Showing 18001 words to 21000 words out of 56602 words

Chapter 7 - YAREEMA JAWAD 1 To end Book Complete Writing by SUMAYYA SALEES SADEEQ -.txt

19 Feb 2025

5152










"Da sallama bala ya shiga d'akin, yareema jawad bai amsa masa ba dan haka ya nufi toilet dan had'a masa ruwan wanka, bayan ya kammala ya sanar dashi,still yareema jawad bai amsa masa ba dan bayasan magana mikewa ya yi ya nufi bathroom d'in. As usual Bala ya d'aukowa yareema jawad kayansa ya ajiye gefen bed ya nufi kitchen dan had'o abinci.






" Yareema jawad, shirye yake cikin English wears, blue jeans and orange shirt, kansa d'auke da P cap ya bala'in yin kyau, watch d'in dake d'aure a wrist d'insa ya duba, bedside ya nufa ya d'auki phone d'insa da key d'in mota ya nufi parlour, cin karo sukayi da Bala hannunsa d'auke da tray, murmushi Bala ya k'irk'iro "yallabai ga abincin" a yatsine jawad ya kalli tray d'in a hankali ya furta" bana ci Bala"yayi gaba abinsa, Bala kam binsa yyi da ido har ya fita daga parlour d'in.






Fulani maryam ma kam ta tsorata amma ta basar, sosai hankalinta ya karkata ga jawad dan fitar da yayi tasan ya fusata ne, sai dai tasan tunda areef yabi bayansa komai xanxo da sauk'i. Zaljameel kam jitayi kunya ta kamata, cikin ladabi ta durk'usa har k'asa ta gaida Fulani maryam, da fara'a ta amsa mata ta kuma tambayeta jiki, zaljameel jitayi xaman parlour ya isheta dan haka ta nufi bedroom d'inta, sosai ta shiga dana sanin ihun da tayi duk kuwa da cewa ba tana sane bane tsorata tayi, fitar yareema jawad a fusace ta shiga tunawa, omg tasan ihun ne ya b'ata masa rai. Kwanciya tayi a bed d'inta tana kallon ceiling, a hankali bacci yyi awon gaba da ita duk da uwar yunwar da takeji sai taji ta koshi.






Mom da Ammi xaune a parlour suna hirar yaushe gamo, amma hankalin Ammi ya karkata ga jawad, tasan sa da mugun xucia, tasan yana chan yana fushi, a daddafe suka kammala hirar Fulani ta nufi part d'inta da kuyangunta. Aikawa tayi a kira Mata jawad, dan aiken ya dawo da bayanin jawad bayanan, hankalinta ya kuma tashi dan haka ta d'auki phone d'inta ta fara neman layinsa, wayar ya shiga sai dai baiyi picking ba hakane ya k'ara tashin hankalin fulani.








Yareema jawad a wani katafaren garden, wanda yaji kayan fruits da korayen bishiyu, xaune yake a k'asa kan grass carpet, iska mai sanyi da dad'in k'amshi na kad'awa, sosai yaji dad'in xamansa a wajen jiyay duk bak'in cikin dake ransa ya yaye, nishad'i yakeyi. Sai daf da magrib ya bar garden d'in ya nufi wani babban mall, a lokacin ya tuna da phone d'inshi daya bari a car d'in, dan haka da sauri ya d'auka ya duba, 50 missed calls ya gani a raxane ya danna dan ganin waye, Ammi ya fad'a a bayyane, gaba d'aya hankalinsa ya tashi, xuciarsa ta damu tasan abinda ke faruwa Ammi ta masa wannan missed calls d'in , juya kan motar yyi dan bayajin xai iya xuwa mall d'in.






