Showing 36001 words to 39000 words out of 137467 words

Chapter 13 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE BOOK By Hauwa Shehu Aliyu .pdf

12 Apr 2025

9411

kasancewa ta 'yar
talaka kika tsalleke su kika za6e ni a matsayin wance ta dace da d'anki ta ya ya zan bad'a miki
k'asa a ido nace banaso jininki"?
"Tun lokacin da narasa yaya Habeeb nasan cewa nayi bankwana da farin ciki na har abada,
don haka "mommy na amince da yaya Habeeb ko ba komai yana d'auke da suna mutumin da
yake mahad'in rayuwa ta na gode da wannan karamawa ta ki tana k'arasa magana ta mik'e da
gudu tashige d'akin Ammi tafad'a sama gado tafashe da kuka mai k'arfin gaske. "Malam Usman yace Hajiya ko za'a hank'ura da wannan al-amari saboda naga har yanzu
Haleesa bata fitarda marigayi Habeebu a ranta kada aje gyara gira arasa ido ta je takasa
zaman lafiya da d'anki kin ga anyi ba'ayi ba d'aukar makaho photo.
Karka damu malam Usman kayi 'ko'kari ka yak'i wannan tunani daga zuciyarka karka manta har
yanzu Haleesa tana fagge na jinyar mik'i da ke zuciyarta na rashin marigayi Habeeb a cikin
wannan yanayi Habeeb za'ayi amfani da wannan damar yakafa sanssani yak'i neman za6e
zuciyar Haleesa Wanda a sannu za ya maye gurbi Marigayi Habeeb har ta manta ta ta6a
rayuwa da wani Habeeb addu'arku kawai nake nema a cikin wannan tafiyar.
"Shikenan Hajiya Allah yasanya alkhairi yasa abunda za'a ci amfaninsa ne Allah yahad'a Kansu
ya kad'e fitina a tsakaninsu.
_Ameen malam Audu_
Yayin da madam Hindu tacigaba da cewa sai magana tagaba Habeeb zai zo yagana da
Haleesa su fahimce juna daga bisani zan yi magana da d'angin mahaifinsa su kawo kud'in
gaisuwa a kuma sanya, lokacin banaso auren yadauki dogon lokacin.
A wannan karo baffa ne yayi magana yace ba damuwa Hajiya duk yadda kika tsara haka za'ayi
Allah yasanya alheri _Ameen_ daga haka su baffa suka mik'e had'e da ficewa daga gidan
Hannah da zainab suka shiga d'akin Ammi cikin tattausa lafazi suka soma rarrashi Haleesa da
kyar suka samu tadaina kuka da take yi Hannah tace Haleesa kidaina kuka domin yaya Habeeb
mutumin kirki ne bashida matsala za ki ji dad'i zama da shi wani d'agowa Haleesa ta yi ta
watsawa Hannah mugun kallo mai cike da tambayar kinada hankali kuwa daga bisani tace.....

```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```

Jeeddah Aliyu🌹
[30/09 2:43 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [20/09 8:56 am] Jeeddah Aliyu🌹: . ```�NI DA YAYA
HABEEB�```

_�the sweetest love_�

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```53```

Ki daina ya6o d'an uwanki a wurina saboda hakan bashida amfani a tare da ni, zainab tarik'o
hannu Hannah tace tashi mu je kiyi alwala Hannah ki kyale Haleesa saboda a halin yanzu bata
cikin haiyyacinta batare da Hannah ta furta uffan ta bi bayan zainab bayan madam ta gama
sallah tanufi gadon Ammi inda Haleesa take kwance tadinga rarrashinta har tayi nassara shawo
kanta tadaina kuka, sai misali k'arfe _8:20pm_ madam Hindu tabaro gidansu Haleesa.

