Showing 3001 words to 6000 words out of 180982 words
Chapter 2 - CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE Book .txt
ma Umma da Hajiya, ba a dau lkci ba ya dawo ya dauki nasu ledan na masu gadi da masu wanki da share sharen gidan ya fita don xuwa su raba bayan yyi godiya. Junaid ya kalli Mumy yace "Mumy xan je gidansu El-Ameen!" Mumy tace "Gidansu El-Ameen kuma, wae wnn sintirin xuwa gidansu El-Ameen da kke kwana biyun nn kalau kuwa Ahmad? Ko dae gun budurwa kake xuwa?" Ta kare maganan tana murmushi, Dariya yyi ya shafa kansa yace "Kai Mumy budurwa kuma, shi dae nake rakawa fa" Mumy na murmushi har lkcn tace "uhn uhn kai dae fadi gskya Ahmad" ya shagwabe mata yace "Mumy ni da gske wllh ba gun budurwa nake xuwa ba, El-Ameen nake raka wa" Mumy tace "In ma gun ta kake xuwa ae ba laifi bne Ahmad, it's high time yhu start planning of settling down with a wife yanxu son" murmushi yyi ya mike yace "Allah ya kawo lkci mumyna" tayi murmushi tace "Toh Ameen" yace "Bari in kai ma su Umma kudin Mumy, daga can xan wuce" Mumy tace "Toh Allah ya tsare kar dae ka yi dare plss Ahmad" yace "In'sha Allah mum" daukan wayarsa yyi ya fita daga falon, gun Umma ya fara shiga ya samu Muhibba ce da wata kawarta a falon, ya wani hade rae ba tare da ya damu da amsa gaisuwar da suka yi masa ba ya mika mata 15k din yace "Gashi ki ba ma Umma" juyawa yyi ya fice daga falon, Kawar Muhibba me suna Salima tace "Kai amma wllh kina bada mata Muhibba, har wannan dan karamin alhakin ne xaki dinga barin yana walakanta ki don yana da kyau, ubansa kuma na da dukiya, sae kace ba gogaggiyar 'yar jami'a ba?" Muhibba tayi murmushi tace "Baki san Ahmad bane Salim, ya fice tunanin ki wllh...." Salima ta katse ta tana kalle kalle tace "Da'alla banxa tsaya ki saurareni, mu je daki in baki wani plan ki ga ko baxae yi aiki ba" mikewa Muhibba tayi suka yi daki da kawar tata cike da xumudin jin plan din. Junaid na fita bangaren Hajiya ya nufa ita ma ya bata kudin, tana jujjuya kudin tace "Duk kudin da Alhaji ya bari Ahmad ka rasa abinda xaka kawo min sae wani shegen dubu sha biyar, wato sauran kuma ka ba uwar ka koh, toh wallahi ka ji tsoron Allah don hakkinmu baxai bar ka ba" Junaid ya daga kafada yace "Ni Abba bae bar min kudi ba, kawae gani nayi hakan ya dace shi yasa na kawo maki na kai ma Umma don ko mahaifiyata ban ba kudi ba gidan nn, gobe ko jibi ae Abban xae dawo, in kina da wani bukatar da ya wuce na wannan idan ya dawo sae ki tambayesa" yana kai wa nn ya fice mata daga palo, ta bi sa da kallo baki bude, idonta ya kankance don bacin rai, rufe bakin tayi tana gyada kai tace "yaro yaro ne" kwafa tayi ta juya ta koma don ci gaba da abinda take tana wani murmushi. Karfe shidda saura Junaid ya isa gidansu El-Ameen sanin ya baro clinic yanxu, Mum din sa ya samu falo, bayan sun gaisa yace "Ummi El-Ameen ya dawo koh?" Hajiya