Wani wawan gudu yakeyi a titin burinsa ya ganshi a gida, yana isa gida kam part d'in Ammi ya nufa, tun daga parlour ya fara kwala mata kira, Ammi! Ammi! Ammi, sauri tayi ta mik'e ta nufi parlour jin muryar jawad, dama xaune take ta buga uban tagumi tana tunanin inda jawad ya shiga da yakasa d'aga kiranta. Tana fitowa ta rungumeshi, had'e da sauke ajiyar xucia, kuyangunta kam tuni sukayi waje dan basu guri, breaking hug d'in yareema jawad ya yi ya kama hannunta suka xauna a 2cter dake parlour n."Ammi na mai yake faruwa naga missed calls d'inki da yawa?" Kallon sa Ammi tayi bata gano b'acin rai a tare dashi ba sai damuwa, hakane yasa ta gane ya sakko daga fushin da yayi. Murmushi tayi "bbu komai jawad kawai na aika a kira mini kai akace baka nan, shiyasa na nemeka naji a ina kake" murmushi yyi had'e da kama hannunta "my Ammi ki daina d'aga hankalin ki haka, I'm not a small boy, kuma na manta phone d'ina a mota that's why banga call d'inki akan lokaci ba" ok my jawad, please ka dinga yayyafawa xuciarka ruwan sanyi, ka rage saurin fushi bashi da amfani kaji"gyad'a kai yyi, ya gane inda maganarta ta dosa amma ya share. Watch d'insa ya duba jin kiran sallah magrib, dan haka ya mik'e yayi ma Ammi sallama ya nufi masjid.






After two weeks






"Yareema jawad yayi tafia xuwa Egypt dad d'insa ya turashi ganin lapiar company d'in su dake chan. Areef kam ya samu damar xuwa gidan dan samun had'uwa da zaljameel, yau ma kamar kullum, tafe yake cikin motarsa sanye yake da manyan kaya, shadda milk colour kansa bbu hula k'amshi mai dad'i ke tashi a jikinsa, driving yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, wani wani Bash Bakery ya shiga ya siyo snacks da ice cream, tsarabar nawal ce dan yasan tana san ice cream and yaga yanayin shakuwarsu da zaljameel. Direct part d'in su zaljameel areef ya nufa, xaune suke a bakin swimming pool suna wasa da ruwa, "nawal inasan na iya hausa gashi kema naga baki iya sosai ba ballantana ki koyamin" daria nawal tayi "wallahi kam my aunt, nima ba iyawa nayi sosai ba sai dai na fiki" daria suka saka, "ok haka kikace ko?" yeah" nawal ta fad'a," gashi uncle jawad bayanan daya koya miki "shiru zaljameel tayi jin sunan jawad, ok dama guy d'in nan baya nan, ai naxata fushi yayi shi yasa naga ko wajen mom baya xuwa." Assalamu alaikum "sallamar areef ta katse musu hira, da gudu nawal ta mik'e ta nufe shi tana murna, uncle areef oyoyo, ledar hannunsa ya saki a k'asa d'aga ta yyi chak yana daria." Nawal yan mata, kin girma sosai "daria tayi" haba uncle dubani fa "hancinta areef yaja ya sauke ta, hankalinsa ya karkata ga zaljameel da duk ta dururuce, sanye take da English waers riga mara hannu sai igiya da ake d'aurewa a wuya rigar iya gwiwa ce, sai tree guater pencils gaba d'ayansu pink colour ne, a kame suke a jikinta,gashinta xube a gadon bayanta. Wani mugun yawu areef ya had'iya, zaljameel ta gama tafia da imaninsa, jiyay sha'awarta ta kamashi, areef kam dama bbu dama a wannan fannin, sai dai ko jawad bai san yana harkalla da mata ba, sirrinsa ne shi kad'ai.




















Sumyn Bash ce💋




🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮










Pure moment of life writers


p. m. l. w








A romantic love story
2017












July 2017










Story & written by


SUMAYYA SALEES SADEEQ












Nan gani nan bari, Idan kaji wane ba banza, ina kuke yan'uwa yan PURE MOMENT OF LIFE WRITERS, yabon gwani ya xama dole, gaskia tsarin ku dana novel din ku abin birgewa ne, Allah ya kara kaifin basira ya kuma kara had'a kanmu ameen, much love sister ❤












