Showing 36001 words to 39000 words out of 56570 words

Chapter 13 - BAMAGUJIYA BY OUM HAIRAN.txt

sun fita ƙima, Habeeb Khausar tazomin jiya ta faɗamin irin rashin mutuncin da kayi mata wai harni zanyi maka zaɓi kace bakayi na'am dashi ba? To ka sani wlh muddin baka tsaya kun daidaita da Khausar kafin raina ya gama ɓaci idan ka kuskura ka kaini ƙarshe zanci mutumcinka da gaske...."








Kashe wayarsa yayi inda yabar Habeeb da dukan zuci ya cillar da wayar a cinyarsa ya furzar da wasu hawaye Masu ɗumi, hannunta yaji a fuskarsa tana share masa hawayen da baisan ya zubo ba.
Riƙe hannun nata yayi ta tashi zaune ta sanya hannunta ta tallafo fuskarsa ya lumshe idanunsa tayi ajiyar numfashi tace “Ban fahimci komai cikin maganganunka da Mai Martaba ba amma na fahimci mgnr daya faɗa maka itace Ummul aba'isin shigarka wannan doguwar damuwar Hero meye dalilinta da har tayi girman da zata sanyaka zubar da hawaye?"
Janye hannunta yayi daga kuncinsa yaja ajiyar zuciya yace “Inada babbar damuwa da take neman kumbura min zuciya Wyf na rasa waye zan tunkara yayimin maganinta duk dangin mahaifina sun juyamin baya sun kasa fahimtata wlh inajin tsoron su takura nayi biyayya wa auren Khausar kuma nazo a cikin zaman na kasa adalci idan hakan ta faru nine suka jefa a ruwa su suna gefe babu ruwansu cikinsu babu wanda Allah zai kama....."








Tunda ya fara mgnr idanunta ke kansa ƙirjinta yana harbawa da ƙarfi tace a “Ban fahimci komai ba Hero kayimin magana yanda zan gane"
Miƙewa yayi yanajan ajiyar zuciya yace “Meye kikeso ki gane Beebah? Karki damu da jin abinda zai ɗaga Miki hankali duk da cewa sun dage banji a raina hakan zai tabbata ba Allah bazai amince ba insha Allahu"
Ficewa yayi a ɗakin ya barta tsaye da zullumi a rai batada me warware mata sai shi, dole ta sanyata ta shiga bathroom tayi brush ta fito ta nufi ɗakin su Khalisa ta murɗa ta shiga da sallamarta suka ɗago suna binta da kallo a kasalce kuma a kunyace ta nemi guri ta zauna Hudah ta matso kusa da ita tace “Aunty Beebah bani lbrn darenku na jiya nasan dai an kashe arna ba kaɗan ba ko?"
Harara ta watsa mata tace “To ai kinfini kusa dashi sai kije ki tambayeshi shi saiya baki labarin duk abinda ya faru...." Rufe mata baki tayi tace “Rufamin asiri Ni yanzu na isa nayi wannan kasassaɓar waima don Allah ya akayi hakane nifa dama ko kinsan tun zuwanki gdannan zuciyata bata amince da cewar da Kilishi tayi kedin daga Daura kike ba domin na jima da samun labarin akwai wacce Bro yakeso ashe kece, Ni duk ba wannan ba meye daɗin da ake ji muma fa kinsan lkc ya kusa....."








Numfashi ta sauke tace “Wai da gaske ne bikin naku an sauko dashi saura sati biyar?" Khalisa ce tace “To ya zamuyi mijinki yaja mana Ni tashin hankalin da akace asabar ɗin nan za'a ɗaura auren nan da wata guda ayi bikin...." Da sauri ta ɗago tace “Kuma da gaske hardashi?"
Wata ajiyar zuciya Khalisa ta sauke tace “Shine ma dalilin sauko da auren Khausar na masifar son Bro shi kuma kamar wanda aka raba da ita baya ƙaunar ganinta ko sunanta baison yaji an ambata, wulaƙanci yakeyi mata na sosai har tayi zuciya tace ta hƙr da auren wannan tasa hankalin su Mai Martaba ya tashi har suka yanke wannan ɗayan hukuncin nikam Allah ya sani banson Najeeb baimin ba" Wani gwauron numfashi ta sauke ta miƙe zata fice wani jiri ya ɗebeta tayi baya zata faɗi ya tareta da sauri ta faɗa jikinsa a sume ya ɗago idanunsa sun kaɗa sunyi jawur yace “Meye ya sameta?"........