Maryam da ake kira da Ummi tace "Ehh ya dawo daxu amma ya fita yanxun nan, ka kira sa kaji inda yake don nasan baya asibiti" Junaid yace "Toh shknn Ummi xan kirasa, ni xan koma" Ummi tace "Toh ko ruwa baxa ka sha ba Ahmad?" Yyi murmushi yace "Alhmdllh Ummi" Ummi tayi murmushi tace "Toh ka gaida min Hajiya Amina" yace "Xata ji Ummi" fita yyi daga falon yana tunanin inda El-Ameen ya tafi, sae da ya shiga mota snn ya kirasa, bugu daya ya d'aga Junaid yace "Kana ina ne?" El-Ameen yace "Au! ai nayi xaton xuciya kayi ka bar ni da mahaukaciyar taka" Junaid yyi tsaki yace "Kana ina nace?" Dariya El-Ameen yyi yace "Kai dae duk abun ka baxa ka iya xuciya da ni ba wllh, come over ina gidana, na samo mai gadi, ya kuma min hanya an samu wata dattijuwa, we are ol there 2gether ynxu, mind yhu duk wata xaka dinga biyan mai gadin dubu 30, ita kuma warce xata tsaya da mahaukaciyar xa'a bata dubu 50 monthly, coz its not an easy job, ga kuma risk din dake tattare da job din, and yhu make sure ka shiga kasuwa ka siyo mata kayayyakin da xata dinga sawa including inner wears" Junaid yace "Ni ban san inda ake sai da kayan mata ba" El-Ameen yace "So? Ba sae ka ce a raka ka ba, ko ka shiga kasuwar kayi tambaya" tabe baki Junaid yyi ya katse wayar ya kama hanyar gidan. A waje yyi parking ya shiga, sabon mai gadin da ke xaune compound din ya gaishesa da ladabi, Junaid ya amsa ya nufi kofar shiga palo, daga bakin kofar ya tsaya yana kare ma palon kallo, duk an share barnar daxu ko ina yyi fess, kallon El-Ameen dake xaune kan daya daga kujerun falon yana danna waya yyi snn ya karasa shiga falon, El-Ameen ya kallesa yace "Kayan fa, ni fa I can't put her under medication da suturan jikinta, it's very irritating, na dae yi mata alluran barci daxu don ban ga alaman tana yi ba" Junaid ya xauna gefensa yace "Toh don Allah ka raka ni mu siyo kayan mana, serious ban san ina xan samu women wears ba" El-Ameen yace "Nace idan ka shiga kasuwar kayi tambaya mana sae kace ba wayayye ba" shiru Junaid yyi yana kallonsa, wata yar dattijuwa ce da baxata haura sittin ba ta fito daga kitchen da alama ita ce ta yi gyaran gidan gaba daya, gaishe da Junaid tayi, yyi murmushi yace "Sannu da aiki mama" mikewa El-Ameen yyi ya haura sama ba a dau lkci ba ya sakko rike da sabulan wanka tsadaddu da sponge, sae toothbrush da toothpaste yana kallon dattijuwar yace "Mama ga wannan, wanka xa ki taimaka kafin mu dawo, xae kai maki ita bayin yanxu," Matar tayi shiru tana kallonsa sae dae da ganinta kasan a tsorace take, El-Ameen yyi dariya yace "Babu abinda xata maki wllh mama, bacci ae take kuma baxa ta tashi ba yanxu, mu je ki ga" bin bayansa tayi suka haura sama, Junaid ya bi su da kallo kafin ya shafa kansa, El-Ameen ne ya fara shiga dakin snn ita ma ta shiga, tana nan kwance yanda ya bar ta bayan yyi mata allura, idanuwanta duk a rufe, kallon