Showing 63001 words to 66000 words out of 151322 words

Chapter 22 - Ke Alkhairi Ce Book (Complete) BIEBEE ISA--.pdf

16 Mar 2025

8031

don batayi wanka ba,
tayi wa nene da hajjo sallama ta wuce gida don shirin Makaranta saboda sauran kayan da ta da
ke Asibitin sun yi Datti.

6:50 ta isa gida, sai da ta share gidan ta ta gyara ko ina kafin ta fada toilet tayi wanka ta
shirya ta, ta fito Gida 7.55am. Sauri take ta isa bakin titi don ta samu abun hawan da zai kaita
National don kar tayi missing Bus.

Kamar kullum, Tuk'in shi yake cikin qasaita, daga nesa ya hangota, kamar ita kamar ba ita
ba, kai itace, wannan yarinyar ce, a ransa yace "Wannan kuma me takeyi a nan? (kuji se kace
be san nan gidansu yake ba) guntun tsaki yayi yace "Da naje daukan ta a Asibiti da nayi zuwan
banza kenan" ya sake wani tsakin kamar yana gabanta. Horn taji da karfi, da sauri ta dode
kunnenta tare da juyawa a k'ufule don ganin me neman kashe mata dodon kunne, ita da ba kan
hanya take ba, Idonta ya kai ga Motar Rafeeq, haka kurum taji dadin ganin shi duk da ta san ba
wai kulata zeyi ba, ko ba komai, ba zatayi latti ba, kuma zata samu daman mishi magana.

Bude motar tayi ta shiga don tasan ba ce mata zaiyi ta shiga motar ba, cikin wata muryar da
bata san tana da shi ba tace "Ina Kwana Hamma Rafeeq"
Jan motar shi yayi, ya dau hanyar school yayi kamar be jita ba, har ta cire rai da zai amsata,

don sunyi tafiyar kusan 4mins kafin taji yace *"lafiya"* da mamaki ta kalleshi, ta ma manta da ta
gaishe shi, a ranta tayi dariya tace *"bakasan waye jikar nene ba sai ka dawo hanya da Yardan
Allah"* wani kwarin guiwa taji, ta gyada kao tace "i can do it" Cikin sigar shagwaba tace
*"Hamma na please..."* sai kuma tayi shiru tare da duban sa. Wani uban tsaki ya buga da sai da taji tsoro, ya maida hankalin shi ga tukin sa, don duk yanda
ta kirashi da *"Hamma Rafeeq"* sai numfashin sa ya dauke, balle yanzu da ta zak'e wai
*"Hamman ta"* "wannan yarinyar ta fara koyon surutu, ta fara zak'ewa"
Kamar ba zai ce komai ba yace " what?" ta ji dadi tare da samun karfin guiwa, tace dama
zance ko in munje wancan shagon zaka dan tsaya na sai Ziza Milk, don banci komai ba ina
sauri kar nayi latti.

Besan lokacin da murmushi ya subuce masa ba, cikin sakwan da be wuce 2 ba ya daure
fuska, a ransa yace "what is funny?" ji yadda take sunne kai kamar mara gaskia, lazy girl she
cant even skip breakfast. Be dai ce da ita komai ba

Daidai wani shago ya tsaya, tayi murmushi tace "yawwa Hamma na Nagode" Ta dauki jakarta,
tana k'okarin bude kofar taji ya bude tasa kofar ya fita tare da rufowa. Gyada kai tayi cike da
tausaya wa, don shi duk abunda yakeyi bata jin haushin, illa ma tausayin da yake bata. Be
dauki lokaci ba ya dawo da leda kunshe da soft drink da kuma date bars ya aje mata kan cinya,
ta masa godia suka dau hanya.
Ta bude jakarta don saka ledar a sama ta tsinci muryar sa *"EAT NOW"* tace " *to Hamma na*.
Ta bude tana ci har suka iso School, har bakin Department dinsu ya kaita, kimtsa bakin ta tayi
masa godia ta fice. Shikuma ya ja motarsa ya k'ara gaba.
Yana wucewa ta sauqe wani gauron numfashi tace "Wai Allah nagode maka da ka sa min
dauriya, Allah ka kara shige min gaba Ameen"

