Showing 30001 words to 33000 words out of 56602 words

Chapter 11 - YAREEMA JAWAD 1 To end Book Complete Writing by SUMAYYA SALEES SADEEQ -.txt

19 Feb 2025

5155

ina tunanin yana wani abun ne shiyasa kika jishi shiru, amma nasan duk inda yake hankalin sa yana kanki Gimbiya Zaljameel".




Sanyar yar ajiyar zuciya Zaljameel ta sauke ta d'auke phone d'in a kunnenta ta fara k'ok'arin tashi a bed d'in, yatsina fuska tayi jin cikin ta ya murd'a she's feeling hungry, Annah ta kalla!.


"Annah yunwa nake ji" baki Annah ta washe, Gimbiya Zaljameel ai dole kiji yunwa, gaskia kinsha bacci, dubi har rana tayi"


Sake kallon window Zaljameel tayi, rana ta fito ta haske dunia.


"Ai break fast d'inki ya kammala sai ki yi wanka kizo kice"


"To Annah" mik'ewa Zaljameel tayi ta nufi toilet, sai da ta d'au wajen 30mint tana wanka sannan ta fito d'aure da towel a kirjinta, mirror ta nufa ta fara shafa, light make up tayi ta nufi gefen bed d'inta ta duba kayan da Annah ta zab'o mata, wani swiss lace ne, mai tsadar gaske, an mata d'inkin riga da siket, sun kama ta sosai, sun bayyanar da tsantsan kyan Zaljameel, d'auri ta kashe ta d'auki chewing gum mai k'amshin pineapple ta zuba a bakinta ta na tauna a hankali,dining area ta nufa. Nan ma yaji kayan alatu ya tsaru iya tsaruwa.




Tana fitowa kuyangu suka fara bajewa suna gaishe ta, da sakin fuska ta amsa musu! parlour d'in ta k'arema kallo shima ya tsaro, an mishi decoration har yaso ma yayi yawa,ko ina fes sai kamshi dake tashi. murmushi Zaljameel tayi dan tana son taga ko ina tsaf kuma tana son k'amshi.



Kuyanga d'aya taja mata kujera ta zauna cike da k'asaita, d'aya kuma tayi sarving nata abinda take so, bayan ta k'oshi ta nufi parlour ta zauna kuyangun ma suka zauna a k'asa.








Yareema Jawad Zaune a fada gaban mai martaba, sanye yake da wani yadi irin shara sharan nanAsh colour, kansa da hula sumar sa ta kwanta luf, yayi kyau sosai.


"An gaida Yareema mai jiran gado" bai kalli inda suke ba bai kuma ansa ba! ya gaida sarki cikin kulawa mai martaba ya ansa, a hankali ya fara magana irin ta sarakuna.



"Yareema Jawad na kira ka ne dan in sanar da kai ya kamata ka karb'i hospital d'in nan dana sa aka gina maka ka cigaba da kula dashi, dan dama na rabo ka da London dan ka taimaka wa talakawan mu ne".


Mamaki bayyane a fuskarJawad ya kalli sarki!


"ranka ya dad'e dama an gina hospital ne?"


"Eh Yareema nasa an gina hospital ansa masa sunan kai da Zaljameel, J&Z special hospital"


Ji yayi gabansa ya fad'i jin sunan Zaljameel beautiful face d'inta ya bayyana a fuskar sa, wani smile yyi sannan ya gyara zama ya kalli sarki!


" Nagode mai magana, Allah ya k'ara girma da d'aukaka"


"Ameen" Sarki ya amsa, fadawa ma suka amsa.


Tashi yayi bayan sun gama magana da sarki nan da one week zai fara zuwa aikin.




Tafe yake ya nufi part d'insa Bala na biye dashi, phone d'insa da ke hannun Bala ta fara ringing, Bala ya duba yaga Areef, cikin sauri ya d'aga dan kar ya katse, ya mik'awa Jawad, karb'a Yareema yayi ya kara a kunnensa.