_Idan kika karanta min littafi baki biyani ba ban yafe Miki ba, idan ka/ki karantamin littafi a YouTube batare da izinina ba Allah ya fitarmin da haƙƙina a kanki/kanka da gaggawa_
[5/9, 8:49 PM] AM OUM HAIRAN: BMGJY 31-32




_Haramun ne a juyamin wannan labarin ta kowacce siga ko a karantamin shi a YouTube channel_




_Don ci gaba da karanta wannan littafin ki biya ta 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank, ko hoton kati MTN ta WhatsApp number 09013718241 idan a Niger kike zaki tura katin Airtel na 400CF ta wannan number +227 95 04 58 22 sai kiyi screenshot ki turomin nasaki a group._




★★★~~~★★★~~~★★★




Kallon kallo suka shiga yima juna kowa na jin tsoron sanar dashi asalin dalilin faduwar tata, tsawar daya daka musu ce tasa Khalisa saurin cewa “Bafa komai bane kawai kanta ne ke ciwo shine ta mike jiri y ɗebeta" ajiyar zuciya yayi ya miƙe da ita a jikinsa ya nufi ɗakinsu, ya ɓata lokaci wajen bata kulawa kafin daga bisani yaji taja ajiyar zuciya ya sauke numfashi tare da neman guri ya zauna yana me kallonta.
Ajiyar zuciya yaji tana saukewa yasa hannu ya ɗago fuskarta, hawaye yaga tana fitarwa yasa yatsansa yana share mata ya haɗa kalmominsa daƙyar yace “Meye kuma Wyf?" Bata ko kalleshi ba bare ta bashi amsa saima ƙoƙarin tashi da takeyi ya riƙota yace “Meye ne banason damuwa wlh Habeebah"
Hannunta tasa ta zame hannunsa tunaninsa ko bayi zata shiga maimakon haka sai yaga ta fice masa a ɗakin, nan ne zuciyarsa ta fara raya masa lallai da damuwa akwai abinda ya taɓa zuciyar Rayuwar tasa amma takaicin yanda ta watsar dashi yasashi kwanciya yasan dai itan bata da ɗabi'ar riƙe fushi.
A tunaninsa ya fita damuwa ya kamata daya rasa mafaka ya taho gareta ta danne ko mene yake damunta ta bashi lokaci da kulawar da zai samu nutsuwar da zata kwantar masa da hankali.








Da wannan tunanin yaji wayarsa tana ruri ya ɗagota ganin me kiran yasashi jan dogon tsaki a fili yace “Wannan halitta kwai mayya" a zahiri kuma ya kashe wayar saboda baisan wata kalma ɗaya da ta rage da Khausar zata sanar dashi da tayi saura a kwanciyar hankalinsa bayan tasa ƙafa tayi ƙoli da duk wani farin cikin da yake tanadawa rayuwarsa.
Kiran ɗaya kuma shigowa ne ya sashi gyara kwanciyarsa ya danna wayar ya ajiye ya sake jan bargo saboda sanyin zazzaɓin da damuwa ta saukar masa.
Cikin Murya me nuna alamun karaya da tsantsar damuwa Khausar tace “Prince Habeeb nasani a yanzu duk duniyar ka baka da wata matsala data wucce ni, nasani kanamin kallon wata halitta data addabi rayuwarka take neman zama katanga ga samuwar farin cikinka, A matsayina na damuwar da kakeji da kallon haɗa rayuwa da ita matsala ne a gareka ina mai baka hƙr bisa kasancewata a hakan, kayi sani bani na jarabci kaina da ƙaunarka ba kamar yanda Allah ya jarrabeka da son wani jinsi da kukasha bambam a addini da al'ada haka Nima ya jarabceni dakai, Habeeb nasan abubuwa da yawa da kake ɓoyewa a rayuwarka idan ka bani haɗin kai zanci gaba da rufa maka asiri harma na baka dama, barima kaji wani abu bayan aurenka da Habeebatullah da kayi ba tare da sanin kowa ba still a yanzu haka nasan tanada shigar cikinka na watannin da basu gaza biyu ba......"








