Showing 90001 words to 93000 words out of 180982 words
Chapter 31 - CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE Book .txt
wucewa ya mike yana kallon kayan da El-ameen ya ajiye masa, wani takaici ya rufesa, sai kace irin yana son auren, tsaki yayi ya fixgo rigar yana kallo, ya kusa wani minti goman tsaye ya sake jan tsaki ya xura rigar ya dau wandon ya sa, kayan suka haska sa sosai, da ganinsa ka ga Ango, toilet ya koma ya dauro alwala ya fito ya tafi gun hulunarsa ya dau daya ya gyara ya daura a kai ya dau takalminsa ma ya saka, ko agogo bae kalla ba bare ya fesa turare ya fice daga dakin rike da wayoyinsa. Kallonsa El-ameen ke yi daga sama xuwa kasa yace "Ina sabon takalmin da hular, kuma ina babban rigar?" Wani uban harara Junaid ya xabga masa yace "Baxan sa ba" El-ameen ya fashe da dariya yace "Oho dai bbu wanda zai ce wa ennan ma da ka sa ba sabo bane, nima bari in je inyi wankan in shirya as babban abokin ango" daga haka ya shige dakin, junaid ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido, banda faduwa babu abinda gabansa yake wai shi xa a daura ma aure yau. Daya saura El-ameen ya fito daga dakin sanye da farar shaddar da ya dauka a closet din Junaid, shi ma yayi kyau har ya gaji, kallo daya Junaid yayi masa ya dauke kai, El-ameen ya xauna gefensa yana murmushi ya mika masa agogo yace "Here!" Dauke kai junaid yayi bai ce komai ba, El-ameen yace "Dama ka saki ranka ga su faisal nan xuwa, if not you will be the topic of discussion na cewa an maka auren dole, just pretend as if its nothing and you are happy..." Ko rufe baki El-ameen bai yi ba sai ga faisal da kusan abokansu har biyar, Junaid ya sauke ajiyar xuciya hade da sakar masu murmushi, tsokanansa suka shiga yi kamar shi ya kawo su, shi dai baya cewa komai sai murmushin da bai kai ciki ba, hotuna suka shiga yi gaba daya a parlon, daga bisanni suka fita don xuwa masallaci, sosai gidan ke cike da jama'a, Junaid yaji dama kawai ya gansa a waje ba sai ya bi ta compound ba, kallo aka bi sa da shi barin su Umma da bakin ciki ya cika su kamar su yi yaya, ko kayan arxiki basu saka ba ana xaune bakin murhu, El-ameen yace "Ya kamata ka je Mumy ta sa maka albarka kafin ka fita, sai ka ga anyi a sa'a" part din Mumy Junaid ya nufa, bai bi ta kan mutanen parlon ba ya shiga bedroom dinta ya sameta xaune tare da sisters dinta sai abokan arxiki, kallonsa take har ya iso gabanta ya durkusa cikin sanyin murya yace "Xa mu tafi masallaci Mumy" ta yi murmushi tace "Toh Allah ya tsare, yasa ayi a sa'a" ya sunkuyar da kai yace "Ameen" sai a sannan ya kalli Mutan dakin ya gaishesu ya mike ya nufi kofa, duk suka bi sa da kallon sha'awa ganin irin respect dinsa har ya fita, kanwarsa ce Aysha ta bi bayansa murmushi dauke fuskarta tace "Ya Ahmad" yace "Ya kike" tace "lafiya lau, tun jiya bamu hadu ba" yace "Eh ai kin san inda nake" daga haka ya ci gaba da tafiyarsa. Ana saukowa daga juma'ah aka daura aurensa da warce bai ma sha'awan sani yanxu kam a kan sadaki dubu dari biyu, bai wani tsaya gaishe gaishe ba ya xame ya bar wajen ba tare da El-ameen ma ya sani ba ya koma gida. Bayan isha junaid da El-ameen sai faisal na Parlor xaune Khadija ta shigo tace Abba na kiransa, mikewa yayi ya fita xuwa part din Abbansa, shi da Abban Humainah ne xaune parlon sai wani amininsa, Junaid ya samu waje ya xauna sannan ya gaishe su, nasiha suka yi masa banda Abbansa dake ta kallonsa, shi dai kansa na