dattijuwar yyi yace "Kinga bacci take ko mama, kuma na gaya maki baxa ta tashi ba sae bayan awanni takwas," kai kawae ta gyada masa, bayi ya nufa ya hada ruwan dumi da yawa snn ya fito dakin ya dauketa ya nufi bayin da ita ya kwantar da ita kasan neat bathroom din ya fito yana kallon tsohuwar da ya sa ma Mama yace "Gata can na kai maki bayin, don Allah ki wanke mata wannan gashin da kyau mama, nasan baxa kiyi wahalan fito da ita ba idan kin gama don bata da nauyi, xan fito maki da bargo kawae ki lulluba mata har mu dawo da kaya" tace "Toh yaro" juyawa yyi ya fita ta nufi cikin bayin. Siyayya ba kadan ba Junaid yyi ma Mahaukaciyar, tun daga kan normal English wears wato dogayen riguna, xuwa mayyukan shafawa, turarruka, da inner wears da jallabiyoyi, har man gyaran gashi da combs duk sae da ya siya da takalma sae huluna da 'yan kunnaye, shi dae El-Ameen bin sa kawae yake yana dariya, ganin har xa ayi magrib yasa El-Ameen yace "Kai koh kayan lefe kake hadawa fa sae haka Junaid, for God's own sake kayan nan sun isa haka it's time for magrib" Junaid ya kallesa yace "Ohk" Karfe bakwae da rabi suka isa gida, shi ma don sun tsaya hanya sun shiga masallaci sun yi sllh snn sun tsaya eatry siyan abinci, xaune suka samu dattijuwar a falo kan dankwalinta alamar sllh ta idar, tayi masu sannu da xuwa, Junaid ya ajiye kayayyakin hannunsa, El-Ameen ya bude wani leda ya fiddo doguwar riga da man shafawa da na kai sae inner wears da turare ya mika ma matar yace "Gashi mama ki taimaka ki sa mata" ta mike tace "Toh" sannan ta karbi kayan ta haura sama, durkusawa tayi gabanta ta yaye bargon da ta rufe ta da shi ta bude tsadadden man da aka bata ta shiga shafa mata jikinta, cikin mintuna da basu fi goma ba ta gama shiryata, ta debi hair cream me yawa ta shafa mata a dogon gashinta sannan ta shiga taje gashin a hnkli saboda tsantsin sa, tana yin haka hawaye na xuba idonta kmr daxu da take mata wanka, rayuwa kenan duk yanayin da ka tsinci kan ka ka gode Allah, Coz he knows best, shi kadae yasan dalilin barin wannan Baiwar Allah haka, ba wae kuma don baya sonta ya bar ta a hakan ba, har ta gama tufke mata dogon gashinta da ya kusa bayanta hawayenta bae tsaya ba, gyara mata kwanciya tayi ta rufa mata bargon ta fito tana kallonsu El-Ameen tace "Na gama" El-Ameen ya mike yace "Kin sa mata komae dae koh mama" tace "Na sa mata" yana 'yar dariya yace "Kin tabbata mama" murmushi tayi tace "Na sa mata komai yaro" kallon Junaid yyi sannan ya nufi stairs, Junaid ya mike ya bi bayansa, El-Ameen na shiga dakin ya karasa gabanta ya durkusa ya yaye bargon dake jikinta a hankali, rike breath dinsa yayi yana kallonta ko kiftawa bae yi har Junaid ya shigo ya same sa a hka, shima ya durkusa a hankali nan gabanta yana kallonta.
*Haske Writers Association*
[16/10, 19:05] Hassan Atk: *CAPTAIN AHMAD JUNAID
_By Khaleesat Haiydar_
2....