Wata zabura yayi ya miƙe zaune yana shirin yin magana tace “Dakata Habeebullah banason kace komai kasan nasani cikin abinda na faɗa babu wanda nayi maka ƙarya saboda haka kabini a sannu kawai....."
Kashe wayarta tayi ya ajiye tasa cike da kidima ya miƙe cikin tashin hankali ya fara haɗa kayansa tabbas alama ta nuna masa akwai abinda ke faruwa yau dole ko ta wacce hanya su isa Nigeria.
Wayarsa ya ɗauka ya kira layin Beebah kiran sa yakai biyar taƙi ɗagawa ya canza layi ya kira na Hudah ta ɗaga ya basu umarnin shirya kayansu cikin gaggawa babu wanda ya tambayeshi kasancewar sunsan sarai raine zai ɓaci haka suka shiga rarrashin Beebah da har zuwa yanzun take kukan tausayin kanta daƙyar suka samu ta shirya suka zauna zaman jiransa, ya ɓata lkc kafin ya dawo suka fito suka shiga Mota suka nufi airport duk yanda Habeebah taso raba mazauni dashi ƙin amincewa yayi hakanan ranta baiso sukayi tafiyar nan har kuwa suka isa 9ja bayan bacci daya ɗauke ta ta kwanta a jikinsa babu wata kalma data shiga tsakaninsu.








Motar Gidan sarautar ce tazo ta ɗebe su a Kano abinda ya sake dukan zuciyar Beebah harda Khausar a zuwa tarar tasu, da gaske ranta suya yakeyi zuciyatta tafasa takeyi na yadda taga Khausar na shigewa mijinta har tana wani kama hannunsa shi kuma sai zuƙewa yakeyi yana harararta yana bin Beebah data lafe a jikin Kilishi da kallo.
Ko wajen shiga motar maƙalewa Kilishi tayi wannan takaicin yasashi baisan sanda ya dannawa Khausar ashar ba saboda takurawarta garesa yasan duk tanayin hakan ne don ta kuntata zuciyarsa data Beebah kuma tayi nasara saboda kallon da Beebah take binsa dashi kaɗai ya ishe shi hisabi.
Aikam duk nacinta bai bari sun shiga Mota daya ba haka ta ta shiga tasu Khalisa gwiwa a sage Hudah nayi mata dariya can ƙasan maƙoshi kasancewarta dama abokiyar dabinta ce duk da ta girme mata itan sa'ar Khalisa ce.
Iya jarabar nacinsa na son yasan halin da Beebah ke ciki abin ya faskara da yake Sallah ce gidan sarautar a cike yake da baƙi yasa bai takura ba haka ya hƙr ya shige sashinsa yayi wanka yayi Sallah ya miƙe a gado yana saƙawa da warwarewa, baiji shigowar Najeeb ba sai ji yayi an zauna kusa dashi ya buɗe idanunsa suka zubawa juna idanu na tsayin lkc can Najeeb ya kawar da shirun da cewa “Meyesa Khalisa bata sona ne?"








Yunƙurawa yayi ya tashi zaune yace “Dalilin da nake ta tambayar kaina kenan Najeeb kowa ya kasa ganewa bazan iya koyawa kaina soyayyar Khausar ba zatafi rayuwar farin ciki idan ta auri wani ba ni ba amma taƙi fahimta kowama yaƙi fahimta Najeeb zanyi wani abu da zai tada hankalin kowa domin da wata damuwar gara wata....."
“Zuciyarka tana faɗa maka ka saketa ne?" Da sauri ya ɗago yace “Ya akayi ka san abinda ke raina?" Fasali Najeeb yaja yace “nasanka tun bamusan kanmu ba nasan irin tunaninka a koda yaushe Prince kuskure ne babba zaka tafka da zai tone duk wani ɓoyayyen sirrinka, kayi saurin kawar da tunanin sakinta, tana sonka kai kuma kanason Habeebatullah zakayi amfani da soyayyar da take yi maka ka bawa Beebah guri a gidan da zaku rayu ka bata ƴancin mace itama, duk lkcn da tayi yunƙurin fitar da mgnr kai kuma kayi mata barazanar saki kuyita tafiya a haka har lkcn da gsky zatayi halinta don kasani na sani ramin ƙarya kurarre ne"








