Showing 24001 words to 27000 words out of 56602 words

Chapter 9 - YAREEMA JAWAD 1 To end Book Complete Writing by SUMAYYA SALEES SADEEQ -.txt

19 Feb 2025

5148

sanin zabarta ba a matsayin matar aure? Mai ma zata d'aukesa mai magana biyu? Yace bazai aure taba amma yanzu ya nemeta akan ta auresa, lallai dole ya k'ara kama mutuncinsa dan kar Zahra ta kawo masa raini.wucewa yayi cikin room d'in ya zauna sai wani yatsina yake yi.




Zama tayi a gefensa yana kallonsa kamar zata cinye shi dan so, k'aramin tsaki yaja ya fara magana.


"As u know, zamu wuce Nigeria, kuma a gidan mu zamu sauka, kin san ko ni waye, jinin sarauta ne, masarautar mu bbu masu d'abia irin taki, dole ki koyi sa manyan kaya, dan bazaki dinga mana shigar da kika ga dama ba a chan, ina gargadin ki da rawar kai da fadi ba'a tambaye ki ba, yana zuwa dai dai nan ya kalli Zahra, ganin ta yayi ta zuba tagumi hannu biyu tana sauraransa, sosai taso bashi daria amma ya basar.


Mikewa tsaye yayi y kalleta, "Zahra"


"Na'am my dear Jawad" ta amsa tana murmushi, dan ita Jawad duk abinda zai mata zata jure matuk'ar zai aureta.


" Ki shirya zamuje shopping na dogayen riguna da after dress," dam gaban Zahra ya fad'i, wai dama Yareema Jawad da gaske yake yi ita zata iya cewa tunda tazo dunia bata tab'a sa doguwar riga ta mutunci ba ballantana after dress. Ita ai sun mata nauyi ina zata kaisu.




Katse mata zancen zucinta yayi, "Kinji mai nace ai, and gobe zamu wuce Nigeria, ya kamata ki zubar da duk wani iskancin ki a Egypt, dan wallahi idan mukaje kika jamin magana, gyad'a kai yayi alamar zata san sauran kenan yayi gaba.




Dabas Zahra ta zauna a kasan carpet, lallai ta d'auko ruwan dafa kanta, bbu komai zata jure tunda tana sonsa, tashi tayi ta nufi toilet.




Yareema Jawad yayi handing over da company, washe gari suka dauki hanyar Nigeria.




Already yayi waya ya kuma sanar dasu tare da matar da zai aura yake, an shirya komai akan tsari an kuma tura fadawa tarar su.




Jirgin safe suka biyo dan haka 11pm suna airport, ba tare da b'ata lokaci ba aka d'aukesu sai fad'a.
Zahra gaba d'aya ta rud'e, duk yarda take jin labarin gidan sarauta da yarda akema mutun biyayya kamar za'a lashi k'afarsa, sosai kan Zahra ya fara rawa dan dama abin nema ya samu, Yareema Jawad tun a mota ya lura da Zahra ta fara zubar da fad'an daya mata, gashi ba damar magana saboda fadawa.




A part d'in Fulani aka sauke Zahra, da kyar ta yarda zata zauna wai Yareema Jawad zata bi part d'insa, wani kallo ya mata tuni Zahra ta shiga taitayinta ta bi fadawan.




D'aki guda aka bama Zahra da kuyangu masu kula da ita, jin kanta take so high, dama haka sarauta take? Komai sai dai a maka, kai ita dai taji dad'in had'uwa da Jawad.




Sai da ta huta sannan aka kaita wajen Fulani. Fulani kam yak'e kawai take yi da hausawa sukace yafi kuka ciwo,gaskia Jawad ya gama bata kunya, bata tab'a tunanin haka zata ga Zahra ba, a tunanin ta zata fi Zaljameel komai da komai, sai gashi abin haushi tarbiyar kwarai ma Zahra bata dashi dan akan kujera ta zauna ta gaida Fulani.






Bala bakinsa yaki rufuwa saboda dawo war Jawad, kitchen ya shiga ya dafa masa favorite food d'insa, Yareema Jawad kam yaji dad'in tarbar da Bala ya masa, cikin sakin fuska suka gaisa, "Yallabai ya madam ance da ita kuka taho?" eh yace ya fad'a toilet.




Fes ya shirya cikin wani farin yadi mai tsadar gaske, ya gyara sumar kansa, kamshi mai dad'i ke tashi a jikinsa, man's pride d'insa ya shafa wanda ya k'ara ma fuskarsa kyau, wani k'ayattacen murmushi yayi jin zuciyarsa yake fes bashi da matsala dan ya dawo kusa da abar kaunarsa Zaljameel, burinsa bai wuce ya ganta ba. Fitowa yayi ya nufi part d'in Fulani.






