Showing 27001 words to 30000 words out of 56602 words

Chapter 10 - YAREEMA JAWAD 1 To end Book Complete Writing by SUMAYYA SALEES SADEEQ -.txt

19 Feb 2025

5158

biyu, hawayen fuskarsa ya goge sannan yasa hannu ya goge na fuskar Jawad daya gangaro.




A hankali Jawad ya bud'e idonsa ya d'aura a fuskar Areef, cikin basar wa da nuna baiji abinda ya faru ba Areef ya sakar ma Jawad murmushi,"Jawad barka da tashi,Yareema Jawad kasa magana yayi dan a tunanin sa Areef yaji mafarkin sa, ya naga kwalla a idonka ko duk na farin cikin gobe za'a d'aura maka aure da habibatyn ka Zahra ne? Cikin hassala jin an ambaci sunan Zahra yasa Jawad mik'ewa zaune ya d'auki pillow ya rungume a kirjinsa yana tunanin mafarkinsa, wato da gaske Zaljameel ta masa nisa kuma baya cikin zuciyata, uban tagumi ya buga yana tuna yanayin da suka kasance a dream d'in, wani k'ayattacen murmushi ne ya sub'uce masa batare da yasan yana yiwa. Areef zaiyi magana wayarsa ta fara ringing, dubawa yayi yaga mai martaba mahaifin Jawad, cikin ladabi ya d'auka, cikin girmamawa suka gaisa, sannan sarki Farouq ya fara bashi bayani akan ya same su a J&Z special hospital, kai kad'ai zaka zo kuma bana son Jawad yasani, shikenan Yallabai gani nan. Tunda ya fara wayar Jawad ke kallonsa bai bari ya gane dawa yyi waya ba ya tashi ya fad'a toilet, Jawad ma nasan tambayarsa amma miskilanci ya hanashi, mik'ewa yyi shima ya fara shirin wanka. A gurguje Areef ya nufi hospital d'in.


Ganin, Aliyu Dad d'in Zaljameel da Fulani, mahaifiyarsa hajia Binta da kuma baban Zahra, Alh Zahradden da ita Zahra. sosai jikinsa yyi sanyi ya kuma fara b'ari, ganin fuskarsu bbu walwala, k'arasawa yayi cikin d'akin ya zauna. Cikin ladabi ya gaida iyayen nashi, hankalin sa ne ya koma ga wanda ke kwance a gadon hospital d'in.


Grandfa kwance ansa masa oxygen a baki, numfashinsa sa na fita a hankali, k'arasawa yayi jikin bed d'in hankalinsa a tashe ya kama hannun grandfa, tuni hawaye ya cika idonsa dan Areef akwai tausayi, juyowa yayi ya kalli parents d'in nasa ya fara tambayar su abinda ke faruwa, Alh Zahradden ne ya fara masa bayani tunda ga tahowa da grandfa hospital har lokacin da doctor yace ya samu heart attack, an kuma tambaye shi meye dalili yace saboda rashin had'a auren Jawad da Zaljameel.


Mik'ewa Zahra tayi tsaye dan ba'a bata labarin komai ba an dai aika direba ya kawota, ja da baya ta fara yi idonta ya cika da kwalla, kai ta rik'e tana furta no...... Dats is impossible, kunsan waye Jawad a wajena da kukesan rabani dashi, Dad harda kai ta nunashi da hannu, Jawad shine rayuwata, kunsan irin wahalar da nasha kaifin na samu soyayyar Jawad, ranar da Jawad yace zai aureni wallahi banyi bacci ba saboda murna, naso ace ya fad'a mini yana sona tun kan ranar, ina san Jawad wallahi ina sonsa, idan na rasa shi wazai aureni? d'irkusa Zahra tayi ta fashe da kuka mai tab'a zuciyar duk wani mai jinta, iyaye matan kuwa Hajia Binta, Mom da Fulani tausayin Zahra ya su zubar da hawaye.


