daya side din ya bude motar ya fito da ita, kalle kalle ta shiga yi, ya rike hannunta ya shiga asibitin da sauri, bai saurari nurses din dake gaida sa ba ya haura sama da ita ya bude office dinsa suka shiga, key ya sa ma kofar sannan ya juya yana kallonta ya sauke ajiyar xuciya yace "We've got a good solution koh" kama hannunta yayi ya nufi bedroom din dake office din ya xaunar da ita kan gado yana kallonta, kwan kwasa office dinsa ya ji ana yi ya mike da sauri ya fita, mikewa tayi ita ma da saurinta ta bi bayansa, ganin ta biyosa yasa bai bude kofar ba yace "Who's there?" Muryar nurse yaji tace "ur attention is needed at the theatre sir" a fusace yace "Toh da ban xo ba fa" shiru tayi yyi tsaki ya kama hannun Jasmine ya maida ta dakin, xaunar da ita ya kuma yi a hankali yace "Look jewel, yanxun nan xan dawo kar ki bi ni plss" ya kusa second goma yana kallonta sannan ya mike a hankali xai fita ita ma ta tashi da sauri, yace "Ohhw ina xan kai ki jewel?" Fita yayi ta bi bayansa, ya isa show glass din dake office din me dauke da magunguna da ruwan allurori ya bude ya dauki wani kwalban allura ya rufe, syringe ya dauka ya juya suka kusa cin karo, yace "Sorry!" kama hannunta yyi suka koma dakin ya sa ta xauna, cikin few minutes ya hada alluran yayi mata a lap, 'yar kara kawai tayi masa tana bata fuska, yayi kasa da murya yace "Sorry jewel!" sun kusa minti goma xaune yana yi yana kallon agogo, yaji an kuma kwankwasa kofa, ya mike da sauri ita ma ta mike sai dai da ganinta kasan duk jikinta ya mutu, rike hannunta yayi ganin yanda take layi ya fito office din yace "Yes!" Muryar Abbansa yaji yace "S'ako na bai iso gare ka bane, ka wani garkame office kana ce min yes" xaro ido yayi yace "Ohh No, kaya nake canzawa ne Abba gani nan xuwa yanxu" Abba bai kuma cewa komai ba, hakan yasa ya kama hannunta suka koma dakin, kwantar da ita yayi ta lumshe ido, ya sauke ajiyar xuciya ya mike ya bude inda kayan shiga theatre dinsa suke, ya cire na jikinsa ya saka sannan ya lullubeta ya fito daga dakin ya rufe da key. Sha biyu saura ya fito daga theatre, yana komawa office ya bude dakin yaga bacci kawai take, toilet din dake nan ya shiga yayi wanka ya fito ya saka kananun kayansa ya fito office ya xauna ya kifa kansa kan table don bacci yake ji, wata nurse ta shigo rike da cup din coffee ta ajiye masa kan table tace "Sir" dagowa yayi yace "Thanks" har ta kai kofa xata fita yace "Nurse Sharifah" juyawa tayi ta dawo tace "Sir?" Yace "Nan sama kike ko k'asa yau?" Tace "a nan nake duty" yace "good, akwai patient a dakina, i want you to stay with her throughout the nyt, mental disorder gareta, in case xata farka cikin dare ki rakata restroom" shiru tayi tana kallonsa tsoro bayyane fuskarta, murmushi yayi yace "She won't hurt you, bata komai, just in case kar ta tashi ne yasa nace ki tsaya da ita" a hankali tace "Ohk sir... Let me explain to..." Katse ta yayi yace "No! Xan je in mata bayani" daga haka ya mike ya fita. Ta lallaba ta isa kofar dakin ta tura a hankali ta leka ta ganta tana bacci cikin bargo, a haka ya dawo office din yace "Ki shiga baxa ta maki komai ba nace" gyada masa kai tayi ta shiga dakin, ya dau coffee dinsa ya sha bayan ya huce sannan ya mike yayi kwanciyarsa kan kujeran dake office din. Can misalin Karfe uku ihunta ya farkar da shi ya mike da sauri ya nufi dakin dai dai lokacin da nurse din ma ta fito da gudu, shiga dakin yayi ya ganta tsaye sai ihu