Zaune take gefen nene tana waya da Uncle Zaid, inda take sanar dashi cewa Nene ta
warke, likita yace zuwa magriba zai Sallamesu. Uncle zaid yace "Alhamdulillah, Nene ta ji
sauk'i, idan anyi sallamar ki sanar dani" tace "toh"
Ta masa godiya suka yi sallama. Ta miqe ta shirya tace "Nene zan shiga makaranta bani da
lecture, amma ina da Assignment din da zanyi submitting kafin lokacin sallahr Juma'a, da an
gama sallahr Jumaa'h zan dawo wuraren k'arfe biyu, sai a hada kayan kafin likitan ya zo ya
bamu Sallama". Murna gun Nene kamar me, tace "wlh dama na gaji da Asibitin nan, Mutum da lafiyarsa amma
an kawo Asibiti an ajiye, amma fa zanyi kewar 'yar gasasshen Kazar da dunkum ke kawowa"
(Dunkum ne sunan da Nene ta sa ma Rafeeq) ba Seebi ba harta Hajjo dake gefe sai da ta dara
tace" Kai k'awalliya, jika na ne Dunkum?" Nene tace "yo ehmana, ayi mutum shi he daria, be
murmushi be magana? Hajjo tace "lamarin Rafeeq sai du'ai, haka yake" Nene tace "Shiyasa na
rik'e furfurata, ba ruwana dashi, don in na mai magana ya share ni, ina iya kulle shi daki karfe
ukun dare inci Ubanshi, dan uban mutum" me Hajjo da Nasiba zasuyi in ba daria ba, Nasiba har
da kwallah, Hajjo tace "Lallai Nene Lafiya ta samu" Nene tace "dama garas nike, uwayen fiili
suka daura man zaman dole a Asibiti, wato Seebi da Zaidu bawanAllah" Nasiba dai ba ta tanka
ba.

Dan zaman da sukayi na kwanaki biyar Hajjo da Nene suka Saba don Nene akwai surutu da
saurin shiga rai, hajjo kuwa akwai barkwanci..

Ku daga daga k'afa mu isa on time kunga yau Friday, Buses cika zasuyi da wuri. Seebi ce
mai maganar nan, Usheey tace "in ba haka ba sai mun ci uwar trekking kafin mu samu naAllahn
da zai bamu Lift.

Kamar Baki, ga Buses har uku amma duk a cike mak'il har bakin K'ofa, Seebi ji take kamar
tayi kuka don haushi.
Tasan Nene na chan na zuba idon ganin ta, ita da ce mata 2 zata dawo, gashi har uku.
Miemee ta bada shawarar su fara takawa Ko Allah zaisa su samu lift ko kuma rage hanya kan
Buses su jiyo atleast yafi tsayuwar.
Usheey tace "Miemee don Allah in za a bamu lift yau kar ki yi over sabi please" Seebi na
gimtse daria tana fuska, Miemee ta daure fuska tace "Munafuka, say your mind" Seebi tace
"Kina da Hayaniya" Miemee tace "Kuna da damuwaaa" ai kuwa duk suka fashe da daria,
Miemee tace Wallahi gayen nan ya mugun raina ni" sukayi daria suka fara tafia.
Tafia suke tayi, sun danyi nisa sai ganin motar R-lema sukayi a gaban su, basu tsaya wata
wata ba suka nufe motar, Seebi zata bude kofar baya ta shiga Usheey ta buge hannun tace
"donAllah shiga gaba kar ya chanza raayin shi" Miemee ta harare su tace dama ce muku akayi
zan shiga gaba? Seebi ta shiga gaba duk suka koma baya, a tare suka gaida shi, kai kawai ya
daga musu, ya ja motar shi ya tafi, ko da suka iso cikin gari ya kalli Ushee ta mirror kamar zai yi
magana sai fasa, tsaf Seebi ta dago shi, so yake yace dasu Usheey ina zai sauke su amma ya
kasa, Seebi tace "DonAllah ta wurin Asibitin Dr Dara kayi?ni nan zan sauka" Shiru yayi kamar
be ji ba, ganin be da niyyar tsaiyawa ya sa tace "Kana iya ajiye mu anan" kamar jira yake kiiii
yaci burki, yayi parking, Usheey da Miemee suka mai godia ko uffan be ce musu ba, suka bude
suka fita, Seebi zata bude k'ofar kenan ta fita ya sa lock, su Miemee na kullewa ya ja motar shi
yayi gaba" Su Miemee suka bi motar da Ido baki a hangame.

