Showing 36001 words to 39000 words out of 151322 words
Chapter 13 - Ke Alkhairi Ce Book (Complete) BIEBEE ISA--.pdf
har zai danna kiran Uncle Zaid
ya fasa, sai ya tura mishi sakon message "I'm home" kadai ya tura mai, lokacin da sak'on ya
isa ga Zaid tuk'i yakeyi, ya bude sak'on yayi murmushi yasan Rafeeq ba zai k'i yin abunda yake
so ba, sai ya maida mai Reply da "Nagode".
Haka Rayuwar Rafeeq ta kasance cikin k'una da dacin rai, duk ya koma wani iri, ga wata uwar
K'asumba ya fara ajiyewa, ba ruwan shi da kowa da komai, har mahaifinshi don ya zame mishi
dole ne yake amsa mai magana shima maganar bata wuce "a" ko "aa", Alhaji Habib be jin dadin
yanda danshi ke yin dari dari dashi, ya kira kaninshi Zaid ya kaimai kara, Zaid ko saidai ya bada
hak'uri yace a tayashi da addua. Hakan ba zai hanashi gobe ya koma dakin Rafeeq din ba,
tunda shi ba shiga yakeyi ba, sai a kwana a yini Rafeeq be ce "a" ba, tun Maalesh na damuwa
har ya daina damuwa.
Hankalin Maalesh ya tashi da ya tuna Jibi zasu koma Makaranta, 2nd Semester Level 400 final
Semester dinsu kenan a Jami'ah, ga project ga defence ga wacece, taya Rafeeq zai wuce idan
yana haka? Da sauri ya dialing number Uncle Zaid ringing biyu Zaid ya dauka "Hello Mahmud?"
bayan gaisuwa Maalesh yace "Uncle Zaid Jibi fa muke komawa School, ga shi shine final
semestern mu a makaranta, Dole sai Rafeeq ya kwantar da hankalin shi yayi focusing kan
Semestern nan, shi ke topping din Department dinmu, Uncle Zaid Wallahi duk Sciences bs
kamar Rafeew Lema, lecturers naji da shi, idan ya sa wasa zaiyi k'asa sosai don abun nashi
k'ara girmama yakeyi wallahi, yanzu da idan nazo tayashi fira ya kan dan kulani, amma yanzu
wallahi har inzo in gama surutu na, in gama zama na in tafi in ya tanka ni, kai da ba ka gurin ka
tanka, Uncle am afraid for him" hankalin Zaid yayi kololuwa gun tashi, burin da ya jima yana ci
kan Rafeeq na son rugujewa, tunda Rafeeq ya shiga nursery yake adduan Allah ya nuna mai
randa zai gama Jami'ah, to ga lokacin yazo daidai da k'addarar sa, ya zaiyi? Dole Rafeeq ya
maida hankali, dole Rafeeq ya dawo normal self dinshi, Zaid yace "Mahmud kar ka damu, gobe
InshaAllah muna nan dawowa da Rafee'ah tunda hutu ya kare, komai zai daidai ta."
Sun Iso Katsina Lafia, tunda suka shigo Haraban Gidan taji Gabanta ya fadi, ta kalli Uncle Zaid
tace "Uncle Zaid gaba na ke faduwa, kamar wani abu na shirin faruwa" Zaid yace "kin fara
superstitious beliefs din nan naki ko, ba abunda zai faru kinji Rafee'ah?" tace "Allah ya sa, i cant
wait to see my Mami and my troublesome Hamma Rafeeq" Damm gabanshi ya fadi, ana wata
ga wata sai yanzu ya tuna Rafee'ah bata san wainar da ake toyawa ba, ba ta san me ya
wakana ba tun bayan Zuwan ta kaduna, ko da ta ishe shi Kan tana kiran wayan Mamin ta a
kashe sai yace taje India Medical Checkup, kuma Dr ya bata rest so ko waya bata amfani da
shi, ta yarda dashi don ta san be mata karya, kafin yace wani abu tuni ta fita daga motar, ta na
kiran "Hamma Rafeeq i'm home" da karfi ta ke maganan, Gaban Rafeeq ya fadi jin muryar
Rafee'ah, be san lokacin da ya shige toilet ba ya wanke fuskar sa don kar ta ga damuwa itama
ta tada nata hankalin.
