Showing 45001 words to 48000 words out of 137467 words

Chapter 16 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE BOOK By Hauwa Shehu Aliyu .pdf

12 Apr 2025

9409

ta akan farar kujera roba ta zunguri Hajiya
batula matar k'anin Mahaifin Habeeb ta Wani yatsine fuska had'e da cewa Hajiya batula ta ya ni
figa Saida Hajiya Batula ta kya6e baki daga bisani tace Uwar miji ta Zama kaza anyya kuwa
Madam Hindu tana ciki haiyyaci ta da ta amince Habeeb ya aure 'yar Matsiyata ni da naga
Wannan uban lefe na yi tsanmani 'yar Governor ko 'yar Minister ce yake nema ashe 'yar gidan
babu ce Wannan ae asara ce da rashin sanin zafin kud'i
"Bari kawai Hajiya Batula tun lokacin da muka tunk'aro unguwar nan bak'i ciki da takaici suke
nuk'urkusa zuciyata Jin nakeyi kamar na hadiye zuciya na mutu don takaici ba rok'a da ban yi
wa Madam Hindu ta tilaswa Habeeb ya aure Maryam ta Maye gurbi marigayiya Salma Amma
'yar mata nan ta yi biris da buk'ata ta ke in tak'aita miki labari sai cewa ta yi ita bara ta yi wa ta
d'a aure dole kinga ba ta yi masa dole ba shi kuma ya kwaso mata 'yar Matsiyata duk abunda
suke fad'a akan kunnen inna mairo gani abun naso ba mai k'arewa bane ta mik'e tsanm tabar
musu wuri.
Bayan dangin Habeeb da na Haleesa sun gaisa a tsakaninsu daga bisani dangin Habeeb suka
gabatarda da abunda ke tafe da su yayinda dangin Haleesa sukayi musu sha tara na arziki
suka baro gidansu Haleesa cike da Murna irin karamawa da akayi Musu sa6ani Hajiya
khareema da ta dawo da mummuna k'udiri ko ta Wane sai tashigar da 'yar ta gidan Habeeb.
```8:30pm```
Aunty Juwairiyya da Zainab zaune a d'akin Ammi sun tusa lefen Haleesa gaba suna kallon sai
faman santi da yaba kayan suke yi sa6ani Haleesa da ke kwance rub da ciki akan gadon Ammi
ita ba kuka take yi ba amma a yadda takeji Zuciyarta na tarfafasa gwara ta yi kuka ko za ta
same sausauci k'unci da take ciki babban bak'i cikinta bai wuce yadda Mutane Unguwa har ma
da na cikin gidansu suke zuzuta kayan lefe ta basu San cewa a wurinta atamfar super prints ta
fiye mata tarin kayanan Zainab tace Haleesa bara ki sauko ki taya mu ganin wannan abun arziki
ko kunya kike ji kada Ammi tace bakida kunya tak'arasa magana cikin tsokana
"Cikin zafin rai Haleesa ta diro k'asa ta tsalleke kayan tafice Zainab da Aunty Juwairiyya suka bi
ta da kallon, girgiza kai Aunty Juwairiyya tayi tana mamaki tauri kai da kafiya irinta Haleesa.

```1 WEEK LATER ```

Tuni gidaje biyu sun fara gudanar da tsare- tsare yadda bikin aure 'ya'ya su zai gudana tsawon
wannan lokacin Habeeb da Haleesa ba su k'ara gani Junansu.
Haleesa na zaune bisa kujera 'yar tsuguno a tsikiyar gida tana yanka alayahu almajiri ya yi
sallama Haleesa ta amsa masa yace wani mai mota yana sallama da Haleesa a k'ofar gida, ras
gaban Haleesa yafad'i nan take annuri da ke kan fuskar ta ya gushe tace je kace batanan
Ammi ta lek'o daga cikin kitchen ta ce je ki kace gatanan zuwa tajuya wurin da Haleesa take
zaune ta galla mata harara had'e da cewa me kike Jira ne da bara ki tashi ba da sauri Haleesa
ta mik'e ta jefar da wuk'a hannunta Ta Shiga D'aki tasaka Hijab tafito fuskarta ahad'e tanufi
k'ofar gida dafe k'irji Haleesa ta yi sakamako motar Habeeb Lamido da ta ganin nan take
Numfashinta yafara kai da kawo ta runtsi idanuta...


