Showing 1 words to 3000 words out of 137467 words
Chapter 1 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE BOOK By Hauwa Shehu Aliyu .pdf
[24/08 8:50 pm] Jeeddah Aliyuí ¼í¼¹: [20/08 4:23 pm] Jeeddah Aliyuí ¼í¼¹: í ½í²�```NI DA YAYA
HABEEB```í ½í²�
_�the sweetestlove�_
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyuí ¼í¼¹
```1```
Yarinya ce 'yar kamani _16-17yrs_ tana tafiya a hankali hannuta rik'e da _food flask_ tana
sanye da atamfar _novou_ blue da touch's d'in yellow da hijab _yellow colour_ kaitsaye ta doshi
wani shagon d'inki mai suna ```Ni da yaya Habeeb Teilorings center```
tana shiga shagon yanayi annuri fuskarta ya d'auke chak, kamar anyi ruwan sama an d'auke
tayi tsaye tana k'arewa samari hudu da ke ciki shagon kallo yayin da idanu ta suka ciko da
kwalla cikin zafin rai tanufi wurin saurayin da ke _facing_ d'in k'ofar shigowa shagon tadire masa
_food flask_ cikin sark'ewa murya tace yaya salman ga abinci na kawo maka Wanda aka kira da
suna salman sai lokacin yad'ago tsanani kamanu shi da yarinyar suka baiyana, fuskarsa a
murtuk'e alamu babu wasa a tare da shi yace don gidanku kin saba kawo min abinci ne"?
Da sauri d'aya daga cikin samarin Wanda ke zauna daf da wata kyakyawa budurwa tana nuna
masa _styles_ d'in d'iki a wayarta tun lokacin da yarinyar tashigo shagon ya sada kai k'asa
alamu rashin gaskiya ya tari numfashi sa ta hanyar cewa haba salman miye haka"?
Tsoki yaya salman ya ja cike da jin haushi, yace wallahi Habeeb ina tausaya maka yarinya
k'arama tana juya ka kamar waina a tanda sai an waye gari ta Kore maka _customers_ tass
sannan za ka yi hankali in ka aure ta naga da uban da za ka ciyar da ita, ke kuma me kike jira
ne"? maza ki koma gida kuma duk ranar da na k'ara gani k'afar ki a shagonan sai na balla ki wannan
wace irin fitina ce sai kace akanku aka fara soyayya ina lissafi a sati nan ak'alan Haleesa ta
Kore mana _customers_ sun fi 10 za ki fita ko sai na taso na falla miki mari"?
Da gudu ta fice daga shagon tana kuka ta nufi gida.
A fusace yaya Habeeb yace banaso abunda kake yi min salman, ka fi kowa sani duk fad'i
duniya ba abinda na tsana irin bacin rai _baby love_ amma shine don tsabar wulaqanci had'e
da musgunawa zuciyata kayi mata Koran kare.
Salman ya galla masa harara cike da jin haushi yace wallahi Sa'a kayi da banyi mata dukan
tsiya in yaso gaba d'aya zuciyar taka ta tarwatsi har yaya salman yadasa aya yaya Habeeb
yana watsa masa mugun kallo mai cike da jin haushi, daga bisani yaja dogon tsoki yanufi k'ofar
fita daga shagon da sauri kyakyawar burduwa tace Habeeb ya za'ayi katafi batare da mun
gama magana ba"?
Harara ya galla mata yace ke har kina tsanmani ina da kwanciyar hankali da za ki yi magana da
ni"?
Ga salman nan ki yi masa bayani d'ikinki in nadawo ya sanarda ni yana k'arasa magana yasa
kai yafita, yaya salman ya ja tsoki had'e da cewa shege namamajo yayin da raguwa samari da
ke shagon suka kyalkyale da dariya shak'iyanci.
Gudu takeyi tana kuka mutane da ke wuce sai kallota sukeyi, wanda suka santa kuwa sai
tambayar ta sukeyi Haleesa lafiya kike kuka"?
Amma ko kallon basu eshe ta ba muradinta taga ta kai gida, tana shiga zaure gidansu taci karo
da katuwar akuya Ammi ta korota saura kiris ta bangaje ta daka tsalle a gefe d'aya akuyar na
ficewa ita kuma ta danna kai Ammi na tsaye da bulala rik'e da hannuta da alama da bulala tayi
amfani ta kori akuyar, tana shiga tsakiyar gida ta cire takalmi ta had'e da hijab ta jefar ae kuwa
sai bisa tukunya ruwa hijab d'in yafad'a tasaki kuka mai matuk'ar sautin gaske ta shige d'akin
Ammi ta fad'a bisa gadonta na _silver_ tayi rub da ciki tana shasshekar kuka kamar raita zai
fita.
