Showing 9001 words to 12000 words out of 56570 words
sauƙi wajen haɗuwa da Habeeba ya rasa dole yaja ya dangana da gdan hakimi da rasa masa kuka yana roƙonsa ko nawa sukeso kome sukeso matsayin sadakin Habeeba a sanar dashi zai bayar kuma yayi alƙawarin matukar ba ita taso musulunci ba bazai rabata da addininta ba.
A zahiri Mati Dagaci yaji matukar tausayin Habeeb musamman dake yana yawan kawo masa gaisuwa yasanshi yana lura da yanda ya susuce ko aikin daya kawo shi garin ya dainayi shikenan daga ka sameshi a bakin kogi ya zubawa ruwa idanu saidai ace anganshi a jeji a zaune ko kuma yana gda yana karanta wasiƙar jaki.
Ɗagowa Mati Dagaci yayi yace “Yaro hakikanin gaskiya duk da bambanci addini naji tausayinka matuƙa domin so mugun ciwo ne da bashida magani sai saidai samun abinda zuciya ta kwaɗaitu dashi Habibu banida maganin matsalarka na rantse da Allanku da Bibo ƴata ce nice na haife ta a yau bazaka bar gurin nan ba saina bawa Limamin Hayin Fulani damar ɗaura muku aure bisa tsarin addininku amma kash banida wannan damar”
Numfasawa Dagaci Mati yayi ya sake duban Habeeb da idanunsa suka rine suka koma jajaye yace “duk da haka bazan kashe maka gwiwa ba kaje kaci gaba da addu'ar kasa malaman addininku su tayaka Habeebu inda rai da rabo"
Miƙewa yayi cikin mutuwar jiki yace “Shikenan Baba Dagaci na gde amma bazan iya ci gaba da zama a garin nan ba zan koma Garinmu saidai inason kafin na tafi kayimin alfarma ɗaya” da sigar tausayi Dagaci yace “Wacce iri ce Habeebu" sunkuyar da kansa yayi yace “Ka aika a kira Habeebah nasan idan Baba Jimo yaji kiran nakane zai barta ta fito inason magana da ita kalma ɗaya tak nakeson ji daga gareta wlh indai har Habeebah tace bata sona zan hƙr da ita domin nasan ƙaddarar sai soyayyarta ta wahalar dani ce tasa na zaɓi wannan garin matsayin inda zanzo idan kuwa ta amsa min tanasona to ko duk dangina da nata zasu ƙare saina mallaketa domin itaɗin mahaɗin raina ce"
Shiru Dagaci yayi yana jinjina kalaman can ya ɗago yace “shikenan Sarkin zagi tashi kaje ka sanar munason ganin Bibo yanzu a gabanmu" babu ɓata lkc sai gata tun daga nesa ya kafeta da manyan idanunsa da suka rine da damuwa itama shi take kallo ganin ya zabura ya miƙe yasata tsayawa a inda take jikinta ya ɗauki ɓari saboda tuna mugun kashedin da Baba Uda yayi mata.
Ji takeyi kamar ta juya amma batada ƙarfin gwiwar hakan domin Zuciyarta tana kwaɗayin ganin ɗan birni ko ba komai tasan zata samu sauƙin abinda take ji a ƙasan ruhinta.
Takowa yayi gabanta ya tsaya ta gyara tsayuwarta cikin dakiyar zuciya ta dubesa kafin yayi mgn ta rigashi da cewa “Dan birni meye ya sameka ka rame kamar kayi jinya?" Tana mgnr tanakai hannunta fuskarsa ta shafa ƙasumbarsa da ta kwana biyu bai gyarata ba hakan yasashi lumshe idanunsa ya kamo hannun nata yayi kissing nasa yace “Ha... Habee..bah kina iya rayuwa me daɗi batare da kinsan halin da nake ciki ba?" Da rashin fahimta ta dubesa zatayi mgn ya ɗora yatsansa a saman bakinta yace zo muje inason tambayarki ne a gaban Dagaci duk amsar da kika bani ita ce zatayi aiki wajen sama mana mafita Ni dake baki ɗaya"
Kama hannunta yayi suka isa gaban Dagaci suka zauna Dagaci ya dubeta yace “Habeebah kwana biyu kin ɓuya ɗan goron ma da ake siyowa a kawomin na toshi an daina kodai an daina auren dani ne?" Murmushi tayi tayi ƙasa da kanta tace “Aa su Baba ne suka tsareni suka hanani fit...." Girgiza kai yayi yace “to ai shikenan dama Habeebu ne yakeson ganinki zai koma garinsu yanaso kuyi sallama" ɗagowa tayi tace “Habeeb!"