Jeeddah Aliyu🌹
[10/24, 11:44 AM] +234 813 417 9191: [11/10 6:25 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```�NI DA YAYA
HABEEB�```

_�the sweetest love_�

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```60```

Jiki a sa6ule tak'arasa fita Wannan karo ma Bala ne yafito daga cikin mota yak'araso wurinta
"Barka da fitowa ranki yadad'e"
Yauwa Bala ya gida"?
Lafiya Qalau ya hidimomi biki"?
Shiru Haleesa ta yi had'e da sada kai k'asa gani yadda ta yi yasa Bala ya yi murmushi yace ba
fa ni kadai bane tare nake da "Boss'
Wani fad'uwa gaba Haleesa tak'ara ji tsanani tsoro ya lullu6e ta tamkar mai ciwo hak'ora ta
bud'e bakinta tace Bala kace da shi yak'araso ciki ranar ma da na tsaya da shi a k'ofar gida
saida Baffa ya yi Fad'a "Bala yace okay ba matsala bara na yi masa magana Bala yanufi wurin
mota ya bud'e k'ofar da Habeeb yake Zaune fuskarshi ahad'e ba bu annuri ko misk'arazairatil a
tare da shi da alama zuwan sa na dole ne "Boss tace ka shigo daga ciki saboda Baffanta
bayaso tsayuwa a k'ofar gida"

A harzuk'e Habeeb ya ke kallon Bala daga bisani yace banida buk'atar shiga gidansu don haka
za ka iya bata dalilin zuwa na gidansu"
Ka yi hank'uri "Boss ka daure ka k'arasa daga ciki karka manta ko yanzu kafin mu zo gidanan
irin Fad'a da Madam ta dinga yi ta nuna 6aci ranta k'arara a dalilin rashin waiwaye Haleesa da
ka yi Yakamata ace ka danne duk wata k'iyayya da ka ke yi mata saboda saura d'a k'ank'ani
lokacin ta zama mallaki ka in tashigo gidanka kana da iko yi mata duk abunda ka ga dama ba
bai hanaka saboda ikonka ce.
Habeeb yadage gira sama yana duban Bala cike da gansuwa da kalaman Bala yasaki tsadade
murmushinsa mai narkar da Zuciyar 'yan mata
Haleesa nagani Bala na musu-musu da baki da alama magiya ya ke yi wa Habeeb haushi ya
turnuk'e ta ta juya cikin gida tana shigawo ta ci karo da Ammi sai kawai tace Ammi Key's d'in
d'akin yaya Salman za ki bani batare da Ammi tace da ita komai ba tashiga d'aki tadauko mata
Key's ta mik'a mata a sanyaye Haleesa tak'ara juyawa k'ofar gida tana fita taci karo da su a
bakin k'ofar shigowa Zaure ba shiri ta taka birki had'e da sunkuyar da kai Kallo d'aya Habeeb
Lamido ya yi mata ya d'auke kai tsawon "5-6 minutes suka dauka a tsaye daga bisani Haleesa
tanufi d'akin yaya salman ta bud'e k'ofa tajuya batare da ta bari sun had'a ido tace "Bissimillah!
Banza Habeeb ya yi kamar bai ji abunda tafad'a "Bala yace Boss ka k'arasa daga ciki bara na je
na fito da kayan da ke cikin mota Wani tsuke baki Habeeb ya yi kamar mai tsotsa "Sweet ko mai
shiri d'aukar selfie ya yi kici-kici da fuska, yajuya ya kalle d'akin yaya Salman Wanda tuni
Haleesa ta tsofa a ciki tana jiranshi ya ta6e baki yanufi d'akin batare da yacire "cover shoe d'in
k'afarsa kawai yadanna kai Haleesa na Zaune akan kujerar roba kanta na sunkuye tana wasa
da yatsu hannunta ''Ba don sani daraja da sallama da ke ita a musulunci da ba yadda za'a yi ya
yi mata sallama"
"Assalamu Alaikum" yafad'a chan k'asan mak'oshi''
"Batare da Haleesa tad'ago kanta ta amsa mai masa da cewa "Wa'alaikum sallam
warahmatullahi wabarakatih...''
Habeeb ya kya6e baki a zuciyarshi yace ka ji su Al-Sheikh za ki yabawa aya zak'i ta in kika
shigo hannuna 'ya nema mai kai Kamar dunk'ule "cabbage' ya ja ya yi tsaye Haleesa bata ce da
shi ga wurin zama hakan ne yasa yacigaba da zance zuci tana nufi bara tace na zauna ba
amma bara naga iya gudun ruwanta kafin na wanke mata allonta saboda naga kanta na hayak'i. A fakace Haleesa tad'ago ta sace kallonshi yana nan tsaye k'ikan hannaye shi zube cikin aljihu
wandoshi da sauri ta d'auke kai a zuciyata tace tofah wata sabuwa inji 'yan caca shi wannan
mai tsawo kamar fol waya yana nufi bai ga wurin zama bane ko kuma duk cikin, salon tsabar
kwarewa da wulak'anci ne amma bara nace ya zauna a karo na biyu da tasake d'agowa amma
bata dube shi ba tace "please have a seat''
Zaro ido ya yi daga bisani ya gyatsine fuska kamar ya ga "cockroach a zuciyarshi yace "Humm!
I can't believe this Illiterate girl she known how to speak English''
Ya dube kujera da ta nuna masa da yatsanta akwai tazara tsakaninta da wance ta ke Zaune
yafito da "handkerchief fari kal daga gaban aljihu "black colour coat d'in da yake sanye da ita ya
shinfid'a akan kujerar sannan ya zauna ya yi crossing legs nashi yafito da "phone in shi yafara
buga "game in crush candy'' Haleesa ta cika ta yi dam! Me wannan mutumin yake nufi me ye laifinshi Haleesa ke yakamata
ki fara gaida shi abunda d'ayan 6angare Zuciyata yace da ita kenan......."ina Wuni yaya

