Showing 54001 words to 56570 words out of 56570 words

Chapter 19 - BAMAGUJIYA BY OUM HAIRAN.txt

sunanta sai hawaye sharrrr a ijiyarsa itakam itama zamewa tayi ta zauna a ƙasa ta rungume Ayyana mikin ciwon dalilin nesantata dashi yana dawo mata sabo ta rushe da kuka me ciwo tare da rungume Ayyana ƙam a ƙirjinta.
Tausayin kansu yaji ya ƙara nunkuwa a zuciyarsa ya zauna yana share hawayen idanunsa yace “Bantaɓa....." Saurin ɗaga masa hannu tayi tace “Don Allah kada kacemin komai Habeeb basai ka sanar dani halin da zuciyarka ta shiga ba saboda yanayinka ya nuna hakan idan kace zaka sanar dani zaka cusamin tausayinka a lokacin da tausayin bazai mana amfani ba nasan kanasona ka rayu dani a ranka tsayin shekaru ka zaɓi rabuwa da manyan jigogin rayuwarka saboda ni so amma hakan ta gaza samuwa kayi ƙoƙari inada yaƙini bazan taɓa maye gurbinka ba....."








Yanda ya ambaci sunanta da ƙaraji yasata miƙewa yakai hannunsa zai karɓi Ayyana ta janye har zuwa lokacin idanunta hawaye yake zubarwa yace “Meye yasa zaki hanani ɗaukar jinina" girgiza kai tayi tace “Ba jininka bace" daga haka ta nufi hanya ta fice daga dakin da sauri tanaci gaba da kukanta me taɓa zuciya. Safeenah data rako baƙi ta tsaya da mamaki tace “Beebah...." Bata kulata ba ta shige daki ta faɗa gado ta rushe da kuka me sauti tana cewa “Na shiga uku Ni Habeebah ya akayi Habeeb yasan ina garin nan har ya biyoni maɓoyata?"
Safeenah ce tace “Waye shi?" Ɗagowa tayi a gajiye idanunta ya kaɗa yayi jajir tace “Shine wanda nake baki labari mijina a baya uban ƴaƴana, Maman Ahmad nasan mijina yana sona amma inajin kamar mun rabu kenan"
Girgiza mata kai Safeenah tayi tace “ ba zaku rabu ba zakuci gaba rayuwa fiye da baya me daɗi kuma kyakkyawa bari naje naga meye ke faruwa Beebah har abada Habeeb naki ne"








Ficewa tayi daga ɗakin ta nufi ɗakin baƙin ta zubawa Habeeb idanu babu ko tantama ga kama nan a fuskar Ayyana.
Miƙewa sukayi dukkansu Dr Amin da jikinsa ya jima da yin sanyi tausayin Habeeb ya cika zuciyarsa tabbas Habeebah ta cancanci soyayya a gurinsa shima ya cancanci ta soshi ashe shiyasa kullum take cikin damuwa, hawayen Habeeb ya share yace “Insha Allahu zaka rayu da matarka da yaranka wannan abu duka ya faru ne a cikin gaibu sama da watanni biyar Beebah take gdana take zaune da iyali na nasani Tanaji da ganin mutumcin Safeenah ita kaɗai ce zatayi maka aikin rarrashin zuciyarta nasan zata sauko"
Kallon Safeenah yayi yace “Mijinta ne kije ki ɗauki masa ƴarsa ya ganta ashe Ummusalma ɗin da ta zaɓawa yarinyar sunan surukarta ne" fita Safeenah tayi ta dauko Ayyana ta dawo ta miƙawa Habeeb ya rinƙa zuba musu hoto shida yarinyar don a yau yakeson zuwa ya dauko Kilishi tazo taga takwararta tunda yasani yanzun ko giyar wake yasha bazaice zai ɗauki Beebah yakaiwa Kilishi ba duk da alamu sun nuna cikin waɗanda ta riƙe a ranta babu Kilishi.