Zaljameel kwance tayi pillow da cinyar Annah, a wani babban garden, ita da Anna da kuyangun nan guda biyu, tun daga ranar da suka je gidansu Areef Fulani tace su cigaba da kula da ita. Labaran daria Annah ke bata Zaljameel kam daria take bbu saurarawa,fuskarta tana kallon bakin Annah kamar zata fad'a ciki dan dama Zaljameel akwai san labari, sosai take jin dad'in zama da Annah dan yarda suke da ita ta dauke ta kamar granny d'in ta.






Yareema Jawad tafe cikin kasaitarsa kamar bazai taka k'asa ba, kuyangu da bayin sarki nata kwasar gaisuwa yana basar wa, wucewa yazo yi ta dai dai garden d'in, kamshin perfume d'in daya ji ya d'auki hankalinsa zuwa wajen, sanyayyar ajiyar zucia ya sauke yana godia ga Allah daya sa yaganta a lokacin da idanunsa ke buk'atar kallonta, da yake garden d'in babba ne sai ya shiga ya zauna chan nesa dasu, ganin yarda Zaljameel ke daria ya daure masa kai, gashi yaji tana dabura hausa, abin ya bashimamaki, waye yayi kokarin ko yawa Zaljameel hausa? Gaskia ko waye yayi kokari.




Ya shagala sosai da kallon Zaljameel, gani yayi ta Mike zaune an miko mata wayarta, cikin zumud'i da fara'a ta d'auka, jiyay wani mashi ya soki gefen zuciyarta, ranshi gaba d'aya ya baci, wani kishine ya tokare masa kirji, cikin sauri ya tashi zai bar wajen yaji an rike masa riga, da sauri ya juyo, "Uncle Wana kama, wato dan kaji ance ina neman ka shiyasa ka gudu garden ko? Hannun ta ya kama suka fara tafia dan shi bai da burin daya wuce ya bar garden d'in kan zuciyarsa ta tarwatse.




Part d'in Fulani ya nufa, a dakin ta ya sameta abin dunia ya isheta, daga ganin Zahra yar dunia, idonta a bud'e yake, bata dace da Jawad ba, ita dai batasan mai ya gani ba a tare da ita.




Bayan ya gaida Fulani bai samu wata fuska da zaiyi hira da ita ba, dan bala'in haushinsa take ji, haka ya tashi jiki bbu kwari ya nufi part d'in Mom dan yasan ita kad'ai zata faranta masa.






Tafe suke shi da Nawal suna hira, yakusa part d'in Mom ya gano abinda zai iya sawa zuciyarsa ta daina aiki, Areef tare da Zaljameel a jikin mota, sai hira suke cikin annashuwa da jin dad'i, tsayawa yyi chak daya tuna wani abu, phone d'insa ya d'auka ya fara neman layin Zahra, bugu d'aya ta d'auka, "hello baby"
"ki fito ina waje, kuma na fad'a miki ki ajiye duk wata rawar kanki, wallahi Zahra zan iya fasa aurenki"bakinta na rawa ta fara bashi hakuri, katse wayar yayi ya tsaya jiran Zahra.


Cikin rangwada da karairaya Zahra ta tunkaro inda Jawad yake, yana yin fuskarsa ya chanja ya fara fara'a, jerawa sukayi suka nufi wajen, kai kace arziki suke da Zahra, sai wani kallonta yake yi, baki ta saki tana kallon ikon Allah, a haka suka k'arasa har inda su Areef suke.


Basu san da zuwansa ba suna ta hira, hakane ya k'ara kular dashi, amma ya basar.


"Sannan ku romeo and Joliet" , tare suka d'ago kai suka kalli Jawad, Zaljameel ji tayi zuciyarta bugun ta ya k'aru, kallon Zahra tayi daga sama har k'asa, ganin yarda ta tsaya kusa da Jawad kamar zata rungumesa, ji tayi haushinta ya kamata, wannan kuma wacece mai matsayin tsayuwa kusa da Yareeman da bbu irinsa?














SUMYNBASH CE💋




🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮




©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L




A romantic love story
2017




July 2017






Story & written by
SUMAYYA SALEES SADEEQ






Wannan page d'in naku ne


SUMYNBASH NOVELS
NOVELLAS LODGE
AUNTY AND SADDY NOVELS
P.M.L WRITERS FANS
ZEE AND HUSSY NOVELS
FUTHUHATUL KHAIR 1
FUTHUHATUL KHAIR
HOME OF HAUSA NOVELS
HAFSAT MUSA NOVELS (INDON KAUYE)
MACEN GABAN GOSHI




BARI IN DAKATA HAKA DAN KUNA DA YAWA AND I LUV YOU ALL ❤😍




Chapter






41&42






D'auke kai Zaljameel tayi sakamakon had'a idon da sukayi da Jawad, wani kallo ya watsa mata wanda bazata ta iya fassara abinda yake nufi ba, gaba d'aya jikinta yayi sanyi, cikin sanyin muryarta ta gaida Jawad.