kasa, har suka kare cikin sanyin murya yayi masu godiya, Abbansa ya kara da cewa Allah yayi ma rayuwar aurensa albarka, yace "Ameen" Abokin Dad dinsa Alhaji Umar ne yace Ya tashi ya tafi don tuni aka kai masa matarsa, mikewa yayi bai ce komai ba ya fita daga parlon, part din Mumy ya tafi a sanyaye ya sameta ita da Ummin El-ameen a dakin, ya isa gabanta ya durkusa murya can kasa yace "Abba yace in tafi Mumy" Mumy tace "Toh Allah ya albarkaci rayuwar auren ka Ahmad, Allah ya baka xuri'a ma su yi maka biyayya kamar yanda kake min" kasa dago kansa yayi, lokaci daya idonsa ya kada, a hankali ya daura kansa kan kafarta cikin sanyin murya yace "Mumy ban san matar ba har yanxu" murmushi tayi ta dago kansa tana kallonsa sai dai bata ce komai ba, Ummi tace "kasan mahaifinka baxai maka xabin da xai cuce ka ba Ahmad, Allah ya baku xaman Lafiya, tashi ka je" mikewa yayi a hankali ya juya ya fita. Karfe tara saura suka bar gidan shi da El-ameen da faisal, xuwa yanxu kam sun daina tsokanarsa ganin yanayinsa, El-ameen ji yake kamar shi aka yi ma hakan yaji tausayinsa sosai, gun masu gasassun kaji El-ameen yayi parking ya fita ba a dau lokaci ba ya dawo rike da ledan kaji da drinks, tafiyar kusan minti talatin suka yi suka isa gidan Junaid, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya ya juya yana kallonsa bayan yayi parking a compound din, gidane duplex mai kyau da girman gaske, compound din ya kawatu da kayan shuke shuke iri iri ga haske ko ina kamar rana, faisal sai danne dariyarsa yake ganin yanda Junaid ya hade rai yana kallon gidan, El-ameen yace "Toh ni dai a nan xan bar ka, gobe da safe zan kawo maka motar ka" junaid ya kallesa yace "Haka koh?" El-ameen yace "Allah baxan shiga ba sai dai ko faisal" faisal yace "No, sai dai mu dawo ganin amarya gobe" El-ameen yace "Exactly" ficewa junaid yayi daga motar El-ameen yace "Wait ga kajin amarya baka dauka ba" ko saurarensa junaid bai yi ba ya nufi cikin gidan, El-ameen ya dauki ledojin ya bude motar ya fito yana dariya ya bi bayansa, tsaye ya gansa a parlor yana bin ko ina na parlon da kallo, kamshi me dadi ne ke tashi ta ko wani angle, komai na parlon brown nd milk, El-ameen ya karaso cikin parlon ya ajiye masa ledan a kasa yace "Sai da safe ango" junaid ya kallesa yace "Yanxu da gaske ba xa ka raka ni ba" El-ameen yace "Kila yanda gabana ke faduwa naka baya faduwa haka, I just can't, gobe dai xan dawo..." Daga haka ya fice daga parlon, Junaid ya sauke ajiyar xuciya ya kalli hanyar stairs, a hankali ya karasa ya haura sama, ya dde tsaye corridor din dakunan yana kallon kofar dakin da ya san tana ciki, karasawa yayi bakin kofar ya murda a hankali lokaci daya ya tura yana kallon cikin dakin, xaune ya ganta can karshen gado ta takure waje daya fuskarta rufe da babban veil, ya kusa minti biyu yana kallonta sannan ya karaso cikin dakin ya isa gabanta ya tsaya yana kare mata kallo yace "Ke kika ce ma iyayena kina so na?" Shiru bata ce komai ba, yace "Magana nake maki" Mikewa tayi xata bar wajen ya fixgota har sai da ta fado kansa fuskarsa daure yace "Ina maki magana xaki wuce" turasa tayi tace "Ni ka kyaleni, ko kuma kai kace kana so na ba" saketa yayi ya bude ido yana kallonta da mamaki, ta bude mayafin fuskarta ta hararesa ta bar wajen, rungume hannayensa yayi ya bi ta da kallo har ta xaga daya side din gadon ta xauna, murmushi kawai yayi ya fita daga dakin ya shiga nasa, wayarsa ya dauka ya shiga