Sun jima suna tattaunawa kafin su miƙe su fice a gidan kai tsaye gidan Prince Habeeb suka nufa wato ya kashe dukiya bata wasa ba wajen tsara gidan cikin watanni bakwai akayishi aka gama rayuwa da buri komai don Habeebansa yayishi idan ya tuna wata akeso tazo ta rayu cikinsa ba Habeebah ba sai yaji ransa ya bakanta komai yana neman kwace masa amma da shawarar Najeeb yaji ya samu nutsuwa ya yarda da abinda ya faɗa masa a yau yakeson yayima Habeebansa albashir na samuwar ƴancinsu amma taƙi sauraronsa ya lura zasu rina da Habeebah domin dukkan alamu sun nuna irin matan nan ne masu masifar kishi bata ƙaunar taga an raɓeshi ko kaɗan to shima baso yake yaga wata mace ta raɓeshi ba itanba saidai yanzu da dole take neman kamasu.
Washegari tun safe yakeson ganinta taƙi ganuwa har ya gaji dayi mata aike da kiranta a waya, gashi Kilishi tanada baƙi a bangaren bakuma son yawan magana ya cika ba shine kawai ya hanashi zuwa ya nemota da kansa.
Har dare yana jiran tsammanin ganinta amma abu ya faskara dole ya hƙr ransa na suya haka aka kuma kwana aka yini tafi-tafi har kwana biyar ranar dai ya muttsike kunyarsa ya nufi sashin Kilishi yayi Sa'a kuwa duk sun tafi kallon hawan ƙarshe ya haura saman ya buɗe ɗakinta bai ganta ba ya janyo ya rufe ya buɗe ɗakin Kilishi ya ishe ta kwance a ƙasan carpet sai juyi takeyi riƙe da ciki Kilishi nayi mata sannu.
Tsayawa yayi ya zuba musu idanu ƙasa ƙasa, Kilishi ta ɗago ta kalleshi tace “Akai yarinyar nan asibiti Habeeb wannan fetus ɗin na wahalar da ita....." Ƙasa yayi da kansa cike da kunya yace “Kilishi fushi takeyi dani fah ko wayata ta daina ɗagawa rabona da sanyata a ido tun a airport"








Murmushi Kilishi tayi tace “meye kuma na damuwa akan abinda kariga kasan zai faru Ni tayimin kyan kai ma daya kasance kaiɗin take fushi dakai bani ba Habeebah tanada kawaici kuma kishi halal ne dole tayishi"
“Amma Kilishi....." “Amma me Habeeb ka ɗauko mota akaita asibiti nace ba dogon surutu ba" juyawa yayi ya fita bai jima ba ya dawo ya ɗauki Beebah da take cikin mawuyacin hali ya fice yasata a mota Kilishi ta fito ta shiga duk akan idon Hajiyan ƙofa tayi murmushi ta juya ciki su kuma suka fice daga gidan suka nufi Emirates Hospital ɗin aka bata gado suka fara bata kulawa.
Haka ta kwashe kwanaki biyu a asibitin anata shagalin ɗaurin auren ƴaƴan gdan sarautar itakam ta kanta kawai takeyi ranar da aka daura wannan aure Habeeb kamar mace haka ya rinƙa kukan baƙin ciki itako Khausar har kyautar mota tayi saboda farin ciki burinta ya cika ta samu muradin zuciyarta itakam Beebah baiwar Allah tanacan a kwance a gadon asibiti Kilishi da ƴaƴanta da uban gayyar na bata kulawa, ji yake kamar ya cire ciwon ya dawo dashi kansa duk ya susuce.
Duk da damuwar dake damun Najeeb ta watsin da Khalisa takeyi dashi amma yafi tausayin abokin nasa saboda yasan yafishi shiga jarabawar rayuwa wacce ya kwallawa rai gata a kwance cikin halin jinya ga kuma aure an ɗaura masa da halitta mafi bakin jini a duniyarsa.