A tsorance Ammi tashigo d'akin ta daka mata tsawa ta hanyar cewa ke lafiya kika shigo mini
gida kina wannan taratsi na fitar hankali"?
Batare da ta juya ta kalli Ammi ba cikin dasashiyar murya tace Ammi yaya Habeeb nagani tare
da wata a shago suna fira, Ammi bakiji irin zafin da nakeji a zuciyata duk lokacin da naga yaya
Habeeb yara6i wata 'ya mace jin nakeyi kamar zan yi hauka kum.....kee! Ammi ta daka mata
mahaukaciya tsawa da tayi sanadiya da ta hadiye sauran kalamai ta, cikin takaici Ammi tafara
fad'a wai ke Haleesa wace irin fitaniya yarinya ce ke"?
Wane irin hauka da shirme k'urciya ne yake da mu ki"?
Domin wannan abun naki ba kishi bane shirme ne da tsabar samun wuri to ki bud'e kunne ki da
kyau ki saurara, ni saboda nafara gajiya da wannan iskanci naki uwarki ce ta Haifa miki
Habeebu da za ki ce ba zai kula kowace 'ya mace ba sai ke"?
ko don kina tak'ama Habeebu d'an uwanki ne shiyasa kike yi masa abunda kika ga dama shi
kuma shashasha yana biye miki, don haka kiyi maza ki rufe min bakinki tun kafin raina ya baci
na lakkada miki shege duka.
Nan take ta hadiye kukan ta saboda tasan halin Ammi kad'an daga cikin aiki ta ne, yanzu nan
za ta had'a mata jini da majina don haka ta rufawa kaita asiri ta hadiye kuka ta Ammi ta ja tsoki
ta fice daga d'akin had'e da cewa kuma kifito ga wanke-wanke yana jiranki.
Ba yadda ta iya dole ta mik'e jiki a sab'ule ta fito tana sharar hawaye had'e da majina da ke
tsiyaya daga hancita, kaitsaye bakin famfo ta nufa inda tuli kwanuka wanke-wanke ke jiranta
kujera 'yar tsuguno ta d'auko ta zauna ta fara wanke kwanuka lokacin-lokacin tana share
hawaye da baya hannuta zuciyarta cike da jin zafin yaya Habeeb wai miyasa Ammi da yaya
salman suka kasa fahimtar cewa tsabar son da nake yiwa yaya Habeeb ne yake haddasa mini
matsananci kishinsa"?
_Assalamu Alaikum_
Sallamar yaya Habeeb ce ta katsi mata zance zuci da takeyi da sauri ta d'ago kaita
_wa'alaikum sallam_
Ammi da ke _kitchen_ ta amsa masa tafito hannuta rik'e da ludayi miya ta galla masa harara
tace kai kuma, shashasha ta je har shago ta tayar maka da hankali shine ka biyo bayanta koh"?
Yaya Habeeb ko kallon gefen da Ammi take baiyi ba, balle tasa ran zai bata amsa sai kawai ta
shafawa kanta lafiya ta hanyar Jan tsoki ta koma _kitchen_
Yaya Habeeb na tsaye ya jigina rabin jikinsa a jikin bango ya wani lamgwabe kai yana kallota,
ita ma k'asa d'auke ido ta tayi akanshi kallon ```so``` mai had'e da ka bata rai take aika masa
yayin da shi kuma yake aika mata kallo mai d'auke da tsan-tsan ```so``` had'e ban hak'uri gaba
d'aya yadawo Kala ban tausayi harara ta galla masa had'e da murgud'a baki ta kauda fuska. Cikin mutuwar jiki ya tunk'aro inda take........
