Showing 66001 words to 69000 words out of 151322 words
Chapter 23 - Ke Alkhairi Ce Book (Complete) BIEBEE ISA--.pdf
Hajjo ya bude baki "Laaaah Hajjo, kece nan?" tace "Maalesh yaushe a gari?"
yace "jiya na shigo, na tambayi Mom kina ina tace ba kya nan" tace aiko dai gani anan, ya
durkusa ya gaida Nene, ta amsa mai cikin Fara'a, yace "kece Nene daga gani" ta nuna kanta da
Yatsa tace "Nice nan Aminene Yar Mamman, duk duniya ba wata Nene sai ni" ta nuna Nasiba
da hannu tace "Nenen Seebi kake ji" ya juya ga wacce aka cema Seebi, ya ga shi take kallo,
tsaf tagano shi, shine wanda kwanaki da zai basu Lift yace sai ta cire Nikab, kuma Shine Abokin
R-Lema, ta dai maske ta gaishe shi, "Lord have Mercy" inji Maalesh, tuni Nasiba tayi gaba da
Imanin shi, da kyar ya amsa mata fuskar shi cike da Annashuwa.
"Hajjo tace Maalesh wannan kayan fa?" yace "Uncle Zaid yace a kawo" Nene ta chafe "Allah
Sarki Zaidu Bawan Allah, Allah shi biyaka ya saka da Alheri, Malush kaima Nagode maka" Yayi
daria yace Nene "Maalesh nake ba Maalush ba" duk sukayi daria, na da nan Maalesh suka
dinke da Nene, k'wank'waman su iri daya na surutu, sai yi suke tayi yanda kasan sun dade da
sanin juna, dama shi Maalesh saurin Sabo ne dashi, nan Hajjo ta zubo mai Burabusko ya
kwasa kamar ba gobe, sai kallon Nasiba yake tayi, ita kuwa sai smilling take tayi tana jin
diramar su da Nene, har kusan Laasar be da niyyar tafiya. Wayar sa tayi k'ara, ya ciro daga
Aljihu ya duba, ya kalli Hajjo yace dan gidan ki ne, tayi murmushi tace "Rafeeq Ho" ya dauka
"my guy howfa?" kusan sakwan 3 beyi magana ba chan yace "kana ina? Nazo gida baka nan"
Maalesh yace "Wallahi gani ta wurin gida Uncle Zaid ya aikoni" tsaki Rafeeq yayi yace "ina
jiranka" ya kashe wayar, Nasiba ta tsura wa wayar Maalesh ido, kamar tana jiran Rafeeq ya fito
daga ciki, Nene tace "Wannan uban Yan k'asaitan ne ko?" Maalesh yayi daria yace "Nene
kinsan Rafeeq ne?" ta ta6e baki tace "ai wannan sai kun hada mai da tofi" yayi daria yace barin
je, sai na dawo ya musu Sallama ya kalli Nasiba yace "Bye Beautiful" ita kunya ma ya bata ta
rufe fuskar ta da tafin hannayen ta.
Yana shiga Dakin shi ya ga Rafeeq kwance kan Gado, ya bubbuga mai k'afa, kamar ba zai
tashi ba, ya mike sukayi side hug, Maalesh cike da doki yace "I met her, Wallahi naganta yau"
da k'yar Rafeeq yace "Who?" Maalesh yace "The love of my life, Seebi, Uncle Zaid ya aike ni
Gidan su yanzu in kai ma Nene sak'o" a dan tsorace Rafeeq ya kalleshi, kamar zaice wani abu
sai ya fasa, be damu da Rashin Ansashi da Rafeeq yayi ba, Maalesh ya cigaba "Shes beautiful,
ai kasanta, ta hadu ko? Zamu dace? Haka ya ishe Rafeeq da maganar Nasiba, yace " Guy do
you think she'll like me? Wallahi ina sonta, kawai ganinta nayi gefe na kamar an jefo ta, ina
ganin ta naji She's the one, wannan shi ake kira "LOVE AT FIRST SIGHT" cikin kufula da daga
murya Rafeeq yace "Will you Shut the f**k up?