Ɗagowa yayi tare da jinjina mata kai yace “Sunanan kenan Habeeba don Allah ki nutsu ki bani amsa ɗaya tak ita kaɗai nake buƙata daga gareki kada ki cutar da kanki ki faɗa min iyakar gskyr abinda ke ranki game dani Habeebah kinaso na?"
Ɗagowa tayi da sauri ta kalleshi shima itan yake kallo cikin tsoro ta kawar dakai gabanta na faduwa ta miƙe ya riƙe Rigarta ta baya yace “Wlh bazaki bar gurin nan ba saikin amsa min tambayar nan don itace hadafin mafita ta Habibah kalma ɗaya ce eh ko a'a zata cireni a zullumi sannan zata ƙarfafamin gwiwa Please ki faɗamin matsayin da kika ajeni kinasona zaki aureni ko baki sona?" Ido ta zubawa Baba Uda sake shigowa zauren majalisar dagacin shima ya kafeta da idanu yana nufosu tana ƙoƙarin ture Habeeb ta kasa saima riƙon tsauri daya ƙara yima damtsanta wata ƙara kakeji kau... Kau... Abinda yasata saurin sauke idanunta kan babanta Jimo dake tsaye da wani yaro Lanti ya zare wuƙa yayi kan Habeeb Najeeb ya taso da gudu ya nufosu ya riƙe wuƙar ta yanke shi hakan yasa ya saki ya sake nufar Bibo da Habeeb ya ɗaga wuƙar zai cakawa Habeeb Bibo tayi hanzarin tureshi wuƙar ta soke ta a gefen cikinta take ta saki wata ƙara me nuni da irin azabar da taji hakan yasa Habeeb juyowa don shi kwata² baima lura da dalilin tureshin da tayi ba.
Ganinta a ƙasa a zube cikin jini yasashi sakin ihu da dira kanta ya ɗagota yana jijjigata yana kiran sunanta yana cewa “Habeebah wayyoh matata don Allah kada ki mutu bamu cika burinmu ba wlh in kika mutu nima mutuwa zanyi....." Sunkutarta Najeeb yayi suka fice da ita da mugun gudu suka nufi gdansu Dagaci yana biye dasu saboda haukan iyayen Habibah ya wucce tunaninsa baitaɓa tunanin da gaske sukeyi zasu iya kashe ƴarsu da hannunsu ba.
Tun a hanya suka rinƙa kiran James dake babban likita ne shine yake kula da lfyrsu suna zuwa ya dira akanta ya fara treatment nata sai bayan ya gama sannan su Jimo suka shigo Jumme ta shiga ɗakin da sauri ta faɗa kan Habeebah da take farfaɗo wa yanzu tana faɗin shikenan nikam rayuwata ta lalace Jimo zaka kashe mana ƴarmu ɗaya tilo akan wani bare meye yasa kukeson kubawa zuciya dama ta barku da nadama...."
Ajiyar zuciyar da Bibo ta sauke ce ta sanya Habeeb saurin tashi daga inda yake ya nufeta ta kuwa buɗe idanunta akansa ya riƙe hannunta yana jera mata sannu ta sake ƙanƙame hannunsa cikin kuka da Muryar jinya da wahala tace “Meye ribata idan banbi wanda naji a raina zan iya sadaukar da rayuwata don kare tasa ba? Habeeb bazan zauna dasu Baba Uda ba inka tafi kasheni zasuyi ka tafi dani garinku na amince zan aureka ina sonk....." Tsalle Jimo yayi ya haye ruwan cikinta ya naushi bakinta jini yayi tsartuwa zuwa sama ........
[4/7, 9:16 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*
NA
*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*
https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg
*Paid book*
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.
*Free Page 7*
★★★~~~★★★~~~★★★
Ya wankewa Habeeb fuska da yake ta kokarin daga Jimo a kan cikinta daƙyar aka ƙwaceta don cewa yayi kasheta zaiyi ya huta da baƙin ciki ya furta da haihuwar Habibah Gara ɓarinta yafi sau ba adadi, Jumme banda kuka babu abinda takeyi saboda tunda take a rayuwarta bata taɓa hasaso tashin hankali kwatankwacin wannan ba, rayuwa sukeyi me daɗi wacce ta cika da kwanciyar hankali da rufin asiri sunason junansu da ƙaunar farin cikin juna.
