Showing 75001 words to 78000 words out of 151322 words
Chapter 26 - Ke Alkhairi Ce Book (Complete) BIEBEE ISA--.pdf
is, i cant eat that" kamar ta san abunda yake cewa
tayi saurin cewa "Karya yake, a shinshina hannun shi" Maalesh ya shashantar da maganar ta
hanyar tambayar Nasiba tace "ai Nasiba kwananta 4 Kaduna Jibi zata dawo" "Lord of Mercy" inji
Rafeeq, so All this While Nasiba na Kaduna? Yake bata lokacin shi on this Woman? Yazo ya
sha zaman banza amma bata ce mishi Nasiba ba ta nan ba? (Ka tambayeta ne?) dogon tsaki
yayi ya fincike mukullin hannun Maalesh ya fita, Nene ta bishi tana dariya tana fadin "Dunkum
tsaya kaci Fara, tsaya a k'ulle maka Leda" daria takeyi sosai, don ta san yau tayi maganin
Dunkum, Maalesh yayi Dariya, yace "ranshi ya baci, barin je" tace ranshi ne ya baci? To ya sa
omo ko kilin ya wanke shi" Maalesh yayi dariya, yace barin je Nene zan dawo Anjima nima iso
wata kenan" tace "Allah huta gajiya" ya fita amma be ga komai ba sai k'urar Motar shi,
Murmushi yayi ya taka zuwa Gidan Lema a k'afa.
Yana shigowa dakin ya fada Toilet dinsa, Shower ya sakar ma kanshi, tunani kala kala,
wai me ke kaishi gidan Nene ne? Zuciyar shi ta bashi amsa da "Kana kewar wannan Yarinyar
ne" da sauri yace "Noo, ba ita nake missing ba, i only miss seeing my Sister in her" tsaki yayi
yace "stop getting to my head i dont want" haka ya cigaba da magana shi kadai kamar zararre.
*5:00pm*
Zaman kadaici ya ishi Nene, ta rasa yanda zatayi, gashi ita ba gwanar shiga Makota ba, don
gidajen makwabtan akwai Karnuka, kuma ai ta k'wank'wasa wa ba a amsa, Wayar Nasiba ta
dauko ta kura wa wayar ido tana jira a kirata, shiru, ta na ta 'yan latse latsen ta, bata san ma dai
abun da takeyi ba, tsaki ta buga "ina dalilin zaman mutum shi kadai" (Nene ke kika jawo) ta
jawo Gyalenta ta fita waje,tana kallon Unguwar, Mugun tsaki ta buga da ta ga Unguwar Wayam
ba ko dabban da ke wucewa, Kamar a sama taga wata Mota Me kalar bula(blue) ta doso ta, ai
da murna ta fara sa ma Motar Hannu.
Birki na cikin motar su ka ja k'ii, don ba su lura da ita ba, a fusace Meema ta fito, Aneesa ma
ta fito, Nene da Murmushin ta tace "Sannunku 'yan jikokina, kuyi hak'uri na tsaida ku, DonAllah
ku dan latso min Zaidu bawan Allah a wayar nan" ta na me mik'a musu wayar Nasiba, Meema
ta kalli wayar cike da tsana tace "Ke Almajira, in banda jahilci, ba ki sanmu ba zaki tsaida mu
kice mu kira miki wani? Har kina daura k'azamin hannun ki kan mota ta?" Aneesa tace "Aunty
Mee mu tafi don Allah, irin wannan da su ake conspiring a maka wani mugun abun, its all a
ploy" Ta ja hannun Auntyn ta, suka koma Mota, Meema ta ja motar tare da bad'e Nene da k'ura,
yanda kuka san Hoto haka Nene ta tsaya, wai yau ita a ka ci ma fuska kuma ba tace komai ba,
haushinta daya da ba ta ci uwar babbar su ba, amma a fili tace "Ubangiji Allah ka sake hadani
da su" ta koma Cikin Gida tana jin haushin kanta.
