Showing 42001 words to 45000 words out of 56602 words

Chapter 15 - YAREEMA JAWAD 1 To end Book Complete Writing by SUMAYYA SALEES SADEEQ -.txt

19 Feb 2025

5156

suna hira sukaji shigowar Zaljameel, a razane suka tashi tsaye suka nufeta, fad'awa tayi jikin Fulani ta kuma fashewa da kuka.




Fulani ce tayi k'arfin halin tambayar ta," Zaljameel meke faruwa ne? Mai ya samu Jawad d'in"


D'ago wa tayi da jan idonta ta kalli Mom, "Fulani babu abinda ya same shi,Fulani koroni yayi gida wai dan ina da ciki, yace sai an zubar ni kuma nace A'a ban yarda ba ina son cikina shine yace nabar gidan.




Mai martaba bai son lokacin daya zube a kujera ba yana salati, Jawad d'in ne yace ki tafi gida" Eh mai martaba shi yace na taho.




Shikenan Zaljameel, kiyi hak'uri, Fulani shiga da ita ciki. Fulani da ta kasa magana dan takaicin abinda Jawad yayi tana kama Zaljameel suka nufi ciki.






KUYI HAKURI DA WANNAN, SAI DA NAYI TYPING MAI YAWA WALLAHI YA GOGE, NA SAKE WANI NE SABODA NA MUKU ALKHAWARI, SAI KUN JINI.


SUMYNBASH CE 💋




🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L


(We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers)




A romantic love story
2017


July 2017




Story & written by


SUMAYYA SALEES SADEEQ


Chapter 62&63








Wani katafaren room Fulani takai Zaljameel, an cika shi da decoration kala kala, sosai ya burge Zaljameel, zaunar da ita tayi a akan sofa tana zauna itama, a time d'in Zaljameel sai matsar hawaye take, kallonta Fulani tayi cike da tausayawa halin da Zaljameel ke ciki, hannun ta ta kama ta rungume ta ta fara lallashi!






"Zaljameel kiyi hak'uri ki daina kukan haka, ai kukan ki ya k'are saboda kinzo inda za'a nema maki mafita, duk duniyar nan babu wanda ya isa ya zubar da cikin nan, kin birgeni da baki biyema rud'in shed'an ba saboda soyayya miji ku aikata zunubi, amma ki bar mini komai a hannu na ".


Fulani ta cigaba da shafa bayan Zaljameel," Zaljameel a hospital aka fad'a muku kina da ciki?".

"A'a Fulani shi ya auna ni dakansa, shine yace wai ina maganin hana d'aukar cikin daya ke bani nace ai bana sha, Fulani da kyar nasha har marina fa yayi" Zaljameel ta sake fashewa da kuka.




"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,Yareema Jawad haka ya lalace ban sani ba, lallai zamansa na london bai amfane mu da komai ba sai barna" Fulani tayi shiru tana jinjina maganar a ranta.




Tashi tayi tsaye, "Zaljameel bari naje, dan zama bai kamani ba" ta fice ta bar Zaljameel zaune.






Kuyangu sun cika room d'in Zaljameel sun hau gyara duk da a gyaren yake amma Fulani ta tura su a sake gyarawa, sun had'ama Zaljameel ruwan wanka a bathroom sun kunna turaren wuta mai k'amshi, bayan Zaljameel ta fito daga bathroom ta bada umarnin a d'auka mata kayanta a motar ta,an d'akko kayan an jera mata a wardrobe, coolers na abinci masu kyau da tsada aka ajiye ma Zaljameel, dan takanas Fulani tasa aka shirya mata girki, ga fruits kala kala suma an ajiye, bayan sun gama tsara komai sauran suka fita kuyangun Zaljameel lantana da jummala suka tsaya cuz ta saba dasu.