Areef tsaye yyi yana k'arema Zahra kallo, tunda tazo sai yau ya kalleta sosai, tunda ta fara magana yake kallonta, gaba d'aya ta tafi da shi, murmushi yyi lallai yyi mata,dan Zahra ba baya bace a kyau, matsalar ta rashin tarbiyya amma tunda tasan so, to son nan zai gyarata.




Areef ne zai aure ki, sukaji muryarsa, ita kanta Zahra d'aga kai tayi ta tsaya da kukan tana kallonsa, yarda yayi shiru sai taga kamar maganar ba daga bakinsa ta fita ba. Gira ya d'aga mata had'e da kashe mata ido d'aya ya sakar mata wani murmushi, Yes Zahra ina sonki kuma zan aure ki,ni dama na hakura da auren Zaljameel tun banzo hospital d'in nan ba. Gaba d'aya sun maida hankalinsu ga Areef dan jin dalili sa, labarin mafarkin Jawad ya basu da kukan da yake yi yana kiran karta tafi ta barshi yana sonta, "Tunda naji haka na bawa zuciyata hakuri, dan nima Zaljameel tunda Jawad ya dawo ta chanja mini gaba d'aya, hankalin ta yafi karkata ga Jawad.


Zahra ke meye ra'ayinki akan Areef, Dad d'in ta ya tambaye ta? Kallon Areef tayi shima ita yake kallo ya hard'e hannunsa biyu a kirji, gani tayi ya mata wani kwarjini ya kuma birgeta dan Areef akwai kyau shima, Ina sonshi Dad na amince zan auresa. Wani dad'i ne ya lullube duk wanda ke wajen harda grandfa da yanzu fitar numfashinsa yyi normal, hawayen farin ciki ya fara bin gefen fuskarsa.




Sosai iyayen suka musu addu'a da kuma sadaukarwar da sukayi, tare direba ya maida su gida.




Duk abinda ya faru Jawad da Zaljameel basu sani ba har aka fara biki, dan ance ya zama sirri tunda duk tare za'ayi bikin karsu bari a gane.




NIMA KAM SAI SHOKIIII NAKE KWASA SABODA MURNA💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻






SUMYNBASH CE💋
CE💋







?🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮




YAREEMAH JAWAD




🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮






©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L




A romantic love story
2017




July 2017








Ina kuke masoyan littafin yareema jawad da ni mai rubutashi Sumyn Bash, na matuk'ar k'aunar ku fiye da yarda bakwa zato, ina alfahri daku masoyana, ina godia da addu'oin da kuke mini kuma ana tare#One love❤






Chapter 43&44








Zama Jawad yyi a kujerarsa da irin babbar nan ta sarauta, wani irin annushuwa yake ji aransa, yau dream d'insa ya tabbata, ya mallaki Zaljameel cikin sauk'i, bai tab'a tunanin hakan ba, gaskia grandfa ya masa k'ok'arin da bazai da hakan ba, a hankali ya furta


"luv u grandfa, how will i forget u in my life ka min komai a rayuwata".


Fuskarsa ya d'aga sama yana kallon ceiling, ya lumshe idonsa fuskar sa d'auke da murmushi.


Sallama Bala yyi a parlour, ganin Yareema Jawad zaune a karagarsa yasa ya k'arasa, a gaban sa ya zauna a k'asan k'afarsa. Fara'a ya fara magana!


"Barka da hutawa ranka ya dad'e"


"Barkan ka dai Bala" ya fad'a fuskar sa d'auke da murmushi.


Mamaki bayyane a fuskar Bala, dan rabon da Jawad ya k'ira sunan sa har ya manta, hakan ya bashi damar cigaba da zancen sa! Ina taya ka murnar Aurenka, ina rok'on Allah ya baku zaman lpy kaida gimbiya Zaljameel, ya azurtaku da salahan ya'ya masu biyayya ga iyayen su"




Wani dad'i ya ratsa zuciyar Jawad, Bala bai tab'a faranta ransa ba sai yau, tunda Bala ya fara magana idonsa a rufe yake, dag'o kai yayi had'e da gyara zaman sa, tar ya d'aura idonsa akan Bala dake zaune! Sai da yyi wani murmushi sannan yace!


