Showing 93001 words to 96000 words out of 151322 words

Chapter 32 - Ke Alkhairi Ce Book (Complete) BIEBEE ISA--.pdf

16 Mar 2025

8034

of the Damn Car" itama cikin muryar kuka take cewa "Nace maka ba
inda zani, i am not done talking to you, if you dont want to realise your good side, then i'll make
you realise them, lokacin da aka kai Nene Asibiti, mesa ka ke kula damu? Abinci safe rana da
dare? Me sa kake kaini makaranta? Zuciyar ka me kyau ce amma ka danneta kai a dole ba ka
damu da kowa ba, ko kuma ba wannan ba, ka tuna randa kace in fitar maka daga mota, randa
zaka kawo ni Makaranta? Randa nake ta maka tsaki? Ka direni a tsakiyar daji? Na san ka tuna,
ka tafi me ya dawo da kai? You could'nt leave me there because you care" da sauri yace "No i
dont, i was only saving you from your Stupidity, kin tsaya tsakiyar titi kar mota ta bigeki, people
would get hurt people like my Uncle Zaid and Maalesh" tace "koma dai meye you care about the
people you love, ba dole sai ni ba, dama ai ni ba kowa bace, amma su ka damu da damuwar
su, ka kasa barina sabida su, ka ga kuwa wannan shine abunda nake so ka fahimta, you have a
beautiful heart" "ke i dont care about anyone, Uncle Zaid is all i care about and maybe Maalesh,i
can sacrifice anything for them" ta mai wani kallo tace "really? To tell me, har yanzu me kakeyi
da Zoben hannunka? Me kakeyi da danuwa Zoben da ka ba Maminka? Saboda kana sonta,
akwai 6angaren zuciyarka da ke sonta, akwai 6angaren zuciyarka da ke son sake ganinta, fushi
da bak'ar zucciya suke hanaka, Rafeeq na girgiza kai yace " Ki min Shiruuu please, Ya isheni
Nasiba" da sauri ta kallo shi, a iya saninta da shi ko Seebi bata ta6a ji yace ba, amma yau ita
yake kira da Naseeba? Ya ilahi, yaba ta tausayi ama dole ta ya gane abunda yake yi ba me
kyau bane, tace "kaga matsalar ka ko? Baka son gaskia, da an fara gaya maka gaskia sai ka
tsaida mutum, ita gaskia kwara daya ce kuma daci gareta, Listen now, i am going to make this
Straight to you, Incase you dont know, Aljannar namiji yana k'asan tafin Mahaifiyar shi, sai ya
bita zai samu shiga, sai da Manzon Allah ya kira Uwa so uku kafin ya kira Uba so daya, ko
kasan duk wanda ya sa Mahaifiyar sa kuka be ganin daidai? Ka san iyakar hawayen da tayi a
kanka? Kasan zunuban da kake kwasa a ranar da tuna da kai ta zubda hawaye? Ya Illahi! i dont
have to lecture you on this, kai kasan wannan abun amma fushi ya hanaka ganin hakan, ka
ta6a tambayan kanka? Shin yanda nake ma Iyayena musamman Mahaifiya ta ina kyauta wa?
Duk abunda ta mun tun ina cikin ciki har girmana ta chanchanci abubuwan da nake mata, kai ko
me tayi, She's still your Mother, ko kisan kai tayi, she'll remain your mother, balle something you
are not sure of, something no one is sure of, You didnt bother to find the truth, kai an maka laifi,
ba wanda ya kuma isa ya ce kayi, ask yourself if this is the way you want your children to treat
you when they're grown. Don abun da kayi shi zaai maka wallahi, fiye da ma wanda kayi, dole a
maka, If you're not measuring up, it's not too late. You can make a change this very day. Uwa ta
fi karfin wasa Wallahi, ka tashi ka fusknaci matsalar ka tun kan dare ya maka, tun kan ka wayi
gari ace ba kai ko ita a duniya, Only then zaka higa damuwan da yafi wannan matsi i've said my

peace" ta na kuka ta ciro paper da biro tayo rubutu, ta ajiye mai a cinya, tace "gashi this is her
address, bance kaje ba, you decide what to do with it, ina so kayi tunani, ka tuna Who is your
mother" ta share hawayenta ta bude motar ta fita tabar Rafeeq zaune kamar gunki.