"Ango! Ango! Ango na amarya"


Areef ya fara tsokanar Jawad, murmushi Jawad yayi wanda sai da beauty point d'in sa suka lotsa ya fara magana!.


" Areef ya a kayi ne? Ai banyi tunanin zaka kirani yau ba dan nasan ana chan ana kwasar soyayya"


Areef da ke zaune a parlour sa Zahra Rungume a kirjinsa ya k'ara matseta a jikinsa, yana daria," Ha Jawad ai kaima kasan fad'a b'ata baki ne ya Amarya Zaljameel? Sai da Jawad ya d'auke wuta ya saci kallon Bala dan yasan bai maga Zaljameel ba, amma kuma bai san dalilinsa nayin hakan ba.


"Tana lpy"


To ka gaida ta, dama ina son fad'a maka ka shirya zamu je gaisuwar surukai da yamma, "Surukai?"


"E surukai "


" Gaskia Areef baka da hankali, Mom da Dad d'in zanje gaisarwa, gaskia bazan iyaba, sai dai na raka ka mu gaida Alh Zahradden "




" Ok bbu damuwa tunda ka zama dan kanka, su d'au yarsu su baka kace baka zuwa ka gaida su, ka shirya kawai malam dole muje "


Shiru Jawad yayi jin hakan Areef ya kashe wayarsa dan yasan Jawad bazai ce ya yarda ba zashi ba, amma shirunsa ya tabbatar masa daya gamsu.






Alh Zahradden suka fara gaisarwa sannan suka nufi part d'in su Zaljameel.




Mom zaune a parlour ita da Nawal! Nawal nata zuba mata rigima sai an kaita wajen Zaljameel, tana cikin bata hak'uri akan ta bari anjima zata sa akaita, sukaji muryar Jawad! Da gudu Nawal ta nufeshi tana


"Oyoyo Uncle, wallahi sai ka tafi dani gidan ka naga Aunty Zaljameel, sai hawaye"


D'aukarta yyi yana share mata hawaye, "haba Nawal! Indai akan zuwa ne to karki k'ara kuka dake zan tafi"


Peck ta bashi a kumatu "Thanks my Uncle, dats why i love you".


Sauke ta yayi ya nufi cikin parlour dan Areef da sauran Friends d'insu har sun zauna.


Bajewa yayi a k'asa ya gaida Mom kansa a k'asa, kunyar Mom yake ji,bayan sun gaisa suka yi sallama suka tafi, tare da Nawal.




Zaljameel zaune a main parlour d'in gidan tana duba pic d'in biki, sanye take da wani material green colour d'inkin doguwar riga, ta amshi jikinta, high neck aka mata duk boobs d'inta a rabinsa a waje yake, d'auri tayi emergency, jikinta na tashi k'amshi.




Muryar da taji ta nufo parlour yasa numfashinta ya kusa d'aukewa, bata gama tunani ba taji sallamar sa a parlour ya shigo hannun sa rik'e da Nawal,Zumbur tayi ta mik'e tsaye tana kallon bayan Jawad ko zata ga Areef ya shigo, kallo d'aya ya mata ya d'auke kai ya nufi part d'insa, da gudu Nawal ta nufi Zaljameel da tsanin farin ciki, gaba d'aya tunanin Zaljameel ya birkice, to mai Jawad yazo yi part d'in ta,? wata zuciyar tace wajen Areef yazo, Areef d'in da bayana nan ta sake tunani! To ko ai koshi yayi ya d'auka masa wani abu, "Yeah hakane ma, ai ko shi yayi" zuciyarta ta gasgata hakan.


Rungumar da Nawal ta mata ya dawo da ita tunanin ta, nan ta fara murna ta kuma kama hannun Nawal suka shiga ciki dan bata b'ukatar sake had'uwa da Jawad.