*Malali Kaduna*
"Nasiba, kin taba ganin uwar da tayi fushi da danta? ko tayi fushi dashi na wasu lokaci ne, ko
me ya ke mata ba za ta tab'a fadin Mummuna kalami a kanshi ba, tsakanin d'a da Mahaifi sai
Allah, balle ni da ban taba ganin Laifin Rafeeq ba illa Laifina, nice na sakashi a halin da yake
ciki yanzu". Nasiba ta kamo hannun Mami tace "karkiyi Blaming kanki, k'addara ce ta riga Fata,
nidai DonAllah kice kawai ki yafe mishi duk da kince be miki komai ba" Mami tayi Murmushi tace
"Toh Nasiba, na Yafe ma Rafeeq Duniya da Lahira, na yafe mishi, Ubangiji Allah ya sa ya gama
da Duniya lafiya, Allah ya bashi saar karatu, Allah ya ma Rayuwar shi Albarka" da sauri ta
Rungume Mami dadi kamar ya kasheta, ita a ganinta zataji Saukin komai tunda Rafeeq na tare
da Adduar Mahaifiya, tace "Ameen Mami, ki Cigaba da mishi addua kullum, InshaAllah ba zai
tab'a tab'ewa ba" Mami ta tsura wa Nasiba ido cike da k'auna tace "Bless you Daughter, you
have an Amazing Heart, Ke Alheri Ce" Murmushi kawai Nasiba tayi, don bata son tayi magana
Mami ta cigaba da kukan da takeyi, tace "Mami yaushe zakizo Katsina? Katsina na missing
dinki" Murmushi tayi tace "i have no Bussiness left in katsina, Duk Wata Baba na da Mama na
su na zuwa duba ni" Nasiba ta sigar zolaya tace " are you sure you have no Bussiness in
Katsina? Mahaifarki ce fa, besides, your One and Only Love is there, nasan he still inside that
pure heart of yours" Mami ta daburce tana unconditional Murmushi, tace "ke Nasiba maganar
me kikeyi haka? Shuttup ni ba kowa a zuciya na, na tsufa" Nasiba tayi dariya tace "Is that so?
Then why are you blushing?" Murmushi Mami tayi tace "How i wish zan sake ganin Habibullah"
"Awwwn Mami ta tuna da tsohuwar Zuma" tace "Kinsan ana cewa Zaid me kyau ne, Hafiz Me
kyau ne, amma Wallahi duk Habib ya fi su kyau, harta Rafeeq da ke kama dashi be kamo k'afar
shi ba" Sosai Nasiba tayi daria tace "zai k'ara kyau idan kika koma dakin ki" Mami tace "Hmm
nagaji da tsammanin Ranar nan" Nasiba tace "Dont worry Mami,Akwai Allah, gaskiya zata
baiyana, zai gano gaskia da na rashin bincike ne ya sa shi daukar mataki take yanke, amma kar
ki damu, Have faith" Mami tace "dadi na dake you give me Hope" Sukayi Murmushi, kuma chan
sai Mami ta fara matsar k'wallah, Nasiba tace bari in kira miki Nene ki sha dariya.
*Washegari*
Ina Nasibar ne? Sai mun rasa Motar K'arfe 10? Ummi tace "wai ta shiga yi ma Mamin Ayman
Sallama yanzu zaka ga ta taho" Abii yace ai gwara tazo mu ta tafiya.