_Idan kika karanta min littafi baki biyani ba ban yafe Miki ba, idan ka/ki karantamin littafi a YouTube batare da izinina ba Allah ya fitarmin da haƙƙina a kanki/kanka da gaggawa_
[5/10, 8:33 PM] AM OUM HAIRAN: _*Paid book 33-34*_




_Ku biya ta acct detail 3184512451 First bank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241._
_Normal 300 PC 700_




_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba_






★★★~~~★★★~~~★★★






Abu kamar wasa Saida Beebah tayi kwana goma sha uku a asibitin sannan ta samu ƙwarin da aka sallame ta, a zaman nan nata babu wani daga gidan sarautar da yazo dubata in ka ɗauke Hajiyan soro da tazo itama don ta fahimci kowa ma a gidan fushi Habeeb yakeyi dashi ne kuma ta fahimci da gaske ya damu da damuwar yarinyar fiye da yanda ya damu da kansa sannan zuwa lkcn anyi walƙiya a cikin gidan sarautar duk wanda ya isa yasan Habeebatullah matar Habeeb ce mai martaba ne har yanzu zancen baije masa ba yaketa sha da gwiɓa.
Wani abu da yaso ya ja masu samun saɓani da Kilishi lkcn da aka sallami Habeebah daga asibiti fir yace bazata koma Emirates House ba gdansa zata wucce domin kuwa baiga dalilin da zaisa Khausar ta tare a cikin gidan daya gina da sunan Beebah ita kuma taci gaba da zama a inda ba don ita aka tanadeshi ba.
Kilishi taƙi yarda shikuma ya kafe itakam data gaji hakanan ranta badon yaso ba ta raka Habeeba har Prince area inda gdan nasa yake ita kanta Beebah bata amince da wannan hukuncin ba saidai batada mafita tunda Kilishi ta amince haka zata hƙr shikam ransa har kunne zuciyarsa fari tas haka suka shiga gidan yana riƙe da hannun Beebah da gabaɗaya jikinta babu ƙwari.








Kilishi ce tayi sallama babu kowa a parlourn farkon sai ƙamshi da yaketa fitarwa na amarci Beebah ta lumshe idanunta ta sauke kan wani babban hotonta da sukayi kwanakin baya lkcn bikin naɗin Maje Dutse, neman gurin zama takeyi ya hanata ya ja hannunta ya buɗe wata ƙofa suka shiga parlour ne madaidaici da aka kashe masa manyan kudade wajen haɗashi sai wasu ƙofofi biyu dake facing juna a cikinsa.
Kilishi ya kalla yace “ya kikaga gurin Kilishi?" Ajiyar numfashi tayi ta zauna tace “gurin yayi kyau Habibu ina Khausar ɗin?" Nandanan fara'ar kan fuskarsa ta ɗauke ya bagarar da zancen da cewa “Da alama kinajin yunwa Wyf ki kwanta naje kitchen na dafo Miki Indomie" murmushi Hajiya Kilishi tayi ta miƙe tace “sai ayita hƙr da kai zuciya nesa zaman mata biyu Habeeb sai ansa lura saboda abokan adawar junane ko dariya babu wacce keso taga kayiwa wata fiye da wacce kayi mata, to nidai ina horon ka da adalci domin shine hanyar tsiranka"
Miƙewa tayi tayi musu sallama ta fice ya rakata ya dawo har yanzu baiji motsin Khausar ba bai wani damu ba ya shige kitchen ya fara dube-dube yayi Sa'a ya tarar da shinkafa da wake ga salat da cucumber da Bama an haɗa an yanka masa kwai gefe kuma ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login