Washe gari


Yareema Jawad da kyar ya iya zuwa office, shima fita yayi ko zai samu sassauci, tabbas yasan Mom bazata bari Zaljameel ta zauna mata a gida ba bayan ga gidan mijin ta, kuma yasan duk abinda Zaljameel zata fad'a akansa Mom bazata yarda ba, hakan ne yasa hankalinsa ya d'an kwanta.




Meeting d'in gaggawa Sarki Farouq ya had'a a part d'in grandfa, da shi da aliyu sai sai grandfa sai matan su, Fulani da Momy.






Mom da Dad k'iran meeting d'in ya tashi hankalin su, suna ta tunanin meke faruwa har suka je, Sarki Farouq ne ya fara magana, bayan an bud'e taro da addu'a.




"Assalamu alaikum! Nasan zakuyi mamakin abinda yasa na taramu anan, to ba komai bane sai akan 'ya' yanmu Jawad da Zaljameel".






Ras gaban Mom ya fad'i "Wani abune ya same su?" cewar Dad hankalinsa a tashe.




Sarki Farouq ya fara jawabi tunda ga zuwan Zaljameel da yayin data zo musu tana kuka da labarin data basu.






Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, shine abinda suke nanatawa a fili, grandfa kam yama kasa magana tsabar takaici, Dad ne ya fara magana, To Farouq yanzu ina Jawad d'in?".




Tab'e baki Sarki Farouq yay cike da takaici, haba ai kasan bazai zo ba, sai dai mu mune shi tunda ya riga ya shuka tsiya, al'adar yahudawa, Allah ne ya soni na farga na rasa shi da k'asar nan da bansan abinda Jawad zai aikata ba, amma duk da haka sai ya d'and' ani abinda ya shuka indai nine "Sarki Farouq ya fita a fusace Fulani ma data k'ara tinzura ta bi bayansa.




Aliyu da Ayshat zaune gaban grandfa daya kasa magana, Aliyu ne ya fara magana cikin sigar lallashi" Allah ya taimaki sarki Allah ya k'arama sarki tsahon rai".


Dan Allah ranka ya dad'e ka kwantar da hankalinka, wannan ai k'aramar matsala ce, kuma shawo kanta bazai yi wuya ba, banson ka saka damuwa a ranka ".




Duk maganar da Aliyu keyi sarki najinsa amma ya kasa magana, dan indai zai magana to babu wanda zata yima dad'i, shiyasa yayi shiru yayi koyi da sunnar ma'aiki annabin mu muhammad (S.A.W) daya ke cewa hak'uri yayin fushin farko,idan ranka ya b'aci karka d'au wani action a time d'in sai ka huce, dan zai iya zama hukuncin da zaka d'auka kai kanka sai kayi nadama a gaba.






Suma haka suka nufi part d'insu da jimami, Mom kam ta gama hassala da abinda Zaljameel tayi, saboda me Zaljameel zatayi haka? Meye ribanta idan ta had'a Jawad da iyayensa, ita inda tazo ta sanar mata da maganar bata kai haka ba, tsaki taja ta zauna tana tunanin mafita, "Ya Allah ka kawo mana komai da sauk'i" Ameen Dad ya amsa ya shige room d'insa, Momy kam ta zauna a parlour.






Jawad ya kasa zaune ya kasa tsaye, komai na duniya ya daina masa dad'i, dumin jikin Zaljameel kawai yake da buk'atar ki gashi ta masa iyaka da ganin ta, aikin Office d'in yak'i samuwa hakan yasa ya nufi gida, part d'in Areef ya nufa bayan sunyi waya ya sanar dashi yana gida.




Da sallama Jawad ya shiga gidan, shigarsa ta farko kenan tunda Areef ya tare, zaune ya tarar da Areef yana kallon aljazeera, jin sallamar Jawad yasa ya tashi ya tare shi suka zauna tare. Areef yasan duk abinda yake faruwa cuz bai dad'e da dawo wa daga wajen Sarki Farouq ba, dan haka shima ya gama hassala da Jawad.