Hannu ya sa a kai ya damk'i gashin kanshi, Jijiyar kanshi kamar ta fito, Nan ya soma tunanin
halin da ya iske Mami a ciki, sai ya tuno Õ®aÕ®Õ®aÕ®an lokuttan da sukayi da Mami Daddy and
Rafee'ah ad a Family, Ya tuna wacece Mami, abunda be taba yi ba, kanshi ya hau sarawa, ya
kusa Minti 30 bayan fitar Nasiba yana hawaye, hawayen da ya rasa na meye, ya kunna motar
shi ya fita a guje kamar be shirin tashi Sama" Nasiba ta fito daga maboyarta tace "Allah ka sa
yaji, Allah ya tsareka R- Lema".

_Malali Kaduna_

Shigowar ta kenan daga Gidan Ummin Anan, ta mik'a musu Coolern Danwake, don yau
Danwake tayi, ta kalli agogo taga k'arfe 3:16, tace kaii bari inyi bacci kafin laasar tayi, kan kujera
ta dan kishingiÕ®a ji tayi motsin mutum tana dan kallo kofar ta ga Mutun tsaye, jiki na 6ari ta
mik'e tsaye, ta kasa yarda da abun da idonta yake gane mata, baki na rawa ta nuna shi da
yatsa tace " Rafeeeeeeq" A hankali yace "Mamiiiii" Da sauri ta runtse ido daidia digar
hawayenta tana adduar kar ta farka da wannan mafarkin da takeyi, yau Rafeeq ne ke kiranta da
Mami? Ba zata so ta ta6a tashi daga barcin nan ba, takowa yayi kusa da ita ya sa hannu ya
share mata hawayen da ke zuba a idonta, jin an tabata yasa ta gane ba nafarki bane, a hankali
ta bude idon ta fes kan fuskar shi da ta koma ja, girgiza mata kai yayi, da sauri ta rungumeshi
tana kuka, "Rafeeq, Rafeeq my Child, Rafeeq ka yafe mini, Rafeeq na hallaka rayuwar ka,
Rafeeq ka yafe mini DonAllah" shima kukan yakeyi sosai, kukan da be taba irin shi ba, yace
"Mami meyasa? Mami Why? Why? Why?, Mami meyasa zakiyi haka?" ta dago da sauri tace
"Wallahi bansani ba, bansani ba Rafeeq, ni nasan banda mafita, Allah kadai ne gatana shi kadai
yasan me ya faru a wannan ranar, amma Wallahi bansan komai da ya faru a ranar ba i totally
have no idea, please believe me my son" Zuciyar shi ta tambayeshi Wai kai dama tun farko
meyasa ka yarda da Mamin ka zata iya aikata abu makamancin hakan, ita da kullum take maku
Nasiha kan ku nissanci Zina, wata Zuciyar tace da idonka ka ganta" da sauri ya kawar da
tunanin nan, ya sake rungume ta, yace "it doesnt matter anymore, ba zaki iya aikata hakan ba, i
was blind to see, we all were blind to see the good in you, but not anymore, I swear on my Dead
Sister whoever did this to you will pay" tace "Aa Rafeeq kadaina irin rantsuwar nan, be da
amfani, ba kyau, kuma dont let anger have control over you, calm down" Yayi ajiyar Zuciya yace
"Mami, whatever i said to you in the past, please forgive me, i dont mean any of it, i was stupid
to forget who You are, someone said in har kina fushi dani ba zan taba ganin daidai ba ki yafe
min" "Shhhh my baby, ba ka min komai ba, I got you, i always do" ta jawo hannun shi ta zaunar
dashi ta dinga shafa hannun shi tana murmushi tana ganin komai kamar mafarki, tace "kasan
me na dafa? Ya girgiza kai, tace "Danwake" yaui dariya yace kina son danwake har yanzu?
Tace "kai ka koya min danwake" ya tashi yace barin zubo mana ko? Ya shiva kitchen ita kuwa ta
dubi gabas tayi sujjada (Sujjudush Shukur) tana me godia ga Allah da ya dawo da danta gareta,
saura Baban shi da take adduar Allah ya sa shima ya fuskanci gaskia, Rafeeq ya zubo musu
Danwaken ya kawo parlor ya ajiye a kan Carpet, ya rik'o hannun Mami ya zaunar da ita a k'asa