Kuɗi ya zara masu nauyi ya bawa Safeenah yace a bawa Beebah kafin yawo sukayi sallama suka tafi zuciyar Habeeb wasai yau yaga abar ƙaunarsa, suna zuwa gidansa ya haɗa kayansa yace da Wali yakaishi airport yau ɗin nan Dutse zai kwana.
Bakwai ya shiga gdansu ya tarar da kowa a babban parlourn ciki harda Khausar tana durƙushe gaban Sarki Khalil tana kuka.
Bai sauraresu ba ya wuce zuwa ɓangaren mahaifiyarsa tana ganinsa tace “Ya kiraka kenan?" Dubanta yayi da rashin fahimta yace “Wa ba?" Kawar da zancen tayi tace “Ina labarin ƴata da jikata" fara'arsa ya faɗaɗa yace “yau naga Zuciyata taganni saidai taƙi aminta dani Kilishi Kinga shaida" nan ya fara nuna mata hotunan ta rungumeshi tana dariya tace “Alhmdllh Ya sunan Bbyn?" Shafa kansa yayi yace “yau da yamma yayan abokina Engineer Wali wato Dr Amin ya kiramu ana suna a gidansa ƙanwar matarsa ta haihu muka tafi domin tayasu murna shine ya kira matarsa domin ta kawo mana Bbyn abin mamaki sai ga Wyf ɗauke da wannan kyakkyawar yarinyar tana ganina ta kira sunana na mike, amma fah Kilishi Wyf ta sanar dasu Ni mijinta ne a baya banda yanzu inda Ni kuma nayi musu bayanin komai yanzu dai sun bani hƙr sunce zasu tausheta"
[5/25, 3:12 PM] AM OUM HAIRAN: _*BMGJY Bonus 51-52*_




_Ku biya ta acct detail 3184512451 First bank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241._
_Normal 300 PC 700_
_Ƴan Niger zaku biya 500f ta wannan number +227 95 04 58 22_




_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba._




_End! End!! End!!!_






Tunda Habeeb yabar garin Abuja yabar Safeenah da Dr Amin da rikicin Beebah don gabaɗaya ta rikice musu cikin kwanakin batada wata walwala indai kaga tana dariya to ba'a sako mata zancen Habeeb bane da zarar anyi mata zancen shi zata haɗe rai ta fara kumbura ga Safeenah da nacin magana ta rinƙa nuna mata damuwarta da lamarin Habeeb kenan har sai taga ta ƙosa tana shirin tashi tabar gurin sannan zata ƙyaleta.
Abin da yake bawa Safeenah mamaki bai wucce yanda tasha kama Beebah tana kuka ko kuma cikin bacci taji tana ambaton sunan Habeeb ɗin ba amma kuma a zahiri idan akayi mata batunsa sai walwalarta ta ɗauke, to yauma kamar ko yaushe tana zaune a ɗaki ta gama yima Ayyana kwalliya tana taje mata gashinta taji Muryar Safeenah na cewa.
“Ashe bakine damu a gidan sannunku da zuwa" duk da batasan su waye ba Saida gabanta ya faɗi haka tadai maze taci gaba da yiwa ƴarta wasa a haka Safeenah ta shigo ta sameta fuskarta wasai alamun farin ciki tace “Kizo kinada manyan baƙi a parlourn baƙi" bata jirayi abinda zata ce ba duk da taga alamar cewar a tattare da ita ta juya ta fice bayan ta karɓe Ayyana a hannunta, jiki babu ƙwari haka ta miƙe ta ɗauki mayafinta ta yafa ta fice daga dakin ta nufi ɗakin baƙin gabanta naci gaba da faɗuwa.