Cikin gida ta shige ta na fadin wai ya na ji Gidan shiru ne? Ba kowa ne? Alhaji Habib ya fito
yana Oyoyo Baby, hajia Sauda tana biye dashi a baya, da sauri Rafee'ah taje ta rungume
Daddyn ta tana "Daddyna i've missed u" daga ta yayi sama yana juyi da ita kamar wata baby ita
ko tana ta daria. Ya direta yana "i missed u more my angel" taje ta rungume Sauda, Sauda na ta
murmushin munafurci tana "haba ai gwara da Zaid ya dawo da ke, tunda ya dauke mana ke
gidan ba dadi" ita ko Rafee'ah sai k'yalk'yala daria take yi, tace ina Aneesa? Sauda tace tana
chan BUK wurin kanwata, zuwa k'arshen wata zasu dawo" Daddy yace ya Safiyya(Matar Zaid)?
Rafee'ah tace "Daddy ta na nan lafia, ta kusa haihuwa ma" Allah ya raba lafia. "Daddy wai ina
Uncle Hafiz da Hamma Rafeeq?" Daddy yace Uncle dinki na Yobe na aike shi, Rafeeq kuma na
Dakin shi. Tace "Ohh yana jina yayi shiru ya kyale ni ko? Barin je in iske shi" ta sauka k'asa tayi
hanyar dakin Rafeeq.
Tunda daga waje take kiran "Bigbro Rafeeq, wai ba zaka fito ka ganni ba? ta kutsa kai cikin
dakin, turus ta tsaya ganin Rafeeq zaune kan kujera sanye da Bak'in Gilashi, mamaki ya
baiyana fuskarta, da sauri ta je ta rungume shi, ganin yanda ya mata ne yasa ta dagowa da
sauri, "Hamma na, baka ganni ba? A hankali yace "naganki, Rafee'ah" baka yi murnan gani na
bane? Shiru ya mata, ta dinga mishi tambayoyi be bata amsa ba, Ga mamakin ta sai ganin
hawaye tayi ya gangaro kan kumatun sa, cikin rudewa tayi saurin zare Gilashin idonshi, tace
"mai ke faruwa ne? Baka da Lafia ne?" Daidai nan Zaid ya fito daga toilet din dakin yace
"Rafee'ah, ki rabu dashi, be da lafia ne, kuka ta fashe da tace be da lafia? Wani irin rashin lafia
ne wannan? Uncle Zaid ko kallona fa beyi ba, Hamma da kullum ya ganni burinshi ya takura
min, ya nemi tsokana na, tunda na tafi Kd be kirani ba, idan na kirashi beya dauka, and yanzu
kuma na dawo irin welcome din da zai min kenan? Ko kallo ban ishe shi ba? Ina mai magana ko
tanka ni beyi ba? Uncle Zaid ko wani abu yace "na mishi?" da sauri Rafeeq ya rungume
kanwarshi ya na kuka itama tana kuka ama ya kasa ce mata komai, sun ba Zaid tausayi, da
sauri ya rabasu yace "fee'ah tashi ki shiga ciki" ba musu ta fita daga dakin tayi sama, Zaid ya
kalli Rafeeq, yace "if you really dont want her to find out, then be yourself" yana kaiwa nan ya
kabbara Sallah don ya san bazai samu amsa daga bakin shi ba. Yana idar da Sallah ya kalli
Rafeeq yace "muje cikin Gida" Rafeeq ya dago ido ya kalleshi zaiyi Complain amma maganar ta
mai nauyi, Zaid yace "ina jiranka" yayi gaba ya bar shi Zaune be da niyyar motsawa".