Zama sukayi a kujera Jawad ya rufe idonsa ya d'aura kansa a saman kujerar yana jin yarda zuciyarsa ke bugu da k'arfi, hawaye masu zafi suka fara fita a idonsa.




Areef ne ya kalli Jawad ransa a b'ace, "Kai saurara mana malam, lallai Jawad abin naka ya girmama, harda hawaye saboda Zaljameel tak'i bin umarnin abinda ka sata shi ya saka ka cikin wannan halin, wallahi Jawad ka bani mamaki, kai da ya kamata kayi murna ka gode ma Allah akan baiwar daya maka, amma kake k'ok'arin ja da shi, kasan mutane nawa ne ke neman haihuwa Allah bai basu ba, amma ka samu kai sai ka kasa godiya ka yima Allah butulci.




Tunda Areef ya fara magana Jawad ya zuba masa ido yana kallonsa dan bai gane mai Areef ke k'ok'arin sanar dashi ba, sai da ya gama sannan Jawad yayi k'arfin halin bud'e baki ya fara magana "Areef banfa gane mai kake nufi ba, ina son ka fahimtar dani please"




"Ok haka kace?, to bari kaji, Zaljameel matar ka tana d'auke da cikin ka a jikinta, wanda kace baka so sai dai a zubar, wallahi Jawad ka bani mamaki a matsayin ka na misulmin kwarai kuma dan sarki, a tunanin ka idan maganar nan ta fita ba cin mutuncin masarautar nan bane? ".




Banda zufa babu abinda ke bin jikin Jawad, tashin hankali ya tsinci kansa a ciki da bai tab'a shiga cikin sa, sai yanzu ya tabbatar da da hankalinsa a kwance yake yanzu ne tashin hankali ya same shi.




" Areef Zaljameel ce ke d'auke da ciki a jikinta kuma nawa?" wata harara Areef ya makawa Jawad,"Jawad keep jokes a part, karka raina mana hankali, ok wato tanan ka b'ullo, cikin kake so kace bana ka bane? To idan ba naka bane na waye? ".




Mik'ewa tsaye Jawad yayi ya fara zagaye parlour," Areef wallahi tallahi bansan maganar da kake yi ba, Zaljameel na dauke da ciki, nace ta zubar, to yaushe ma na mata cikin, ni da ko gado d'aya bamu tab'a had'awa da ita ba "




Shiru yayi yana hawaye ya tafi wajen Areef ya zauna dab dashi," Wallahi Areef bamu tab'a had'a gado da Zaljameel ba, ka yarda dani".




Areef kam ya shiga rud'u dan shima abin ya fara bashi mamaki, anya Jawad bai fara shaye shaye ba? Taya ma za'ai yace bai tab'a saduwa da Zaljameel ba, to cikin jikinta ta ina ya fito? Shine tambayar data addabe shi.




"Jawad ka nutsu ka mini bayani please, kaina ya kulle, ina son na fita daga cikin rud'ani".




A hankali Jawad yabama Areef yarda zaman su da Zaljameel ya kasance, Areef kam banda innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, babu abinda bakinsa ke furta wa, Jawad ya kalla da hawaye ya wankewa fuska yana tunanin waya ma Zaljameel ciki?








Nikam na koma gefe nace kaine mana Jawad 🤣😜.




Areef ya yarda da maganar Jawad, saboda bai tab'a masa k'arya ba a zamansu, nan suka zauna suna tunanin mafita suna zaune Zahra ta dawo daga wajen Zaljameel, bata yima Jawad kallon arxiki ba ta nufi dakinta bayan ta buga masa tsaki.binta yayi da kallo har ta shige.




After 2 weeks


Zaljameel tana samun duk wata kulawa daga Fulani, sai dai har yanzu Mom bata zo ba, hakan kuwa ba k'aramin tada hankalin Zaljameel yayi ba dan tasan Mom bata bayanta.