Yau gashi rana a tsaka komai ya goce tabbas Habibah takai mahaifinta ƙarshe don kuwa a tarihin rayuwa bai taɓa yi mata irin bugun mutuwar da yayi mata yau ba bare kuma har a halin jinya ita wannan wacce irin ƙiyayya suke yiwa mutanen birni da har suka zabi kashe tasu akansa? Tambayoyin da suke ta yawo a ranta kenan batada me bata amsa don zuwa yanzu ta rayuwar Habibah akeyi da ta shiga wani yanayi na buƙatar agajin gaggawa, a wannan yanayin James ya dubi Habeeb da jikinsa ya keta rawa tabbas badon Jimo haihuwar Beebah yayi ba da babu abinda zai hanashi rama mata wannan dukan zalumcin da yayi mata.
Hararar juna kawai akeyi tsakaninsa da Najeeb duk da cewa Najeeb ya fara saukowa yana ɗan tausaya masa akan wannan soyayya ta masifa daya faɗa ciki amma abubuwan da suka faru yau yasa yaji ya ƙara tsanar Habiba da garin Tsaunin gawo sukam wanne lefin sukayiwa Allah ya jefosu wannan gari na arna marasa imani waɗanda suke jin a ransu zasu iya kashe jininsu don wani dalili nasu mara kan gado? Ya rasa wacce jaraba Habeeb ya liƙewa jikin yarinyar duk da yasan ta fita babu algus ta zanu ba ƙarya amma a tunaninsa sai yaga batakai yayi wannan haukacewar akanta ba meye ma abinso a mutum mara gamsasshiyar nasaba?
Wannan tunanin yasashi yin tsaki ya fice daga ɗakin daidai lokacin da Jimo shima ya hassalo ya matsa zai sunkuci Beebah Habeeb yayi saurin dakatar dashi ta hanyar dafe ƙirjinsa suka kalli juna cikin mugun bacin rai yace “karka taɓata na rantse da Allah idan ka taɓata sai nasa an ɗaureka" baƙauyen mutum da tsoron tozarcin hukuma hakan tasa Jimo da Uda komawa gefe suna huci kamar wasu mayunwatan zakoki.
Da haka aka samu ta dawo cikin nutsuwarta ta sauke ajiyar zuciya tare da buɗe idanunta Jumme ta matso gabanta da sauri tace “Bibo kin tashi sannu..." Juyowa tayi ta kama hannu Jumme ta kafe Habeeb da ido shima ita yake kallo ya sakar mata wani tsadadden murmushi daya sanya jikinta mutuwa ya tako ya sunkuyo kanta yace “Inane yake ciwo?" Lumshe idanunta tayi ta kawar dakai yaja numfashi yace “karki damu komai zai hucce soon Ni kaina nasan akwai yaƙi a gabana amma zan jure don ke Beebah indai zan sameki wlh duk wata wahala zan ɗauketa"
Fincikota Uda yayi ta zube a ƙasa baya ko tunanin ciwon dake cikinta wannan abun ya hassala Dagaci ya daka masa tsawa yace “Wai meye yake damunku ne ko an faɗa muku ƙiyayya haukace da zaku nemi kashe yarinyar nan meye laifinta akan abinda ba ita ta dasawa kanta ba to wlh ku dawo hayyacinku ku kiyayeni idan kuka fusatani tsaf zan yanke hukuncin da bazai muku daɗi ba sakarkaru"
Sakinta sukayi sarai sun san halin Mati idan suka fusatashi babu abinda bazai iya yi ba shiyasa suke shayinsa, miƙewa tayi ta nufi Jumme ta faɗa jikinta ta rungumeta tana kuka tace “Jumme kema baki sonsa" ajiyar numfashi tayi tace “Inasonsa mana tunda kina sonsa Uwata nidai nafison kiyiwa iyayenki biyayya bazasu cutar dake ba ki cire komai a ranki bakida gatan da yafisu" ɗagowa tayi taga idanunsa akanta tayi ƙasa da nata ya matso ya riƙo hannunta yace “Kada ki sanya damuwa a ranki ki kulamin da kanki nabar amanarki gurin Dagaci zan dawo bada jimawa ba zamu mallaki juna soon insha Allahu"
Janye hannunta tayi daga nasa Dagaci ya kamata suka fice ya nufi gidansa yanata faɗa kamar zai ari baki, suna shiga ya fara ƙwalawa uwargidansa kira ta fito daga Madafi tace “gani Mati meye yakar buzu da ranar Allah?" Mika mata Bibo yayi yace “Marka ga Habiba nan ki bata kulawa da tsaro daganan zuwa lkcn da ƙura zata lafa nan ya kwashe lbrn komai ya sanar mata ta tafa hannu tace “To banda abinsu shi wannan lamari ai abin asa idanu aga ikon me sama ne yaran nan ba wanda ya haɗasu su suka haɗa kansu Inma mutum yace zai raba saidai yasha wahala bare ma meye laifin Habibu yaron kirki da hayaniyar ma ba damunsa tayi ba kagani fa Mati tunda suka zo garinnan kullum sai yazo ya gaisheni da ɗan alkhairinsa to maji ma gani wai an binne rayayye"
Kama hannu Bibo tayi suka shiga daki ta nufi madafin ta haɗa ruwa me ɗumi ta kamata suka nufi bayi da kanta ta rinƙa gasa mata jikinta tun tana wash² har ta dawo tanajin daɗin ruwan.