"Bala na 'yanta ka na kuma biya maka aikin hajji, na d' auki dawainiyar aurenka na kuma baka gidan da zaka zauna, kai na daban ne yanzu a wajena, tunda aka d'aura mini aure Areef shine wanda ya fara faranta ta raina da kyakkyawan labari, sai kai Bala"




Mutuwar zaune Bala yayi dan jinin dake jikinsa jiyay ya daskare, anya abinda kunnensa yaji gaskia ne?D'aga ido yayi ya kalli Jawad wanda shima d'in Bala yake kallo, Bala gani yay kamar maganar ba daga bakinsa ta fita ba, tsantsar mamakin da Jawad ya gani a fuskar Bala yasa ya nanata masa abinda ya fad'a a baya.


Fashewa da kuka Bala yayi dan bakinsa ya gaza gode ma Jawad, kuka sosai Bala yayi ba tare da Yareema Jawad ya lallashe shi ba, sai da yayi mai isarsa sannan ya fara magana muryarshi a shak'e!


"Ranka ya dad'e godia nake, duk da bakina ya rasa kalmaomin da zanyi amfani wajen gode maka, akwai alfarma da zan nema a wajen ka, Dan Allah ka barni a matsayin bawanka, ina son na dawwama ina maka hidima, bana son rabuwa dakai ranka ya dad'e.




Cikin kulawa Jawad ya d'auke idonsa akan Bala ya maida part d'in Zaljameel, ji yake inama zata fito ya ganta, Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya fara magana!


"Muna tare Bala, bbu wanda zai iya d'aukar dawainiyata sai kai, kasan komai nawa, dakai kad'ai na yarda, ina ganin' yanta ka ba matsala bane".




Bayan ya gama yi ma Jawad godia ya nufi bedroom d'insa dan had'a masa ruwan wanka.


Zaljameel zaune a d'akinta, tana jiran shigowar Areef da friends d'insa dan taji muryar su, jin shiru yasa ta sauke mayafin kanta tana k'arema d'akin kallo, babban d'akine an masa decoration da Arabian furniture, design d'insu irin na sarauta ne,gefe cushion ne white colour an masa ado da golden, sunyi kyau, a gefe wata shegiyar plasma ce bango d'aya ta cinye, kamar ta fad'owa mutum dan girma, a hankali Zaljameel ke bin d'akin nata da kallo, gaskia iyayen ta sunyi k'okari.




Wall clock ta kalla, 11:56pm hankalinta ya tashi, to ina Areef ya shiga? Ni sumy nace yana wajen matarsa suna rak'ashewa. Lol


Wasa wasa bbu Areef bbu alamunsa, ganin haka yasa Zaljameel ta fara shirin bacci, kayan jikinta ta cire ta nufi toilet dan yin wanka.




Bayan ta fito ta shirya cikin wasu tsadadden sleeping dress red colour, silk ce, rigar iya gwiwa tabi jikinta ta lafe,duk surorin jikinta ya bayyana, a hankali ta taka gaban standing Ac ta rage ta nufi bed ta kwanta, tunanin inda Annah take Zaljameel ta fara yi, badai Annah ta tafi ba, dan bata tunanin akwai wanda yayi saura a gidan, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ina Areef ya shiga? Anya bazata kira gida ta sanar dasu ba, wata zuciyar tace ki bari anjima ko akwai abinda ya tsare shi bai shigo da wuri ba, phone d'in ta ta jawo ta hau online, messages ne suka fara shigo mata na congratulations, a wani group da take ciki, na class mate d'in ta dake Qatar.