_Bibilicious Biebee_
í ½í±§í ¼í¿½KE ALHERI CEí ½í¹‡í ¼í¿¼â€�♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg4⃣1⃣
Maalesh ya kalleshi da mamaki yace "Guy, Calm down" Rafeeq yayi guntun tsaki cikin
yanayin shi yace "ban ga dalilin da zai sa ka dinga min maganar wata yarinya ba, duk ka bi ka
ishe ni" Maalesh cikin doki yace "Feeq ba zaka gane ba, Wallahi ina sonta, sosai fa" kamar ba
zai ce komai ba yace "She's Innocent, dont hurt her" da sauri Maalesh yace "Wallahi i wont,
shes not like the rest of the girls i'm with, Wannan ta dabance, guy bani shawara ya zanyi?"
chan cikin mak'ogaro yace "Tell her" "bansan mesa ba i lost the courage, ai da tun dazun na
gaya mata" Rafeeq yayi shiru ya cigaba da latsa wayar shi be ce komai ba, Maalesh ya yi
rigingine kan Gado, Rafeeq ya dora wayar shi kan cikin Maalesh, Maalesh ya tashi da sauri ya
dauki wayar Rafeeq ya duba, kan Screen din ya ga Message ya karanta, ya kalli Rafeeq don
neman k'arin bayani, guntun tsaki Rafeeq yayi yace "The girl's Number" wani irin super
Maalesh yayi ya duro, ya rungume Rafeeq, donAllah numbern ta ne? Kai Nagode Breh, naji
dadi Wallahi" Shi dai be ce dashi komai ba, Maalesh yayi copying number din yayi saving a
wayanshi.
Tana tsakiyar su Nene suna fira, wayar ta yayi ringing, ko da ta duba New number ne, ta
dauka da Sallama, Muryarta yafi komai dadi inji Maalesh, ya amsa yace "Hello, Beautiful" wani
ajiyar zuciya ta sake ta amsa da Ina wuni don ta san me muryar, yace "kingane me magana ne?
Cikin jin kunya tace "eh" to waye? ta yi Murmushi tace "Ya Maalesh ne" Waiyo dadi, Ya
Maalesh, karo na farko bayan Rasuwar Rafee'ah yaji an kirashi ta wannan sigar, yace "Seebin
Nene, you are a Blessing, kinji Voice dinki kuwa?" kunya ya bata sai bata amsa shi ba, yace
"are u there? Kinyi shiru?" a hankali tace "i'm here" "Seebi will you be my friend?" Daria kawai
tayi, ya kike daria? "Ba kya so in zama Abokin ki? A hankali tace "Aa" yace "Aa mene? Kina
so? Will you be my friend? A hankali tace "yes" Darian jin dadi yayi yace "let me warn you, my
friends usually say i'm a Sweet Soul, abun nufi shine Wata rana Abokantakar mu na iya rikidewa
ya koma Soyayya" Daria kawai tayi, nan suka sha fira don Maalesh akwai Zance, sun dade
suna waya inda ya shaida mata zaizo Gobe don Jibi zai wuce Kano inda yake Service.
*Washe Gari*
K'wank'wasa k'ofar yayi, sai da ya kusa minti 3 kafin yazo ya bude mai, hararar shi Maalesh
yayi ya ra6a ta gefen shi, ya shige cikin Dakin, Da k'yar Rafeeq yace "Sorry i missed your call"
Maalesh yace "and you cant call back?" Guntun tsaki Rafeeq yayi yace "I said i'm sorry didnt i?"
