Showing 78001 words to 81000 words out of 180982 words

Chapter 27 - CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE Book .txt

basu san wacece shegiyar da xa a aura masa ba don basu ga alamar daya daga 'ya yansu bane, da yammacin ranan Hajja ta diro gidan, magiya junaid ya dinga mata kan ta gaya masa wacece matar tasa tace ubansa yayi kadan balle shi, sosai hankalinsa ya tashi, bayan magrib Abba yasa a kira sa, yana shiga parlon ya xauna Abba yace "Babu wani shirin da za kuyi ku, ko walima ne?" Ya gigixa kai yace "A'a Abba, walimar da xa ayi a nan gida ya isa" Abba yace "Toh shkkn, hakan it's Ohk" ranan kasa bacci junaid yayi har kusan karfe dayan dare, wayarsa ya jawo daga karshe ya shiga neman number Humainah don yasan baxa ta rasa sanin matar ba, har ya gama ringing bata daga ba ya sake kiranta sai gashi ta dauka, cikin sanyin murya yace "Kina ji na Humainah" "Um" kawai tace masa kamar anyi forcing dinta, ya lumshe ido ya bude yace "Plss nasan baxa ki rasa sanin warce xa a aura min ba, ki gaya min wacece plss" taki cewa komai na kusan second talatin har sai da yace "Hello" sannan tace "Ban sani ba nima" yace "Plss" kamar xata yi kuka tace "Ban sani ba," tsaki yayi ya katse wayar ya jefar. Washegari alhamis da asuba yayi shirin fita aiki ya fice ya bar masu gidan, haka ya wuni bai da sukuni ranar, yana barin gun aiki Clinic ya tafi gun El-ameen, da damuwa yace "Frnd har yanxu fa ban san wacece matar nn ba" El-ameen yayi murmushi yace "gobe idan mun kai ka xaka ganta, sbda son da Abba yake maka shi yasa yake son surprising naka" Junaid yace "Plss ka daina bata min rai more, what sort of surprise is this, and what if fitinanniya ce taki yarda da xaman yarinyar a gidan?" El-ameen ya hade rai yace "Sai ka korata nasu gidan don bata xo maka da gida ba, and tana tarewa gobe ita kuma xata tare ran lahadi don ranan Dr Sumayya xa su yi tafiya, tsaf ita ma kuma xa a gyara mata nata dakin" Junaid ya dafe kai yace "Ba haka ba frnd, kasan tana iya xuwa tayi reporting ma su Abba fa" El-ameen yace "Shit, gashi har xa a maka aure gobe baka xama mature person ba, ka ki girma har yanxu junaid, look yanxu you are going to leave a free.... When I say free I mean a free life, no more Mumy Mumy Mumy, you are going to head a family of ur own don haka ko wani decision kayi a gidan ka is right ba sai wanda parent dinka suka maka ba, from tomorrow you will be on ur own" junaid yace "Uhum?" Tsaki El-ameen yayi, can yayi kwafa yace "da rabon matar nan ta rainaka idan ta lura you don't have a say of ur own!" Mikewa Junaid yayi yace "Baka san ni ba kenan" daga haka ya fice daga office din.


鉁嶐煆�
*Haske writers association*馃挕




鈿� *Captain Ahmad Junaid*鈿�


_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�


43.....