neman layin El-ameen, yana dagawa yace "Guess wacece amaryar" El-ameen yace "Uhun! Humainah!" Junaid yace "Ohh dama ka sani?" Dariya yayi yace "No! I only guessed" tsaki junaid yayi yace "Very funny wai Humainah, all the same xata yi girki dai ta gyara gida ta kula da jasmine, shikenan an wuce wajen" El-ameen ya xaro ido yace "Wacece jasmine kuma?" Shiru junaid yayi can yace "Sai da safe" daga haka ya ajiye wayar ya shiga cire kayan jikinsa, wanka yyi yayi alwala ya fito ya canxa xuwa jallabiya snn yayi shafa'i da wutr ya jima xaune kan darduma daga bisanni ya mike ya koma kan gado, har ya kwanta ya mike xaune, murmushi yayi da ya tuna wai fa Humainah ce matar da aka aura masa, wai Humainah, dariya ya fara yi, ita wannan har ta isa aure yarinyar da ko secondary bata kare ba, though yaji dadin da ya kasance ita ce don baxa ta wani bada wani matsala gun kawo jasmine gidan ba, tabe baki yayi ya mike ya fita ya koma dakinta, kwance ya sameta ta takure waje daya tana bacci, tabe baki yayi ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa can nesa da ita, ya kusa awa daya kwance kafin bacci ya daukesa, can cikin dare ya ji tana tashin sa, ya mike xaune ya kunna bedside lamp yana kallonta da kumburarrun idonta alamar ba kuka kadan tayi ba, yace "What?" Kamar xata yi kuka tace "Ni yunwa nake ji" ya kalli agogo ya ga sha biyu har ya gota yace "Yunwa? Baki ci abinci daga gidanku bane" tace "Eh ni ban ci ba" d'an tsaki ya ja yace "Toh ni yanxu ina xan samo maki abinci tsakar daren nan?" Tace "Ni dai wllh yunwa nake ji" ledan da El-ameen ya ajiye parlor ya tuna yace "Tafi parlor xa ki ga leda ki duba meye a ciki" ta xaro ido tace "Ni dai tsoro nake ji" ya hade rai yace "Xan fa kwada maki mari idan kina damuna ina bacci" ta fashe da kuka ta mike xaune, tsaki ya ja ya sauka daga kan gadon ita ma ta sauko ta bi bayansa da sauri, a tare suka sauko parlon ya kunna wuta ya dau ledan ya bude ya nufi kitchen ya dauki plate da wuka da fork sai cup ya fito, nan parlon ya dawo ya xauna kan rug ya fiddo kaza daya ya Yanyanka a plate yana kallonta yace "Ga shi" matsowa tayi a hankali ta dau daya ta fara ci, ya mike yace "Idan kin gama ki kashe wutan parlon" da sauri ita ma ta mike tace "Don Allah ka jira ni ya A.jay wllh tsoro nake ji" ya hade rai yace "Kina fa damuna" ta d'an marairaice ta koma ta xauna ta ci gaba da cin kazar, xaunawa yayi shi ma yace "Idan sha biyu da rabi yayi baki gama ba xan yi tafiyata" ta d'an hararesa bata ce komai ba, dauke kai yayi sai dai lokaci lokaci ya kan saci kallonta, suna hada ido yyi saurin cewa "Haka aka koya maki a gidan ku Idan xaki kwanta kar ki cire kayan da kika yini da?" Tace "Kai ma ai gidanku ne" bai kuma ce mata komai ba har ta gama, ta mike ta dau plate din tace "Raka ni kitchen" harararta yayi ta rama ta nufi kitchen, ya bi ta da kallo, tana fitowa ya mike ya kashe wutan parlon yyi hanyar stairs ta bi bayansa da sauri suka shiga dakin a tare, wutan dakin ta kunna yace "Meye haka?" Tace "Xan wanke baki mana" gado ya nufa yayi kwanciyarsa ta shiga toilet, ba a dau lokaci ba ta fito ta nufi closet ta bude ta fiddo doguwar riga da hijab ta koma bayin, tana fitowa tayi kwanciyarta nesa da shi ta juya masa baya, yace "Ke wa kika bar ma wuta a kunne?" Tace "Nafi son haka, ni bana son duhu" tsaki yayi ya mike ya tafi ya kashe wutan kan ya dawo har ta mirgino ta dawo gefensa, yayi kwanciyarsa hade da juya mata baya.
