Showing 18001 words to 21000 words out of 56570 words
duniya keɗin ƴar aiki ce da muka ɗaukoki domin wasu aikace-aikace nawa Ni kaina bazan jingina ki da mijinki ba domin kusancinku idan yayi yawa zaisa kokwanto a zukata saboda haka ki zauna da nutsuwa watarana komai zai wucce"
Tunda Kilishi ta fara mgnr idanun Beebah ke zubar da hawaye data rasa na Meye ne, Hajiya Kilishi irin matan nan ne da basa ƙaunar ganin wani na ƙasansu cikin damuwa hakan yasata dafa kanta tace “ko hukuncin dana yanke dan gujewa faɗawarki cikin takura da tsangwamar gdannan baiyi Miki bane Habeebah?"
Saurin girgiza kai tayi tace “badon shi bane inayin kuka ne saboda rashin sanin halin da Jumme take ciki...." Kilishi kallon Habeeb tayi ya shafa kansa ya juya ya fice daga ɗakin tasan halinsa da miskilanci amsar bawa matar tasa ya rasa shine yasashi ficewa haka ta kirkiro murmushi tace “inaji a raina kowa yana cikin amincin Allah Haby ki saki jikinki a gdannan kada ki tsangwami kanki hakan zai sama maki kusanci da jama'ar cikinsa wanda kusancinki dasu shine matakin nasarar aikin dake gabanmu"
Nuna mata komai ta rinƙayi tace “Wannan ɗakin wata hadima ta ce Sakina da Allah yayiwa rasuwa zakigansa kusa da ɗakina itan amintacciya ce gareni tana kula da dukkan lamuran da suka jiɓanceni shiyasa ban yarda tayi nesa dani, can kuma ɗakunan ƙannenki ne Huda da Khalisa yanzu suka fita sunje makaranta" jinjina kai tayi Hajiya Kilishi ta juya tace “zanje ƙasa zan Turo a kawo Miki abinci kici sosai kafin zuwa anjima na gabatar dake a gurin mutanen gidan"
Fitar Kilishi ya bata damar ƙarewa ɗakin kallo tana ayyana abubuwa da yawa a ranta bayan mamaki itakam harda tsoro ace wannan ɗakin a ciki zata rinƙa kwana ita kaɗai tasaba gdansu ita da Jumme da Jimo suke kwana ɗaki daya tunda Tani ta mutu.
Da wannan tunanin taji an buɗe ƙofar ta dago kanta wata mata ce tazo ta ajiye mata kayan abinci ta zuba mata shinkafa ce da miya miyar taji kifi banda sai farfesun naman zabo a gefe sai lemo kala² sai sinasir da yaji miya duk ta zuba mata itadai batace komai ba har ta gama ta ɗago tace “Yarima Habeebu yace na tabbatar kinci abinci sannan ya damƙa amanarki a hannuna duk abinda ya dace zanke nuna Miki"
Gdy tayi cikin ladabi Larai ta miƙa mata abincin da takurawarta taci shinkafar sosai tana yabawa da daɗinta tunda take bata taɓa cin abinci mai daɗin wannan ba haka ta yagi naman zabin ta ture Larai na kallonta tana mamakin zubin sirrin ɓoyayyen jyawun yarinyar zallar ƙuruciyar ta bayyana akan fuska da jikinta babban abinda yafi ɗaukar hankalin Larai wata suma lufluf kwance a jikinta me ban sha'awa, hakanan Larai taji yarinyar ta shiga ranta fiye da yanda tayi tunani.
Haɗe kayan Larai tayi ta fara ɗebewa Habeeba babu ƙyuya itama ta fara diban kayan suna fita dashi sai gashi cikin yinin sun samu wata shaƙuwa da Beebah da Larai kamar dama sunsan juna hakan yayima Kilishi daɗi sosai duk da ta lura Beebah irin yaran nan ne masu kunya taƙi sakin jiki da ita sannan bata bari ko idanu su haɗa ko magana takeyi da taganta zatayi shiru ta fara ƙasa dakai.
Sai dare Khalisa da Hudah suka dawo suka ishe Beebah dake sunada son mutane kuma Kilishi ta faɗa musu zatayi baƙuwa batason raini batason kyara ko tsangwama tsakaninsu itama matsayine da ita a gurinta kamar su shine yasasu janta a jika tsakanin yammar da daren sai gashi sunyi wata shaƙuwa ta ban mamaki da ƙannen mijin nata.