Suna zaune Marka na shafe mata ƙafafu da mai me gurguwa ya shigo da sallamarsa babu wanda ya amsa sai maraba da Marka tayi masa suka gaisa tace “Habibu ɗan makaranta ashe kuma haka abu ya faru babu daɗi sai hƙr kasan mutanen namu ne sai shiru sai saurare basuda dadin sha'anin akan abinda suka jahilta musamman irin gidan Sarkin Noma Nomau tsaurinsu akan ra'ayinsu yayi yawa"
Murmushinsa yayi me daraja idanunsa akan Beebah data daga kanta sama tazuba idanunta akan rufin azarar dake ɗakin yace “Zai wucce kamar ma ba'ayin ba Baba Marka nidai roƙona ki kulamin da ita kafin na dawo ba jimawa zanyi ba inason naje na shirya komai ne ayi a wucce gurin idan na ɗauke ta dai inace shikenan?”
“Shikenan kuwa yaro” Marka ta faɗa ya janyo ledojin daya shigo dasu ya miƙawa Marka yace “magungunanta ne Dagaci yasan yanda ake amfani dasu Baba Marka a kula wajen shansu, naga nan kunada service ga waya nan ƙarama nasa layi ta rike a hannunta saboda in rinƙajin lfyrta kafin na dawo ba jimawa zanyi insha Allahu"
Buɗe ɗaya ledar yayi tsire ne sai tiriri yakeyi duk ya cika dakin da ƙamshi ya ɗauka ya kai mata bakinta.
Kautar dakai tayi ta kalli Marka itama kau dakai tayi ta miƙe ta fice musu daga ɗakin yayi murmushinsa me cike da isa yace “Bazakici ba?" Daga masa kai tayi ya sake ɗaukowa yakai bakinsa ya tauna yace “kuma kinga sai kinci tunda kikace kina sona" miƙewa yayi ya zagaya bayanta batayi aune ba kawai sai jinta tayi kwance a ƙirjinsa ya daga kanta ya riƙe sosai yanda bazata iya ƙwacewa ba ya sanya bakinsa cikin nata ta kuwa rintse idonta da ƙarfi cikin wata masifaffiyar faɗuwar gaba da tashin hankali ta rinƙa kiciniyar ƙwacewa shi kuma ya matseta ya lumshe idanunsa yana sake saƙalo harshen ta me masifar zaƙi yana fitar da wani numfashi me wuyar fahimta yana kusa sake shigar da ita jikinsa ya saki fuskarta don yasan yayiwa bakinta riƙon da bazata iya ƙwacewa ba ya sanya hannunsa tsakanin ƙirjinta da cikinta shafaffe wanda zaka iya rantse wa bata sanya masa komai.
Yawo yake da hannun a hankali tsakanin cibiyarta da ƙirjinta yana son kaishi ga kyakkyawar dukiyar fulaninta dake tsaye kam kamar zasu tsonewa mutum idanu duk da bata taɓa sanya musu bra ba a tsayin shekarunta sha bakwai a duniya amma hakan baisa sunyi komi ba.....