Tura ƙofar tayi ta shiga tare da sallama idanunta ya sauka kan Jumme dake zaune gefenta mahaifinta ne riƙe da Hudais sai Kilishi dake dauke da Ayyana, tsayawa tayi turus tanajin wani faduwar gaba na shigarta tare da bin iyayen nata da kallo ɗaya bayan ɗaya.
Riƙo hannunta akayi ta juya ta dubi wanda ya riƙe hannun nata ganin Habeeb ne ya ɗaganta gira tare da janta har zuwa inda mahaifan nata ke zaune tana isa ta zube a gabansu da sauri jikinta na rawa tana wani irin kuka ya ƙwace mata data kasa sanin na meye farin ciki ko nadama? Tabbas tayi farin cikin ganin iyayen nata sun taso takanas dominta, sannan nadamarta ta tsayin watanni ta dawo mata sabuwa tabbas da tabi umarnin Mahaifanta ta nuna jajircewarta da bata fuskanci wani wulaƙancin ba tasani yan ɗakin da mijinta yafito da mahaifiyarsa sun sota sun kaunaceta da kaunar da mijinta yake yi mata, duk da tasan cewa bata isa kaucewa kaddararta ba tunda Allah ya ƙadarta Habeeb shine uban ƴaƴanta to ko bataso sai ya zama mijinta amma tayi wasarairai da ƙimarsu.....
Cikin kukan me taɓa zuciya ta buɗe baki tace “Jumme Baba nasani na cusa baƙin ciki da damuwa a zuciyarku duk da cewar kunyi ɗawainiya dani tundaga samuwata har zuwa girma na, a lokacin da zan nuna muku tabbas kuɗin iyaye ne na kwarai duk da rashin hasken musulunci a cikin rayuwarku baisa kunyi wasarairai da tarbiyya ta ba, kawai sai ƙaddara ta jefomin shi cikin rayuwa ta har naji a raina gara na barku dana barshi, inason Habeeb nasani shima yayi domin Ni yayimin halaccin da maza masu irinsa sunyi ƙaranci a duniya saboda Ni ya amince ya rasa komai daya mallaka ta bangaren mahaifinsa ƙarshe kuskuren mu mu biyu ya haifar min da damuwar da har na mutu bazata goge ba, ko sanda bana cikin musulunci ban kaunaci zina ba na ƙyamace ta na tsaneta har kawo lokacin da Habeeb ya zama mijina, kwatsam waini Habeebah saboda son zuciyar kishiyata kishiyar surukata da iyayen kishiyata yasa sukayi amfani da ƙiyayyar da mahaifin mijina yakemin aka barratani da mijina a lokacin da nake buƙatarsa aka rabani da ɗana da nake kallonsa a matsayin gata na..."








Kukanne yaci ƙarfinta daƙyar ta buɗe bakinta tace “nasani haƙƙinku ne wlh badon banason Habeeb ba amma na zaɓi yi muku biyayya wannan karon matuƙar zaku yafemin kuskurena na baya da rudin ƙuruciya yasani aikatawa kuyimin afuwa ku yafemin don...."
Rufe mata baki Jimo yayi yana murmushi yace “Kayyah Bibon Baba wannan ai ya zama shuɗaɗen labari ƙaddararki ce kamar yanda Liman ya fada mana ina zamukai rabon Waɗannan yaran Habeebah dakin matsa ma wajen yimin biyayya da tuni ba labarina akeyi ba kila da tuni ƙasa ta jima da rufe idanuna kece da hƙr Bibo da ban hau dokin zuciya ba da baki wulakanta ba kuma da da haka ta faru mu zaki nufo mu share Miki hawayenki nikam na yafe Miki tun ranar da hasken musulunci ya ratsa Zuciyata Habeebatullah kije ki rayu da mijinki da yaranki cikin aminci kuma na tabbatar kafin Ni mahaifiyarki ta jima da yafe miki"