Sune suka rinƙa janta lungu da sako na gidan suna zagawa da ita sune har gaban Mai martaba suka kaita matsayin baƙuwa da tazo daga Daura dangin Kilishi kenan aikuwa ya jima yana kallon yarinyar nutsuwarta ta burge shi da kuma yanda ta saki jiki da komai na gidan.
Abu ɗaya ne ya basu mamaki idan suka tashi zasuyi sallah saidai suga tanata kallonsu har suyi su gama su dawo suci gaba da harkokinsu sai gashi da akazo kwanciya rigima ta sarke Kilishi tace taje ɗakinta ta kwanta su kuma sunce saidai su kwana ɗaki daya da ita, kan dole Kilishi ta barsu saboda ta lura itama tafi son shiga cikinsu.
Kwanciyar ma Saida akayi rigima wannan tana cewa a gadonta zata kwana wannan tana a gadonta zata kwana itadai kallonsu kawai takeyi ƙarshe ma tayi shimfida a ƙasa tace ita tafijin daɗin kwanciya a ƙasa.
Kwanciyarta tayi a ƙasa Saida Kilishi ta lekosu taganta a ƙasa ta kuwa rufesu da faɗa dole ta koma gadon Hudah ta kwanta baccinta na yau dabanne dana koyaushe daɗinsa ma dabanne donma sanyin A C ya hanata sakat saijan bargo takeyi tana kudunduna.
Haka sukaci gaba da rayuwa sati guda ta wucce sukaga bata sallah saidai tayita kallonsu hakan yasasu tambayarta Meye yasa bata sallah ta dubesu tace bata san ya akeyi ba sun cika da mamaki nan Khalisa taje ta fadawa Kilishi Kilishi tasa aka kirata da hikima da komai suka rinƙa cusa mata son addinin Musulunci cikin satin biyun kafin yabar ƙasar Saida ta karbi kalmar shahada yayi murna sosai duk da ba shiga harkar su yakeyi ba ko Itan baya sauraro saboda gudun tonuwar asirinsa hakanan yake daurewa saidai kawai duk inda yagansu zaune yakan yawaita zagaya gurin wani lkcn har idanu suke haɗawa ya kawar dakai itama sai ta koyi shareshi duk da a farko abin yayi mata bambarakwai amma dataji yanda ƴan uwansa suke tsoronsa kuma suke fadin miskilancinsa sai tasawa zuciyarta dangana ta mayar da hankalinta wajen ɗaukar darasinta gurin Kilishi data ware mata makaranta islamiyya take koyar da ita duk wani abu daya kamata ta sani a matsayinta Na baliga.
Ana gobe zai tafi da dare wajen takwas da rabi dukkan yaran gidan suna babban falon suna kallo ita kam ba ma'abociyar kallo bace tana kwance a dakinsu dake tayi kaura daga nata ɗakin bata kwana a ciki saidai yini ko daukar kaya ke kaita Larai ta shigo tace “Beebah kije inji Yarima yana ɗakinki" wani ras taji gabanta ya faɗi saboda cikin kwana biyun hakanan taji itama tana tsoronsa kamar yanda ƙannensa da sauran hadiman gidan suke tsoronsa.
Juyawa Larai tayi zata fice Beebah ta miƙe tabi bayanta ta jima tsaye bakin ƙofar ɗakin kafin tayi ƙarfin halin buɗewa yana tsaye a tsakiyar ɗakin goye da hannunsa a bayansa ta tsaya jikin ƙofar ya juyo ya zubanta idanu tayi ƙasa da kanta ya tako ya tsaya a gabanta tayi ƙasa zata durƙushe ya riƙota tayi baya kamar zata fadi yasa hannunsa ɗaya ya tallafi bayanta ya dago fuskarta ya zuba idanunsa a kanta tayi saurin lumshe nata yaja numfashi ya haɗata da jikinsa yana sauke ajiyar zuciya ya ɗora lips nasa a wuyanta ya sauke mata kisa me kashe jiki hakan yasata jan fasali itama tana ƙoƙarin janyawa yajata zuwa gefen gadon ya zaunar da ita yana saita nutsuwarsa ya sauke numfashi me ƙarfi yace “Habeebah!"
Yanda ya kirata da karsashi yasata saurin buɗe idanunta suka shiga cikin nasa yayi mata murmushi tare da lakace mata kumatu yace “ke yarinya ce ƙarama me ƙarancin lissafi wato dana kawoki nan Ni na gama amfani a gurinki kin manta da wayeni a gurinki kawai harkar gabanki kikeyi babu ruwan ki da mijinki ko?"