Chapter 29&30














"Gaba d'aya ya zuba mata idanu, a hankali ta mik'a hannun ta inda ta ajiye k'aramin mayafin data fito dashi, kafin takai areef ya rigata ya kai hannunsa ita ma takai, wani irin shock taji jin haduwar hannunsu, da sauri ta saki veil d'in, wani killer smile areef yyi sannan ya d'auki veil d'in, matsowa yyi dab da zaljameel ya durkusa a gabanta, tuni kirjinta ya hau dukan uku uku, d'aga idonta tayi tana dube-dibe cikin fad'uwar gaba, ganin bbu nawal a wajen ya k'ara tashin hankalin ta, murmushi areef yyi ya yafa mata veil d'in a kanta , jin hakan yasa ranta ya d'anyi sanyi, zama yyi a inda take xaune ya zura k'afafunsa a cikin swimming pool d'in,cikin mamaki ta d'aga ido ta kalleshi, idonsu ne ya had'u dan dama beautiful face d'in ta yake kallo, wani shu'umin murmushi yyi a hankali cikin salonsa na yaudara ya furta "zaljameel"bata juyo ba ta cigaba da wasa da zara-zaran yatsunta," oh ni zaljameel na shiga uku, waye wannan yake k'ok'arin shiga rayuwata, gashi dai handsome, sai dai ya jawad ya fishi kyau "my aunt nawal ta nufo wajen da gudu, sanyin dad'i zaljameel taji dan haka da sauri ta samu kwarin gwiwar mikewa tsaye, cikin sassarfa ta bar wajen tana mai jin kunyar ganin da areef ya mata.








" Nawal binta tayi da kallo, juyowa tayi ga areef, "uncle dan Allah ka koyama aunt zaljameel hausa, tace tana son ta iya gashi uncle jawad baya nan da ya koya mata" Murmushi areef yayi dan ya samu damar shiga rayuwar zaljameel, hannun nawal ya kama suka fara tafia, "baby nawal kice mata zan koya mata, kuma gobe zamu fara" wani tsallen murna nawal tayi ta rungume areef," thanks uncle areef, Allah ya biyaka "bbu komai nawal ai mun zama d'aya, sai da suka k'araso part d'in su zaljameel ya cika hannunta," kije gida nawal zamu had'u gobe, ki gaida mom kinji "ok uncle areef zata ji,da gudu ta shige part d'in.










" Jawad zaune a office d'insa na cikin company, files ne masu yawa a gabansa, da kagansa kasan aikin yasha kansa, cikin nuna gajia ya ajiye wani file, kansa ya dafe dayaji yana sara masa, watch ya duba 9:55pm,tsaki yaja ganin dare yyi, tun 7:00am yake wajen yana fama da files, gaskia banda maimartaba bbu mai bashi wannan aikin yayi. Cikin nitsuwa ya fara tattara abinda xai tafi dashi hotel din daya kama, motar company ce ta kaishi har hotel din.






"Zaune yake cikin shirin bacci, laptop a gabansa yana typing, green tea din daya had'a yake sha, tunanin zaljameel ya fad'o masa, tsaki yaja dan tana d'aya daga cikin abinda yasa yake jin dad'in zama a Egypt dan ko fuskarta bayasan gani, yana gama tunanin sa ya buga wani tsakin, jiyay ransa ya baci dan haka ya tattara ya kashe laptop din ya nufi bed.






"Tunda nawal ta bawa zaljameel labarin koya mata hausa da areef zaiyi taji abin bai kwanta mata ba, ita dai tafisan ya jawad ya koya mata, and waye wannan din daya keson shiga rayuwar ta, "nawal wanene areef?" daria nawal tayi ta d'ane cinyar zaljameel "my aunt areef frnd din uncle jawad ne kuma amininsa tun suna yara, uncle jawad ya yarda dashi sosai kowa a masarautar nan ya San areef, mai martaba sarki mai murabus yana ji dashi"ni kaina uncle areef yana birgeni, saboda yarda ya iya zama da uncle jawad, kin sansa da saurin fushi ga izza, bbu mai iya zama dashi sai areef d'in, fulani ma naji dashi, dan ita duk mai san jawad mai kuma kula dashi to fa tana sansa shima,kinji matsayin areef a gidan nan.








Ajiyar zuciya zaljameel tayi, sai ynx hankalinta ya kwanta kuma sai ynx ta fara murna za'a koya mata hausa, rungume nawal tayi," thanks my proudly sister, I luv u so much"love u 2 "nawal ta fad'a tana murmushi.