take, ya karasa da sauri ya rike hannunta yace "Jewel!" Tsit tayi tana kallonsa, ya sauke ajiyar xuciya ya xaunar da ita gefen gado, ya juya xai fita ta mike ta bi sa da sauri, nurse din na tsaye bakin kofar fita office har lokacin yace "Taho ki rakata restroom nace babu abinda xata maki" da kyar ta karaso ta shigo dakin, shi ya kaita toilet din, ya juya yana kallon Nurse din ta karaso a hankali ita ma ta shiga toilet din ya juya ya fita. Da asuba yana kwance idonsa lumshe bayan ya dawo daga mosque yaji mutum kusa da shi, bude ido yayi da sauri ya mike xaune yana kallonta, murmushi ya sakar mata yace "Good morning jewel" dagota yayi ya xaunar da ita gefensa, remote ya dauka ya kunna mata tv, wani kallo ta dinga yi ma TVn kamar idonta xai fito, dariya ta basa ya mike ya shiga daki yaga nurse din rakube kasan gado tana bacci, yace "Nurse Sharifa" mikewa tayi da sauri tana murxa ido duk da ganinta kasan a tsorace take, yayi murmushi yace "Kin yi sllh?" Tace "Yes sir" yace "Good" toothbrush da paste dinsa ya dauko ya mika mata yace "Xaki wanke mata baki" ta karba tana kallonsa, ya fito ya dagota taki tashi idonta kyar kan TV ko kiftawan kirki bata yi, dariya ta basa sosai ya kuma dagota ta fasa masa ihu har lokacin bata dauke idonta kan kallon ba, ya dau remote ya kashe tvn, sai a sannan ta juya ta kallesa, yayi murmushi ya dagata ta mike ya shiga daki da ita, kin yarda nurse din ta wanke mata baki tayi, hakan yasa ya wanke mata da kansa, ganin hadiye komai take yasa bai mata amfani da ruwan toilet din ba, ya fita ya dauko table water ya bude ya bata ta sha ya kama hannunta suka fita, ya kalli nurse din yace "Tea xaki je ki hado min plss" ba musu ta fita sai ga ta ta dawo da cup din tea ya karba yace "Thank you, kafin ki tafi ki dawo" tace "Ohk sir" sannan ta fita, jasmine ya shiga ba tean, ta sha kadan taki shan sauran da alama tea bai dameta ba, mikewa yayi ya tafi ya wanke bakinsa toilet, juyawan da xai yi ya ganta tsaye bayansa, murmushi yayi ya kama hannunta suka fito office, ya xaunar da ita sannan ya shanye sauran tea'n, TV ya kunna mata don yana son fita ya gaida Abbansa, ai ko ta nutsu sosai tana kallon mutanen dake yawo a tvn, ya mike a hankali yanda baxata lura ba ya fita ya haura last floor xuwa office din Abbansa, wani aikin Abban nasa yasa sa, ransa bai so ba amma bai yi musu ba ya shiga yi, yana cikin yi aka yi interrupting power, ya xaro ido sanin kila yanxu xata fara ihu, da sauri ya dinga signing files din, cikin minti sha biyar ya gama ya fice, ya sauka xuwa office dinsa, yana budewa yaga wayam daki ya nufa ya tura nan ma wayam, ya xaro ido ya shiga toilet nan ma bbu ita, wani mugun tashi hankalinsa yayi ya fito da sauri ya dinga dube dube ya sauko har downstairs yana kallon nurses din yace "wata patient bata sauko ba yanxu" bai jira cewarsu ba ya fita haraban asibitin da sauri, ya dinga dube dube bai ganta ba, gun masu gadi ya nufa da sauri ya tambayesu suka ce basu ga kowa ba, komawa reception yayi ya dinga yi ma nurses din masifa basu ga wata ta sauko ba yanxun nan, nan suka shiga dube dube su ma cikin ward,haka aka yi ta nemanta cikin asibitin har da likitoci da cleaners, wasu na tunanin anya kuwa Dr El-ameen dai dai kansa yake ganin yanda ya wani rikice nurse Sharifa ma duk hankalinta ya tashi barin da tasan ba mai hankali bace patient din, har Abba sai da ya sauko jin wai ana neman patient daga bakin wani likita, kallon d'an