Sunkuyar da kanta tayi tace “To ba kaina ba sai ka rinƙa hahhaɗemin fuska nikuma tsoronka nakeji" zubanta idanu yayi yanda take sarrafa harshenta wajen furucin ya bashi nishadi yaja numfashi yace “Ok yanzu na sake Miki me zaki bani gobe zan tafi...."
Da sauri ta ɗago tace “Gobe?" Jinjina mata kai yayi yace “Banason tafiyar nan kawai babu yanda zanyi ne ta kamani dole Beebah kinsan dai matsayin da kike kai yanzu, ke ba daidai kike dasu Hudah da Khalisa ba bare Amna da Khaulat ke matar aure ce kada rashin ganina yasa kiyimin wasa da igiyar aurena dake hannunki Beebah amanar kanki na hannunki shekara ɗaya tanada tsayi amma kamar yau ne insha Allahu zan dawo ina fatan kafin dawowata komai ya daidaita mu fara rayuwar ƴanci kamar kowanne ma'aurata"
Jikinta ya mutu ta kasa cewa masa komai Saida tajita kwance flat a gadon yayi mata rumfa gabanta yabada wata irin muguwar faɗuwa data sanyata rintse idonta da ƙarfi zuciyarta nabada wani sauti dam² musamman lkcn da taji dumin lips ɗinsa a saman bakinta, wannan yanayi ya sanyata tsumar jiki data zuci wacce ta sabbaba mata neman sume masa lkcn da ya ɗora hannunsa a ƙirjinta ya zurasu cikin rigarta ya zuge zip ɗin ya fito da dukiyar fulaninta ya damƙe a hannunsa.
Azabar da taji da kuma firgicin data shiga yasata sakin ƙarar da yayi saurin toshe mata baki da hannunsa ya sanya lips ɗinsa ya kama nipples ɗinta da bakinsa....
Tuni firgicinta ya sake bayyana ta shiɗe masa tare da ƙanƙameshi numfashinta na shirin ɗauke wa hakan ya sanyashi saurin sake mata boobs ɗinta ya miƙe a kasalce ya zubanta idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur, ga mamakinsa sai yaga ashe bama ta numfashi wani yawu ya haɗiye yana ƙoƙarin saita nutsuwarsa ya buɗe freezer ya dauko ruwa me sanye ya ɓalle murfin bottle ɗin ya tsiyaya a hannunsa ya shafa mata a fuskarta, babu jimawa taja ajiyar zuciya ta fara shure² tana kai masa duka yayi saurin riƙe hannunta yace “Ya isa matsoraciyar matata na hƙr akwai lkc".........
*Sanarwa*
Daga wannan paging na gama free indai kin ganshi a waje to na haramun ne sannan promo ɗina ya ƙare daga yau on 15 12:00am indai yakai gobe to saidai ki/ka biya 300 ɗinka PC Kuma 700.
*share please*
[4/17, 10:22 AM] AM OUM HAIRAN: BMGJY
KIYIWA GIRMAN ALLAH KI BIYANI HAƘƘINA KAFIN KI KARANTA NORMAL 300 PC 600, KI BIYA TA WANNAN HANYOYIN ACCT DETAILS 0255526235 FAUZIYYA TASIU GTBANK KO KATIN WAYA MTN TA WHATSAPP NUMBER NA 09013718242 ƳAN NIGER ZAKU TURA KATIN AIRTEL 400CF TA WANNAN NUMBER +227 95 04 58 22 SAIKU TUROMIN SCREENSHOT NA SHAIDAR KUN TURA MATA NIKUMA NASAKU A GROUP.
*15-16*
★★★~~~★★★~~~★★★
Yana faɗin haka ya saki hannunta ya miƙe yana cewa “ki kula da kanki" ajiyar zuciya ta sauke tabisa da kallo hakanan zuciyarta tayi mata babu daɗi ta tsinci kanta da kewarsa da tunanin makomarta idan bayanan da wannan ta koma ta kwanta a gadon zuciyarta nayi mata babu daɗi hawaye na bin gefen idanunta tana sharewa taji an buɗe ƙofar an shigo bata ɗago ba Khalisa ta zauna a gefenta tace “Beebah faɗa wannan masifaffen yayi Miki ko?" Numfashi ta sauke ta tashi zaune tana gyara rigarta tace “Wa kenan?" Tana binta da kallo tace “Bro mana naga ya fita a dakin nan yanzun kuma nasan idan ba masifarsa ce ta ciyoshi ba baya shiga ɗakin mu bare kuma naki" ƙasa tayi da kanta tace “to Meye laifi Inma faɗan yayimin ai ya isane bakiji abinda manya suke cewa ba “yaro yi kuka in ka rasa me maka faɗa” saboda haka Ni daɗi ma naji da yasan da zamana har yaji a ransa na cancanci yayimin tsawa akan rayuwata"
Jinjina kai Khalisa tayi tace “hakane Allah yasa mu dace amma nikam haushi nakeji idan anamin faɗa saboda wani abin ma bai kai laifi ba yanzu ranar nan da akasa babban Yaya ya zane Amna da Khaulat laifin baifa kai ba wai kawai don sunyi video sun ɗora a TikTok shine akayi kamar za'a kashesu wlh yaran Saida suka bani tausayi"
Sauya akalar mgnr tayi da cewa “yaushe zaki fara yimin lesson na turancin" don batamasan Meye TikTok ɗin ba.