SUMYNBASH CE๐Ÿ’‹






๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ


YAREEMAH JAWAD


๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ




ยฉPURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L




A romantic love story
2017




July 2017








Wannan page d'in naki ne maman khady, Allah ya bar k'auna ya kara zumunci ๐Ÿ‘Œ๐Ÿปโค








Ina mik'a gaisuwa ga yan pure moment of life writers, kungiyar da bbu irin ta, Allah ya kara had'a kanmu ya k'ara mana son juna, Allah ya k'ara mana basira ameen. #ana tare๐Ÿ’‹.








Chapter 47&48








Yareema Jawad na shiga room d'insa ya fad'a kan katafaren bed d'insa yana sauke ajiyar zuciya, surar Zaljameel yake hangowa cikin wannan rantsantsan material d'in, komai nata bayyane, boobs dinta daya hango cikin riga sun fi tafia da imaninsa, ni ko nace Jawad daga kallo d'aya,lol.pillow ya jawo ya hugging d'insa tight yana jin wani feelings na shigar sa, how long zai mallaki Zaljameel da gangar jikin ta? Tambayar daya dad'e yana yima kansa amma bbu amsa , a hankali yaji relief hakan yasa ya mik'e a bed d'in ya nufi toilet. Bayan ya fito yaji phone d'in sa na ringing, duba yayi ya ga Fulani, dan haka ya tattaro nutsuwarsa cikin fara'a ya d'aga.


"Fulani barka da yamma"


Murmushi Fulani tayi dan itama burinta ya cika Jawad ya auri Zaljameel, zama take gyara a kujerar ta ta karaga!


"Jawad ina fatan zaka rik'e Zaljameel da amana, tunda kana sonta, kaga Zaljameel yarinya ce ba komai zata maka kace sai ka d'au mata ki ba, nasan ka sarai da d'aukar fansa, matar kace, duk wani responsibility nata yana hannun ka!" Jawad"! Fulani ta sake kiran sa, b'acin ran Zaljameel b'acin raina ne, wallahi kar naji kar na gani "


Gyada kai yayi kamar tana ganinsa,


"Insha Allah Fulani bazaki ji wani abun ba daidai ba "a zuciyar shi kuwa cewa yake haba Fulani, indai ba biyayya kike so nayi ma Zaljameel ba, kyace kar na b'ata mata rai?


" tana ina Zaljameel d'in"


Muryar Fulani ta dawo dashi daga tunanin daya keyi.


Tashin hankali dabar bar cewa yayi ya fara kame kame," Am... Uhmmm dama sun fita ne parlour da Nawal ni ina d'aki amma ki kashe sai in kai mata"


"A'a Jawad basai na kashe ba, kai mata kawai".




Cikin rawar murya ya fara bayani!


"Fulani yanzu na fito a wanka, ina son shiryawa ne sai na kai mata ".




" Ok bbu matsala" ta kashe wayar zuciyar ta fal farin ciki, daga jin yarda Jawad ya amsa mata tana ganin sun samu jituwa da Zaljameel.




Zaljameel zaune ita da Nawal akan sofa suna hira,"Aunty dama zaki iya tafia ki barni? "Ta had'e rai, ta juyama Zaljameel baya, daria Zaljameel keyi," Haba my sweery, ni dake ai bama b'aci, kinsan kullum tunanin ki nake, dama da kaina nace zanje na d'akko ki sai gaki kinzo "


Juyowa Nawal tayi ta kalli Zaljameel,"Aunty ni zaki yima dad'in baki, gaskia ni ban yarda ba" ta cigaba da k'unci.


Zaljameel ce ta fara yi mata chakul kuli, hakan yasa Nawal ta fara daria tana k'ok'arin guduwa, da gudu itama Zaljameel ta bita Nawal ta nufi k'ofa tana k'ok'arin fita sukaji an murd'a handle an turo! Yarda Zaljameel ke gudu ta rasa control hakan yasa taci karo da Jawad, sosai ta fad'a jikinsa tana koma k'ok'arin fad'uwa yayi saurin rik'e ta, "wani yar sukaji a jikinsu hakan yasa Jawad jikinsa ya mutu ya kusa sakinta ta fad'i, sai da ya tattaro nutsuwarsa sannan ya sake ta! Zaljameel tak'i d'aga kai duk a tunaninta Areef ne, jin k'amshin perfume d'in da bazata manta k' amshin sa ba yasa ta d'aga kai ta kalle shi, wani irin zabura tayi ta fara ja da baya, tsayuwarsa ya gyara yayi crossing hands fuskar shi bbu annuri.