[20/08 8:59 pm] Jeeddah Aliyuí ¼í¼¹: í ½í²�```NI DA YAYA HABEEB```í ½í²�
_�the sweetest love_�
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyuí ¼í¼¹
```2```
Tsawon _5 minutes_ yad'auka a tsaye yana kallonta yayin da ita kuma ta sada kai k'asa ta
cigaba da wanke-wanke ta, daga bisani ya tsunguna daf da ita cikin muryar sa mai matuk'ar
dad'i da gard'i yace _I'm so sorry baby love_ wallahi ba abunda yake tsakanina da yarinyar nan
_believe me baby love no thing between us_ kawai d'iki ta kawo min shine take nuna min
_styles_ d'in da takeso a wayarta Dan Allah kiyi hank'uri kidaina kuka nan saboda yana masifar
tayar mini da hankali kinji"?
Saida ta ja majina da tafito mata a hanci ta koma inda tafito, cikin muryar kuka tace miyasa
kake min haka yaya Habeeb"?
ko don ni bana cikin Jeri kyawawa mata shiyasa kake kula kyakyawa 'yan mata"?
Na shiga uku babylove na ta6a cewa da ke ina so kyakyawar mace kuma, wane munafuki ne
yace da ke bakida kyau"?
Ta turo baki had'e da cewa ni ce nagano da kaina banida shaharare kyau, kuma ga shi a kullum
'yan mata masu shaharare kyau suna zarya a shagonku kuma saboda kai kadai suke zuwa kai
d'inki.
Yaya Habeeb yadafe kai ya wani zaro ido yace in har baso kike yi nima nayi miki kuka ba
babylove ki ajiye wannan zance a gefe ki yarda da ni ki kuma daina kwakwato akan irin so da
nake miki, da ace ana bud'e zuciya da wallahi na bud'e miki tawa zuciya ki shiga idanu ki su
hasko miki irin masifafe son da nake miki wannan ce kadai hanyar da zanbi ki yarda da cewa
zuciya ta mallaki, ki ce ke kadai.
Ta lumshe idanu ta tsanani dad'i kalamai yaya Habeeb suka soma ratsa jijiyoyi jikinta shauk'i
sonshi yak'ara samu mafaka a zuciyarta, cikin shagwa6a tace _ina sonka yaya Habeeb_
Yaya Habeeb ya yi murmushi yace kina sona amma kuma kina wahalar da zuciyata, tayi dariya
_tace ba laifi na bane_
To laifi waye na hukunta shi saboda ni kan yana mini barazana da rayuwa"?
kallon ido cikin ido mai d'auke da tsan-tsan so ta aika masa, daga bisani ta kauda fuskar ta tace
laifi sonka ne yaya Habeeb da ya yi nasara kanainaye zuciyata ya ratsa jini da tsoka ya bi sassa
jikina ka koya mini sonka tun kafin na mallaki wayo gane ```menene so``` har nayi wayo nagano
manufa da dad'i da ke cikinsa na rayuwa da sonka yaya Habeeb ina kuma fatar na mutu da
sonka ,shiyasa banaso ka ra6i kowace 'ya mace.
Wani irin dad'i ne ya lullube zuciyar yaya Habeeb ya haddasa masa sakin sanyaye murmushi ya
nad'e hannu _blue shirt_ d'in da ke jikinsa yasoma tayata wanke-wanke tana wankewa yana
d'aurayewa yasaka cikin _basket_
Hannushi yatara a famfo ruwa suka cika masa hannu ya watsa mata a fuska a tsorace ta d'ago
ya kyalkyale da dariya, cikin yanayi na shagwa6a tace Allah ba zan yarda ba yaya Habeeb nima
sai na rama
yaya Habeeb ya zaro idanu had'e da cewa yi hank'uri babylove karki jik'a ni shago zan koma.
_cup_ ta d'auka ta debi ruwan d'auraye kwanuka ta kwara masa tun daga fuskarsa har jikinsa
ruwa ne ke d'iga ya 6ata fuska yace haba babylove ruwan wanke-wanke ne kika zuba min a
_my favourite shirt_
Ta yi masa gwalo had'e da cewa ba kai bane kafara
Don ni ne nafara shine kika za ki watsa min ruwan wanke-wanke"?