Maalesh ya k'ulu ya mik'e zai fita da sauri Rafeeq ya rik'o shi, kasa magana yayi ya girgiza
kanshi, Maalesh ya dawo ya zauna, Rafeeq yace "Look, wannan Aneesar banzan ce take
takura min, shisa na kulle k'ofana, coz duk abunda zan mata bazata yi zuciya ba, so da ka kirani
i thought itace shisa ban dauka ba" Maalesh ya girgiza kai cikin takaici, ya akayi sunana da na
ta yayi kama, har da ka zata itace?" a takaice yace "ban duba wayar ba" "Oh lord have Mercy"
Inji Maalesh da sauri Rafeeq yace "Kayi kyau Sosai, ina zakaje ne haka?" Don dai ya 6atar da
zancen don yasan Maalesh da mita kamar Nenen Seebi. Murmushi Maalesh ya sake yace
zanje Gidan Nene ne, zanje musu bankwana, Tsaki Rafeeq ya sake "Do you really have to go
there?" Maalesh ya amsa da sauri "Yes My other Half is there" wani Mugun tsaki Rafeeq ya
sake tare da kwanciya kan Gado, Maalesh ya mik'e yace "Feeq, barin je sai na dawo" da sauri
Rafeeq yace "Wait" da Mamaki Maalesh ya kalleshi, Rafeeq ya dauke ido be so su hada Ido da
Maalesh yace "I'm Bored, i'm coming with you" be jira cewar Maalesh ba ya fice daga dakin,
Maalesh da mamaki ya maimaita "He's Bored?" Sabon Salo, gemu a kafada, yau Rafeeq yake
cewa he's bored, shida be k'i ya kulle kanshi a daki ba, be komai, lallai kam, toh K'ila ya fara
Chanza halinshi, Allah ya sa don sai nafi kowa Farinciki, ya fita tare da kulle dakin da Mukulli ya
bi bayan Rafeeq.
Bakin Zauren Gidan Maalesh ya doka Sallama "Assalam Alaikum" daga Ciki Nene ta Amsa,
tare da cewa "Bismillan ku" Maalesh a gaba Rafeeq na bin shi a baya sai shan k'amshi yake
tayi, kamar an ce dole sai ya shiga, ta Window Nene ta hango su, da sauri ta fito tana tafa
hannayen ta, tana fadin "Ga Maalush ga Maalush" wani Murmushi Rafeeq ya saki ba tare da ya
sani ba, suna hada ido da Nene yayi saurin daure fuska tare da dauke kai, ko meyasa be so
taga Murmushin shi oho,a fili Nene tace "Chan ta Matse maka a matsatsen wandon ka"Maalesh
ya fashe da daria, yace Nene ke dawa?" ya juya ya kalli Rafeeq da ya hade girar sama da ta
kasa, Nene tace ni rabani da wannan Mara fara'a, Sannun ku da zuwa dai" ta bude baki tace
"Seebi, fito da tabarma, ga Malush da Dunkum" Maalesh dai sai daria yake tayi, Hajjo ta fito,
suka gaisa da Maalesh, tace "Rafeeq" Murmushi kadai ya mata, ya dauke kai, Nene sai ikon
Allah take kallo, a ranta tace "Lallai yaro, kazo gidana ka dinga sha min kunu? To uban tauri ma
yaci ubanshi" ta gyada kai ta shiga cikin kichin don ita kadai tasan me zata ma Rafeeq, Nasiba
taji dadin zuwan su, ta dauko Tabarma ta fito kanta a k'asa ta shinfida musu, Maalesh ya fara
zama sai Rafeeq, Maalesh ya bita da ido, ta dukursa ta gefen da Rafeeq ke Zaune tace "Ya
Maalesh, Ina Wuni?" Maalesh yace "Lafiya lao Beautiful, ya Jikin Nene?" "Nene ta ji sauk'i
Alhamdulilah" Kafin yace komi wayar shi ta fara ringing, ya dauka, Nasiba ta kalli Rafeeq, duk
da ba ita yake kallo ba yasan shi take kallo, kamar ance ya kalleta, Idanuwan su suka hadu, ido
cikin ido suke kallon Juna, a sanyayye Nasiba tace "Hamma na Ina wuni?" tsaki yayi ya dauke
kansa, ko a jikinta ta tashi ta koma ciki, da sauri ya bi bayanta da ido, duk ya ji haushin da be
amsa ta ba, tsaki yayi ya juya ga Maalesh, ashe tuni ya gama wayar, kallon juna sukayi, Nene
ta katse musu hanzari, gaban Maalesh ta ajiye kwano, tace "Maalush dan Albarka, ga Zogale
na kwandon ta maka kaci kai kadai kar ka ba kowa" ta karasa fadin haka tana kallon Rafeeq ta
gefe ido, sosai ta ba Rafeeq daria, kallon Gefen shi yayi ya dinga Murmushin mara sauti a
ranshi yace "Chill Tsohuwa, i cant eat this Sh*t" Maalesh yace "Kai Nenen mu kina ji dani fa,
duk wannan ni kadai?" Ehmana dole nake ji da kai, wasu ko kallo basu isheni ba ai" Rafeeq ya
kawar da kanshi gefe don yana gudun kar daria ta kubuce mai, wai don shi tsohuwar nan ke
habaice habaice, lallai tana da damuwa, ta shekara tanayi ko a jikin shi, haka Maalesh ya zage
sai cin Zogale yakeyi, da yake shi yana son abubuwan gargajia, Nene ta dauko kujerar tsakar
gida ta zauna, don ta na ta Rok'on Allah sa Rafeeq ya nuna yana son ci ta k'are mai tanadi. Ga
Mamakin ta har Maalush ya gama Rafeeq be dago kanshi ba, Rafeeq ya zunguro Maalesh, ya
k'agara su tafi, Maalesh yace "Nene, bari mu tafi, gobe zan koma kano InshaAllah" Nene ta hau
suburbuda mai Adduo'i kala kala, ta kwalawa Seebi kira tace kuzo kuyi bankwana Gobe zai tafi,
ta fito ta raka su har Waje.