Habeeb"? tafad'a cikin sark'ewa harafi"
"Ignoring nata ya yi saida d'auke almost 3-4 minutes sannan yace da ban Wuni ba kya gani
saida ya furzar da zazzafa iska yacigaba da cewa ke! Wai me yasa a duk lokacin da na zo
gidanku sai kin yi "Wasting time in na"?
Numfashi da Haleesa ta sauke yafi a kirga da kyar ta iya controlling in "temperature' ta Co's
wannan karo guy nan yakawo ta k'ul tace am sorry Yaya Habeeb wallahi.....
"Shut up please don't give me that fucking excuse yak'arasa magana had'e da cigaba da buga
game in shi girgiza kai Haleesa ta yi cike da takaici tafara zance zuci na Shiga uku ni Haleesa
wannan wane irin aure ne zan yi"?
"Very slowly yafara magana Kin d'auki kanki Wata tsiya sai kace ana sonki sai wani jiji da kai
kike ko kin manta kina gaban Habeeb Lamido ne Wanda ba ya gajiya da furta miki kalma
```Tsana``` amma da yake ke Heartless ce har Wani Jan aji kike yi na kuma San duk wannan
abu da kike yi kina yi ne don ki burgeni ni mutum ne kaifi d'aya ban ta6a sauya ra'ayi na
musanmman akan abunda nace banaso don karki yi tsanmani in na aure ki wata rana za ki
same gur6i a zuciyata tun daga lokacin da kika shigo rayuwata na nemi farin cikina narasa bana
sonki wallahi na tsane ki tsanar da bara ta6a gushewa daga Zuciyata yak'are magana had'e da
Murmushi.
Tun lokacin da yafara magana kai Haleesa yana sunk'unye a k'asa hawaye na bi kumatu ta,
Habeeb ya mik'e tsaye hannunshi guda yana ciki aljihu yanufi inda Haleesa take Zaune daf da
ita ya tsaye yad'an rankwafa yace ke!
A firgice ta d'ago tasauke ganinta akan fuskarshi k'asa jure kallon tsanar da yakeyi mata ta yi ta
sada kanta k'asa.
Murmushi jin dad'i Habeeb yasaki sakamako hawaye da yagani akan fuskar Haleesa yace you
hears all what's am saying right"?
K'asa magana ta yi kawai tad'aga masa kai cikin isa da tak'ama yacigaba da cewa "Don't you
think is too early ace kin fara zubar da hawaye ki"?
"Is better ki share hawaye ki saboda bai kamata kifara zubar da su tun yanzu domin ina da
buk'ata su a gida na Haleesa tacigaba da share hawaye ta masu masifar Zafi da k'ona Zuciya.
"Habeeb ya ja tsoki had'e da cewa kina da aiki yarinya ya yi dialling number Bala yak'ara a
kunnenshi "Hello! Bala wai me kike yi ne da har Yanzu ba ka k'araso ba"?
"Boss ina k'ofar gida nufina na dan ba Ku wuri za ka fi jin dad'i sakewa Ku sha fira
Kai! Banaso shirme banza da Wofi na baka _3 minutes_ ka shigo ko nayi maka abunda ba kayi
tunani ba yana k'are magana ya yi hanging up"
Haleesa ta sa gefen hijab d'inta ta goge hawaye ta "Bala yashigo had'e da sallama yadire wani
k'aton kwali had'e da farar Leda Habeeb ya dube Bala yace na ba ka "5 minutes kayi Mata
bayani abunda ke ciki ni ina k'ofar gida kuma karka sake ka wuce time d'in na ba ka yaficewar
shi batare da ya dube inda Haleesa take Zaune. Bala yace ranki yadad'e dama "invitation card's ne mu kawo miki ga kuma waya nan akwai sim
card a ciki had'e da numbers in "boss duk abunda Ku ke buk'ata Ke da k'awaye ki a lokacin biki
sai ki kira "boss gobe insha Allah Zan zo na fita da Ke 'kawayeki Ku kai wa 'yan uwa da abokai
arziki katin gaiyyata [11/10 7:01 pm] Jeeddah Aliyu🌹: Har Bala yadasa aya a zance shi Haleesa bata ce komai ba
gani ta yi shiru yasa yace ranki yadad'e kin yi shiru ba ki ce komai ba"?

Saida tasauke Numfashi daga bisani tace Zai fi kyau kayi min Serving in number domin bana
tunani zan iya "calling in wani''
"Bala d'an murmusa yafito da Biro daga gaban aljihu shi ya rubuta number shi akan kwalin da
yashigo da shi ya yi mata sallama yafice.
Saida Haleesa ta share tsawon "10 minutes kafin tashiga cikin gida kaitsaye tashiga d'akin
Ammi ta ajiye kwalin hannunta bata ce da Ammi komai ba ta nufi d'akinta.