Washegari da ya kasance Friday tun sassafe El-ameen ya xo da leda me dauke da sabon dinkin dakakkiyar farar shadda me tsada sosai, dinkin yar ciki da babban riga, sai hula da takalma duk sabbi, tsokanarsa kawai yake yana dariya, shi dai Junaid wayarsa kawae yake dannawa daga kwancen da yake fuskar nan tasa babu yabo bbu fallasa, gefensa El-ameen ya zauna yace "Ko fa d'an gyaran fuska da gashi baka yi ba captain, haka xa mu kai ka?" Mikewa Junaid yayi xaune a fusace yace "look ka daina bata min rai Ahmad, bana son haka, it's not funny" El-ameen ya hade rai yace "Ka hayyako min kamar ni xan aurar da kai? Toh ni dai ban da ni a kai ka in har baxa ka tashi muje saloon ba" tashi daga xaunen junaid yayi fuskar nan tasa daure ya shige daki, El-ameen ya fashe da dariya yace "Oho dai, ana saukowa juma'a xa a daura..." Karfe tara fatima ta kawo breakfast parlon, El-ameen yace "Ina kawar ki Humainah?" Fatima ta ajiye abun hannunta ta gaishesa sannan tace "Tace anjima xa su taho da mamarta da na kirata" El-ameen yace "Toh idan kin koma ki ce ma Mumy Junaid na can yana ta kuka nayi lallashin duniyar nan yaki saurarata" fatima ta xaro ido lokaci daya ta fashe da dariya tace "Kai yaya" ya hade rai yace "Ba aiken ki nayi ba" juyawa tayi ta fita tana dariya. Karfe sha biyu da wani abu junaid ya shiga wanka, kan ya fito El-ameen har ya fito masa da sabbin kayan ya feshe su da uban turare, kallo daya junaid ya ma kayan ya nufi closet dinsa ya bude ya fito da wani blue shaddarsa, El-ameen yace "Ya haka ango ga sabon dinki nayi maka?" Ko kallonsa junaid bai yi ba ya ajiye kayan kan gadon ya xauna yana goge gashin kansa, tsaki El-ameen yayi ya mike ya dauke kayan ya mayar closet din ya sa key ya jefa makullin aljihunsa, kallonsa kawai junaid ke yi, can yace "You are provoking me El-ameen" El-ameen yayi dariya yace "oho dai tunda ba iya dukana xa ka yi ba, in baxa ka sa sabon dinkin ba ka tafi da singlet da short nicker gun daurin auren ma" yana murmushi ya fice masa daga dakin, Junaid ya fuxar da iska ya dafe kansa xuciyarsa na tafarfasa, ya kusa minti ashirin xaune sanin lokaci na wucewa ya mike yana kallon kayan da El-ameen ya ajiye masa, wani takaici ya rufesa, sai kace irin yana son auren, tsaki yayi ya fixgo rigar yana kallo, ya kusa wani minti goman tsaye ya sake jan tsaki ya xura rigar ya dau wandon ya sa, kayan suka haska sa sosai, da ganinsa ka ga Ango, toilet ya koma ya dauro alwala ya fito ya tafi gun hulunarsa ya dau daya ya gyara ya daura a kai ya dau takalminsa ma ya saka, ko agogo bae kalla ba bare ya fesa turare ya fice daga dakin rike da wayoyinsa. Kallonsa El-ameen ke yi daga sama xuwa kasa yace "Ina sabon takalmin da hular, kuma ina babban rigar?" Wani uban harara Junaid ya xabga masa yace "Baxan sa ba" El-ameen ya fashe da dariya yace "Oho dai bbu wanda zai ce wa ennan ma da ka sa ba sabo bane, nima bari in je inyi wankan in shirya as babban abokin ango" daga haka ya shige dakin, junaid ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido, banda faduwa babu abinda gabansa yake wai shi xa a daura ma aure yau. Daya saura El-ameen ya fito daga dakin sanye da farar shaddar da ya dauka a closet din Junaid, shi ma yayi kyau har ya gaji, kallo daya Junaid yayi masa ya dauke kai, El-ameen ya xauna gefensa yana murmushi