"Ya Maalesh a kano kake aiki? Yace aa, Service nakeyi, befi wata 2 in gama ba, sai in samu aiki
sai in fito a sa bikin mu ko? Dariya tayi sosai tace "you are funny" yace "you think so ko?" ya
kalli Rafeeq yace "Guy, tell her ba wasa nakeyi" tsaki Rafeeq ya buga tare da bude mota ya
shiga, duk ba su damu ba don sun san saran Rafeeq na tsaki, sai da sukayi Sallama kafin ya
Shiga mota suka wuce.
*MAFARKI*
"Assalam Alaikum Nasiba" Murmushi tayi tace "Sai yau Ko Yaruwa ta Rafee'ah?" "Afuwan
Ukhti, Ya Hakuri da Hidima?" Nasiba tace "Toh mungode Allah" Rafee'ah ta fara magana cike
da natsuwa "Da farko zan fara da gode miki, kin aiwatar da Aikin Farko da na saka ki, ina me
miki albishir da kin riga da kin shiga Rayuwar Rafeeq, kinyi Namijin k'ok'ari, ina jinjina miki, abu
na gaba shine, kinsan ance duk yanda mutum keso ya ci Nasara, ya kuma samu Albarka da
Ribar Rayuwa, to ya bi Mahaifanshi, Musamman Mahaifiya, duk yanda kake son samun
Nasarar Rayuwa, Idan baka bi Mahaifiyar ka ba, to ba zaka taba ganin daidai ba, duk me ka
taba zai ruguje, kai ko da ka samu to bazaiyi Albarka ba" Nasiba ta jinjina kai tace "Haka ne"
Rafee'ah ta cigaba "Toh abu na gaba shine, ki daidaita tsakanin Rafeeq da Mahaifiyar shi, indai
kina so Rafeeq ya gama Makaranta wannan Zangon, to dole sai ya samu Albarkar Uwa, ba
wannan ba dai, Duk da yana cikin Duhu, ya nemi gafarar Uwarsa, don ko yau ya fadi ya mutu
sai Allah ya tambaye shi, don be nema samun Haske ba, ki Daidaita tsakanin su, Nasiba"
Nasiba cikin Firgici tace "Ta ya zanyi haka? Kinfi kowa sannin kafiyar Rafeeq, ina zan nema
Mahaifiyar ku? Ina zan ganta? Ta ina zan fara?" *Ke Alheri Ce* *Ke Alheri Ce* *Ke Alheri Ce
Nasiba Muhammad* bat ta Rafee'ah ta bace, a firgice Nasiba ta farka daga Baccinta, "ki
taimake ni Rafee'ah, atleast give me hint ya zanyi? duk ta bi ta jike da zufa, Minsharin Hajjo ya
tunasar da ita Mafarki ne tayi, da sauri ta sauka kan Gado ta fita daga Dakin, ta dauro Alwala
tazo ta kabbara Sallah, sai da tayi Raka'ah Shidda kafin ta dukufa da Adduoi, Alkah ya shige
mata gaba, ya kawo mata komai a Sauk'ak'e.