Tunawa da Nawal a room d'in yasa Jawad ya kalleta yana smiling," Baby Nawal je parlour akwai ice cream a fridge ki d'auka "


Wani ihun murna Nawal tayi ta fita da gudu.




Cikin tashin hankali Zaljameel ke ja da baya tana nuna Jawad da hannu, ganin ya fara takowa ciki yasa ta fara hawaye, cikin sanyin murya da ba komai zaka ji ba ta fara magana!


" Ya Jawad mai kake yi a gidan nan, dan Allah dan annabi ka fita, kasan fa ni matar abokinka kace, duk da kai dan uwana ne shiga bedroom dina ya haramta a gare ka, komai kake nema kaje sitting room ka zauna gani nan"




Cigaba yayi da binta har ta dangana da bango, hakan ne ya k'ara tashin hankalinta ganin bashi da niyar tsayawa, sai da yazo daf da ita har tana jin saukar numfashinsa, idonta ta runtse tana hawaye, wani irin k'arfine yazo mata ta ture Jawad da k'arfi ta fara k'ok'arin gudu, ji tayi ya rik'e hannun ta hakan yasa ta hassala, dan taga Ya Jawad na neman zubar mata da mutunci, Yanzu idan Areef ya shigo ya tarar dasu a haka mai zaice?.


"Ya Jawad wallahi zan maka ihu idan baka cikani ba"jin sallamar Annah yasa taji dad'i a ranta, takarkare wa tayi da dukkan k'arfinta zata kwalama Annah kira Jawad yayi saurin rufe mata baki da hannunsa, k'ara tsorata tayi shi kuma ganin hakan yasa ya wullata gefen bed d'inta tana k'okarin tashi ta gudu ya k'araso! Cikin lion voice d'insa ya fara magana!


"kar ki kuskura ki tashi, a tunanin ki mai zan miki, mai zanyi dake ballantana jikin ki, Kuma karki k'ara kiran Areef a matsayin mijinki tunda bashi aka aura miki ba, ni Jawad ni aka lik'awa auren ki, ya wani runtse ido alamun takaici ya cigaba!baki da gurbi a zuciyata, Zahra nake so an hanani aka bani ke, dan haka ki daina tunanin akwai abinda zai shiga tsakani na dake"wayarsa ya mik'a mata kin karb'a tayi dan tunda ya fara magana ta daskare a zaune, duk ilahirin jikinta rawa yake, idonta kuma na kallon fuskar Jawad, allahumma ajirni fi musibati, wa yukulufni khairan minha.hawaye ya gagari idonta, dan shima samun damane! Bata k'arasa tunanin ta ba taji muryarsa cikin tsawa "Karb'i mana" hannun ta ya mata nauyi hakan yasa ya d'aura mata wayar a hannun ta, Fulani zata yi magana dake, saura ki fad'a mata abinda zai tada mata hankali, idan haka ya faru Zaljameel! Gyada kai yayi alamun she will suffer.




Zaljameel zaune kamar an dasa ta a wajen, zuciyarta na bugawa da k'arfi, taji phone d'in ta fara ringing, kallon phone d'in tayi amma bata da niyyar d'aga wa hakan ne ya hassala Jawad dake tsaye a kanta, phone d'in ya d'aga ya kuma gaida Fulani, "Jawad baka je wajen Zaljameel d'in bane na jika shiru"


Hannun sa d'aya ya zura a aljihu ya kalli Zaljameel da idonta ke kallonsa har a lokacin, wani killer smile yayi ya cema Fulani, "Gatanan Fulani sai rigima take min wai bazata gaisa dake a phone ba sai dai na kawota"




Murmushin jin dad'i Fulani tayi "A'a banda abin Zaljameel waya ce mata amarya na fita, ta bari dai ta kwana biyu sai ka kawota.