```WASHE GARI ```

Tun misali k'arfe 10:30am Bala ya zo yadauki Haleesa da k'awaye ta suka tafi raba "invitation
saida suka share kwana ki 3 suna raba invitation tun safe in suka fita sai da yamma lis suke
dawowa.

```ON TUESDAY ```

Ita ce ranar da aka fara gudanar da shagalin biki kamu za'a yi a gidan Aunty Juwairiyya tun
daga Lagos Madam Hindu ta yo "Booking d'in Aunty funke da yaranta suka k'awata gidan Aunty
Juwairiyya da "Decoration yayinda Aunty funke za ta yi wa Amarya Haleesa Makeover tun
lokacin da Haleesa tashiga "bathroom da suna wanka ta rufe k'ofa tun Aunty funke tana saka
ranta fitowar ta har tagaji da jira tafito daga bedroom ta nufi parlour wurin Aunty Juwairiyya ta
Fad'a mata abunda ke faruwa a harzuk'e Aunty Juwairiyya tanufi bedroom d'in tadinga knocking
in k'ofar had'e da kiran sunan Haleesa shiru kamar ba mai rai a ciki Haleesa da ke Zaune
dirshan a tiles d'in bathroom tasaka kanta tsakiyar cinyoyinta sai faman shashekar kuka take
bata tunani akwai Wanda ya isa yasaka ta ta bud'e k'ofar nan har sai sun gama shirme su, jin
yadda Aunty Juwairiyya take duka k'ofa yasa Haleesa tace Aunty ki daina wahalarda kanki bara
ta6a bud'e k'ofar nan har sai kun gama shagalin bikinku.
Cikin 6aci rai Aunty Juwairiyya tace a gidan uban wa Haleesa kika ta6a gani anyi kamu ba
Amarya"?
"Daga yau za'a fara a kaina Haleesa tafad'a had'e da murgud'a baki...


Jeeddah Aliyu🌹
[10/24, 11:44 AM] +234 813 417 9191: [15/10 4:53 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```�NI DA YAYA
HABEEB�```

_�the sweetest love_�

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