Wata zabura yaji tayi tare da shiɗewa lkcn da ya ɗora hannunsa kan yar ƙaramar rigar data rufe su dasu hakan yasashi saurin janye hannunsa ya cire bakinsa daga nata yana sharce gumi gabadaya jikinsa ya mutu murus sai zufa dake karyo masa ta ƙofofin gashin jikinsa, wata ajiyar zuciya yaja me ƙarfi yana arowa kansa juriya yana sawa kansa ya sake ta ta janye jikinta sai rawar mazari yake ƙirjinta kuwa banda bugawa babu abinda yakeyi ta zabura ta miƙe zata runtuma da gudu yayi saurin riƙota ta zame ta rushe masa da kuka yayi saurin zama yace “Nikam banason kuka wlh Beebah meye na kukan?" Tureshi tayi da ƙafarta tace “na daina sonka tunda kaima irinsu Jami ne haka sukayita sa nonon Tani a bakinsu suna matsa mata shi da hannunsu shine kaima zakayimin to banasonka...."
Da sauri ya rufe mata baki yace “Ya isa Ni ba irinsu bane Beebah na daina kiyi shiru karki faɗawa kowa muje kici abincin yau banga sanda kikaci abinci ba" noƙe kafada shima noƙewa yayi ta rufe idanunta tana dariya, dariyar tata ta sashi dariya ya cafko hannunta ya zauna da ita da lallami ya samu taci tsoka uku ganin taƙi sakewa taci a gabansa ya sashi karkacewa ya zaro kuɗi yan ɗari biyu rafa guda ya bata yace “ki riƙe a hannun ki saboda sa kati ban yarda a kira kowa ba bayan Ni" zaro wayar yayi da kwalayen turare ya aje mata ya miƙe ya kama hannunta ya sumbata ya fice da sauri saboda ganin idanunta ya kawo ruwa yasan tsaf zata karya masa gwiwa gara karma ya tsaya domin tafiyar tasa tafi zamansa muhimmanci........
*Share please*
[4/9, 6:25 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*
NA
*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*
https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg
*Paid book*
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.
*Free Page 8*
★★★~~~★★★~~~★★★
Koda ya fito tsakar gdan Saida ya bawa Marka kasonta sannan ya ƙara mata wasu masu tsoka da zata kula masa da habibansa kafin ya dawo duk da ya ƙudurce a ransa bazai daɗe ba hakan bai hanashi jin kewar abar ƙaunar tasa ba,
Cikin ƙaramin lkc yayi sabo da ita sabon da yake jin zagawarta a cikin jininsa yanajin zuciyarta na bugawa daidai da bugun tasa zuciyar, yana shiga masauki jakar kayansa kawai ya ɗauka drivern campanyn simintin na mahaifinsa ya ɗauke su suka ɗauki hanyar Dutse tsakanin Tsaunin gawo da Birnin Dutse tafiya ce ta gaske kasancewar Tsaunin gawo cikin ƙasar Kano take a rankin wata babbar ƙaramar hukuma.
Sun gajiya lkcn da suka shiga Dutse dare yayi nisa wannan tasa ba kowa ne yasan da dawowarsu ba, kai tsaye sashinsa ya nufa ya watsa ruwa yayi sallar magrib da Isha ya kwanta yana hucce gajiya amma zuciyarsa taki barinsa a Jigawa ta ɗauke shi ta mayar dashi Tsaunin gawo, hakanan ya wanzu yanata murmushi yana tunano irin wani yanayi da ya tsinci kansa ɗazu da yana kissing kyakkyawan bakin Beebansa tabbas akwai nutsuwa a cikin kasancewa da abinda zuci take muradi dole yayi bakin kokarinsa yaga ya mallaki Beebah bada jimawa ba ko ya samu zuciyarsa ta samu salama.
Da waɗannan tunane² bacci ya ɗauke shi me sihirtaccen daɗi cike da mafarkin abar ƙaunarsa cikin kyakkyawan yanayi wanda ya sanyashi jin shauƙin kasancewarsu tare aikam yana tashi da asuba ya watsa ruwa ya sanya doguwar riga ya nufi masallacin cikin gdan sarautar sai lkcn ƴan'uwa barori da kuyangi suka fahimci ashe autan Kilishi ya dawo Auta me dakawa maza gumbar wuya a hannu.
Kaffatan duk wani ma'aikaci dake cikin wannan gda yana masifar shayinsa bawai don tsabar zalumcinsa ba a'a saidai don masifar kwarjininsa ko kusa baya ɗaukar raini da wargi tun ma yana ƙarami bare yanzu da yake jinsa sama da kowa a duniya.
Bayan idar da sallah kamar yanda al'adar gdan take Saida suka gama gaisawa da juna ƴan'uwansa sunata