```9:30pm```

Madam Hindu na kishigid'e a had'ad'e parlour yayinda Hannah take zaune a gefe tana chat a
"phone d'inta, Habeeb ya yi sallama had'e da shigowa parlour kaitsaye yanufi kujera da madam
Hindu take zaune ya zauna kusa da ita had'e da daura kanshi a kafad'arta, ya wani narke sai
kace 'karamin yaro madam tashafi sumar kanshi cikin kulawa tace da alama _son_ ka kwaso
gajiya ga shi inaso zan yi magana mai matuk'ar mahimmanci da kai"?
"Don't worry about me mom ba wani gajiya a tare da ni da bara nayi fresher up nadawo mu yi
magana ya mik'e tsaye cikin tsokana yace Allah yasa kud'i ne za ki bani domin nasanki da
kyauta tun da na shigo parlour nan naga fuskarki shinfid'e da farin ciki naji a jikina babba kyauta
za ki yi min ni kadai batare da Hannah ba Hannah ta kyalkyale da dariya tace kai yaya Habeeb Sam baka rabo da abin dariya to abunda
yafi kud'i ne mommy za ta baka
Murmushi yayi yana shafar sumar kanshi da gaske ne sweetheart za ki bani abunda yafi kud'i"?
Haka ne son ka je ka yi wanka kadawo ka ji babbar kyautar da zan baka.
"Your wish is my command sweetheart yafad'a had'e da juyawa ya haura upstairs Hannah tace
wannan kyautar "special ce mu biyu za mu raba batare da yajuyo ba yace karya ki ke yi yarinya
ni kadai mom za ta ba.
Mom kina gani yaya Habeeb zai amince da za6inki kuwa"?
Ajiyar zuciya madam ta yi daga bisani tace bana tunani zan same matsala daga wurin Habeeb
saboda tun yana yaro ba mu ta6a samu sa6ani ra'ayi duk abunda nakeso shima yana sonshi,
so bana tunani akan wannan za'a same matsala, kuma da bakinshi ya sha fad'a min cewa na
nemo mishi mata kin ga kenan fad'uwa ce ta zo dai-dai da zama. Habeeb na shiga bedroom ya cire kayan jikinshi yasaka rigar wanka {bathrobe} yashiga
bathroom bayan yafito daga wanka, farar jallabiya yasanya yafice daga bedroom d'in madam da
Hannah na zaune inda yabarsu a zaune, tun kafin ya zauna yace Hannah ki je kitchen ki dauko
min "soya milk mai sanyi Hannah ta mik'e tanufi kitchen yayinda ya mayarda ganinshi wurin
mom yace "sweetheart ga ni nadawo madam ta yi murmushi tace son lokacin ya yi da za ka aje
iyali domin zamanka haka bai dace ba
"Hannah tadawo hannuta rike da kwalin soya milk had'e da "handle glass cup ta mik'a masa
harara ya galla mata yace bara ki iya zuba min bane"?
Hannah ta yi murmushi ta bud'e murfi kwalin soya milk d'in ta zuba masa a cup ta ajiye kwalin
bisa stool ta koma wurin zamanta ta zauna yayinda madam tacigaba da cewa a dalilin haka
yasa na nemo maka yarinya mai hankali da natsuwa babban abunda yak'ara Jan hankalina
agareta kyakyawar tarbiyya da ta ke da ita. Tun lokacin da madam tafara magana Habeeb yake kallonta had'e da snipping d'in soya milk
d'insa, gani ta dasa aya a zanceta ya yi d'an bazawari murmushi kamar mai rad'a yace mom

kina nufi aure za ki yi min"?
Kwarai kuwa _son_ nagaji da gani ka haka domin basan har wane tsawon lokacin za ka dauka
kafin ka nemo wance ka ke so shiysa, na nemo maka wance ta dace da kai kuma na tabbata za
ka so ta.
Numfashi yasauke yace mom wacece wannan yarinya da kike ta faman zuzutawa"?
Haleesa k'anwar Juwairiyya matar masa'ud manager ita ce yarinya da na za6a maka kuma
nasan za ka yaba da za6i na.
Habeeb ya zaro ido soya milk d'in da ya kur6a baisan lokacin da yahadiye ta da k'arfi ta sark'e
shi yafara tari kamar ranshi zai fita madam da Hannah sai faman sannu suke masa da kyar tari
ya tsaya yad'ago jajaye idanushi yasauke su bisa fuskar mom d'in tashi cikin yanayi na tashin
hankali yafara magana mom duk wad'anan ababbe da kika lissafa akan wannan yarinya ni ba
ko d'aya da nagani a tare da ita asalima banta6a gani, mahaukaciya irinta ba wai ina kushe
za6inki bane mom ki yi bincike akanta kafin ki yanke hukuncin aura min ita yak'arasa magana
tamkar zai fashe da kuka.
"madam Hindu ta gyara zamanta had'e da rik'o hannunshi "Son Haleesa batada matsala duk
wani bincike da addini ya yarje ayi kafin anemi aure nasa ayi min akanta da iyayyeta kuma,
gaba d'aya su sun same kyakyawar sheda a wurin jama'ar gari....
[22/09 4:08 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```�NI DA YAYA HABEEB�```