"Ya Jawad ina yini? Fatan ka dawo lpy?"


Ba tare daya kalleta ba ya amsa a dak'ile,
"lpy "




Areef ya bud'e baki zaiyi magana Jawad ya d'aga masa hannu "stop it"


Ya kalli Areef, kasaitarsa gaba d'aya ta tashi, ya koma Yareema Jawad d'in sa.


"Meet me in part, kasan I don't want to talk in front of kids " ya kalli Zaljameel yana yatsina fuska.




Wucewa yayi yabar su a tsaye a wajen, Zahra kam da, kishin Zaljameel ya hanata kata b'us tabi shi suka jera, jinta take so high, lallai Jawad yana santa, ji yarda ya tsalama zankad'ed'eyar budurwa rashin mutinci, ita kam taji dad'i abinda yama Zaljameel, dan da har kishin yarinyar ya shiga ranta, dan Zaljameel takai ayi kishi da ita, saboda ta had'u ta ko ina.




Tunda suka tafi Jawad bai k'ara kallon Zahra ba har suka shiga part d'in Mom.


Annah zaune a k'asan carpet suna hira da Mom, sallamar Jawad ta katse su, cikin farin ciki da zumud'i Annah ta mik'e tsaye tana washe baki a nitse ya shigo parlour, bayan ya tattara duk wata shagwabarsa, yana shiga ya nufi cinyar Mom da itama fara'ar take masa.




Zama yayi kusa da ita ya d'aura kansa a cinyarta, fuskar sa kamar zaiyi kuka ya fara magana.


"Mom bakya missing d'ina ko? Duba yarda wuya ta maidani a Egypt, duk na rame nayi bak'i, amma Mom kalli yarda kikayi k'iba, ni wallahi keda Fulani kun daina sona"


Ya k'arashe maganar fuskarsa d'auke da damuwa.


" Baiwar Allah shigo mana" Annah ta bawa Zahra dama.


Zahra kam mamaki ya gama cikata, dama haka Jawad ya iya magana ga kuma shagwaba kamar baby.


Shigowa tayi parlour ta zauna tana k'are ma parlour kallo, gaskia akwai arziki a gidan nan, ji yarda suke decoration kamar bada kud'i suka siya ba, ta saba ganin manyan gidaje, masarautar su Jawad tasha kanta.




Sai da Annah tama Zahra iso sannan Jawad ya tuna da ita, Mom sai shafa gashin kansa take yi, idonsa a lumshe ya fara magana


"Mom ga Zahra, itace my 2 be d'in" , ya fad'a yana murmushi.


"Kai masha Allah, ok ashe itace wacce ta tafar mini da zuciyar Yareema, gaskia Zahra kina da babbar sa'a, samun dan sarki Yareema Jawad"


Wani killer smile Jawad yayi ya shafa man's pride d'in shi.


Sai a lokacin Zahra ta gaida Mom, itama a kujera ta hard'e ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya.


Cikin kulawa Mom ta amsa, "Zahra kinzo lpy? Lpy lau Mom," ta fad'a kamar yarda taji Yareema ya fad'a.




Duk da Annah bata jin turanci amma taji labarin Yareema yak'i auren Zaljameel cuz yana da wacce sukayi alkawarin aure da ita, indai ko wannan ce ita bata ga abin so a tare da itaba,dan kuwa Zaljameel ta fita komai.




Yan matan nan biyu Mom ta basu umarnin kawo wa Zahra abin tab'awa, da hanzari suka nufi kitchen.




" Yallabai uban gidana ina mik'o gaisuwa"


Jin muryar Annah yasa Jawad mik'ewa da sauri, ganin ta yasa ya saki wani smile da yake k'ara masa kyau, "Annah" ya fad'a yana kallonta.
"Na'am Jawad kazo lpy?" Annah fushi nake dake, Annah ai nazata kin manta sunana ma, Annah bakya nemana, ko a waya ai kya ara ki buga mini mugaisa ballantana gaki a kusa da Mom d'ina "


Ya k'arashe maganar yana wani b'ata rai.


" Tuba nake Yareema Jawad, Allah ya huci zuciyar maza, wallahi kana raina ko yaushe, ya za'ai na manta ka Jawad, ai har a gidanka sai na zauna, yarda na rene ka haka zan raini d'anka idan Allah ya ara mini rai da lpy"




Wani kallo Zahra ta watsa wa Annah mai kice da tsana, wannan tsohowar ce zata raini d'an da zata haifa, Allah ya kiyaye, ji tayi har ta tsani Annah, ai ita masu renon ya'yanta a London zata samo su, turawa take bukata.