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼�♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg4⃣0⃣

A tsorace ta dan kalleshi, ko bi ta kanta beyi ba ya hau titi kanshi a tsaye, Maimakon suyi
hanyar Asibiti, sai bani tayi ya dauki hanyar *Sally's Cuisine* ba tace da shi komai ba har ya iso

yayi parking, fita yayi ya shiga, nan ta samu damar amsa Wayar Usheey da tun da suja aje su
take ta faman kiran ta, "Hello Seebi ina zai kaiki?" tayi daria tace "Asibiti" "haba har hankalin mu
ya kwanta" tana ganin ya fito tayi saurin katse wayar, Hannun shu dauke da ledoji 4 ya aje mata
3, dayan kuma ya aje a seat din baya yaja mota sukayi Asibiti.
Ko da suka isa Asibtin, har ta bude murfin mota zata fita, Zuciyar ta ta bata shawara, ko bazai
amsa ba, ki masa godiar dawainiyar da yake tayi daku, Abinci lunch da dinner baya fashin kawo
muku, ga kai ki makaranta da dawo dake duk da ba kullum ba.

Ta juyo ta gyara zama yanda tana fuskantar sa tace *"Hamma Rafeeq, Yau Dr ke sa ran
Sallamar mu, mun gode kwarai da dawainiyar da kakeyi da mu, Allah ya biya ka, Allah ya saka
da Alheri ya, Allah ya ji kan Magabata, Albarkaci Rayuwar ka, Allah ya kuma Saka maka duk
Zalincin da aka taba maka, wanda ba za ka iya yafe su ba"* tana kaiwa nan ta fice daga motar,
bata tsaya sauraren abun da zai ce ba, Yanda kuka san Hoto, haka Rafeeq ke zaune a gun, ko
yatsar shi ya kasa dagawa, be san lokacin da ya furta *"Ameen*" ba.
Haka kurum yaji dadin Adduointa, Shi be san meyasa ba, amma yana jinta a jikin shi, kawai
yaji ya bata babban matsayi a ran shi, jinta kamar FEE'AH.

Da k'yar ya kunna mota, saboda jikin sa ya mace gabaki daya, ji yayi ya kasa tafiya, guntun
tsaki ya sake ya duba Aljihun motar shi ya ciro paper da biro, rubutu yayi sannan ya fita ya
shiga Asibitin, daidai Dakin ya chokara a jikin kofar yadda in an bude zaa gani, yayi tafiayar sa.
Seebi na idar da Sallah ta dauki Abincinta, Su Nene har sun gama da Abincin da Nasiba ta
shigo dashi,nan zaman jiran Sallama sukeyi, Nasiba tace "bari inje in ga Dr, k'ila ma ya mance
da yace yau zai sallame mu" Nene tace "E danAllah, na k'agara inga nayi juyi kan Gadon K'arfe
na" sukayi daria duka.
Tana murda kofa wata kaaramar Takarda ta fado, duk'awa tayi ta dauka, ta na budewa tabi
rubutun da ido, Murmushi tayi a hankali tace "R-Lema" a nutse ta fita daga dakin ta fara
karantawa ga abun da yace
_"Ameen to your Duas. Idan an sallame ku, ga number na ki min text you DONT have to Call
just TEXT"_.
Seebi tayi murmushi ta sake karantawa, tace *"R-LEMA kenan Allah ka bani ikon taimaka ma
beautiful soul dinnan"*. Tasa kai ta wuce office din Dr. A hanya suka hadu da Dr da Nurse Sai
suka juya suka koma dakin.