Mami tace "Yanzu ba zaki k'ara mana hutun ba? Kin bari mun saba sosai sai kice zaki wani
koma?" tace "Ayyah Mami, nima na saba dake Sosai, idan mun tafi ba zamu dade ba zamu
dawo, trust me zan dawo" Mami tace "to shikenan, ga wannan kiyi using as Pocket Money"
"Nooo Mami i cant accept your Money" Mami ta tsura mata ido, tace "ni na dauke ki ne a
matsayin Rafee'ah, and i can do anything for you, don break my heart" "Mami kudin sunyi yawa
ne ki raba biyu" " Haba Nasiba dubu Goma ne fa, ba yawa, inshort why dont you be like
Rafee'ah? Be like Mami kudin sun min kadan, i need more" daria Nasiba tayi tace "Okay, I'll
accept this Nagode" "Yauwa diyata" tace "One more thing" ta zaro dan karamin Zoben da ke
k'aramin yatsar ta ta sa ma Nasiba a yatsa tace "this is my love for you" Nasiba ta bi zoben da
kallo, tana so ta tuno inda ta san Zoben, Zoben me kyau ne sosai, kuma Azurfa. Mami tace
"kinsan waya bani Zoben Nan?" ta girgiza kai, Mami tace "Rafeeq ya bani shi on my 40th
Birthday, Daga Dubai ya sa akayi su Guda 2, ran Birthday na ya sa min a yatsa yace "Mamina,
this is my love for you" ya bani gudan yace in sa mishi a, yace "this is the twin of your ring, even
if we are far from eachother, this Ring is linked to Our hearts" daria kawai nayi nace dashi"he's
Crazy" amna Nasiba yanzu Rafeeq ya tsane ni, nasan Ya dade da wurgar da Zoben shi" Nasiba
tace "Aa Mami, wallahi be wurgar dashi ba, yana nan a yatsar shi, ni na san na san Zoben nan
a wani wuri, a Yatsar Rafeeq na sanshi" Mami tayi dariya tace"Nasiba kenan, you want me to
feel better, shikenan naji, its yours now" Nasiba tace "Aa Mami, wannan naki ne, ki ansa" Mami
tace "bansan gardama tashi muje, ni ma zan kai ku tasha, kar ku rasa motan hawa" suka fita
tare, a ranta tace "with this Ring Rafeeq, you'll be your Mother's Son Again". Da sauka shiga
gida ne ta nuna ma Ummi kudin da Mami ta bata, Ummi ta mata fadan meyasa ta amsa, Mami
tace don na ba diyyata kudi shine nayi laifi? Ko iko zaki nuna min kanta ki nuna min diyarki ce,
tace "laaaah Mamin Ayman be kai nan ba, ai an fi so diyarki taji tausayinki" Mami tace kya dai ji
dashi, gabaki daya sukayi daria.
*4:00pm*
*Layout, Katsina*
"Sannun ku da zuwa, kun sha hanya" Ya mutan Kaduna? Duk suna lafia, Nene ta gabatar
musu da Danwaken da ta musu, tana basu labarin zaman kadaicin da tayi, Nasiba tace "Oho
dai, ke kika jawo, sai da na ce miki ki taho mu tafi kaduna, ki ka k'i" tace "ke ni ban son mita ba
gashi kin dawo ba? Ko wani abun ya kamani?" tace"kin daiyi kewa ta" Nene tace ko kadan, ban
k'i ki koma ba, ko a habar zane na" Abbi dai na jin su sai dariya yake musu. Suna cikin cin
danwake sai ga Maalesh da Rafeeq sunyi Sallama, da Sauri Nasiba ta kalli kofar zaure don jin
muryar shi, sanin kanta ne tayi missing din Hamman ta, shima karaf idonshi kanta wani
naunauyar Ajiyar Zuciya yayi, "Finally! shes back" Maalesh kuwa Murmushi ya bita dashi,
Maalesh ya matso ya ba Abbi hannu, ko be sani ba yasan Baban Nasiba ne, Abbi ya bashi
bayan hannu don yana cin danwake da hannun, Maalesh a ladabce ya gaida shi, Nene kuwa
cewa takeyi Sannu da Zuwa Malush, Nasiba ta tashi da sauri tayi kamar zata shiga kichin,
daidai yanda zaijita tace "He's my Dad, show some Respect" harara ya bi bayanta dashi, yayi