Ta gama yi musu reply ta sauka zuciyar ta fal damuwa, dan ma Zaljameel bata da tsoro hakan yasa tayi kwanciyarta tana jiran dawowar Areef, a haka bacci ya d'auke ta.




Areef da Zahra kam sun raya daren su sosai cikin farin ciki da k'aunar juna, da yake Zahra duk wayewar ta bata tab'a yarda wani d'a namiji ya kusanceta ba, hakan yasa Areef daya dan tab'a bariki ya birkice mata gaba d'aya, su Zahra ansha kuka kamar rai zai fita, sai da suka raya daren sannan suka yi bacci.





The next day






Jawad ya tashi da asuba yayi wanka ya shirya cikin jallabiya ya fito zai nufi masjid, kamar yarda suka saba yana fitowa yaci karo da Bala a tsaye yana jiran fitowarsa, d'urkusawa Bala yayi ya gaida Jawad, bayan ya amsa masa cikin kulawa suka nufi masjid.


Bayan sun idar Yareema Jawad ya hango grandfa a gefe yana tasbihi, wajensa ya nufa fuskar sa d'auke da fara'a.


Grandfa na ganin Yareema Jawad ya nufeshi yayi kicin kicin da fuska, ganin hakan bai hana Jawad k'arasa wa ba.




A gabansa ya zub'e yana dariar ganin yarda grandfa ke cin magani, zama yayi a kusa dashi ya fara gaida shi!


"Grandfa nawa ni kad'ai"


Harararsa Grandfa yayi!


"Ina kabar Zaljameel? Da zaka ce naka kai kad'ai ".


Daria Jawad yayi dan dama yasan zasu fafata da grandfa, saboda abinda ya masa, sai da yajanyo yayi rashin lpy.



" Dan nema! Wato kana so kana kaiwa kasuwa ko? Yanzu badan na tubure ba da tuni ka rasa farin cikin ka ko? Zaljameel alheri ce a tare da kai na dad'e da gane hakan, burina ya cika Jawad dama shi kad'ai ne ya rage mini a duk buri kana, sai kuma fatan na cika da imani.


Cikin barkwanci Jawad ya bawa grandfa hak'uri, abinka da jika da kaka tuni grandfa ya saki jiki sukayi magana da Jawad.




Nasiha sosai grandfa ya masa akan ya rik'e Zaljameel da amana, ya bata duk wata kulawa data kamata, nasihar ta ratsa Jawad sai dai a zuciyarsa bashi da wani buri da zai bama Zaljameel damar shiga rayuwarsa, kamar yarda yayi alkhairi bazai tab'a bayyana mata yana sonta ba, yanzu ma kam haka za'ai, lokacin bayyana mata soyayya baiyi ba, so yake sai ta gama kamuwa da sonsa shima dan zata fi sanin darajar sa, sallama yayi ma grandfa, anan grandfa ya bashi sak'on gaida Zaljameel.












SUMYNBASH CE💋




🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮




©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L



A romantic love story
2017




July 2017




Story & written by


SUMAYYA SALEES SADEEQ




I proudly to dedicated dis page 2 u guys u are so special in my heart.




Aishat A Muh'd (Aunty)
Aunty cute Zahra Bukar
Ummi hambali
Rahma(momyn sultan)
Faridat sweery
Maryam s bello
Maryam Abdul
Hafsat musa(indon k'auye
Aunty kausar
Aisha Ali garkuwa
Feedy luv


Dama sauran wanda ban fad'a ba, duk ina sonku.




Ina kike Aunty na


Zahra Uba Leader


Ina matuk'ar alfahri dake ina kuma godia da k'aunar da kike nuna ma littafin yareema jawad, # much love 💋






Chapter 45&46






Wani doguwar mik'a Zaljameel tayi tana salati, a hankali ta fara bud'e idonta, a zabure ta mik'e zaune ganin gari yayi haske, phone d'in ta dake a gefenta ta jawo ta duba time, ganin lokaci yasa ta fito da idonta waje a tsorace ta hannu tasa ta dafe kanta, omg! Yau wane irin bacci nayi, ace har 12:00 pm tana kwance, zata iya cewa rabonta da bacci irin haka tun kafin a fara shirye shiryen bikinta.