鉁嶐煆�
*Haske Writers association*馃挕
[16/12, 00:57] Hussaini Atk: 鈿� *Captain Ahmad Junaid*鈿�
_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�
44/45
Da asuba Junaid ya dade xaune gefen gado daga bisanni ya mike, kallo daya ya ma Humaina dake bacci ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito har xai fita xuwa masallaci ya dawo ya isa kusa da gadon ya buga kafarta, bude ido tayi a hankali tana kallonsa ya juya ya fita daga dakin, ko da ya dawo daga masallaci samun ta yayi kwance tana bacci har lokacin, bayi ya shiga ya debo ruwa ya fito ya watsa mata, ta mike xaune da sauri tana kallonsa, yace "Sllh!" Daga haka ya fita daga dakin, tsaki tayi ta bi sa da harara ta sauka daga gadon ta shiga bayi. Tana idar da sllh tayi jigum kan darduma, can ta mike ta shiga gyaran bedroom din, tana gamawa ta shiga bayi ta wanke baki tayi wanka ta wanke bayin ta fito daure da towel, gaban mirror ta xauna ta gama shafe shafenta sannan ta shirya cikin Abaya baki da veil dinsa ta d'an gyara fuskarta ta koma gado ta xauna tayi tagumi. Bude kofar dakin aka yi fatima da khadija suka shigo, Humainah ta mike da sauri lokaci daya tayi murmushin jin dadin ganinsu, fatima tace "Uhum Amaryar yayarmu, Antynmu!" Hade rai tayi can ta fashe da kuka tace "Ni ba amaryarsa bace, ai Hajja tace sbda a raba sa da mahaukaciyar nan ne aka aura masa ni, amma da ya rabu da ita sai a sa ya sakeni in ci gaba da karatuna" innocently tayi maganar tana kallonsu, Khadija da fatima suka fashe da dariya barin khadija, juyawa Humainah tayi a sanyaye ta koma gefen gado ta xauna, hade kanta tayi da gwiwa tana kuka, fatima ta karasa kusa da ita da sauri tace "Toh ai ba mu ce ba haka bane ba fa Humainah" Humainah ta girgixa kai tana kuka tace "Ba wani nan nasan wayo aka min baxa a ce ya sakeni ba, yar yarinya da ni xan je ss3 za ayi ma aure bayan ku ba a maku ba....." Khadija ta xauna gefenta tace "Ni dai ba dariya nake maki ba, ba ruwana, ga abinci Mumy tace a kawo maki" Humainah ta dago kanta tana share hawayen idonta tace "Hajja fa?" Khadija tace "Ta ce anjima xata xo" Junaid ne ya shigo dakin ya tsaya daga bakin kofa yana kallonsu yace "A baki aka ce ku bata abincin?" Kallonsa suka yi gaba daya basu ce komai ba, ya nuna masu kofa duk suka mike, Humainah ta hade rai tana kallonsa tace "Ba yanxu xa su tafi ba toh" Ko kallonta bai yi ba, ganin su fatima sun nufi kofa kamar xata fashe da kuka tace "Don Allah kar ku tafi" murmushi fatima tayi ta raba ta gefen yayan nata ta fita khadija ta bi bayanta, kuka sosai Humainah ta shiga yi, ya karaso cikin dakin ya xauna d'an nesa da ita yace "baki san ke ba yarinya bace yanxu tun da har aka aurar da ke" hade rai tayi tana