Showing 30001 words to 33000 words out of 137467 words

Chapter 11 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE BOOK By Hauwa Shehu Aliyu .pdf

12 Apr 2025

9420

ke ta fama da zance zuci na hadu da 'yan mata kala
daban-daban ban ta6a haduwa da very smart girl irin Haleesa, zuciyata tana bani cewa Haleesa
ta zo d'aukar famsa abunda na ta6a yi mata ko kuma ta fad'a a tarko sona shiyasa take
bibiyana in kuwa d'aya daga ciki ya kasance gaskiya lallai sai na wulaqanta ta Co's ban ta6a
haduwa da yarinya da naji farat d'aya na tsaneta irinta, kamar daga sama ya ji sautin muryar
Bala driver yana fad'ar Boss mu iso gida Habeeb yasauke ajiyar zuciya had'e da yafito daga
cikin mota.

```BAYAN KWANA BIYU ```

Haleesa na kitchen tana wanke plate's da cups d'in da sukayi amfani da su kasancewa yau
Sunday Janet tana church, madam Hindu kuma tafita ba yadda batayi da Haleesa su fita tare
Haleesa ta k'i a cewarta bataji dad'i cikin sanyi jiki take wanke plate's d'in K'amshin turare

intense man da tashak'a ya haddasa mata fad'uwa gaba, Habeeb Lamido ne tsaye a k'ofar
kitchen yana aika mata kallo mai cike da tsana Cikin tsanani tsoro Haleesa tajuya karaf suka
had'a ido, da sauri ta sada kai k'asa Habeeb ya ja tsoki yak'arasa shiga kitchen d'in cikin
muryarshi mai matuk'ar dad'i yafara magana kamar mai rad'a ke! Uban me kike jira a gidanan
da har yanzu baki tattara komaitsa ki kibar mana gida"?
Wani irin shock yaja Haleesa jikinta yafara sharking, takasa furta uffan yadaka mata tsawa ke!
Ba magana nakeyi da ke ba"?
Yak'arasa magana cikin k'unar zuciya muryarta na rawa tace Dan Allah kayi han'kuri ba laifina
bane mommy ce har yanzu bata bani izzini tafiya gida.
_You're very stupid kina nufi mom ce mai laifi ashe bakida mutunci"?_
A lokacin d'aya mamaki had'e da tsoro sukayi nassara lullu6e Haleesa ko kwakwara motsi
takasa yayinda haushinta yak'ara turnuk'e Habeeb a harzuk'e yafisgo hannuta yace wai ke me
kike tak'ama da shi waye ubanki duk fad'in African da har zanyi miki magana kiyi ignoring
nawa"? Hawaye suka wanke fuskar Haleesa tsanar Habeeb ta kanainaye zuciyarta, da k'arfi ta fincike
hannuta saidai kash takasa kwace hannu nata ranta a 6aci tace dallah malam kasake min
hannu, kallon uku saura kwa6o ya watsa mata ya yatsine fuska cikin sigar wulaqanci yace ki
kwace hannunki mana Haleesa ta girgiza kai tace kai kanka kasan da zan iya kwace hannun
nawa ba bazan tsaya ina rok'a mutume da baisan daraja da k'imar d'an Adam irinka.......
[14/09 11:02 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```�NI DA YAYA HABEEB�```

_�the sweetest love_�

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```48```

Da k'arfi Habeeb ya murde mata hannu yace kin tafka babban kuskure na shigowa rayuwata
tuni nagano cewa kina bibiyana, kuma sai na tabbata miki da cewa bansan daraja da k'ima
mace banza 'yar iska irinki mai bin d'an namiji har gidansu da wannan Neman gindi zama da
kike yi a wurin mom da fitowa kika yi kika fad'a mata gaskiyar dalili zuwanki gidanan. Haleesa ta zaro manya idanuta masu cike da tsoro ta hadiye miyau masu masifar d'aci ta rushe
da matsananci kuka tace karka jefeni da mummuna kalma yaya Habeeb don ina zaune a
gidanku bashi zai baka damar ka fad'a mini magana son ranka, ka tambaye mahaifiyarka za ta
fad'a maka dalilin zama na a gidanku. Habeeb ya galla mata harara had'e da cewa ke!
Munafuka ni fa nagano cewa abu biyu ne yakawo ki a gidanan kodai kin zo daukar famsa
wulaqanci da nayi miki a baya ko kuma kin zo neman soyayyata jin wannan furuci na Habeeb
yak'ara rud'a Haleesa ta runtse idanuta tana kuka kamar ranta zai fita saboda zafi biyu Habeeb
Lamido yahad'a mata ga zafin murd'e mata hannu da yayi ga kuma na magaganu da yake ta
faman gasa mata, yayinda Habeeb yacigaba da cewa bara na fad'a miki ko a k'afa aka daura
min ke zan kwance na yar Co's nafi k'arfinki infact ban ta6a jin na tsani wata 'ya mace sai

akanki don haka kidaina yaudara mom ta hanyar ihun da kike yi kina cewa yaya Habeeb ya
mutu ba zai ta6a dawowa gareki wai ke ga ki 'yar duniya Haleesa ta bud'e idanuta tasoma
watsawa Habeeb kallon mamaki daga bisani tace tir da wannan duk'usashiya kwakwalwa taka
da har ta tasanya maka tunani cewa ni Haleesa ina sonka me zanyi da kai bana d'aya daga
cikin shashashu 'yan mata da kudinka da kyakyawa surarka za su rud'a kuma yau d'inan zan
bar maka gidanku bara ka k'ara ganina ba har abada Habeeb Lamido ya ja tsoki wulgar da
hannunta da k'arfi ya juya cikin tafiyarshi ta k'asaita yafita daga kitchen d'in Haleesa ta
dur'kushe 'kasan tile's tafashe da kuka tasoma danasani zuwa garin Lagos da kyar ta mik'e
tsaye ta nufi room d'in Hannah tafad'a kan bed tafara zance zuci ashe Habeeb Lamido
mahaukaci ne in banda hauka don kawai ya ganni a gidansu zai ce ina sonshi mtss shashasha
kawai mai k'aramar kwakwalwa nan take tafara tunina rayuwarta da yaya Habeeb da yaya
Habeeb yana raye me zanzo yi a garin Lagos da har wannan arrogant zai same damar
wulaqantani, Haleesa tacigaba da shashekar kuka madam Hindu ta murd'a handle tashigo d'aki
ta hango Haleesa kwance tana kuka da sauri tanufe ta Haleesa lafiya me kike yi ma kuka"?
Cikin muryar kuka Haleesa tace mommy gida zan tafi, inaso gani Ammi naa nagaji da garinan
tak'arasa magana had'e da rushewa da kuka madam Hindu ta rungume ta tace haba Haleesa
don kinaso zuwa gida shine za ki dinga kuka"?
Yi maza ki share hawayenki ki tashi mu tafi na ajiye ki gidan Juwairiyya gobe masa'ud yasaka ki
a flight ki koma Yobe da sauri Haleesa ta k'ank'ame mommy tace na gode mommy Allah yasaka
miki da alkhairi, madam Hindu tad'ago ta tana murmushi tace Ameen Haleesa 'yar gidan
mommy jiki na rawa Haleesa ta had'a kayanta madam Hindu sai faman dariya take yi mata
had'e da tsokanarta a haka suka fice daga gidan zuciyar Haleesa cike da farin ciki tabar ma
Habeeb gidansu, suna isa gidan Juwairiyya tun kafin Aderwale yabude mata k'ofa ta bud'e da
kanta tafito Aderwale yabud'ewa madam Hindu k'ofa tafito tana dariya tace Haleesa sai murna
kike yi za ki tafi kibar mommy koh"?
Haleesa ta rufe fuskarta da tafin hannuta Juwairiyya nagani su tafara washe hak'ora saboda
kullum sai yaya salman ya kira waya ya tambayi Haleesa, madam Hindu ta zauna a parlour
yayinda Haleesa tanufi d'akinta juice da ruwa masu sanyi Juwairiyya takawowa madam Hindu
ta tsiyaya mata, a glass cup ta mik'a mata kur6a d'aya zuwa biyu madam tayi ta ajiye cup d'in
bisa stool tajuyo tana facing Juwairiyya, tace Juwairiyya akwai magana mai matuk'ar
mahimmanci da nakeso zanyi da ke akan Haleesa.....