Aunty Yaushe Mami Zata dawo? Kafin Sauda tayi magana Zaid dake shigowa Parlorn yace
"nace miki sai taji Sauki, Dr ya bata bed rest, soon zata dawo" ya karashe maganar yana me
kallon Sauda yana mata inkiya da ta goyi bayanshi, sai a yanzu ta gane dalilin da yasa dazun
Rafee'ah ba tace ima mamar ta ba, wato sun boye bata, aiko ba zai sabu ba, sai ta samu
hanyar fallasa mata. Zaid yace "Aunty ina Yaya?" tace "yana nan Office in kusa da dakin shi"
Zaid yace da Rafee'ah "ki shiga ciki ki kwanta ki huta" ta mik'e ta nufa daki. Sauda tayi Parlorn
Alhaji Habib, Zaid ya rufa mata baya.
Yana zaune, Zaid ya gaishe shi, Alhaji Habib yace "Engineer har an iso? Ya hanya? Ina aka
tsaya ne sai dai na ga shigowar yar gidanka? Zaid yace "Alhamdulilah, Ina Dakin Rafeeq ina
Sallah" Alhaji yace "hmm lamarin Rafeeq sai gaba yake k'arayi, bansan me na mishi ba" Zaid
yace "ba ka mishi komai ba, lokaci kawai yake buk'ata maganar shi ce ma nake so muyi" kamar
an jefo shi ya shigo parlorn, yayi Sallama amma Zaid kadai ne ya fuskancin Sallama yayi, ya
samu wuri ya zauna kusa da Zaid, Zaid ya tsura mai ido yana mai nuni da ya gaida Mahaifin shi
da Auntyn su, fuska yayi yaki kallon side dinsu. Zaid dai ya san bazai tanka ba ya juya ga yayan
shi yace "Rafeeq dama na kiraka ne nan gaban Ubanka mahaifi, shawara zamu baka, ba mu da
gatan da zamu maka da ya wuce Addua da Shawara, kai Baligi ne kasan ciwom kanka, kasan
abun da yake daidai kasan wanda ba daidai ba, kasan fari kasan bak'i, Rafeeq Abun da ya faru
ina so Ka dauke shi a matsayin kuskure, Kaddara, ka rungume kaddararka, Kai musulmi ne, ba
wai nace ka yafe ma mahaifiyar ka bane, so nake ka gano gaskia ka gane kurenka dukda ba
laifinka bane, shisa kaga na daina takura maka da maganar ta. Alhaji Habib da matarshi dai ba
su ce komai ba Zaid ya cigaba da cewa " Well this is not about your mom. Its about you, ina so
ka maida hankali ka fara last semester din nan naka da kyau, yanda kowa ke Alfahari da kai kar
ka bamu kunya, kamar yanda kake yi da, make us proud like always, ka fita da first class dinka
that you truly deserve kajih?" Rafeeq kallon window kawai yakeyi, be tanka Zaid ba.
Don dai ya sa Rafeeq Farin ciki Zaid yace "kuma zan siya maka mota son ranka, ka fadi wanda
kake so Gobe ka ganshi a gidan nan" nan ma be ce komai ba, Hakan yasa Alhaji Habib yace
"toh nima Uncle din Yara baza a barni a baya ba, nima ina da kyautar da nakeso in ma Rafeeq"
ya mik'e ya fita duk suka bishi da ido gaban Sauda ya fadi tana ta tunanin meye kyautar da
Alhaji zai ma Rafeeq, Jim kadan sai gashi ya dawo da wasu files ya zauna, yace "Sauda da
Zaid kuyi shaida, Kafin a samo Shaidu, Companyn Tie and Dye na Sokoto, da Hide and Skin
na Keffi na Mallaka ma Rafeeq, ko na mutu ba su a cikin Gado, kuma da ka gama Service,
komai na other Companies dina zasu dawo k'arkashin ku kai da Rafee'ah, Zaid ya washe Bakih
yace kai MashaAllah, Angode Allah ya k'ara girma" Sauda kuwa Ba tasan duniyar bakin cikin da
ta lula ba, kiris ya rage ta fashe don ta kumbura, ta kasa boye bakin cikinta da hassadar ta.
Amsa Rafeeq, Alhaji ya miko mishi Files din, Zaid ya mai Alama da ya amsa, kamar ba zai
karba ba ya sa hannu ya amsa a hankali yace "nagode" Daddy yace tashi kaje ka adana.