Zaljameel kullum da hijab kamar wata munafuka haka take yawo.




Kamar kullum zaune take a bed dinta bayan ta tashi daga bacci, dan bata da aiki yanzu sai bacci, kayanta take son d'auka a gidan ta dan wanda ta d'ebo ya k'are, kuma bata son ta aika da kanta take son zuwa, shiri ta fara ta nufi room din Fulani, da sallama ta shiga.




Fulani zaune kuyanga na matsa mata k'afa, jin sallamar Zaljameel yasa suka fita, zama Zaljameel tayi a jikin Fulani ta shagwabe fuska, "Fulani zanje gida na dauka kayana sun k'are,"




Shafa kanta Fulani tayi," Zaljameel ki aika mana ai basai kinje da kanki ba" sake shagwabe fuska tayi, " Fulani ba komai zasu d'auka mini yarda nake so ba, please naje na d'auka da kaina" Ok Zaljameel sai kin dawo, ki bi a hankali kinji "Rungume ta Zaljameel tayi ta bata peck a kumatu ta fita.




Binta Fulani tayi da kallo tana murmushi, Zaljameel na matuk'ar birgeta, tana k'aunar yarinyar,amma Jawad yana nema ya cuceta, itakam banda takai zuciya nesa ai da tuni ta dad'e da tsine ma Jawad.






Zaljameel motar ta ta shiga ta nufi gidan ta, cikin sanyin muryarta tayi sallama, Jawad na kitchen yana had'a coffee yaji sallamar Zaljameel, mamaki bayyane a fuskarsa mai ya kawo ta, bai amsa ya gano ta tana takawa a hankali, tana sand'a ta shige room d'inta.




Wani murmushin mugun ta Jawad yayi ya fito a kitchen d'in ya bi bayan Zaljameel.




Zaljameel ta manta bata rufe k'ofa ba ta nufi wardrobe ta fara d'ibar kayanta tana zubawa a trolley, jin an murd'a handle yasa Zaljameel tsorata, dan bata tunanin da wani a gidan.




Ganin Jawad tayi ya shigo ya maida k' ofar yasa key, yayi crossing hands yana kallon ta.




Tsorata Zaljameel tayi ganin ramar da Jawad yayi, yayi bak'i, sanye yake da singlet sai boxers, sajensa ya cika fuskarsa dan bai samu kwanciyar hankalin yin aski ba, a hankali ya fara takawa zuwa inda take tsaye ita kam tausayinsa yasa ta fara zubar da hawaye.










SUMYNBASH CE💋




🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮




©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L


(We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers)




A romantic love story


2017


July 2017




Story & written by


SUMAYYA SALEES SADEEQ




Kuyi hakuri naji shiru, hakan ya faru ne sanadin wayana daya lalace, har yanxu ma ba gyara ta a kayi ba, amma insha Allah zaku jini.




Ina kuke masoyan Yareema jawad, ina alfahri daku a duk inda kuke,ngd da so da k'aunar ku gare ni. # much love 💋❤😘




Chapter 64&65






Fara ja da baya tayi tana hawaye, har ta bud'e baki zatayi magana taji takai bango tsaida maganar tayi ta cigaba da hawaye. Tuna abinda Zaljameel ta masa yasa ya ja da baya da sauri yana kallonta fuskarsa k'unshe da tsantsar b'acin rai da damuwa, zuba nata narkakkun idanunsa yayi yana mata wani irin kallo da ta kasa fassara shi, maganar Areef ke masa yawo aka, "Matarka Zaljameel na d'auke da cikin ka a jikinta wanda kace ta zubar" rintse ido yayi, a take yanayin Jawad ya chanja, idonsa ya rikid'e yayi ja, sai huci yake, Zaljameel ya nufa gadan gadan ya fincike hijab d'in dake jikinta, yana k'are mata kallo tun daga sama har k'asa, cikin ta ya zubama ido yana nazari, "Zaljameel cikin waye a jikinki?".