```62```

Note:- _na yi kuskure a wurin fadar sunan garin a farko labari mai karatu zai ji nace yola a wani
wurin kuma zai ji nace Yobe to yola ne ba Yobe da fatar za'a gafarce ni_

_10:30am_

"Habeeb na tsaye gaban "dressing mirror yana sharce suma shi da "Comb Mus'ab ya murda
handle ya shigo ta mirror ya had'a ido da Habeeb ya kyalkyale da dariya da sauri Habeeb ya
had'e rai ya d'auke kai yace banaso iskanci Mus'ab hali yanzu ka fara kaini bango tun dare jiya
ka ke ta fama yi min dariya shin akwai uban da baya mafalki ne da za ka sakani a gaba kana
dariya, Mus'ab yak'ara kyalkyalewa da dariya har yana dukan gefen bed abunda yak'ara
harzuk'a Habeeb ya jefa masa comb in hannunshi ka ga Mus'ab na rok'e ka da ka had'a
"luggage in ka ka bar min gidana Mus'ab ya tsagaita da dariyar da yake yi au abin har da su
kora to ba ida zan tafi ina nan tare da kai har sai Amarya ta zo''
Amma kuma kaima kana da gida sai ka je gidanka ka tare ka jira zuwan Amarya ni kan bara iya
cigaba da zama da mahaukaci"
Kyalkyalewa da dariya Mus'ab sake yi yace to ae ni narasa gane tsakanin ni da kai waye
mahaukaci ko ka manta kuka ka ke yi wa mace a mafalki wannan ke nuna cewa kai d'in zarare
ne Mus'ab bai jira me Habeeb zai ce ba ya juya yafi ce daga d'akin yana dariya shak'iyanci
Habeeb ya bi shi da kallo daga bisani ya ja tsoki kai amma yarinya nan ta gama da ni me ke
shiri faruwa da ni da na ke mafalki na sadu da ita"?
Lallai sai na musgunawa yarinya nan sai ta yi danasani zuwa mini a mafalki cike da takaici ya
murd'a handle yafi ce Mus'ab ya tarar akan dining table yana breakfast batare da ya dube ida
yake zaune ba ya ja kujera ya zauna, chef Peter ya yi masa "saving har suka gama breakfast
ba Wanda ya tankawa d'an uwanshi Habeeb ya dube ida yake zaune yadauke kai in ka ga
dama katashi mu tafi Mus'ab ya yi murmushi had'e da cewa gaskiya tsarin gidanan ya burgeni
matuk'a ba k'aramin more rayuwa za Ku yi kai da Amarya Haleesa wai... Ina nufi dream girl
domin Haleesa bata kai matsayin da za'a more rayuwa da ita ko ba haka bane aboki na"?
Ran Habeeb yak'ara 6aci jin yake kamar ya zabgawa Mus'ab mari ya ja tsoki ya fice daga
parlour Mus'ab ya Mara masa baya yana dariya har suka iso gidan Madam Hindu Mus'ab yana
tsokanar Habeeb tun yana jin zafinshi har yagaji ya zuba masa na mujiya.

_8:00pm_

```HALEESA```

Duk lokacin da Haleesa ta tuna cewa saura kiris ta zama mallaki Habeeb Lamido sai ta zubar
da hawaye ta yi nisa a tunani Aunty Juwairiyya tashigo Haleesa ki tashi ki je wanka Aunty funke
na jiranki za ta yi miki makeover na tafiya _Dinner_ Haleesa ta kwa6e fuska wai ni Aunty dole
ne sai na je dinner"?

"Dole ne Haleesa sai kin je don haka ki tashi ki je ki yi abunda na umurce ki Karki 6atawa
mutane lokacin''
Haleesa ta shar6e hawaye na fahimce cewa Aunty Juwairiyya ko tausayi na bakyaji ta kare
magana had'e da mik'ewa Aunty Juwairiyya ta tabe baki sai anan a gaba za ki gano alkhairi da
ke cikin wannan aure"
Tun da zuciyata bataso
Ya za'a yi na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login