Turo baki tayi yayin da yaya Habeeb ya yi murmushi mugunta ya sunkuce _bucket_ d'in ruwan
gaba d'aya ya kwara mata tasaki mahaukaci ihu had'e da kwalawa Ammi kira wayyo! Ammi
kinga yaya Habeeb ya jik'ani da ruwan wanke-wanke, da gudu yaya Habeeb yanufi k'ofar fita ita
ma ta bishi da gudu, tuni ya shige gidansu yabarta labe a zaure tana lek'e sa, daga bisani ta juya cikin gida
Ammi ta kalli ta ta tabe baki tace narasa gane tsakani ke da Habeebu waye mashiririci"?
murmushi kawai tayi ta d'auki _basket_ d'in kwanuka takai _kitchen_ tadowa rik'e da tsintsiya
ta share wurin da tayi wanke-wanke daga bisani ta cire jak'ak'u tufafi ta ta d'aura zani a k'irji
Ta cika _bucket_ da ruwa kaitsaye bandak'i{bathroom} ta Shiga tayi wanka, ta shirya cikin _dark
blue d'in _uniform_ na islamiyya had'e da _whites hijab_ tafito rik'e da jakka mai d'auke da
_Al-qu'arni mai girma da saura littafai addini_ ta nufi k'ofar _kitchen_ tace _Ammi na tafi
islamiyya_ Ammi da ke ta fama fifita wuta saboda itace basu bushe sosai ba tad'ago tace
adawo lafiya sannan karki manta in an tashi isalamiyya ki biya gidan Delu dallaliya ta baki ciko
kudina, tajuya had'e da cewa to Ammi amma kuma in bata bani ba na k'arbo abin kudi"?
Ammi tace bansakiba uwar 'yan kaud'i ta fice tana dariya had'e da cewa kai Ammi daga zan yi
miki abun kwarai
Kaitsaye gidansu yaya Habeeb tashiga had'e da sallama inna mairo na zaune a tsakiyar gida
bisa kujera 'yar tsuguno cikin sakin fuska ta amsa mata, yayin da Haleesa ta durk'usa har k'asa
ta gaidata _ina wuni inna"?_
_lafiya qalau Haleesa an fito"?_
_Eh! Inna zainab na ciki kuwa?_
Kafin inna tabata amsa taji muryar zainab a bayata tana cewa ba'a saniba sai yanzu kika damar
fitowa"?
Harara ta galla mata tace nima bansaniba in kuma baki tashi tafiya ba, nayi tafiyata inna dai sai
faman dariyar su takeyi saboda tasan da kyar ne Haleesa da zainab su had'u ba tare da suyi
fad'a ba. sallama sukayi yiwa mata had'e da ficewa daga gidan.....
_DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S_
Jeeddah Aliyuí ¼í¼¹
[24/08 8:51 pm] Jeeddah Aliyuí ¼í¼¹: [20/08 11:16 pm] Jeeddah Aliyuí ¼í¼¹: í ½í²�```NI DA YAYA
HABEEBí ½í²�```
_�the sweetest love�_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyuí ¼í¼¹
```3```
Suna fitowa zainab tace ke kenan kullum sai kinsa muyi latti kin je kinyi zamanki, kina zuba
wanke-wanke soyayya ke da yaya Habeeb bayan kinsan yau muna da _hadda_
Haleesa ta kyalkyale da dariya tace zainab kin Shiga uku a ina kika ganmu muna wanke-wanke
soyayya"?
Duk abunda kuke yi ina kallonku ta Katanga saboda turmi na hau ina lek'e Ku, idanu ku ya
bud'e da soyayya ko kunya Ammi bakwaji shi kuma yaya Habeeb da yafi ki rashin kunya da ya
shigo inna ta tambaye shi dalili jik'ewarshi ba ko kunya yace wai baby love ce ta jik'a ni da
ruwan wanke-wanke, ni da inna mu ka bishi da kallo har ya chanzo kaya yafice ba mu daina
binsa da kallon mamaki ba.
_umhh_ me zai sa mu ji kunyar Ammi"?
Mu kayi a gaban inna ballatana Ammi, ```NI DA YAYA HABEEB ``` soyayyarmu a jini take ko
munaso mu boye ta ba za ta boyu ba kuma ae ba yau nasaba jik'e shi da ruwa ba.
mtss zainab ta ja tsoki tace chan ta matsi muku ni dai ki d'aga 'kafarki saboda yau tafiyar sauri
za mu yi sai wani tafiya kike yi kamar kina jin tausayi taka k'asa, duk da Haleesa bata iya tafiyar
sauri ba amma dole ta dinga d'aga k'afafuta domin ta huta da masifar zainab
Daga bisani Haleesa tace zainab wane irin _colour_ kaya da yaya Habeeb zai fita ya sanya"?