Areef zaune a parlour d'in mom yana jiran fitowar zaljameel, sanye yake cikin kananun kaya, sun karb'i jikin sa, zaljameel tafe cikin tafiar ta mai daukar hankali, da sallama ta shigo parlour, jin muryarta ta daki kunnensa ya sashi d'agowa bbu shiri, "wow" ya fad'a a zuciyarsa, sanye take cikin Arabian gown blue black an mata ratsin pink colour, pink veil tayi rolling kanta dashi, flat shoe ne a kafarta, k'amshi mai dad'i ke tashi a jikinta, a hankali ta k'araso har inda yake zaune ta zauna a gefen kujerar dake kusa dashi, areef kam baisan da k'araso war zaljameel kusa dashi ba"gud afternoon "zaljameel ta gaida areef, firgigit yayi ya dawo daga duniar tunanin daya tafi, murmushi ya k'akaro sannan ya amsa mata. Bayan sun gaisa areef ya fara koyawa zaljameel hausa cikin kwarewa, tun daga( a e i o u) sosai zaljameel ke ganewa and tana jin dad'in karatun, a cikin 2 weeks zaljameel ta iya hausa sai dai idan tanayi daria take bawa mutane har mom, duk da ana gane abinda take fad'a, sosai mom taji dad'in yarda areef ya koyama zaljameel yarenta, gaskia yyi namijin k'ok'ari, wani irin shakuwa ya shiga shakanin areef da zaljameel, indai areef baizo ba zaljameel bata jin dad'i, yana bata duk wani lokacinsa dan kula da ita, shi kansa areef ynx ya rasa mai yake masa dad'i, a da kam san daya kema zaljameel yana tattare ne da kyan fuskarta da jikinta, amma ynx kam soyayyarta yakeji har cikin ransa, kuma aurenta yake buk'ata.








"Yareema jawad na Egypt duk da ya kammala aikin da mai martaba ya turashi amma baya jin xai dawo a wannan lokacin, dan Nigeria tafita a kansa, dama ba'a san ransa ya dawo ba.










"Soyayya mai karfi ta shiga tsakanin zaljameel da areef, wanda tun sunayi a boye har ta fara fita fili, nawal dama ita tasan komai dan da ita zaljameel ke shawara, mom ma ta lura da hakan amma bata nuna farincikin ta ba dan ita ta da zaljameel zata bi tsarinta da sai tace ta mata miji.














SUMYN BASH CE💋






🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮












Pure moment of life writers




P. m. l. w










A romantic love story
2017










July 2017










Story & written by
SUMAYYA SALEES SADEEQ










I dedicated dis page 2 u Sumyn Bash novels group thanks for your love and support. Ilysm












Chapter 31&32












Zaljameel xaune a parlour, sanye take cikin top and jeans, gashin kanta baje a bayanta, light make up tayi, hannun ta dauke da jotter tana duba karatun da areef ya mata, taunar chewing gum take ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya, mom xaune a gefenta tana watching film, Nawal ta tafi part d'in fulani, phone d'in Zaljameel ya fara ringing, cikin zumud'i ta d'auka wani k'ayattacen murmushi tayi sannan tayi picking call d'in. Kallonta Mom tayi tana nazarin farin cikin daya ziyarci babyn tata.






Cikin muryarta mai dad'i ta masa sallama, sai da ya lumshe idonsa ya bud'e a hankali, ajiyar zuciya yayi wanda ta daki dodon kunnen Zaljameel, "wa'alaiki salam sarauniyar kyawawa, murmushi tayi, cikin shaukin so areef ya kira sunanta," Zaljameel "yarda yaja sunan nata ya bala'in birgeta..