Zaljameel da mamaki da al'ajabin abinda Jawad ya fad'a ma Fulani yasa Zaljameel ta rasa irin tunanin da zata yi, miko mata wayar yayi lokaci guda kuma ya b' ata rai karb'a tayi ta fara k'okarin saisaita nutsuwarta.






Cikin dashewar murya ta gaida Fulani, jin muryarta ta chanja yasa Fulani ta zata ko dan Jawad ya hanata zuwa ne, nasiha ta mata sosai mai ratsa jiki akan tabi Jawad tayi masa biyayya a matsayinsa na mijinta , sannan ta kashe wayar. Sakin wayar Zaljameel tayi a k'asa ta kwanta a bed dinta ta fara kuka mai fidda tsantsan bakin ciki da damuwa, shikenan ta tabbata Jawad mijin ta ne, ita yau ta shiga uku, ina Areef yake? Mai ya hanashi auren ta ya bari aka aura mata wannan mara imanin, keeeeee......... Jawad ya kirata, dagowa tayi ta kalle shi, taso ki bani wayata ko a k'asa kika d'auka.mikewa tayi zaune ya kalle shi tunda ga sama har k'asa ta fara k'okarin mikewa ta sakko k'asa ta tsaya," Ya Jawad ka sani ni ba baiwarka bace, dan an aura maka ni baka sona ni an fad'a maka sonka nake, ban ma son kaine wanda kaddara ta zab' a mini ba sai yau, mai kake ji dashi kud'i ko sarauta, kasan nima a sarautar nake kuma a jinin jikina take yaw......... Bai bari ta k'arasa ba ya d'auke ta da kyakkyawan mari, bata dago kanta ba ya sake d'auke ta da mari.








GANIN HAKA YASA NA KOMA GEFE NIMA NA DAFE NAWA KUMATUN DAN ZALJAMEEL TA MARU๐Ÿ˜ฐ๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ณ๐Ÿ™„๐Ÿค”๐Ÿ˜ญ








SUMYNBASH CE ๐Ÿ’‹






๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ


YAREEMAH JAWAD


๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ




ยฉPURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L




A romantic love story
2017




July 2017




Story & written by


SUMAYYA SALEES SADEEQ






Kuyi hakuri najin na shiru kwana biyu, hakan ya faruwa ne sanadin wani uzuri.






Chapter 49&50




A gigice Zaljameel ta d'aga kanta hannun ta dafe a kumatun ta, hawaye ne masu zafi suka fara zarya a fuskarta, tunda take bata tab'a ganin anyi mari a gaban ta, amma yau ita aka mara, kuma ba Mom ba ba Dad ba, Jawad wanda Mom d'in ta ta bata labarin irin k'aunar da yake mata.


Cikin dauriya Zaljameel tace, "Marina fa kayi Ya Jawad?"


A hassale ya kalle ta," An mare ki d'in, ko zaki rama ne? "ya cigaba da magana.


Keeeeee.... Zaljameel kike ko wa? Daga rana irin ta yau karki kurkura ki sake gangancin fad'an magana, wanda ya fiki ma yayi kad'an ballantana ke da wata hausar ta kamar an mata dole sai tayi, yana kaiwa nan ya ja tsaki ya fice a d'akin ransa a mugun b'ace.




Fad'awa bed d'in ta tayi ta fashe da wani irin kuka na ban tausayi, mai yasa parent d'in ta suka mata haka, wane irin laifi ta musu da suka hanata Areef suka d'aura mata aure da Jawad ? mai yasa Anna tayi mata k'arya?.


Duk tambayo yin nan Zaljameel ta rasa ansar su, hakan yasa ta tashi ta nufi parlour inda taji muryar Anna da Nawal.






Yareema Jawad na shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login