_�the sweetest love_�

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```54```

A matsayina na mahaifiyarka ba yadda za'ayi na za6a maka abunda zai cutar da kai Haleesa na
matuk'ar bani tausayi kai kanka in ka ji labari rayuwarta za ka tausaya mata, nan take madam ta
zayano masa labari rayuwa Haleesa tacigaba da cewa _son_ nasan kana da kyakyawar zuciya
da tausayi dalilin da yasa ka aure salma kenan Haleesa ta cancanta ka tausaya mata ka aure
ta domin tana buk'atar kulawa ka yi tunani halin da 'yarka kwara d'aya tal take ciki ka gano cewa
kana buk'atar Haleesa a tare da kai amma tun da bakada ra'ayi akanta ba zan tilassa ka ba
saidai basan ta wace hanya zan bi domin ba iyayyeta hank'uri"
Cikin sark'ewa halshe yace akoda yaushe banida za6i da ya wuce naki sweetheart duk abunda
kike so nima ina sonshi akan wannan bara mu ta6a samu sa6ani ra'ayi, farin ciki na shine na
kasance d'a mai biyayya a gareki don haka na amince da za6inki ni kuma haka tawa k'addara ta
take bara ta6a samu za6ina. Tsanani tausayi farucinshi Yakama madam amma kuma ba taji za ta, iya chanza ra'ayinta akan
Qudirinta"
parlour ya yi tsit kamar ba masu numfashin a ciki baka ji komai sai 'karar sautin tv madam ce ta
yi yunk'uri kawo karshen shiru nasu ta hanyar fad'ar Allah ya yi maka albarka Habeeb biyayya
da kake min kai ma Allah yabaka 'ya'ya da za suyi maka fiye da wance ka yi min.
_Ameen sweetheart_ yafad'a had'e da kwantawa akan cinyoyinta ya lumshe idanu.
A hankali madam ta ke shafar sumar kanshi cikin lafazi mai sanyi ta kira sunanshi Habeeb!