ya koma ya dibo mai da yaji a kwano yazo ya zauna, haka suka fara ci yana sa mata a baki
tana sa mai a baki, hawayen farinciki sukeyi duka, har dai Rafeeq ya koma lallashin Mamin shi
har suka gama, ya kwashe kayan ya shiga daki yayi alwala yayi Azahar ya ja su Jam'i sukayi
laasar, nan suka hau labarin duniya.
"Allah sarki Nasiba, Nasiba Alheri Ce Rafeeq, Nasiba Alheri ce a garemu duka, ko ba ka fada
ba nasan ita ce Silar zuwan ka Kaduna" murmushi kawai Yayi yace "Mami ke ina kika santa?
tace "tashi muje gidansu yanzu" yace "aa i want to spend more time with you" tace ba nisa
makota ne yanzu zamu dawo, suka nufa Gidansu Nasiba, Daidai shigowar Abbi, Rafeeq na
ganinshi yaje ya rungume shi, Abbi ya bubbuga bayanshi, ya ji dadin ganin Rafeeq haka, Lallai
in ciwo cuta ce to tabbas addua Magani ce, yace "Jiki yayi kyau Rafeeq, Allah ya sa a dace yayi
murmushi" "ina Mutuniyar taka? Nenen ka?" guntun tsaki yayi chan kuma yayi murmushi ya
kwashe labarin abun da ya faru jiya ya basu, Dukkansu dariya suke tayi, Abbi ya girgiza kai
yace "nace ma Nenen ta daina biyewa yara ta ki ji, ita jinta takeyi kamar yar shekara 15" suka
sa daria. Anan yazo ya hau kan Rafeeq, Rafeeq ya daure fuska beson yara, amma ganin idon
Abbii da Ummi a kanshi ya sa shi yin yak'en dole, Anan na matukar kama da Nasiba, yace ka
san Adda Seebin Nene? Kai kawai Rafeeq ya gyada, to ka tafi dani gurin su" Rafeeq ya mik'e
tsaye yace "Idan anyi hutu kaji" ya kalli su yace "Ina so in koma Katsina yanzu" Mami ta zaro
ido tace "Feeq 5 saura fa" yace "eh Mami" Abbii yace "da dai ka bari gobe" yace "Gobe zanyi
test karfe 8" nan dai suka mai Allah ya tsare hanya, ya ja hannun Mami suka wuce Gida, sun
dade suna magana, tace "R-Lema anya ba zaka bari sai gobe? 6 har tayi fa" yace "zan tafi dai,
your prayer keeps me moving" bmya rungumeta kafin ya sake ta ya shige mota da sauri don
ganin zata fara kuka. Nan ya dauki hanyar Katsina ta bishi da Addua "Rafeeq Allah ya tsare
hanya ya kaimin kai lafiya, yasa ka iske su lafiya Amin"