Kamar jira yake ace yatashi ya tafi ya mik'e da sauri, Files din ya mik'a ma Zaid, Zaid ya sa
hannu ya amsa, yana bashi ya fita daga Parlorn. Zaid ko Farinciki yake tayi. Sauda kuwa ta na
hada hanya don ta daina gani saboda bakin ciki ta fita.
Daki ta fada ta fashe da wani irin ihun takaici, ta daura hannu a kai, na shiga uku, Alhaji har ya
fara rarraban kamfanonin ka? Be sakani cikin lissafi, wato daya gama Sabis zai maida komai
karkashin sa shi da kanwar shi, ni kuma da tawa diyar oho, wallahi ba zai sabu ba, sai inga ta
inda zai gama makarantar balle yaje service din har ya zama wani tsiya , ita kuma Rafee'ah sai
ta tsani kanta, don boka na kan tudu zan sa ya Sa Rafeeq ya mata Fyade, ko kuma ta zama
karuwar Yayanta, sai in ga ta inda zasu zama abun Alfahari ga mutane. Sai kowa ya tsanesu,
shima Alhaji ya tsine musu ya koresu daga gidan shi, su shiga duniya, sai ya rage daga ni Sai
diyata sai muci karenmu ba babbaka ta sa shewa kamar wata zararriya da sauri ta ciro wayarta
ta latso number Boka na kan tudu ta labarta mishi plan dinta. Yace "Saude wannan magana ba
ya waya bace ki zo Gobe kawai sai a duba" tace "to na kan tudu, ka tsumayi zuwa na gobe, da
Asubar fari zan taho".
_Bibilicious Biebee_
í ½í±§í ¼í¿½KE ALHERI CE
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg2⃣8⃣
As promised, This page is for you Aunty Baraka���
Washegari Alhaji Habib yace da Sauda zata raka shi Kano, haushi kamar ya kasheta don
tayi niyyan zuwa gun boka na kan tudu yau, haka suka tafi Kano ba don taso ba.
Rafee'ah ta rada ta inda zata bullo ma Rafeeq, don har yanzu bata san damuwar shi ba, da
ta matsa ma Zaid sai ya gaya mata, sai yace mata "zaifi kyau ki taya shi da addua, Shi kadai
yake bukata, kar ki tsananta Bincike you might end up hurting yourself" haka Rafee'ah ta cigaba
da shishige ma Yayan ta ko zata samu ya dawo yanda yake a da, amma shiru ba cigaba, haka
zata karashe surutun ta ta barshi, duk yanda yake so ya dan dinga kula Kanwar tasa hakan ya
faskara, abun ya zame mishi jiki, Yanzu magana ya zame mishi wani gagarumin Aiki, da Zaid
kadai zakaji yana magana, shima be wuce ya bishi da kalma biyu ko uku ba, abun Rafeeq ya
wuce Miskilanci, don abun yayi k'amari har ace be iya shiga cikin Gidansu ya ci Abincin da
Matar Uban shi ta dafa, kai ko daki aka biyo shi dashi be ci haka zai bar musu shi inda suka aje
mishi shi, Be cin abincin Gidan su kwata kwata, sai dai yaje gun me indomie ya sha shayi, da
Zaid ya lura da hakan sai ya siyo mishi Cupcakes,Biscuits Shortbread da Drinks kalakala ya
ajiye mai a daki tunda yana ganin asaran cin Abincin Gidan su..
Da kyar Maalesh ya sa shi shirin Makaranta, ba don yaso ba, sai dai kawai baya so su tsaya
gardama da Maalesh, ya shirya suka wuce School, tunda suka isa Sciences aka zagaye motar
Maalesh, Maza da Mata kasancewar R-Lema na kowa ne, Maalesh yace "Guy, dole ka fa sake
fuska, mutanen ka na jiran fitowar ka" be kula Maalesh ba sai ma dauko wani Bakin Gilashi irin
no respect din nan ya k'wama a fuskar shi, ya bude Kofa ya fita, ji kake ana R-Lema, ko kallo
basu ishe shi ba, tafian shi kawai yakeyi, burin shi ya ganshi a Class, duk suka bishi da kallo
suna mamakin wanna Shariya na R-Lema, sai duk suka maida kallo ga Maalesh, Maalesh ya
shiga raba idanu kamar yayi K'arya, da k'yar yace "kuyi hakuri, R-Lema na da dan damuwa ne,
ky tayashi da Addua". Mutanen kam suka jinjina kai, da alamu kam, don ba haka suka saba
ganin shi ba, shi mutum ne mai son jamaa, da da ne, da ya fito zai dinga ba mutanen nan
hannu suna gaisawa, ya dinga jan tsokanan yan matan nan, ana wasa ana daria, lallai dole
suke tayashi da addua Allah ya yaye mishi damuwar shi.