ya mika masa agogo yace "Here!" Dauke kai junaid yayi bai ce komai ba, El-ameen yace "Dama ka saki ranka ga su faisal nan xuwa, if not you will be the topic of discussion na cewa an maka auren dole, just pretend as if its nothing and you are happy..." Ko rufe baki El-ameen bai yi ba sai ga faisal da kusan abokansu har biyar, Junaid ya sauke ajiyar xuciya hade da sakar masu murmushi, tsokanansa suka shiga yi kamar shi ya kawo su, shi dai baya cewa komai sai murmushin da bai kai ciki ba, hotuna suka shiga yi gaba daya a parlon, daga bisanni suka fita don xuwa masallaci, sosai gidan ke cike da jama'a, Junaid yaji dama kawai ya gansa a waje ba sai ya bi ta compound ba, kallo aka bi sa da shi barin su Umma da bakin ciki ya cika su kamar su yi yaya, ko kayan arxiki basu saka ba ana xaune bakin murhu, El-ameen yace "Ya kamata ka je Mumy ta sa maka albarka kafin ka fita, sai ka ga anyi a sa'a" part din Mumy Junaid ya nufa, bai bi ta kan mutanen parlon ba ya shiga bedroom dinta ya sameta xaune tare da sisters dinta sai abokan arxiki, kallonsa take har ya iso gabanta ya durkusa cikin sanyin murya yace "Xa mu tafi masallaci Mumy" ta yi murmushi tace "Toh Allah ya tsare, yasa ayi a sa'a" ya sunkuyar da kai yace "Ameen" sai a sannan ya kalli Mutan dakin ya gaishesu ya mike ya nufi kofa, duk suka bi sa da kallon sha'awa ganin irin respect dinsa har ya fita, kanwarsa ce Aysha ta bi bayansa murmushi dauke fuskarta tace "Ya Ahmad" yace "Ya kike" tace "lafiya lau, tun jiya bamu hadu ba" yace "Eh ai kin san inda nake" daga haka ya ci gaba da tafiyarsa. Ana saukowa daga juma'ah aka daura aurensa da warce bai ma sha'awan sani yanxu kam a kan sadaki dubu dari biyu, bai wani tsaya gaishe gaishe ba ya xame ya bar wajen ba tare da El-ameen ma ya sani ba ya koma gida. Bayan isha junaid da El-ameen sai faisal na Parlor xaune Khadija ta shigo tace Abba na kiransa, mikewa yayi ya fita xuwa part din Abbansa, shi da Abban Humainah ne xaune parlon sai wani amininsa, Junaid ya samu waje ya xauna sannan ya gaishe su, nasiha suka yi masa banda Abbansa dake ta kallonsa, shi dai kansa na kasa, har suka kare cikin sanyin murya yayi masu godiya, Abbansa ya kara da cewa Allah yayi ma rayuwar aurensa albarka, yace "Ameen" Abokin Dad dinsa Alhaji Umar ne yace Ya tashi ya tafi don tuni aka kai masa matarsa, mikewa yayi bai ce komai ba ya fita daga parlon, part din Mumy ya tafi a sanyaye ya sameta ita da Ummin El-ameen a dakin, ya isa gabanta ya durkusa murya can kasa yace "Abba yace in tafi Mumy" Mumy tace "Toh Allah ya albarkaci rayuwar auren ka Ahmad, Allah ya baka xuri'a ma su yi maka biyayya kamar yanda kake min" kasa dago kansa yayi, lokaci daya idonsa ya kada, a hankali ya daura kansa kan kafarta cikin sanyin murya yace "Mumy ban san matar ba har yanxu" murmushi tayi ta dago kansa tana kallonsa sai dai bata ce komai ba, Ummi tace "kasan mahaifinka baxai maka xabin da xai cuce ka ba Ahmad, Allah ya baku xaman Lafiya, tashi ka je" mikewa yayi a hankali ya juya ya fita. Karfe tara saura suka bar gidan shi da El-ameen da faisal, xuwa yanxu kam sun daina tsokanarsa ganin yanayinsa, El-ameen ji yake kamar shi aka yi ma hakan yaji tausayinsa sosai, gun masu gasassun kaji El-ameen yayi parking ya fita ba a dau lokaci ba ya dawo rike da ledan kaji da