_Layout Katsina_
11:45pm

A gajiye likis ya shigo Unguwar, duk ya gama gajia, ya wahala Mota ta tsaya mai gurin Dabai,
Unguwar Shiru ba ka ganin kowa waje, abunka da Unguwanin yan gayu kowa na Gidan shi ya
kulle, daga nesa ya ke hango hayak'i na tashi kan katangar wani Gida, yace "toufa, wannan
hayakin daga ina, ko da ya kusanto gidan sai ya ga Gidan Nene ke ci da wuta, ai be san lokacin
da ya fita daga motar ba, Gidan na ta ci da Wuta, ya rasa me zaiyi, da sauri ya dinga kiran
wayar Nasiba, tana ringing baa dauka, duk ya bi ya damu, ya nufa k'ofar da niyyar ya bude ya ji
wani irin zafi, ya ja da baya, ya fashe da kuka, Uncle Zaid ya fara kira, Zaid be dauka ba a
lokacin yana toilet yana wanka, Yayi tsaki cikin kuka ya kira Maalesh, Maalesh ya daga " Guy
howfa u never sleep?" cikin rudani yace "Nasiba, gidansu na ci da wuta" "What" inji Maalesh,
gani nan zuwa, ya latse wayar, Rafeeq ya dinga kwankwasa ma makotan su Nasiba don suma
Katangar ta hau ci da wuta, nan yayi tunanin yan kwana-kwana(Fire fighters), ai kafin ya samu
taimako daga Makota k'ila gidan ya k'one kurmus, hannu na rawa ya latsa numbern Daddyn shi"
a lokacin yana kwance ba dai bacci yakeyi ba, yana tunanin Wani abu ne da be san meye ba,
ya ga kiran Rafeeq, ya daga da Mamaki "Ibn Zaid ya akayi da daren nan haka?" baki na rawa
cikin kuka yace "Daddy, Daddy" Ya tashi a firgice yace "What isit son? Calm down and Talk to

me" da k'yar yace "its Nasiba and Neh-Neh" zumbur Daddy ya mik'e yace "me ya samesu?"
gidan su na ci da wuta, Daddy bansan me zanyi ba" Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Stay still son
gani nan zuwa, i'll make some phone calls" ya tashi ya zumbura malummalum dinshi kan dogon
wandon da ke jikinshi, ya dialo numbern shugaban Fire Fughters ya sanar dashi komai suka
bashi tabbacin yanzu zaa su fito don ceton su"
Zaid ya kira Rafeeq bayan ya fito daga wanka, amma Rafeeq be dauka ba, a lokacin makocin
su ya bude gida ya fito da yaranshi maza sun fara zuba ma Gidan Nene ruwa, amma kamar
ana k'ara rura wutan, Maalesh ya kira Zaid ya sanar dashi, hankali tashe ya bar Hotel din ya
nufo gidan Nene, a tare yan Fire fighters da Daddy suka iso, sai Maalesh, Rafeeq ya rasa
sukuni, tuni Yan kwanakwana suka kuna injin suka kashe wutan Gidan Nene, Hankalin su a
Tashe, Rafeeq ya dinga bubbuga gidan Nene amma ba alamun akwai me rai a ciki, Da K'arfi
yace duk sun mutu kamar wani zautace, Maalesh cike da tashin hankali yace "Noo ba su mutu
ba, we just need to get in" Rafeeq ya kalli yan kwanakwanan yace "Someone should break the
Goddam Door" sai ya fashe da kuka, Zaid na fitowa daga motar ya nufo su, Rafeeq na ganinshi
ya rungume shi, Zaid ya dinga bubbuga bayanshi yana kiran they'll be fine, Rafeeq yace "Noo
Uncle, i cant loose them both, i cant" Daddy ya taba bayan Rafeeq yace "Rafeeq ka gani an
6alla kofar, yanzu zasu firdosu a kai su Asibiti, InshaAllah they are going to be fine" Rafeeq ya
waiga ya ga Jamian sun 6alla k'ofar a sittin ya ruga gidan ana rirrikeshi yana fizgewa ya kutsa
kai ciki, Zaid bi bayanshi Daddy da Maalesh suka rikeshi, Zaid cikin tashin hankali yace "No he
cant get in there be da facial mask, Rafeeq ka fito please" Attishawa ya fara yi amma be fasa
kutsa kai ba, ko da ya isa har ya ga sun dauke Nene kan Gadon marasa lafia sun saka mata
Oxygen zasuyi waje da ita, sauran kuma suka nufa Nasiba, bangaje su yayi ya nufe ta yana
Attisahawa da Tari ya Ciccibi Nasiba kamar jinjira, ba alamun numfashi a tattare da ita, fadi
yake "Hey hang in there, i cannot loose you too, i lost Rafee'ah" kamar mahaukaci yake sunbatu
ya fita da ita, be tsaya ko ina ba sai motar shi, baya ya sakata, ya shiga ya ja Motar, Maalesh na
kwala mai kira amma ina sam baya ji, Officer yace da Daddy "ku tsayar dashi, she needs First
Aid, Oxygen zamu saka mata, she needs it now, Daddy yace i'm sure Asibiti zai kaita" Officer
yace "i'm afraid kafin a kaita Asibiti maybe ta mutu".