kallonsa tace "Ni dai yarinya ce" murmushi yayi yace "Toh naji! tsoron xama ke kadai kike a dakin da kike son su xauna da ke?" Ta kallesa hade da gyada masa kai, yace "Toh xan samo maki warce xata dinga taya ki xama ai kina so?" Tana kallonsa tace "Amma babba ce?" Ya girgixa mata kai yace "No yar yarinya ce kamar ki sai ta dinga taya ki xama kuna kwana ma tare" sosai ta hade rai tace "A'a bna so, xan iya xama ni kadai" shiru yayi yana kallonta, can yace "Saboda me?" Ta mike tace "Haka nan kawai, xan iya xama ni kadai abuna" daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, lumshe ido yayi ya bude yana naxarin abinda ta ce, Mikewa yayi shima ya fita daga dakin ya koma nasa. Karfe sha biyu saura aka danna bell downstairs, Junaid dake bedroom dinsa yana danne dannen waya ya mike ya fita, dai dai lokacin da Humainah ma ta fito, kallo daya yayi mata ya sauka ya je ya bude kofar, Hajja ce tsaye bakin kofar da Sadiya, ta washe hakora ganin Junaid tace "A'a ango, to gani na biyo ka don kayi amarya sai ka mance da uwar gida?" Juyawa yayi ya bar bakin kofar ya koma parlor, Hajja ta shigo tare da Sadiya da gudu Humainah ta sauko jin muryar Hajja ta rungumeta, Hajja tace "Lalala kinga yanda kika yi kyau kika yi fresh kuwa? Lallai Amadi ya iya kiwo daga jiya xuwa yau" hade rai Humainah tayi tace "Ni babu abinda ya ban na ci har yanxu" Hajja tace "Ehh amma ai kin kwan masa a gida" turo baki tayi ta tafi ta xauna, Hajja ta kalli Junaid tace "Banxa kai kuma ko ka kira ka mana godiya ka ga xukekkiyar amarya ba mahaukaciya ba" Kallonta kawai yake can ya tabe baki yace "Nii ban gode ba tun da ban ce ina so ba, kawai makala min aka yi" Humainah ta fashe da kuka tace "Hajja kin dai ji ko, ni dai tare xa mu koma don ni ma makala min aka yi ban ce ina so ba" Hajja ta hade rai tace "Kai kaga irin hada ta da Allah annabin da aka dinga yi don ta amince da gantalallen auren ka, banda kaddara me xata yi da kai Ahmad, kai da cikakken saiti baka da, wllh wllh 'yar nan tafi karfin ka, kawai ka kara gode ma Allah da ya sa aka baka ita" juyawa tayi tana kallon Humainah tace "ke kuma kar ki kuskura ki bari ya kwana dakin ki tunda haka yace, hanyar jirgi daban ta mota daban kin dai ji ni..." Humainah ta gyada mata kai tana goge hawayen idonta, Hajja ta nemi kujera ta xauna tana cewa "Banda walakanci an samu an lallaba yarinya da kyar ta amince ta rufa maka asiri ta aureka xaka dinga gaya mana magana, ko fa kwandalar ka bbu a bikin nan don tsiya.... Amma bari na fi ka iskanci sai ka xo ka durkusa kana rokona in ce mata ta so ka" girgixa kai Junaid yayi ya mike ya haura sama abun sa. Har Karfe uku Hajja na gidan ita dai Sadiya dama turo ta aka yi ta ga kwakwaf