Junaid na isa gidan su El-Ameen yyi parking daga waje ya shiga, Sumayya kanwar El-Ameen ya samu xaune falo da kawayenta biyu, ya karasa cikin falon cikin tafiyarsa ta k'asaita, yi tayi kmr bata gansa ba ta ci gaba da ba kawayenta labarin da take, gaida shi kawayen nata suka yi suna kallonsa, don Capt Junaid ko namiji bae masa kallo daya, ya amsa gaisuwar su ba tare da ya dube su ba yana kallon Sumayyar yace "Ke yayanki na gida?" Ba tare da ta kallesa ba tana yatsine fuska tace "Nima bn sani ba" wayarsa ya ciro aljihunsa ya shiga kiransa, Kawayen nata biyu duk suka xuba masa ido, El-Ameen na d'agawa Junaid yace "are yhu at home?" El-Ameen yace "Yea are you coming?" Wani kallo ya watsa ma Sumayya ya katse wayar ya nufi dakin El-Ameen, Husnah ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Kai Sumayya waye shi, ya hadu wllh, don Allah ni dae ki hada ni da shi, yyi min ni dae plss" Sumayya tayi dariyar rainin hnkli tace "Uhm Kinga gayen nn irin mace masa da nake a da, na so shi kmr raina amma he looked into my face nd told me baya sona, I cried my life dat day, gashi i downgraded my sef telling him I love him" bude baki duk suka yi suna kallonta, Fiddausi tace "Tabdi! Toh meye hadin ku da shi? D'an uwanku ne?" Tsaki Sumayya ta ja ta dauki lemon gabanta ta shiga sa. Xaune ya samu El-Ameen kan laptop da siririn farin glass a idonsa yana danne danne, El-Ameen ya kallesa yace "Uhnn! Our great Capt Ahmad Junaid Murnai, kaga yanda ka kara kyau ka koma kamar wani Egyptian kuwa" Junaid ya tabe baki ya xauna gefen makeken gadon dakin yace "You will neva change" El-Ameen yyi murmushi ya tura laptop din gabansa ya juya yana fuskantarsa yace "I missed you a lot frnd, am glad you are back" Junaid ya shafa kansa yace "Sai kace gaske," El-Ameen ya kura ma farin shirt din jikinsa ido yace "Wait! Ciwo ka ji Captain" Junaid ya kalli shirt dinsa da sauri ya ga jini daga gefen shirt din, El-Ameen ya mike yace "What's dat? The shirt looks dirty ma" girgixa kai Junaid yayi ya shiga unbuttoning din shirt din yace "Wata mahaukaciya ce wllh" El-Ameen ya kwalalo ido yace "Mahaukaciya kuma" Junaid yace "Yea!" Nan ya ba El-Ameen lbrin abinda ya faru a hanyarsa ta xuwa, El-Ameen yace "Eyya! Poor her, but kai me ya kai ka rike mahaukaciya ma banda abun ka" Junaid bae ce komae ba ya mike ya nufi bathroom, wanka yyi ya fito sanye da Bathrobe din El-Ameen ya goge jikinsa ya bude wardrobe ya fiddo wasu kayan abokin nasa ya sa. Bayan Magrib yace ma El-Ameen xae koma gida, El-Ameen yace "Haba frnd baxa ka raka ni gun Iman ba plss, wllh ban san me xan ce ba idan na je, gashi Mami fushi take da ni, escort me plss, dama jira nake sai ka dawo sai mu je" Junaid yyi d'an murmushi yace "Ohk buh bari in kira mumy kar taji shiru har ynxu" Bayan isha suka bar gidan bayan Capt Junaid yyi ma Ummin El-Ameen sallama, A motar Junaid suka tafi El-Ameen na tukin, El-Ameen ya lura da yanda Junaid ya kafa ma tagar motar ta inda yake xaune ido yana kallon waje, El-Ameen xae yi magana ya ji Junaid yace "Dr d'an tsaya nn don Allah in ga ko an kwance mata igiyar, it's gud ace anyi hkn" El-Ameen ya kafa masa ido sae kuma ya tabe baki ya daga shoulder ya gangara gefen titi yyi parking, Junaid ya bude motar ya fita, tana nn xaune kan bolan, rike da wani bakin Leda a hannunta, rungume hannayensa yyi yana kallonta, El-Ameen ya dafa sa yace "let move on Capt, they've freed her" juyawa Capt Junaid yyi suka koma motar suka bar wajen, suna isa gidan El-Ameen ya kira Iman da nmbr da Ummi ta basa, kanwar ta ce ta fito tayi masu iso har falo ta cika su da drink, mahaifiyarta ta fito suka gaisa ta bar palon, ba a dau lkci