nasa kawai yake yana son sanin wace patient ce wannan wanda shi kadai yasan da ita a asibitin, Salatin da Dr Ibrahim wanda office dinsa ke kallon na El-ameen yayi ya ja hankalin nurses da wasu likitocin, da hanxari duk aka karasa wajen aka gansa tsaye bakin office din yana kallon ciki da mamaki, El-ameen ya karasa shima yana kallon office din, tsaye take a office din duk tayi kaca kaca da uban files din dake kan table dinsa, ta bude show glass duk ta watsar da magunguna da allurorin dake ciki, El-ameen ya d'an saci kallon Abbansa da ya rungume hannu yana kallon ikon Allah, daga likitocin har nurses din kallonta suke su kalli El-ameen, hakan ya bata tsoro sosai ganin yanda aka taru bakin kofar ana kallonta, ta fasa wani shegen ihu da karfi tana kallon El-ameen, sunkuyar da kansa yayi, ta dinga ihu can ta tafi bayan glass da gudu ta labe har lokacin ihu take, da kyar ya dago kai yana kallon Abbansa yace "Abba... Brain disorder gareta, I..I... She's under medication ne Abba, jiya da xan xo na taho da ita..." Wani mugun kallo Abba ke masa yace "Asibitina yayi kama da na mahaukata?" Sosa kai yayi xai yi magana Abba ya masa wani uban tsawa yace "Uwar ka xaka gaya min, wasu mahaukatan iyayen ne suka baka 'yar su ka sata under medication har kake yawo da ita?" Ya lumshe ido ya bude a hankali yace "No, A gida nake mata treatment din Abba, dama...dama akwai injection da nake mata da daddare ne to kuma ka kirani clinic shi yasa na taho da ita... Yanxu ma xan maida ta gidansu..." Abba yace "Amma arnaye ne iyayenta koh?" Shiru yayi bai ce komai ba, Strictly Abba yace "Ka maida masu 'yar su ka basu shawaran su kai ta asibiti, na kuma hanaka aikin nan daga yau, in ma kana son concentrating a field dinka na neurology ne yanxu you can go and apply for work a psychiatry ba ka dinga yawo da mahaukata ba har kana kawo min su asibiti suna min barna" daga haka Abba ya juya ya bar wajen, nurses din ma duk suka juya, jiki a sanyaye El-ameen ya karasa cikin office din ya kamo hannunta suka fita, sai wani shisshigewa jikinsa take a tsorace, likitocin dake gun suka bi sa da kallo, hijab dinta ya sa mata suka fita xuwa gun motarsa yasa ta shiga ya tada mota yyi warming ya bar haraban hospital din. Hotel ya nufa da ita don dat was the only option a lokacin, yana parking a haraban hotel din kiran Junaid ya shigo wayarsa, yayi mamakin ganin kiran don yasan bai xuwa can gidan da safe bare ace yaje ne ya gani a rufe, ya kalli agogo yaga bakwai da wani abu, daga kiran yayi daga daya bangaren Junaid yace "I saw ur text jiya, kuma I hail you da ka nuna kai babba ne" El-ameen yace "what's he talking about" Junaid yace "Really! There's no need of pretending, kana ina yanxu" El-ameen ya kalli inda yake sannan ya gaya masa, Junaid yace "Me kake a hotel" El-ameen yayi shiru sannan yace "Why are you even asking?" Junaid yace "Magana xa muyi, shud I come over..." El-ameen yace "aikin fa?" Junaid yace "Na dau hutun sati daya..." El-ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "Good! Taho ka same ni yanxu" daga haka ya katse wayar, junaid ya sauke ajiyar xuciya ya dafe kansa don maganar da faisal yayi masa jiya ya tsaya masa, so yake yaji mai El-ameen xai ce game da shawaran faisal, in har shima ya basa go ahead xai jaraba ya ga ko me yiwuwa ne.


鉁嶐煆�
*Haske writers association*馃挕




鈿� *Captain Ahmad Junaid*鈿�


_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�


30.....