Addu'ar tashi daga bacci tayi ta fara duba d'akin, so take taga alamun Areef ko ya shigo d'akin da tana bacci amma yarda ta kwanta haka tata shi, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ta fara nanatawa a ranta, mai yake shirin faruwa da ita ne, ina Areef yake, kar dai sace shi a kayi. Zuciyarta ta gama yarda da Areef ya b'ata hakane yasa ta d'aura hannu aka ta fara kuka, shikenan ni Zaljameel na shiga uku, Ya Allah ka bayyana Areef, Allah kasa yana hannu nagari, ni kam daria Zaljameel ta bani, ya za'ayi ace sauri kamar Areef ya b'ata.


Kukan da Annah taji shi yasa ta fito daga kitchen da gudu ta nufi d'akin Zaljameel hankalin ta a tashe, murd'a handle d'in Annah tayi ta fad'a d'akin, wajen Zaljameel ta nufa da ke rusar kuka mai ban tausayi, cikin kid'ima Annah ta fara tambayar Zaljameel meke faruwa.




Rungume Annah Zaljameel tayi tana kuka, cikin sheshek'ar kuka Zaljameel ta fara yima Annah bayani cike da shagwaba.




"Annah ya Areef bai dawo ba, tunda aka kawo ni ban ganshi ba, Annah zama nayi jiransa har bacci ya sace ni, yanzu ma na tashi ban ganshi ba, ta sake fashe wa da kuka.



Turk'ashi! Annah tace a zuciyarta, wato dama Zaljameel bata san Yareema Jawad aka aura mata ba? Lallai akwai matsala. Dama tasan Jawad bazai zo wajen Zaljameel ba, saboda ba ita yake so ba dole aka masa. jin Annah tayi shiru yasa Zaljameel d'agowa ta kalle ta, fuskar sharkaf da hawaye, basar wa Annah tayi ta fara tafa hannu,"Kai amma Areef da shiririta yake, ai na zata ya miki waya tun a jiya".


Zaljameel ta tsaida hawayenta ta zubawa Annah ido tana sauraron ta.


Annah ta cigaba "jiya bayan na fita waje sunzo da abokanan sa, ina tsaye ina gaida shi aka masa waya hajiarsa bbu lpy, an kwantar da ita a hospital, to shine fa hankalin sa ya tashi ya fita bai fad'a miki ba.




Ajiyar zuciya Zaljameel ta sauke, wayyo Allah sarki ai bai fad'a mini ba shi yasa hankali na ya tashi, Allah ya bata lpy.


"Ameen" Annah ta amsa.




Annah Zaljameel ta kalla, "Annah yaushe zamu je duba ta?".
Wani zufa ne ya yankowa Annah ta fara magana, "Haba Zaljameel, waya fad'a miki amarya na fita, ai ita kanta mara lpy idan taji cewa kinje bazata ji dad'i.


" Shikenan Annah Allah ya bata lpy "Ameen" Annah ta kuma amsawa.




Annah tabawa Zaljameel labarin nan ne dan ta kwantar mata da hankali, sai dai abinda Annah bata sani ba tarewar Areef a kusa da gidan Jawad, shin Areef da Zahra zasu k'i shiga part d'in Zaljameel ne ko yaya zata kasance.




Wayarta ta d'auka zata kira Areef Annah ta lura, Gimbiya mai zakiyi? Kallon Annah tayi, cikin sanyin murya tace!


"kiransa zanyi Annah"


Kirjin Annah ne ya buga ta kalli zaljameel!
"Aa Zaljameel, ni dai a gani na karki kirashi, saboda bai kiraki ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login