ba Iman ta fito sanye da wata doguwar riga me adon stone blue da gold, tayi rolling kanta da plane blue mayafin kayan, kyakkyawa ce ba kadan ba, ta karaso falon kamshin turarenta ya cika ko ina ta xauna, kallon Junaid El-Ameen yyi, Junaid ma ya kallesa, suka shiga kallan kallo, ganin El-ameen yaki cewa komai Junaid ya d'an yi gyaran murya yana kallonta yace "Ina yini Hajiya" amsawa tayi ba tare da ta kallesu ba, Junaid ya d'an taba El-ameen alamar yyi magana mans, a hnkli El-Ameen ya matso kusa da shi murya can kasa yace "Me xan ce mata plss" ae Junaid bae san lkcn da ya fashe da dariya ba, El-Ameen ya tsaya kallonsa sai shi ma ya saka dariyar, nan suka dinga dariya kamar tababbu suka yi me isan su suka yi shiru, Junaid ya shafa kai yana kallonta yana murmushi yace "Ehm dama Ummi ce tace in rako El-Ameen wajen ki.... Shine muka xo" El-Ameen yace "Eh Ummi ce tace in xo gurin ki shine ya rako ni" kala bata ce masu ba, Junaid ya mike yace "Toh shknn mu xa mu koma sai mun sake dawowa" El-Ameen ma ya mike yace "Eh xa mu koma, sae wani lkcn, mun gode kwarai" mikewa tayi tace "Allah ya kiyaye" daga haka ta haura sama ta bar su tsaye parlon, dariya suka dinga yi cikin motar barin Junaid, El-ameen ya ja motar suka bar anguwar daga karshe, sae da El-ameen ya kai kansa gida sannan ya fita suka yi sallama Junaid ya koma driver seat ya ja motar ya bar layin, yana isa inda mahaukaciyar take yyi parkin yana kalle kallen inda xae ganta daga cikin motar, sae bae bae ganta ba ya ja motar ya nufi gida. Yana jiran masu gadi su bude masa gate kiran mum dinsa ya shigo wayarsa, jan motar yyi ya shiga compound din ya nufi parkin lot yyi parking snn ya fito, ganin motar Abba yasa shi kallon agogon wrist dinsa ya ga har goma ya kusa, bangaren mumy ya nufa, tsaye ya sameta palo tana rike da wayarta ta rungume hannu, yyi murmushi yace "Ga ni na dawo Mum," ta hade rai tace "Daga ina kake hka Ahmad?" Ya shafa kansa yace "na gaya maki Gidansu El-Ameen na tafi mum, na raka sa xance ne" yana murmushi ya k'are maganar, mumy tace "Zance! Lallai ba ayi abun arxiki ba kenan" dariya yyi lkci daya ya hade rai yace "Allah mum mun yi magana me ma'ana, infact ni ne ma nayi don shi shiru yyi wai kunya" Mumy tayi dariya tace "Au, kace ka kora masa budurwar knn in har kai kayi magana, tab!" Dariya shi ma yyi ya mata side hug yace "Kai Mumyna ni din ne ban iya magana ba" murmushi tayi tace "Kaje gun Abba yana neman ka" ya saketa yace "Ohk Mum" kofar da xae sada sa da part din dad dinsa ya nufa, xaune ya samesa babban falonsa yana kallon news lkci daya yana shan fruit salad din dake kan d'an table gabansa, Hajiya Fatee na xaune gefensa, sae step sisters dinsa su uku gaba daya suna palon, xaunawa yyi kasan lallausan rug din yana kallon Abbansa yace "Barka da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa daga ina kake naga baka duty ae" yace "Naje gidansu El-Ameen ne Abba," kallon Hajiya Fatee yyi yace "Ina yini Hajiya?" Tayi murmushin da bai kai ciki ba tace "Lfya lau, ya aikin" yace "Alhmdllh" Muhibbah ce ta shigo falon da sallama rike da bowl din kankana da akayi slicin, ta duka ta ajiye gefen Abba, xama tayi tana kallon junaid da ya maida hankalinsa kan Tv tace "Ina yini yaya" amsawa yyi ba tare da ya kalleta ba, Hajiya Fatee sae kallonsa ta gefen ido take, mikewa Junaid yyi yace "Sae da safe Abba" Abba yace "Yauwa ka ba Muhibbah dubu ashirin xa tayi amfani da su a makaranta gobe wae," yace "toh Abba" daga nn yyi ma Hajiya Fatee sae da safe, kanninsa ma suka yi masa sai da safe ya fice daga falon rai a bace, mikewa Muhibba tayi ta bi bayansa, bae tarda mumy a palo ba, hka yasa ya nufi bedroom