Ai ba Daliban ba, harta Mallamai sun san da Chanjawan R-Lema, yanda kasan hoto haka
yake zaune a aji, ba motsi, ba kamar da ba, kafin Lecturer ya gama tambaya har ya bada amsa,
amma yanzu ko sun tambaye shi shiru zakaji yayi, bawai be gane abun da ake koyar dashi
bane, tsaf yake fahimta kamar kullum, abunda yake ganin asara shine ya bude baki yayi
magana ko ya bada amsa, yana jin kuiwar magana, kwanaki da ya ba wani Lecturer haushi
koran shi yayi a aji, don ya dinga mishi magana jo tak Rafeeq be ce mar ba, abun ya ba
mutumin haushi ya kore shi, sai da Maalesh ya je ya sanar da Level Coordinator dinsu,
kasancewar Coordinator abokin Zaid ne, Yazo ya bada hakuri, yace yayi hakuri Rafeeq is
Mentally Sick, yayi considering dinshi tunda kowa yasan ba haka yake a da ba. Da haka aka
rufe bakin lecturers, ko sunzo ba sa tambayan Rafeeq don sun san ba tanka su zaiyi ba.
Duk nacin da Yanmatan Rafeeq keyi don ya kulasu haka suka gaji suka hakura, don ko sun
fi k'uda k'wak'wa iskar da ya debo su Rafeeq be kallo, Cafteria da da ya maida shi Gidan Uba, a
rana sai yaje so nawa, yaje ya siya ma yanmata abinci, yanzu kuwa ko kallon hanyan beyi, in ka
ganshi cikin Makaranta yana aji, da sun gama lectures be kara ko minti zai bar ajin don be son
surutu, Chan bayan Labs inda ba ka ganin kowa yake zuwa ya zauna shi kadai. Haka Rayuwar
shi ta cigaba da tafia..
Duk Yanda taso ta kebe ya je gun bokan ta Alhaji Habib ya toshe, be bata damar zuwa ko
nan da chan ba, ko ina zaije da ita yake zuwa, be barin ta ita kadai, ta rasa yanda zatayi, haka
dai ta hakura har suka karaci kwanakin su a garin Kano.
Bayan Sati Uku
Sauda ta kalli Boka cikin kunan rai tace "ya zaka ce min hakan ba zaiyiwu ba? Meye ba
zaiyiwu ba? Kaine fa kake share min hawaye na, kai ke biya min buk'atu na"(Waiyazubillah, ya
mu Mata, mu kula, mu lura, aikin Boka na tasiri ne da Yardar Ubangiji, Boka be Isa Ya biya
mana Bukattun mu ba. Allah sa mu dace). Ta yaya zan ce maka ga abun da nake so kace min
ba zaiyuwu ba? Kasan taya na bar Katsina na zo nan? Ni yanda nake so haka zaayi, Kawai
Rafeeq nake so ya fyade kanwarsa". Boka yace "Saude kar fa ki manta, duk aikin da kike samu
muna miki shi yanda kika buk'ace shi, tunda kikaji nace wannan bazaiyuwu ba toh ki hakura da
wannan, amma na riga na biya miki dayan bukatar hana Yaron Gama Makaranta" Sauda ta
katse shi ta hanyar cewa "yo ni raba ni da wata makaranta, yo ya gama ina ruwana, ni buk'ata
ta shine Alhaji ya tsine musu duka, kai ni ban k'i su mutu ba" Boka yace "Ke Saude saurareni
kiji, jijsan aiki na kamar yankan wuk'a yake, ba wanda ya