Murmushi Khaly tayi tace “toni yanzu Beebah ta ina zan fara a koya Miki turanci Ni abinda naga yafi kuma zan shawarci Kilishi a nema Miki makaranta ki shiga sai a rinƙa yi Miki lesson a gda tunda da alama ƙwanyarki tana ja zaki gane komai a hankali" kallonta tayi tace “Khaly nayi fah karatu a ƙauyenmu nida Yaya Tani ne kawai mukayi makarantar primary da secondary aji uku daga wasu ƙauyukan ma idan aka rubuto sako aka aiko kiranmu akeyi mu karanta mutuwar yaya Tani ne tasa aka dakatar da karatuna" daɗi ne ya cika Khaly tace “kay alhmdllh amma naji daɗi yanzu muje gurin Kilishi ai ba wani girma kikayi ba kawai a sama Miki Form ki juya senior secondary inyaso ma a saki a tamu tunda muma bamu gama ba sauranmu 1 years tashi muje hakama za'ayi"
Hakan kuwa akayi suna zuwa suka sanarwa Kilishi tayi murna da hakan tace “Zan kira Mas'ud zaiyi mata Screening indai takai za asan yanda za'ayi" Beebah tayi gdy sukaje suka kwanta sunata murna tama manta da lissafin tafiyar Habeeb.
Washegari kuma da safe Hajiya Kilishi tasa aka ɗebe su a mota aka kaisu gyaran gashi wannan tasa basuyi sallama ba hakan baiyi masa daɗi ba yaso yaganta suyi sallama amma hakan ya faskara da zai tafi ne ya shiga ɗakinta ya ajiye mata wani tsadadden card a gefen kayanta sai wani ƙaramin akwatu da ATM card da wasu takardu.
Sai yamma liƙis suka dawo sun kuwa yi muguwar gajiya suka zube a parlourn suna mayar da numfashi kowacce ta jefar da mayafin itakam Beebah kwanciya tayi saboda sosai tafi kowa gajiya Gara su sun saba da komai da akayi musu ita kuwa komai sabo ne a gurinta hakance tasa jikinta ya gaji zuciyarta ta gaji brain nata shima ya gaji ta baje a parlourn tana juyi gashin nan yasha gyara sai kyalli yake abin ba'a cewa komai gashi an gyara musu farcensu harda jan lalle ya zauna das a fatarta tayi wani sihirtaccen kyau na ban mamaki Kilishi da kanta satar kallon surukar tata takeyi duk da yammatan nata ma ba baya ba amma sun samu uwarsu a fannin kyau hasken fata kawai zasu faɗa mata sai murjewa itama kuma fatar tata me karɓar sauyi ce cikin sati biyun har wani glowing takeyi.
Gyaran murya Kilishi tayi tace “nayi magana da Dr Mas'ud da dare zai zo Habeebah ki zama ready" cikin ɗoki tace “Ok Hajiya"
Miƙewa tayi ta nufi ɗakinta ta cire kayanta ta ɗaura towel ta faɗa wanka dake tana fashin sallah alwala kawai ta ɗaura kamar yanda Kilishi ta koyar da ita zama da alwala a kowanne lokaci ta dawo ta zauna saman dressing stool ta gyara gashinta ta ɗaure da ribbon a tsakiya ya sauka har tsakiyar bayanta ta shafa powder ita kanta tasan tayi kyau na mamaki ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo taji an buɗe ƙofar ta madubi taga yanda suke kallonta Hudah tace “Barakallahu ahsanal kaliƙin Beebah wlh koni mace ban gajiya da kallonki saima boko ta ratsaki tukunna" murmushi tayi ta zauna tace.