Kwantar da kanta tayi saman cinyar mahaifinta taci gaba da rera kukanta na farin ciki tana gdy ga Allah da ya ƙadarta mata ganin wannan rana itakam da basu yafe mata ba da batasan ya zatayi da rayuwarta ba.
Ji tayi an kama gashinta anja ta ɗago tare dayin murmushi ashe Hudais ne ta miƙa masa hannu ya taho jikinta ya kwanta luf yana sauke ajiyar zuciya ta dubi Kilishi tace “Kilishi dama a gurinki yake ba a matar babansa ba?"
Murmushi Kilishi tayi tace “babanshi ai bashida mata tun washegarin ranar da kika bar gidan itama ta bari gara kema kullum muna hasashen dawowarki itakam ta tafi kenan yanzu haka ma tayi aure shekaran jiya ta tare a gidanta" ajiyar zuciya ta sauke dama tasan auren Khausar da Habeeb wataran dole zai ƙare don da gaske Habeeb yake Khausar bata tsarinsa amma bataso ace itane sanadi ba.








Ranar yini akayi ana hirar yaushe gamo iyayenta kamar su mayar da ita ciki Safeenah sai hidima takeyi da baƙi tsakanin Beebah da Habeeb kuwa Saidai kallo kawai Allah yasani tasan baiyi mata komai ba amma ta ƙudurce a ranta matukar ba Mai Martaba ne ya amincewa zamansu matsayin ma'aurata ba to ta hkr dashi itakam ta daidaita da nata iyayen shima tanaso taga ya samu daidaito da mahaifinsa a washegari suka ɗauki hanyar Dutse harda Beebah tunda suka taho gabanta ke faduwa bata fatan ace su sauka a gidan sarauta saboda komai zai dawo mata sabone.
Ga mamakinta sai taga sun nufi wata babbar unguwa ta manyan attajirai an buɗe musu wani get sun shiga yayi parking suka fito shine yayi musu jagora har cikin gidan yana nuna musu ko ina Saida ya gama nune nunensa sannan ya juyo ya dubi Habeebah yace “gidanki ne da zaki rinƙa sauka idan kinzo hutu daga London saboda ina tunanin nan da 2 weeks zamu tafi" Saida taji wani dam a ƙirjinta tayi masa wani mugun kallo sannan ta kawar dakai anan sukaci sukasha kukunsa ya shirya musu komai Saida suka gama sannan ya ɗebesu suka nufi tsohuwar unguwar su shima tsohon gidan cikin watanni biyar zuwa shidan ya gyara shi sosai ya sake masa kayan cikinsa Saida suka gama dubawa sannan ya dubeta yace.








“Wannan kuma nakine halak malak Habeebah bansan dame zan saka miki soyayyarki gareni ba sannan bansan dame zan goge Miki tabon mikin da akayi Miki a duniya kawai saboda a rabani dake ba wlh tallahi Habeebah tun kafin bayyanar gaskiya Ni nasan bazaki taɓa aikata abinda akace kin aikata ba kuma Kilishi ma da su Hudah sun shaideki akan hakan, mun riga mun yanke hukunci Baba da Jumme zasu zauna cikin wannan gidan saboda wata hatsaniya da tasa suka baro garin Tsaunin gawo dalilin karɓar addinin Musulunci da sukayi"
Tunda ya fara maganar take kallonsa idanunta na zubar da hawaye tana girgiza masa kai har Saida ya gama sannan tace.
“Bana bukatar komai daga gareka Habeeb Ni burina naga kun daidaita tsakaninka da mahaifinka yaci gaba da sonka da janka a jikinsa kamar yanda yake yi a baya burina ya karɓeni matsayin suruka nasani inasonka saidai so bazai rufe mana idanu a karo na biyu mu kara yin abinda zamu zo yaci gaba da bibiyarmu har jikokin mu ba, nasan kafini sanin girman haƙƙin mahaifa akan ƴaƴansu...."