Nurse ta gwada Bp da Temperaturen Nene, komai daidai, Likita yace "Mama, kin ji sauki
sosai, zan sallame ku, Amma donAllah ki rage cin Jan Nama" Nene ta bishi da kallon kai gaja,
tace *"yaro wani Nama ne Ja?"* yace "Naman Sa, ko na Awaki" Nene ta tuntsire da daria, tace
"Su balangu da tsiren da nake ci kake son hanani ci ko? Yace " Mama saboda Lafiyar ki ne,
bawai ina son hanaki bane" ta tabe baki tace "toh dai bari kaji Ubana *Mamman* Shanun shi 31,
duk bayan wata ake kashe mana daya, ba saidawa ake ba ci mukeyi, kuma ban taba jin ance
wani naman Shanu yasa shi ciwo ko wani abun Allah sauwak'a ba, toh nidai _Aminene
Mamman_ da bakin ciki ya kashe ni gwara Dadi ya kasheni Ehe" Nasiba tayi saurin cewa "I'm

so sorry, She's always like this, InshaAllah she'll regulte it" Dr yace "Dont worry i have someone
exactly like her at home" Nene ta cika tayi fam tace "Oho dai, Sai ka sallame mu yau, Ke kuma
ni zaki chanzawa ko? To in ma zagina kukai da Ubanki Mahammadu kuke" Dr ya fashe da Daria
yace "yi hakuri Mama ga takardar sallamar ki" yafi maka don yau ko baka sallameni ba gida zan
kwan" Nasiba ta girgiza kai cike da takaici, Hajjo kuwa sai daria take tayi.

Dr na fita Nene tace " _kinga latso min Zaidu bawan Allah a waya, ba gardama Seebi tayi yadda
nene tace, Yana ganin kiranta ya yanke ya sake k'ira
Zaid yayi Murna kwarai da jin Sallamar su Nene, kuma ya bata shawaran bin yanda Likita yace,
jin shi kawai Nene tayi don ba ta da Mak'iyi kamar me son rabata da Nama, nan dai ta hau yi
mishi Godia da Adduoi, Ya tsaidata ta hanyar cewa Haba Nene, Kun wuce nan, babu godia a
tsakanin mu. Sukayi Sallama. Bayan Seebi ta karba wayar ne yace mata zai turo a maida su
gida, tace ai "Hamma Rafeeq yace in gaya mai idan an sallame mu" da Mamaki Zaid yace
"Rafeeq dai?" tace "eh shi" shi da kanshi yace haka?" tace "eh" "Rafeeq yana zuwa ne?" tace
"Duk da ba shigowa yake ba, amma yana kawo mana Abinci Rana da Dare, sometimes ya na
aje ni makaranta" Allahu Akbar zo ku ga jin dadi gun Zaid, Ashe Rafeeq na da sauran Mutunci
da tausayi a tattare dashi? Be taba ganin Rafeeq ya damu da lamuran wasu ba kamar su Seebi
lallai akwai Improvement, yace da Seebi "to sai kun koma gida mayi waya" sukayi Sallama. Duk
zaton Nasiba da Nene Zaid ne ya sa Rafeeq dawainiya dasu, duk abunda yake yi saboda Zaid
ne, nan suka gane cewa ashe Rafeeq ne ya sa Kanshi, ba kowa ba. Nan Nasiba ta k'ara samun
wani k'warin guiwar Aiwatar da Kuddirinta.