“Yunwa nakeji Wlh" dariya sukayi sukace “waima kekam wanne irin cikine dake zakuwa ki iya azumin Ramadan gashinan yana tahowa saura wata biyu?" Harararsu tayi ta miƙe tana cewa “in kukayi wasa ma saina fiku yi" tana mgnr tana rankwashinsu suka kuwa zuba a guje ta zille musu ta nufi ɗakin hutawar Kilishi ta shige bayanta ta ƙanƙameta tana dariya itama sun bata dariya tace.
“Dama haka kukeso mala'ikin naku ya tafi zaku addabeni zakuyi bayani rubuta duk kalar rashin jinku zankeyi a littafi in yazo na bashi" zaro ido Beebah tayi tace “na shiga uku an fasa aurena Kilishi Wlh idan kika haɗamu da Bro kisa ne kawai nikam na nutsu na daina kai taking care Wlh Bro zai hukunta ku babu ruwana"
Hudah ce tace “ai kafin ya dawo ta manta yauwa Kilishi wannan karon wacce ƙasa zamuje siyan kayan sallah?" Harararsu tayi tace “Aifa nice marainiyar wayon ku to kuje ku tambayi Mai martaba mana ko kuma ku kira Babban Yaya ku tambayeshi" langwabar dakai Khaly tayi tace “Ai ko Ya Naseer bamu isa mu tambaya ba yanzu asamu gwale² Hajiya kece dai zaki faɗa mana inda zamu Ni dama zaki yarda Allah banson azumi a kasar nan Dubai nakeson muje muyi azumi ko Saudi" Hajiya Kilishi akwai son farantawa yaranta hakanan tace “Shikenan zansa ayima Habeebah passport saiku tafi Saudiyya tunda ita bata taɓayin Umrah ba in yaso dagacan in kunyi sati biyu saiku wucce Dubai ɗin" wani tsalle sukayi suka rungumeta itakam Beebah jikinta ne ya mutu komai ya kwace mata zuciyarta tayi rauni “to wannan wanne irin family ne Habeeb ya koka mata matsaloli haka Hajiya Kilishi ranar da aka kawota amma ita har yanzu bata fara ganin matsalar ba ya kawota matsayin ƴar aiki amma mahaifiyarsa ta ɗaga darajar ta ta mayar da ita ƴa a gurinta Bama ta jinginata da aikin in har ba'a gaban sauran mutanen gidan bane, su kansu mutanen gidan cewa suke Hajiya wannan yarinyar tamafi Sakina samun fada a gurinki" saidai tayi murmushi tace “to ai kowa da kalar baiwarsa wai yau ita Habiba bamagujiya ita ce zata tafi ƙasa me tsarki ta gana da ubangijinta data sanshi ta fahimceshi kwanan nan?"
Saurin share hawayenta tayi saboda tasan sarai Kilishi batason kuka ta miƙe zata fita ta riƙota tace “Akwai damuwa ne Habeebatullah?" Girgiza kai tayi ta rusuna ta kama hannun Kilishi tace “a duk lkcn da kukayimin wani abin alkhairi nakanji bankai nan ba yaushe matsayina yakai aimin haka sannan shine sila kuma tunanin mahaifiyata da Babana yakan bijiromin irin rabuwar da mukayi dasu dutsi a hannun riga dominsa....."
Rufe mata baki tayi lkcn da Hajiyan soro take shigowa tace “Shikenan Habeebah Sarkin rigima bazaa kuma ba ku tashi kuje" miƙewa sukayi dukkansu Hajiyan soro tabi Habeeba da harara bata daina harararta ba Saida suka fice ita kanta Beebah ta fahimci Hajiyan soro da Hajiyan ƙofa basa sonta saboda kullum cikin harararta suke wannan tasa bata fiye shiga sharafinsu da ƴaƴansu ba komanta tafi yinsa a inda aka ajeta wai a haka ma gara Hajiyan soro ita Hajiyan ƙofa yaranta ma ta hanasu mu'amala da Habeebah a cewar ta ita kawai yarinyar batayi mata ba har tana cewa garin yakabe²n Kilishi saita ɗauko musu ajalinsu sauƙin ma da take samu dake ana shayin Kilishi da ƴaƴanta tunda sune manya kuma sune masu faɗa aji a gidan shine kawai yasa take shanyarta a inda takeso.
Kilishi ce ta katse shirun da cewa “Soro ya akayi ne?" Hankalinta ta dawo dashi ga Kilishi tace “Gulma ajali Hausawa sunce in baayi ba a mutu yanzu na fito daga gurin Mai martaba ina turakarsa yana Parlour naji