Tunda ta fara maganar yake kallonta har ta gama yayi murmushi yace “hakane kema kince wani abu saidai ki sani Mai Martaba jikinsa yayi sanyi tun lokacin da naje na nuna masa hotunan Ummi na na sanar dashi kin haifa min ƴa mace a ranar yake cemin naje na dawo dake ɗakinki komai ya wucce a manta da duk wani abu daya faru dama shi tunda abin ya faru yake tuntuntuni akan abin sai gashi yaron da kansa yazo ya ƙaryata kansa batare da wani ya takurasa ba yace sashi akayi yazo a daidai lokacin aka shirya plan na yanda za'a gayyato Mai martaba yazo ya kamaki da kansa,
Idan baki gasƙata abinda na faɗa Miki ba yanzun mu wucce gidan sarautar kiji da kunnenki....."










“Basai kunzo ba Ni nazo" sukaji an faɗa a bayansu juyawar da zasuyi sukaga Mai Martaba tsaye da dogarawansa jikin ƙofa ya tako fuskarsa dauke da murmushi har gaban Beebah ya riƙo hannunta yace “So da yawan lokaci munayin hasashe baibai da daidai mukan hasaso abinda yake saɓanin gsky sai zukatanmu su tafi akansu har su rinƙa tursasamu akan cewa wannan abin shine daidai, na hasashi kuskure na tafi akansa nayi jayayya da abinda ubangiji ya hukunta karshe nayi zaɓi sabanin na ubangiji na takura masa Saida ya karɓa bisa shawarwarin Ƙanina Lukman da Hajiyan ƙofa ashe duk a keken ɓera suka ɗora ni yanzu gashi Ni da idanuna yayanku Ahmad ya ɗaukeni ya kaini wani hotel na kama Khausar da hannu na da maza tana shaye-shaye turr da wannan asara da taɓewa Habeebah duk da an daɗe ana faɗamin Khausar ba sa'ar auren Habeeb bace bantaɓa yarda ba sai ranar kuma abin mamaki harda yaron da akace kece kika gayyato shi don buƙatar kanki saboda Kinga mijinku bayanan daganan na tabbatar duk wani abu daya faru makirci ne akayi amfani dani don shiga tsakaninki da mijinki Habeebah kiyi hƙr ki rayu a gdanki tare da ƴaƴanku kamar yanda nakewa kowacce ƴa dana haifa fata"








Sosai Habeeb yaji daɗin yanda mai martaba ya wankesa ya sani ba don Allah ya kawosa yayi bayani dakansa ba da babu kalmar da zai yi amfani da ita wajen fahimtar da Beebah,
Shida mai martaba da Kilishi ne suka tafi inda suka bar Beebah da iyayenta sunata mamakin karamcin surukanta sunata hirarsu ta yaushe gamo nan suke faɗa mata mutuwar Baba Uda taji mutuwarsa sosai har hawaye tayi.
Rayuwarta me takeyi ita da iyayenta saboda Kilishi ta hanata komawa gdansa tace ta bari tayi arba'in ransa baiso ba hakanan ya hkr ya haɗa nasa ya nasa ya wucce London.
Yanda Habeeb ya mayar da hankalinsa wajen kula da iyalinsa abin ba'a cewa komai bayan tayi arba'in ya harhaɗa masu nasu ya nasu suka ɗauki hanyar birnin London daga wannan lokaci komai ya wucce rayuwa ta saitu kamar babu wani abu daya taɓa faruwa komansa Beebah komai ya tashi yi da ita yake shawara, ga yaransu dagwai dagwai gwanin ban sha'awa Saida Ayyana ta shekara Biyar sannan Beebah ta sake haihuwar yaronta namiji yaci Sunan Mahaifin Beebah wato Muhammad kasancewar bayan musuluntarsa cewa yayi akirasa da Muhammad.








_Tammat bih hamdullah_








_Wannan littafi Mai farin jini nan na kawo karshensa kuskuren dake ciki Allah ka yafe mana ba don halinmu ba Allah ka bamu ikon amfana da abubuwan amfanin cikinsu._

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login