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼�♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Kin chanchanci Yabo a guna Masoyiyar Asali, Wannan page din naki ne Ag😘

Pg5⃣1⃣

Yana tuk'i yana kallon bayanshi hawaye na zuba, sambatu yakeyi, "DonAllah kar ki tafi ki
barni, Rafee'ah ta yafi, kema kar ki tafi, bansan me zanyi ba in kika mutu, Ya Allah kar ka dauki
ranta, Allah ka dauki nawa instead" ireiren maganganun da Rafeeq keyi kenan, Sanyi ACn
Motar ya sa Nasiba farfadowa, tari ta hauyi ai da sauri ya juya ya kalleta, wani murmushin da be
san lokacin da ta subulo ba ya sake tare da taka birki ya tsaida motar, fita yayi ya koma baya,
hannunta ya rik'o Yace "Naseebah, Naseeba are you Ok?" tari ta shiga yi ba sassautawa ta
zame hannunta daga nashi tace "I'm fine, ina Nene?" yace "Tana chan gurinsu Uncle Zaid"
Nasiba ta shiga tuno abunda ya faru tiryan tiryan, tace "Hamma mu koma donAllah, Nene na
chan ban san halim da take ciki ba" yace"karki damu nasan Asibiti zasu kawota, right now i
need to take you to a hospital" tace "please mu koma, i'm fine now, i just need Water" da sauri
ya dauko mata ruwa a gaban Seat, ya bude ya bata ta kwankwada" cikin sigar lallashi yace
"Listen to me, zan kaiki Asibiti a duba ki, Neh-neh kuma is in safe hands, barin kira su in gaya
musu kin farfado mu hade a Asibitin" Maalesh ya kira, "Maalesh kuna Ina?" cikin damuwa yace
gata nan zamuzo "Alheri Clinic don ya fi kusa" "bata farfado ba?" Wallahi kuwa feeq, gatanan ko
numfashi batayi" Rafeeq ya cije hak'oranshi, yace mu hade Asibitin ni na kusa ma" sukayi
Sallama, Seebi tace ya jikin Nenen? Rafeeq ya fita ya koma matukin direba tare da cewa "gata
nan zasu kawo ta wanchan Asibitin".
*****
Daidai isowar Ambulance, aka fito da Nene aka shiga da ita ciki already Daddy ya kira Dr aka yi
da Nene Emergency, da kyar aka samu suka tsaya daga waje,Seebi kuwa ta k'i yarda a bata
gado acewarta ba inda ke mata ciwo, Dr's suka buga nan suka ta6a nan ba alamun Nene Zata
motsa suka dukufa da aikinsu a matsayinsu na Kwararrun likitoci. Bayan 'yan mintoci Likitoci suka fito fuskar su ba Annuri.
Dr Sami yace "i'm so sorry, we couldnt save her" luuuuu Nasiba ta zame k'asa ta zauna dabas,
Inalillahi wa ina ilaihir rajiun inji Daddy, Zaid Ya dora hanayensa duka biyu akai, Maalesh ya fara
matsar kwallah, Wtf? Inji Rafeeq, ya chakume shi, what do You mean by you couldnt, save her
huh? Dr Umar yace "kuyi hakuri, kamar tana da Athma, kuma ta shaki hayak'in Sosai, kuyi
hakuri Addua kadai take buk'ata" Bangaje shi yayi ya shiga dakin duk suka biyo bayanshi banda
Nasiban da Hawaye ke ambaliya a fuskarta, Nene ta rasu? Nenenta? Inalillahi, Nan da nan ta
chanza kammanni sabida kuka, tausayi Mahaifinta da Goggonta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login