Seebi ta kwafi numbern da Rafeeq ya bata, ta masa text din as he demanded. Ga abun
da tace;
_"Assalamu alaikum Hamma Rafeeq anyi discharging din mu, mun shirya, we are good to go"_

Yana wanka yaji wayarsa alamar shigowar sak'o, bayan yayi Sallah, ne ya daga wayar ya ga
message daga new number, ya bude ya karanta, dan guntun tsaki ya ja (Ikon Allah! sak kace
bashi yace ta mai ba).
Key kawai ya dauka ya fice daga gidan sai Asibiti, yana isa ya mata text "Ku fito".

Seebi na jin shigowar text ta duba taga Shine, ba su wani dau lokaci ba suka fito harabar
Asibitin da kayan su. Inda yake aje Motar shi sukayi, ta na zuwa ta iske Booth a bude, be fito ba
haka Seebi ta shiga saka a kayan boot sai da ta gama, sannan ta bude gaba ta shiga ta zauna
su nene kuma sun shiga baya. Sai da suka bar Asibitin, da kyar yace " Ya Jikin?" Nene ta murmusa a ranta tace Uban Kasaita,
a fili kuma tace "Alhamdulilah, na watsake" kamar ba zai ce wani abu ba yace "Sannu Fah" tace
"yauwa" a hankali tace kamar dangin Maguzawa wai sannu" Hajjo da Nasiba kadai suka jita,
Murmushi kawai sukayi, tun daga nan ba wamda ya sake magana har sai da suka iso gida, ya
juya ya dan kalli Hajjo yace "Hajjo Mom tace ki k'ara Sati daya sai ki koma gida" tayi murmushi
tace "ba damuwa"
Tare da taimakon Hajjo suka shiga da kayan su ciki, sai da ya tabbatar sun gama kwashe wa
ya danna horn, ta lek'o ta window, ya mik'a mata manyan ledojin Abinci, yaja motar sa yayi

gidan su Maalesh.

*England*

Zaid ne kwance kan tafkeken Gadonsa yana waya da Mami, inda aka bashi Ayman ta dinga
mai gwaran cin ta, har sukayi Sallama sannan ya kira Nasiba,
Suk gaisa ya tambayeta ya jikin Nene ta amsa masa da sauk'i.
Suka danyi hira sannan ya gaisa da Nenen itama ya musu Sallama.
Nan ya hau tunanin wanda zai sa ya musu Grocery shopping, don ya tabbatar suna da Buk'ata,
baya son takura wa Rafeeq, Saboda abunda ya fahinta, Rafeeq has done more than Enough,
kuma baya so ya k'ure shi .

Maalaesh ya fado ransa, Take ya kira wayansa, Ringing biyu ya dauka "Hello Mahmud" nan
take ya gane Uncle Zaid ne, don shi yasan shi kadai ke kiran shi da sunan shi na Asali,
"UncleZee ina wuni" suka gaisa, yace "Mahmud ina so donAllah ka min Shopping na kayan
Abinci, da kayan buk'ata na Gida, ina so ka kai wani Gida na nan ku sa da gidanku na
Layout(Gidansu Rafeeq yake nufi) Nan ya mishi kwatancen gidan. Malaesh yace "Angama,
anything for you uncle Z" barin je yanzu ma, "barin maka transferring kudin" da sauri yace "Noo
akwai kudi hanuna Uncle Z" "dont be Silly Son, i'm sending now" Murmushi Maalesh yayi yace
"Nagode" suka yi Sallama, Nan take Zaid ya mai Transfer din 100k.

2:47pm

Seebi na zaune bisa kujera yar tsugune, tana yi wa Nene tsifa, i Nene da Hajjo na kan tabarmar
k'asa, Sallama suka ji, da sauri Seebi ta zaro Mayafin ta kan Igiyar Shanya, Nene ta daura
dankwali tare da Amsa Sallama, Maaleah yace "donAllah nan ne Gidan Nene?" da sauri tace
Eh Yaro Shigo, nice nan Aminene, yace toh ina zuwa, Yara ya samu ya sa su kwasan kayan ya
ce suka shiga gidan nan, Mamaki ya rufe su Nene, ana haka ne Maalesh ya bi bayan su ya
shigo, yana ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login