drinks, tafiyar kusan minti talatin suka yi suka isa gidan Junaid, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya ya juya yana kallonsa bayan yayi parking a compound din, gidane duplex mai kyau da girman gaske, compound din ya kawatu da kayan shuke shuke iri iri ga haske ko ina kamar rana, faisal sai danne dariyarsa yake ganin yanda Junaid ya hade rai yana kallon gidan, El-ameen yace "Toh ni dai a nan xan bar ka, gobe da safe zan kawo maka motar ka" junaid ya kallesa yace "Haka koh?" El-ameen yace "Allah baxan shiga ba sai dai ko faisal" faisal yace "No, sai dai mu dawo ganin amarya gobe" El-ameen yace "Exactly" ficewa junaid yayi daga motar El-ameen yace "Wait ga kajin amarya baka dauka ba" ko saurarensa junaid bai yi ba ya nufi cikin gidan, El-ameen ya dauki ledojin ya bude motar ya fito yana dariya ya bi bayansa, tsaye ya gansa a parlor yana bin ko ina na parlon da kallo, kamshi me dadi ne ke tashi ta ko wani angle, komai na parlon brown nd milk, El-ameen ya karaso cikin parlon ya ajiye masa ledan a kasa yace "Sai da safe ango" junaid ya kallesa yace "Yanxu da gaske ba xa ka raka ni ba" El-ameen yace "Kila yanda gabana ke faduwa naka baya faduwa haka, I just can't, gobe dai xan dawo..." Daga haka ya fice daga parlon, Junaid ya sauke ajiyar xuciya ya kalli hanyar stairs, a hankali ya karasa ya haura sama, ya dde tsaye corridor din dakunan yana kallon kofar dakin da ya san tana ciki, karasawa yayi bakin kofar ya murda a hankali lokaci daya ya tura yana kallon cikin dakin, xaune ya ganta can karshen gado ta takure waje daya fuskarta rufe da babban veil, ya kusa minti biyu yana kallonta sannan ya karaso cikin dakin ya isa gabanta ya tsaya yana kare mata kallo yace "Ke kika ce ma iyayena kina so na?" Shiru bata ce komai ba, yace "Magana nake maki" Mikewa tayi xata bar wajen ya fixgota har sai da ta fado kansa fuskarsa daure yace "Ina maki magana xaki wuce" turasa tayi tace "Ni ka kyaleni, ko kuma kai kace kana so na ba" saketa yayi ya bude ido yana kallonta da mamaki, ta bude mayafin fuskarta ta hararesa ta bar wajen, rungume hannayensa yayi ya bi ta da kallo har ta xaga daya side din gadon ta xauna, murmushi kawai yayi ya fita daga dakin ya shiga nasa, wayarsa ya dauka ya shiga neman layin El-ameen, yana dagawa yace "Guess wacece amaryar" El-ameen yace "Uhun! Humainah!" Junaid yace "Ohh dama ka sani?" Dariya yayi yace "No! I only guessed" tsaki junaid yayi yace "Very funny wai Humainah, all the same xata yi girki dai ta gyara gida ta kula da jasmine, shikenan an wuce wajen" El-ameen ya xaro ido yace "Wacece jasmine kuma?" Shiru junaid yayi can yace "Sai da safe" daga haka ya ajiye wayar ya shiga cire kayan jikinsa, wanka yyi yayi alwala ya fito ya canxa xuwa jallabiya snn yayi shafa'i da wutr ya jima xaune kan darduma daga bisanni ya mike ya koma kan gado, har ya kwanta ya mike xaune, murmushi yayi da ya tuna wai fa Humainah ce matar da aka aura masa, wai Humainah, dariya ya fara yi, ita wannan har ta isa aure yarinyar da ko secondary bata kare ba, though yaji dadin da ya kasance ita ce don baxa ta wani bada wani matsala gun kawo jasmine gidan ba, tabe baki yayi ya mike ya fita ya koma dakinta, kwance ya sameta ta takure waje daya tana bacci, tabe baki yayi ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa can nesa da ita, ya kusa awa daya kwance kafin bacci ya daukesa, can cikin dare ya ji tana tashin sa, ya mike xaune ya kunna bedside lamp yana kallonta da kumburarrun idonta alamar ba kuka kadan tayi ba, yace "What?" Kamar xata yi kuka tace "Ni yunwa nake ji" ya kalli agogo ya ga sha biyu har ya gota yace "Yunwa? Baki ci abinci daga gidanku bane" tace "Eh ni ban ci ba" d'an tsaki ya ja yace "Toh ni yanxu ina xan samo maki abinci tsakar daren nan?" Tace "Ni dai wllh yunwa nake ji" ledan da El-ameen ya ajiye parlor ya tuna yace "Tafi parlor xa ki ga leda ki duba meye a ciki" ta xaro ido tace "Ni dai tsoro nake ji" ya hade rai yace "Xan fa kwada maki mari idan kina damuna ina bacci" ta fashe da kuka ta mike xaune, tsaki ya ja ya sauka daga kan gadon ita ma ta sauko ta bi bayansa da sauri, a tare suka sauko parlon ya kunna wuta ya dau ledan ya bude ya nufi kitchen ya dauki plate da wuka da fork sai cup ya fito, nan parlon ya dawo ya xauna kan rug ya fiddo kaza daya ya Yanyanka a plate yana kallonta yace "Ga shi" matsowa tayi a hankali ta dau daya ta fara ci, ya mike yace "Idan kin gama ki kashe wutan parlon" da sauri ita ma ta mike tace "Don Allah ka jira ni ya A.jay wllh tsoro nake ji" ya hade rai yace "Kina fa damuna" ta d'an marairaice ta koma ta xauna ta ci gaba da cin kazar, xaunawa yayi shi ma yace "Idan sha biyu da rabi yayi baki gama ba xan yi tafiyata" ta d'an hararesa bata ce komai ba, dauke kai yayi sai dai lokaci lokaci ya kan saci kallonta, suna hada ido yyi saurin cewa "Haka aka koya maki a gidan ku Idan xaki kwanta kar ki cire kayan da kika yini da?" Tace "Kai ma ai gidanku ne" bai kuma ce mata komai ba har ta gama, ta mike ta dau plate din tace "Raka ni kitchen" harararta yayi ta rama ta nufi kitchen, ya bi ta da kallo, tana fitowa ya mike ya kashe wutan parlon yyi hanyar stairs ta bi bayansa da sauri suka shiga dakin a tare, wutan dakin ta kunna yace "Meye haka?" Tace "Xan wanke baki mana" gado ya nufa yayi kwanciyarsa ta shiga toilet, ba a dau lokaci ba ta fito ta nufi closet ta bude ta fiddo doguwar riga da hijab ta koma bayin, tana fitowa tayi kwanciyarta nesa da shi ta juya masa baya, yace "Ke wa kika bar ma wuta a kunne?" Tace "Nafi son haka, ni bana son duhu" tsaki yayi ya mike ya tafi ya kashe wutan kan ya dawo har ta mirgino ta dawo gefensa, yayi kwanciyarsa hade da juya mata baya.
鉁嶐煆�
*Haske Writers association*馃挕




鈿� *Captain Ahmad Junaid*鈿�


_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�


44/45


Da asuba Junaid ya dade xaune gefen gado daga bisanni ya mike, kallo daya ya ma Humaina dake bacci ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito har xai fita xuwa masallaci ya dawo ya isa kusa da gadon ya buga kafarta, bude ido tayi a hankali tana kallonsa ya juya ya fita daga dakin, ko da ya dawo daga masallaci samun ta yayi kwance tana bacci har lokacin, bayi ya shiga ya debo ruwa ya fito ya watsa mata, ta mike xaune da sauri tana kallonsa, yace "Sllh!" Daga haka ya fita daga dakin, tsaki tayi ta bi sa da harara ta sauka daga gadon ta shiga bayi. Tana idar da sllh tayi jigum kan darduma, can ta mike ta shiga gyaran bedroom din, tana gamawa ta shiga bayi ta wanke baki tayi wanka ta wanke bayin ta fito

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login