Bude motar El-ameen yayi ya fito ya xaga ya fiddota yana rike da hannunta suka shiga reception din hotel din, babu wanda xai ganta yace mahaukaciya ce, xa a fi tunanin daga kauye ta fito duba da yanda take kalle kalle kamar idonta xai fito, tana kuma shisshige sa, daki yyi masu book aka basa makulli ya haura sama yana rike da hannunta, xaunar da ita yayi a dakin yana kallonta, tausayinta kawai yake a hankali yace "Allah ya baki lafiya jewel" ta dawo kusa da shi tana kallonsa, wayarsa ne ya soma ring ya dauka ganin Junaid ne ya d'aga ya gaya masa numbern room din da yake, cikin few minutes Junaid ya iso dakin ya murda kofa ya shigo, tsayawa yayi daga bakin kofa yana kallonsu da mamaki, El-ameen ya mike ya d'aga kafada yace "Ummi ta kusa gano abinda muke, so I had to take her away daga gidana" Junaid ya xaro ido yace "Da gaske?" El-ameen ya koma ya xauna yace "nafi tunanin gulma aka kai mata, nd I suspect that khadija" junaid ya girgixa kai yace "No! Khadija baxa taba exposing dinmu ba, kila dai kanwarka ce sumayya..." Kallonsa El-ameen ya tsaya yi yace "Sumayya kuma? Ae bata san komai ba" tabe baki Junaid yayi ya karaso dakin yana kallon Jasmine da ita ma idonta ke kansa, ya juya ya kalli El-ameen yace "Nan ku ka kwana kenan" El-ameen ya girgixa kai yace "Clinic, nd you know what sai da ta tona min asiri ta sa Abba ya ganta and he wasn't happy" Junaid bai ce komai ba ya xauna gefen gadon dakin, ta mike a hankali ta dawo kusa da shi ta tsaya tana kallonsa, ya d'an bude ido yana kallonta shima yace "Good morning!" El-ameen da ke kallonsu ya dauke kai yace "I heard you are taking her to Ogun state" Junaid yace "Yea but na canxa plan yanxu" El-ameen ya kallesa yace "To Which?" Junaid ya rufe ido na kusan second ashirin sannan ya bude a hankali yace "Faisal ya bani shawaran in aureta kawae, you know gidanmu an takura in fito da mata nan da few weeks, but kaga frnd ban san yarinyar nan ba, ban san daga inda ta fito ba, ban san meye sanadin haukatan ta ba, infact ban ma san ko matar aure bace, kana ganin shawaran faisal yayi, ya bani good reasons da yasa yace in aureta but am not even sure it will be possible ba lallai 'yan gidanmu su yarda ba" tunda ya fara magana El-ameen ke kallonsa ko kiftawa bai yi, Junaid ya kallesa jin bai ce komai ba yace "You are quite" El-ameen yayi saurin lumshe ido tara da yin wani murmushin da xa a iya kiransa da na karfin hali yace "Yea shawara ce mai kyau, may be xa a fi samun nutsuwa gun nema mata lafiya babu fargaba...." A hankali Junaid yace "Toh how xan kai ta gida a matsayin warce xan aura a haukace, kuma sai in ce ina iyayenta?" El-ameen yace "Ai tana da nutsuwa, shiryata kawai xa ayi ka hada ta da budurwa kamarta irin ace kawarta din nan ku je tare, bai fi kuyi xaman ten minutes ba ku fito just dat ka tabbatar kana kusa da ita kar ka bar wajen, matsalar da xa a samu a nan shine baxata yi magana ba but wannan ba komai bane Kawar sai tayi mata xa ayi tunanin kunya ne da ita, kuma ai gun Mumy kadai xaka kaita komai xai xo da sauki, iyaye kuma ba matsala bane xa mu san yanda xa muyi...." shiru El-ameen yayi xuciyarsa na bugawa ya rasa dalili, Junaid yace "Uhunn will this be possible kuwa?" El-ameen ya kallesa ya dan yi murmushi yace "idan Allah ya yarda" junaid ya lumshe ido yace "Toh Allah ya sa, idan Allah ya bata lafiya sai in sauwake mata ta nemi 'yan uwanta" kallonsa El-ameen yayi da sauri sai dai bai ce komai ba, Junaid yace "Toh ita mama dake kula da ita ina ka kaita?" El-ameen yace "Na sallameta" Junaid ya kallesa da sauri yace "ohh Why?" El-ameen yace "I had to, don Ummi ta tura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login