Saida zainab yatsine fuska daga bisani tace wane irin _colour kaya zai saka a yammaci nan da
wuce na ball_ Haleesa tayi murmushi had'e da cewa amma kuma ni cemin yayi shago zai
koma.
To yayi miki k'arya saboda haka da kun had'u ki hukunta shi
Harara ta gallawa Zainab had'e da cewa ina ruwanki _NI DA YAYA HABEEB_ ba'a shiga tsakani
mu domin duk Wanda yace yashiga tsakani anta da jini rabonsa kunya.
Dallah yi ma mutane shiru da anyi magana sai ki ce _Ni da yaya Habeeb_ sai kace zautata
Haleesa ta kyalkyale da dariya had'e da kai ma zainab duka.
Duk lokacin da Haleesa da zainab za su tafi islamiyya dole sai su wuce cikin wata _government
primary & secondary school_ anan samari unguwar da ma Wanda suke zuwa daga wasu
unguwanni suke buga _ball_ kasancewar filin makarantar yana da girma sosai kuma anan
Haleesa takeda tabbaci gani yaya Habeeb d'inta duk yawan samari da ke cike da wurin hakan
bai hanata hango shi, ba tasaki gwaron numfashi, da sauri ta bud'e jakkarta tafito da _exercise
book_ had'e da _Biro_ ta yagi _paper_ cikin manya harufa ta rubuta ```I LOVE YOU YAYA
HABEEB ``` ta linke takarda.
Tasaki murmushi mai sauti da sauri zainab tajuyo ta kalleta, ta wani tabe baki,Haleesa kuma ta
kawarda fuskarta ta cigaba da kallon tauraro da ke haska zuciyarta karaf suka had'a ido yasake
mata kyakyawa murmushi taji wani ni'imatace sanyi yaratsa tun daga tafin k'afarta har izuwa
kanta ta lumshe idanuta dai-dai lokacin da aka shuro masa _ball_ cikin kwarewa had'e da
kwarin guiwa ganita ya shuri _ball_ d'in ae kuwa sai cikin raga 'yan _team_ d'insu suka d'auki
ihu had'e da sowa Haleesa batasan lokacin da.....
[20/08 11:44 pm] Jeeddah Aliyuí ¼í¼¹: ```í ½í²�NI DA YAYA HABEEBí ½í²�```
_�the sweetest love�_
```®NWA```
Na Hauwa Shehu Aliyuí ¼í¼¹
```4```
Tace _yeee datz my yaya Habeeb_ da sauri zainab ta taro ta ta hanyar fisgo hannuta, tace
kinyi hauka ne _Haleesa?_ ke da kike bisa hanyar zuwa islamiyya miye had'eki da taya 'yan
kwallo ihu"?
In tsautsayi ya gita _Allah_ ya jefo mallam faruq yaji kina ihu a hanya ba ruwanshi da shauk'in
soyayya ne ya d'ebe ki dukan tsiya zai yi miki.
Duk wannan sarhi da zainab takeyi hankalin Haleesa na wurin yaya Habeeb tana k'are masa
kallo sanya yake da _JC_ blue colour da gejere wando k'afafusa sanye da takalmi _ball_ yaya
Habeeb ba dogo bane kuma ba za'a kira shi gajere ba yana da _round face_ mai d'auke da d'an
siriri gemu na gayu {saboda ba za'a kira wannan gemu da suna na sunnah ba} yana da
idanuwa saidai basuda girma sosai hanci sa yana da tsayi ya kuma d'an bud'e fatar jikinsa
_chocolate colour ce_ yana da tarin suma akanshi irin wance gayu zamani suke bari.
Cikin gudunsu na 'yan kwallo yanufo wurin Haleesa da zainab, da sauri Haleesa chafki hannu
zainab ta rik'e gam yana k'arasowa wurin daf da su Haleesa ta sada kai k'asa yaya Habeeb ya
gallawa zainab harara yace ke dai zainab kin shiga tara kullum sai kin sa babylove tayi latti sai
na raba muku, jam'iyya sannan za ki yi hankali. Zainab tayi dariya had'e da cewa ae ni da ka taimake ni domin a lokacin za ka gano tsakani ni
da ita waye yake sanya wani latti.
Yaya Habeeb ya lek'a fuskarta yace _babylove d'azu kika jik'ani kamar shuka koh"?_
Haleesa d'ago fuskata