"Humm! Yafad'a a kasalance.
Banaso wannan al-amari yadauki dogon lokacin, saboda haka ka Ware _time_ ka je gidansu
Haleesa ku fahimce juna ka kuma gaida iyayyeta, daga bisani na sanarda da Alhaji bello su Kai
kud'in gaisuwa.
Har madam ta dasa aya idanushi na lumshe, yace kina nufi zance zan je"?
Kwarai kuwa ko ba za ka iya zuwa bane"?
Ni na isa nace bara iya zuwa saidai kunya nakeji tun da na zo duniya banta6a tsayuwa da wata
'ya mace da sunan zance Allah kuwa sweetheart kunya nakeji yak'arasa magana yana yatsine
fuska.
Madam ta yi "dumm! Tana shafar gashi kanshi daga bisani tace ka daure my son ka je ta hakan
ce za Ku fahimce juna kuma iyayyeta za su fi gansuwa su gano cewa da amincewarka za ka
aure 'yarsu.
Habeeb yak'ara ya mota fuska da alamu yashiga sark'ak'iya da kyar iya bud'a baki yace
shikenan mom in nasame lokacin zan je'
Wane irin in kasame lokacin son kawai gobe ka je
A kid'ime Habeeb ya mik'e zaune yace mom gobe fa kika ce"? Gaskiya gobe "I don't have time
but I promise you next week zan je
"Next week ya yi nisa son" ranar Saturday kana free saboda weekend ne ba aiki ka yi k'ok'ari
ka je
Tamkar zai fashe da kuka yace na ji
Madam ta yi murmushi had'e da shafar gefen fuskarshi da bayan hannunta tace Haleesa
yarinya ce tagari za ka ji dad'i zama da ita.
"For God sake mom kidaina wannan magana haka nan nace na amince zan aure ta cigaba da
maimaita zance yarinya nan za iya haddasa min "headache yana k'arasa magana ya mik'e
tsaye Hannah ta kyalkyale da dariya tace yaya Habeeb zan yi maka "escort na kware da iya
tsara zance kaitsaye zan tsara maka ita nan take ta zurma a kogin sonka. Wawan tsoki Habeeb ya ja cike da haushi had'e da takaici ya haura upstairs a zafafe ya murd'a
handles yashiga bedroom yafad'a bisa bed yasaki huci bakinshi na fitarda iska mai masifar zafi
hannaye shi ya daura ya yi pillow ya 'kurawa ceiling ido tamkar yana karanta wani abu a wurin
daga bisani yasauke numfashi mai karfin gaske, yafara zance zuci lallai yarinya nan sai ta yi
"regretting na shigowa rayuwa ta saboda tarasa masoyinta don kawai ina da sunanshi shine
take bibiya na har ta yaudare mom da ladabi ta na karya tayi sanadi da mom ta had'ani aure da
ita wallahi sai ta yi danasani sani na a rayuwa domin ba zan ta6a Maye mata gurbi tsoho
masoyinta sai na had'a ta da hawan jini sai na wulaqantata irin wulaqanci da bata ta6a gani a
rayuwarta.
A 6angaren Haleesa kuwa tana gani madam Hindu ta tafi tasake bud'e sabon babi na kuka
Ammi ta watsa mata kallon mamaki tace Haleesa kukan me kike yi"?
Haleesa ta mik'e zaune tana shar6e hawaye tace wallahi Ammi banaso Habeeb Lamido ba zan
iya zaman aure da shi har abada ba zai ta6a maye min gurbi yaya Habeeb asalima ni tsoro shi
nake ji.
Ammi da zainab suka yi sororo suna duban Haleesa duba na rashin fahimtar inda kalamai ta
suka dosa.

Jeeddah Aliyu 🌹
[30/09 2:48 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [28/09 10:45 am] Jeeddah Aliyu🌹: ```�NI DA YAYA
HABEEB�```

_�the sweetest love_�

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```55```

Tsawon lokacin Ammi da Zainab suka share suna kallonta daga, bisani Ammi ta nunata da
yatsa cikin murya mai cike da gargad'i tafara magana ke! Haleesa karki mayarda mu tsofafi
banza mana a gaban matar nan kika ce kin amince da aure d'ata, a bayanta idota za ki dawo ki
ce bakya sonshi ke tsoro shi kike ji to in ma bacci kike yi kiyi gaggawa ki falka domin wannan
shirme naki mu bara mu dauke shi ba ai bakin alk'alami yariga yabushe ke kika amsa da bakinki
kina sonshi ba wani ne ya yi miki dole ba kowa yana miki murna Habeebu yatafi ga kuma wani
Habeebu yadawo, shine za ki tsiro da wani sabon tsirfa to ahir d'inki babban farin cikin mu
Haleesa kindawo da walwala da farin cikin da kika rasa birjirewa wannan aure tamkar kinyi
butulci da musaya da Allah ya yi miki kuma karke sake na 'kara jin wannan zance yafito daga
bakinki, saboda ina tausaya miki in Baffa ki ya ji wannan tatsuniya ba zai yi miki da kyau ba.
Haleesa ta rushewa da kuka tace ni fa na amsawa mommy ne kawai don ina ji kunyar na dube
tsabar idonta nace banaso gudan jininta, amma azahirin gaskiya bana sonshi kuma bana fatar
ya maye min gurbin yaya Habeeb nariga nasakawa raina narasa yaya Habeeb rashin na har
abada tak'arasa magana had'e da rushewa da wani sabon kuka. Ammi ta girgiza kai tace kin yi wauta Haleesa da kika amsawa Hajiya Hindu kinaso d'ata, a
gaban baffanki domin shi mutum ne da bayaso magana biyu don haka ki rungume 'kaddara sai
ki yi 'ko'kari ki danne zuciyarki tafara sonshi Ammi na'karasa zance ta tafice daga d'akin tabar
Haleesa da Zainab kowane su da abunda yake sa'kawa a ranshi, Zainab tarik'o hannun
Haleesa ta yi k'asa da murya Haleesa karki yi haka ya alkhairi yana binki ke kuma kina neman
ki guje masa a tunanina za ki fi kowa Murna da farin cikin, shigowa wannan Habeeb d'in a
rayuwarki, da k'arfi Haleesa tafincike hannuta daga rik'o da zainab ta yi mata cikin k'unar
zuciyar tace da kesan waye Habeeb Lamido da baki furta min wad'anan kalamai Zainab ta tabe
baki daga bisani tace ta za'ayi nasan waye shi batare da kin sanarda ni ba"?
Haleesa taja gwaro numfashi, Habeeb Lamido mugu ne bashida tausayi shine mutumin da
driver shi ya watsa mana ruwan kwatame shekaru biyu da suka wuce ya kuma zabga min mari
har gudu biyu.
A firgici Zainab ta zaburo idanu bud'e cikin sark'ewar halshe tace I can't believe kina nufi mai
siffar labarawa shine Habeeb Lamido"?
Kwarai kuwa shine kuma ba wannan ne kadai had'uwa ta da shi nan take ta kwararu wa zainab
had'uwarta da Habeeb da kuma irin furucin da ya yi akanta, tacigaba da cewa ya kike tsanmani
zamanmu zai kasance"?