" Sarauniyar kyawawa Zaljameel, ina sanki,ina matukar kaunarki, burina bai wuce ki amince da soyayyata ba ni kuma na bayyana miki tsantsar kauna Zaljameel" Duk da tana san Areef sai da taji zuciyarta ta buga, bazata ce bata sansa ba tunda bata san so ba amma tasan tana jin feelings a kansa, "Kinyi shiru Zaljameel, ina san na sanar da jawad akan maganar ya kika gani? " ras taji gabanta ya fad'i jin an ambaci Jawad, "Jawad" ta maimaita a ranta,"Yeah Areef ka sanar dashi," dam gaban Mom ya fad'i" mai Zaljameel ke shirin yi? Badai Areef zata bawa dama ba"shiru tayi tana kallon Zaljameel." Ok my dear insha Allah yau zamuyi magana dashi naji yarda za'ayi, dan ina buk'atar ganin ki a kusa dani Zaljameel " murmushi tayi ta lumshe ido ta bud'e, jin ta take kamar ba itaba bata tab'a tunanin a kwai wani wanda zata so ba, amma yau gashi har ta amince da wani. Sallama sukayi cikin shaukin so, cikin nutsuwa Zaljameel ta hang up d'in call d'in sai a lokacin ta tuna da Mom a parlour, ji tayi kunya ta kamata ganin Mom na kallon ta , hannu tasa ta rufe fuskarta tana daria mara sauti, zumb'uru baki Zaljameel tayi cikin shagwaba, "kai Mom mai yasa kike kallona" murmushi Mom ta k'irkiro






🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮






Pure moment of life writers
p. m. l. w




A romantic love story
2017




July 2017








Story & written by


SUMAYYA SALEES SADEEQ














Chapter 33&34








Wayarce ta subuce a hannunsa ta tawarwatse a k'asa, banda innalillahi wa'inna ilaihi raji'un bbu abinda bakin Jawad keyi, Allahumma ajirni fi musibati wayukulifni khairan minha, zama yyi a k'asa yana bin wayarsa da kallo, kirjinsa ne yaji ya masa nauyi, wani irin tashin hankali ya tsinci kansa a ciki, maganar Areef ce ta dawo masa "eh budurwatace and my wife 2 be insha Allah"


"nayita jira ka dawo na sanar dakai amma najika shiru dan mun gama dai daitawa da ita".




Yareema Jawad ya rasa irin tunanin da zaiyi, wato Areef abinda ya masa kenan? Tunda aka haifi Zaljameel nake kaunarta, Amma Areef ya zama sanadiyyar rabuwarsa da farin cikinsa, wata zuciyarce ta tunasar dashi, "Jawad Areef bashi da laifi, cux kai ka bashi damar yin hakan, zamanka na Egypt bai amfane ka da komai ba sai dana sani" wani kukane ya kwace masa da baima san yana kukan ba, cikin sanyin jiki ya tattara phone d'in shi ya zuba a aljihunsa ya nufi room d'insa na hotel, juwa ke d'ibansa yana dafa bango ya shiga, bajewa yayi Akan bed d'in sa yana mai da numfashi, addu'oin ya cigaba da karantawa a zuciyarsa a hankali, ya fara samun nuts uwa,tunani ne ya fad'o masa a rai, wayarsa ya had'a ya kunna "dole ya d'au revenge amma ko son Zaljameel zai kashe shi ba zai sanar da kowa ba,amma ya k'udiri niyar bai komawa Nigeria sai ya samu matar aure shima.


Contact d'insa ya shiga ya fara scrolling, dai dai sunan daya tsaya yana kallo nima sumyn Bash naketa dogon wuya dan ganin waye, "Zahra Zahradden" na gani a rubuce, ba tare da b'ata lokaci ba ya danna kira. Zaune take a wani restaurant taje yin dinner, gaba d'aya tayi sanyi kamar ba Zahra yar rawar kai ba, takai spoon d'aya bakin ta taji ringing a phone d'in ta, cikin sauri ta zira hannu cikin hand bag dinta ta d'auka wayar, sunan data gani yasa ta mutuwar zaune da har phone d'in ta katse bata sani ba,sai a lokacin ta lura kiran har ya katse,"Yareema Jawad "wani ihu Zahra tayi ta fara taka rawa a wajen gaba d'aya hankalin mutanen dake wajen yayo kanta, bata damu da hakan ba dan bata su take ba, cikin zumud'i ta danna kiransa dan dama bata sa rai zai sake kiranta ba.






Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login