Sosai Jawad yaji dad'in maganar Annah, cikin jin dad'i ya amsa da


" Allah ya nuna mana Annah "Ameen Annah ta amsa.






Zaljameel gaba d'aya hirar tasu da Areef tak'i mata dad'i, lura da hakan yasa Areef ya mata sallama ya nufi part d'in Jawad dan jiranshi yana son sanin wacece wacce suke tare da ita, ko Jawad ya fara harkar bariiki ne, banda haka har ya kawo Zahra cikin gidan nan, bayan duk wanda ya kalleta yasan yar dunia ce, gaba d'aya ransa a b'ace yake, ga kuma wulakancin da yama Zaljameel.






Mik'ewa Jawad yayi yama Mom sallama suka tafi.




A gurguje please




Wasa wasa lokaci tafia yake yi, yayin da aka fara shirye shiryen biki, Dad d'in Zaljameel shi yayi ja ragamar bikin ya kuma sanar da Zahradden mahaifin Zahra, shima kam like father like daughter haka suke da Zahra, duk wani yanayi na dan duniar mutum ya bayyana a tare da baban Zahra, dama ance barewa bazata yi gudu ba d'anta yayi rarrafe.




Wai ina sarki mai mirabus sarki Abubakar. Tunda Jawad ya sanar dasu bazai auri Zaljameel ba wani abu ya tokarema grandfa a zuciya, gaba d'aya ya rasa sukuni, ko Aliyu da farouq ya daina sakar musu, ganin sun goyi da bayan ya'yansu zasu basu wanda suke so, sosai ya hango alheri a auren Jawad da Zaljameel,amma Allah bai nufa ba.Ganin yarda ake shirye shiryen bikin yasa sarki Abubakar ya fara rashin lpy, gaba d'aya hankalin families d'in ya tashi, aka nufi hospital dashi, cikin gaggawa da sanin matsayinsa aka kwantar dashi a emergency, likitoci biyar tsaye a kansa, a gadon asibitin ya fara aman jini, sosai suka bashi taimakon gaggawa suka masa injection for sleeping, dan gaskia he have to rest, cuz akwai damuwa a ransa, wanda yay cussing masa heart attack. Cikin dare abin ya faru hakane yasa Yareema Jawad baima san an tafi da grandfa hospital ba.


Kwance suke shi da Areef a bed d'aya, dan tunda aka fara maganar auren su ya dawo gidan dan su shirya komai akan tsari. Yareema Jawad ya tafi duniar mafarkin Zaljameel wanda ya zame masa jiki kullum sai yayi.




Zaune suke a wani babban garden suna hirar su ta soyayya, Zaljameel sanye da wani wedding gown red colour, tayi kyau sosai, kanta bbu veil sai dai gashin ta yasha gyara sai shining yake yi, zaune take a cinyarsa suna tazuba hannayenta a kafad'arsa, gaba d'aya sun kafama juna ido cik'e da so da k'auna, bakinsa yakai kan nata ya fara romancing dinta cikin kwarewa, sauri tayi ta kwace kanta ta tashi a cinyarsa tana ja da baya, tashi yyi shima wahale dan romance d'in bai ishe shi ba, tafia take da baya da baya tana d'aga masa hannu, cikin azama ya fara binta da gudu,"Zaljameel please ki tsaya don't go, you know I love you, can't do without you Zaljameel, dan Allah ki tsaya, u mean alot to me, yanzu aure xakiyi ki barni, wallahi Zaljameel zuciyata dab take da bugawa, na tabbata duk ranar da aka d'aura miki aure ranar numfashina zai tsaya".


Bata tsaya ba saima b'ace masa daya ga tayi cikin razana ya fara kiran sunan ta da karfi, "Zaljameel................... Zaljameel....fashewa yayi da wani kuka mai cin zuciyar maiysaurare.


Areef dake kwance a gefen Jawad tuni ya farka jin maganganun da yake yi, ganin he is dreaming yasa hankalin Areef ya kuma tashi." Zaljameel? Dama Jawad yana son Zaljameel kamar haka, zama Areef yayi ya fara hawayen tausayin Jawad, shegen girman kai da izzarsa suna so su kaishi ga barin dunia, daga yarda yaji mafarkin da Jawad yake yi yasan ba k'aramin so yakema Zaljameel ba, dan shi zai iya cewa bai tab'a mafarkin Zaljameel suna soyayya ba sai dai suna sex, hakan yasa ya gane har yanzu sha'awar Zaljameel yake yi ba sonta ba idan kuma ya aureta baima Jawad adalci ba, ita kanta Zaljameel tunda Jawad ya dawo ya rasa walwalarta, ya kuma lura da chanjin yanayin ta, ta daina bashi wata kulawa and ya lura akwai damuwa a ranta, shi kuwa ko shed'an ne ya kamata ya cece zuciyoyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login