dan guntun gajeren tsaki ya da zata ji shi ita kadai, ya dan matsa kusa da Abii da k'yar yace
dashi "Barka da Yamma" Abii yace "Muna lafiya?" Ido Cikin Ido suka kalli juna, nan da nan yaga
baban Nasiba ya mai kwarjini, haka kurum ya kasa shiru ya amsa da "Lafiya k'alau, anzo
lafiya?" Abbi yace "Alhamdulilah" Nene tace "Ahh su Dunkum yau anyi Wayau" Hararar ta yayi
ya dauke kai, Abbi na kallon shi, akwai wani Hikima tattare da yaron, akwai wani abun da ya
hango game da yaron, daga gani Yaron dan Baiwa ne, yanda yake abubuwan shi, yana kallon
yanda Maalesh ke bin Nasiba da ido, amma shi wannan kallo bata ishe shi ba, haka kurum yaji
yana son sanin game da Yaron, bude baki yayi yace "Seebin Nene, zubo ma bak'i danwake"
Maalesh Yace "Aa Baba mungode bana cin danwake" "Abokin ka fa?" da sauri Nene tace "Ya
k'oshi da dai Fara ne, wannan ko ba a bashi ba zai dauka" duk suka bita da ido cikin rashin
Fahimta, dauke kai Rafeeq yayi, Abii ya k'ara cewa "a zubo maka Danwaken?"Kamar jira
Rafeeq yake yayi saurin hadiye wani miyau, tun da ya shigo gidan ya ke bin Danwaken plate
din Abbi da ido, ya sha Mai, da kayan hadi, yana iya cewa Danwake ne best food dinshi, rabon
shi da ci tun Mami na nan, kuma gani yake wannan tsohuwar da gayya take abubuwa don ya
nuna ya na son ci ta samu damar Wulakanta shi, girgiza kai kawai yayi alamun aa, in har yace
baya son cin danwaken nan to yayi k'arya, har ranshi ya biya, kuma besan dalilin da ya sa Nene
keyin duk wani abun da yake son ci ba, shi da abinci be damai ba, tsaki kawai yayi, Duk abunda
yakeyi a idon Abbii, ya kalli Maalesh yace "ya sunanka?" Maalesh cikin ladabi yace "Sunana
Mahmud" Nene tace "laah gaka da suna me dadi amma ka yarda ake ce maka Malush" daria
kawai yayi, Abii ya maida hankalin shi kan Rafeeq da kwatakwata ya dauke kai, yace "Kai fa ya
Sunan ka?" Rafeeq yayi kamar be ji ba, shi kuma Abii be sake tambayan shi ba, Nasiba kuwa
jikin ta ya fara rawa, bata so Rafeeq yayi banza da mahaifinta, bata so mahaifinta ya tsani
Rafeeq kan halaiyar shi, da Rafeeq yaji shiru, ba a sake tambayan shi ba, ya dago kai a hankali
ya kalli Abii, shima shi din yake kallo, gajeren tsaki yayi a hankali yace "Sunana Rafeeq" Abii ya
jishi sarai, yace "Banji ba" kamar ba zai tanka ba, amma Abii ya mai girman da ba zai iya share
shi ba, ya dan bude murya yace "Sunana Rafeeq". Abii ya jinjina kai, Rafeeq yayi Zumbur ya
mik'e sabida yana jinshi wani iri gaban Abii, ganin haka Maalesh yace "to Nene mun gaida ku,
bari mu wuce" tace "Toh Malush mungode, su Dunkum a gaida gida" tuni ya kusa Zaure, Abi ya
bude murya yace "Rafeeq" k'yam ya tsaya ya kasa tafia, da k'yar ya juyo, Abii ya kalli Nasiba
yace "Je ki zubo mishi Danwaken" a hankali Rafeew yace "Nak'oshi" Abbi yace "Ka tafi dashi
anjima sai kaci" dama tuni Nasiba ta cika Umurnin Mahaifinta, ta kawo ma Rafeeq Coolern,
dauke kai kawai yayi, ganin haka yasa ta ba Maalesh Coolern, Maalesh ya amsa yayi Godia, ya
ja Rafeeq suka bar Gidan. Nene tace "Yau kam me ke damun Dunkum?" Abii ya zauna yace
"Seebin Nene, Wanene wannan? Me kika sani game dashi?" Gaban Nasiba ya yanke ya fadi,
Nene tace " ai wannan shin d'an Zaidu Bawan Allah da na jima ina baka labari, shi haka yake,
wani Dunkum, ba fara'a, ba ilhamar fuska, yanda kasan takashin shanu, haka fuskar shi take