Wani kallon rainin hankali Zaljameel ta masa, ta yatsina fuska, "Haba Ya Jawad mai kake nufi da cikin waye a jikina? Ina da mijine bayan kai?".


Cikin zafin nama Jawad ya tamk'i gashin Zaljameel ya rik'e kam yana huci,. Wata k'ara Zaljameel ta saki dan azaba, ta fara k'ok'arin kwatar gashin ta, kuma ja yayi da k'arfi hakan yasa ta saki hannunsa tana hawaye "Please Ya Jawad" Keep quiet Zaljameel, banson jin magana daga bakin ki indai ba ansar tambaya na zaki bani ba.


"Ya Jawad gaskia fa na fad'a maka, please ka cikani".


D'auke fuskarta Jawad yayi da wani kyakyawan mari, dan a yarda zuciyarsa na bushe tofa zai iya zubar da cikin dake jikin Zaljameel amma ya bama zuciyarsa hak'uri, cika kanta yayi ya fita a room d'in amma sai da ya d'auka key ya rufe Zaljameel a ciki. Zama tayi ta zura fuskarta cikin cinyoyinta tana rusar kuka, "Anya bazata fad'a ma Jawad gaskia ba, ganin sa cikin tashin hankali yafi komai d'aga mata tunani, ji tayi an cire key d'in ya shigo, bata d'aga kai ba ta cigaba da kukan ta, cikin sauri ya k'arasa inda take ya fisgo hannun ta ta mik'e tsaye, bai tsaya jiran mai zatace ba ya ja hannun ta suka fice a room d'in.




Zaljameel batayi yunk'urin kwace hannun ta cuz bata da wani kuzari a jikinta suka fita, parking space ya nufa ya d'auka wata golden Prado ya tura Zaljameel a front sit ya dawo ya shiga motor d'in ya fara driving, ganin ya nufi hanyar fita daga masarautar yasa Zaljameel ta tsure, kallonsa tayi idonta da hawaye, tana son tambayarsa inda zasu amma yanayin fuskarsa bai bata dama ba, hakan yasa ta tsuke bakinta ta cigaba da kuka mara sauti. Gudu Jawad yake kamar mai shirin tashi sama, Zaljameel ta gama tsorata da al'amarin Jawad, ta runtse idonta dan a zahirin gaskia bata tunanin zasu je inda yayi niya ba tare da sunyi accident ba.






A dai dai wani babban hospital Jawad yayi parking, sai da ya harari Zaljameel sannan ya fita yaja hannun ta suka nufi ciki. D'aga kanta tayi taga inda suka zo, ganin Jawad & Zaljameel special hospital tayi rubuce a jiki, a razane Zaljameel ta fara k'ok'arin kwace hannun ta dan tasan tabbas Jawad ya shiga da ita hospital d'in asirinta ya tuno kenan. Dakewa tayi dan taga tsoro babu inda zai kaita, cikin d'aga voice ta fara magana "Ya Jawad leave me let me go," ta fara kokawar karb'ar hannun ta. Bata ishi Jawad kallo ba ya nufi office d'insa da ita, doctors da nurses nata gaida Jawad amma bata so yake ba.






Gwaje gwaje yasa wata doctor tayi ma Zaljameel na gane idan tana da pregnant, doctor ladi kam bata ga komai ba, ga results kala wajen 4 tayi printing, cuz Jawad bai yarda da test d'in ba har sai da a kayi sau 4, wani kallon tuhuma ya watsa ma Zaljameel, ji tayi kamar tayi fitsari,ga kunya ta lullub'e ta, tsaki Jawad yaja ya kuma kama hannun Zaljameel suka nufi motor, wata unguwa silient Zaljameel taga ya shiga, duk gidajen dake wajen abin kallo ne, daka gani kasan naira ta zauna, a k'ofar wani katafaren gida yayi parking,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login