*9:45am*
"Ki tsaya kiyi Kallaci Seebi" "Aa Nene zanyi a Makaranta, sauri nake kar bus ta tashi" "to
Allah ya taimaka, a gaida miemo gayu" "Zataji sai na dawo" da sauri ta bar Gidan ta na ciro yar
Tecno dinta a jakka ta latso number Usheey, "Usheey, kin isa National? Akwai Bus? Usheey
tace " Eh Seebi, biyu sun tashi saura daya, kiyi sauri kar ta cika mu tafi" Seebi kamar tayi kuka,
tace Gani nan na kusa bakin Titi, zan samu Napep" "Okay to sai kinzo" Ji take kamar tayi gudu,
don in Last bus ta wuce bata san yadda zatayi ba.
Kamar a sama ta ga Motar Rafeeq a gabanta, bata san lokacin da ta sake Murmushin da ke
kara ma fuskar ta kyau ba, ba watawata ta zagaya ta bude K'ofar ta shiga, k'amshin sa ya sa ta
lumshe ido, ta bude baki zata gaishe shi, sai kuma ta tuna wani abu sai ta fasa, har ya ja motar
shi shiru shiru bata gaida shi ba, ya saurara yana jiran ta gaishe shi amma bata ce ko 'a' ba, a
ranshi yace ko lpy? Ta gefen ido ya kalleta sai hura hanci take yi, tana girgiza kaf'a tana kallon
window, yau kuwa meye Haka? Guntun tsaki yayi yace ma kanshi "why do i even care?" ya
dauki hanyar Makaranta, kusan minti 10 ba wanda yace da danuwan sa k'ala, Nasiba tayi wani
shu'umin Murmushi, sun kusa Makaranta daidai Daji-dajin hanyar, Nasiba ta daddage ta buga
tsaki da k'arfi, har cikin kunnen Rafeeq, da sauri ya dafe kunnensa da hannu daya, be yi
magana ba, Tsut ta k'ara jan wani tsakin da ya fi na farkon k'ara, Haushi ya cika Rafeeq, kamar
yayi me, be dai tanka ta ba, ya tsani Tsaki (kuji mun Rafeeq, wai ya tsani Tsaki) Nasiba na lura
dashi, ta k'ara jan wani dogon tsaki daidai ta taka burkin Motar da Rafeeq yayi ji kake k'iiiiiiii,
Nasiba ta tsorata sosai, ta kalleshi cike da tsoro, ba tare da ya kalleta ba yace "Get Out" Nasiba
ta juya ta kalli dajin nan ga sanyi, gashi bata tunanin zata samu na Allahn da zai karasar da ita
Makaranta, har zata bashi hak'uri, sai kuma ta fasa, bude k'ofar tayi ta fita, kamar jira yake ya ja
motar shi ya wuce, ya barta nan tsaye, hawaye suka soma kwaranyowa, tayi dana sani,
meyasa take son k'ureshi? Ita dake son fiddo shi daga yanayin da yake ciki, Meyasa ta k'osa, to
gashi ya direta kan hanya, kuma ba zata iya takawa ba, don tafiar da saura, ta rasa yanda
zatayi ta zauna gefen Titi ta na me rokan Allah ya kawo Bus ta tsaida su ko a tsaye sai ta tsaya.
"Mtswwww" tsakin da Rafeeq yayi kenan Karo Na 8 bayan ya dire Nasiba, meyasa zai
ajiye ta bakin hanya? Yanzu if shes not careful Mota ya bugeta fa? Tsaki ya sake yi tare da
kallon Mirror dinshi, chan ya hango ta zaune gefen Titi kamar Almajira, Tsaki ya sake yi yasa
trafficator yayi U Turn ya koma Baya, horn ya mata da sauri ta dago ta sake Murmushi, a ranta
tace "Ba zai iya bari na anan ba" kawar da kanta tayi gefe kamar bata ganshi ba, tsaki yayi da
k'arfi, ya danna mata horn, ko dagowa batayi ba, takaici kamar me, wai shi yau ake ma haka?
Allah Allah take kar yayi zuciya ya barta nan, amma wani zuciyar ta bata karfin guiwa, Matso da
motar yayi kusa da ita ganin zai take mata k'afa yasa ta tashi ta hau kan dakali, da k'yar yace
"Get In the Car" A takaice tace "No thanks" tsaki yayi yace " Nace ki shigo ko? So