Zainab ta yi ajiyar zuciyar tace dama haka tasha faruwa k'iyayya ta rikid'e ta koma soyayya ni
dai gaskiya ina supported d'in wannan al'amari Allah yasanya alkhairi wata k'atuwar harara
Haleesa ta gallawa zainab yayinda zainab ta kwashe da dariya ta mik'e tsaye cikin sigar
tsokana tace sai da safe Mrs Habeeb Lamido Haleesa ta kai mata duka tafice da gudu cikin
yanayi na jimami Haleesa ta koma ta zauna ta rafka tagumi hawaye masu cike da k'unar zuci
suka wanke mata fuska.

```BAYAN KWANA BIYU ```

Yammaci ne sakaliya yanayi gari kamar akwai hadari sai iska akeyi mai matuk'ar dad'i gaske,
madam Hindu na kishigid'e a "parlour ta hannuta rik'e da newspaper Habeeb ya yi sallama
yashigo yanemi kusa da ita ya zauna kallo guda za ka yi masa ka hango tsantsa damuwa da
take shinfid'e a fuskarshi, cikin kulawa madam tajuya wurinshi hannunshi ta rik'o me ke faruwa
ne son naga kamar kana cikin damuwa"?
Ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba daga bisani ya numfasa kamar mai ciwo hak'ora yace
"nothing mom"
Sam madam bata gansu da amsa da yabata domin tadana yak'ini musanbabin damuwar tasa,
duk bai wuce zance aure ita ko "this time around ba za ta d'aga masa k'afa kawai sai tayi
murmushi tacigaba da cewa ina fatar wannan shiri da ka yi na tafiya gidansu Haleesa ne in
baka mata ba yau ne muka yi alqawali da kai za ka je"? "Habeeb ya lumshe ido game da 'kan'kame yatsun hannu mom ya yi k'asa da murya yace
"please mom ki d'auke min tafiya nan bara iya ba tun da na amince da aure banga wani amfani
zuwa na ba yak'arasa magana tamkar zai fashe da kuka.
"Madam ta yi murmushi had'e da cewa haba Habeeb bansanka da magana biyu ba naga cewa
tuni mun gama wannan zance me yasa za ka dawo da hannu agogo baya, katashi katafi Allah
ya yi maka albarka.
"Ba yadda Habeeb ya iya dole ya mik'e tsaye cikin sanyi murya yace sai nadawo mom"
Adawo lafiya ka gaida ta batare da yak'ara furta uffan yafice daga parlour yayinda madam ta
bishi da kallo.
Yana fita Bala P'A ya shek'o da gudu yanufo wurinshi yace "Boss fita za mu yi ne"?
A kasalance Habeeb yafurta kalma "eh Bala yanufi "parking space yajanyo mota kirar
"mercedez benz c class" ash colour kafin Bala ya bud'e masa k'ofa ya bud'e da kanshi yashiga
Bala yaja mota maigadi yabud'e gate suka fice daga gidan.......

Jeeddah Aliyu🌹

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login