murtuk'e kullum" Abbi ya jinjina kai, yace "Seebi, bakin ki akwai Magana, me kikasani game
dashi? Ni na hango bak'in duhu tattare dashi" Nene tayi karaf tace "bawani bak'in duhu, Fadin
Rai ne kawai ya mai yawa" Seebi tace "aa Nene, akwai wani Labarin da ban sanar dake game
da Rafeeq ba, kunji kunji••••••••••. Tsaf ta kwashe labarin Gidan Lema ta basu, kamar yanda
Baba Maigadi ya sanar da ita, kamar Yanda ta gaya ma Mami, Ta dai b'oye Mafarkin da take da
Rafee'ah. Allahu Akbar inji Nene "Allah Sarki Dunkum, ashe ba yin ka bane, Lallai akwai
B'oyayyen Alamari a tattare da Gidan nan, ni gaskia ina zargin matar Baban su" "aa Nene kar
kiyi saurin zargi" "tace dole iz zargeta mana Mahamman, ita kadaice zata yi hakan" Abbii yace
"kamar yanda shi da kawun shi suka taimaka miki lokacin da baki da lafiya, InshaAllah zan
taimaka mishi da wasu Adduoi, kuma kafin in bar Katsina zanje gun Abokina Me *Arriyadh
Islamic Medicine* a taimaka mishi da magunguna, har shi mahaifin shi, in ma akwai Kaidin
Mace da yardar Ubangiji komai zai warware cikin iko na Allah" Nene cikin jin dadi tace "Yauwa
dan Mallam Jikan Mallam, da ba ka shashanatar da kanka kan boko ba, da yanzu ni nasan kai
babban Malami ne da ake tak'ama dashi a k'asa baki daya, yanzu ma na san zakayi k'okarin ka"
Nasiba kuwa bata san kalar Farincikin da zata yi ba, hak'k'un ta yarda da Mahaifinta, kuma ta
na murnan zai taimaka ma Rafeeq, sai dai su Rok'i Allah ya basu nasara.
_Bibilicious Biebee_
í ½í±§í ¼í¿½KE ALHERI CEí ½í¹‡í ¼í¿¼â€�♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Assalam Alaikum, ina muku fatan Alheri, ina godia da yanda kuke biye dani a wannan
labarin, ina me baku hak'urin rashin ji na da kukeyi kullum, hakan na faruwa ne saboda wasu
'yan dalillai, kuyi min uzuri don zan dinga tsallake kwana daya banyi typing ba, in kuma an samu
yanda nikeso, zaku dinga jina kullum kullum, Nagode Allah bar zumunci.
Pg4⃣5⃣
Abbii da Nasiba gaban Mallamin *Arriyadh Islamic Medicine* bayan Abbii ya karanto ma
Mallam Matsalolin Gidan Lema. Mallam Usman ya jinjina kai, yace "Alhamdulilah, wannan labari
da kuka bani akwai 'kulalliya, ko ba sihiri zamu taimaka da adduoi, balle wannan ma daga ji an
san akwai Sihiri, ta iya yiwuwa Shi Alhajin an sa shi ya mance Uwargidansa, tunda kunce be
sake waiwayarta ba, sai kuma shi Rafeeq baa so ya gama Makaranta tunda ance shekarar sa
ta biyu kenan yana maimaita aji, kuma ba wai don ba ya ganewa ba, kuma ba ya k'aunar
uwarsa, alhalin duk yanda Uwarka take to akwai wannan So da K'auna dake tsakanin su, toh
tabbas akwai Mak'arkashiya a ciki kuma InshaAllah zaa warware komai da yardan Ubangiji. Abu
na farko;
Ina so su sa a ransu cewa duk abunda ya samu bawa to da yarda da ikon Allah ya same shi. Su
kasance masu Adduoi da Tauhid, Zaa musu magani duka, Shi Alhaji zaa bashi maganin da zai
taimake shi ya tuno abubuwan da suka faru a baya, shi kuma Rafeeq zaa bashi Maganin da zai
sa mai dangana a ranshi, yanda zai yafe ma Mahaifiyar shi, wani Jarka Mallan ya dauko, yace
"Wannan Ruwan Karatun Kurani mai girma da Addu'oin Shifa, Lallai Rafeeq da Habib su maida
shi ruwan Sha din su, in so samu ne ko abinci a dinga dafa musu da shi, shi zai tsare su daga
Sharrin mai Sharri" ya ciro wani robar swan, yace wannan kuma Man itattuwa