```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```


Jeeddah Aliyu🌹
[15/09 8:00 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [15/09 4:50 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```�NI DA YAYA
HABEEB�```

_�the sweetest love_�

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```49```

Tun daga lokacin da nadaura idanuna akanta naji tashiga raina matuk'a, nayi matuk'ar
tausayawa Haleesa a dalilin labari rayuwarta da yaya Habeeb da tabani gani halin da take ciki
da Kuma yabawa da ingantaciya tarbiya da takeda ita yasa na yi wa d'ana Habeeb sha'arwata
ko ba komai tarasa Habeeb ga kuma wani Habeeb yadawo watakila ko don sunan Habeeb
kadai zai iya saka tarage tunani marigayi Habeeb bansaniba ko iyayyenku za su amince su ba
wa Habeeb aureta har madam Hindu ta dasa aya Juwairiyya tana mata kallon mamaki daga
bisani tace mommy karki ce na katsi miki hanzari sai naga kamar Haleesa bata dace da
Habeeb ba saboda mu talakawa ne duk zuri'armu ba mai kud'i Juwairiyya tak'arasa magana
had'e da sada kai k'asa, madam Hindu tayi murmushi tace Juwairiyya Yakamata ki bada
kyakyawa sheda akaina da zuri'arta bana d'aya daga cikin masu kud'in da ke kyamar talaka a
wurina mai kud'i da talaka duk d'aya ne shawara na zo neman a wurinki ya kamata ki k'arfafa
min guiwa domin na cima aikin alkhairi da nayi niyya karki manta shekaru biyar a baya da suka
wuce Habeeb yarasa matarshi a waje haihuwa, dalilin haka yakasa k'ara aure Juwairiyya ina
buk'atar Habeeb ya yi aure saidai duk lokacin da na tuntube shi da zance aure sai yace na
nemo mishi matar aure, ni kuma narasa yarinya da zan nemo masa wance za ta soshi tsakani
da Allah ba don kud'inshi ko kyakyawa sura da Allah yabashi sai gashi kwatsan Allah yakawo
min Haleesa har gida, kuma ta cika duk wasu sharudd'a da nakeso matar Habeeb ta kasance
da su Juwairiyya tasauke ajiyar zuciya tace shikenan mommy sai kifara sanarda Habeeb in ya
amince da Haleesa a za6inki daga bisani sai a sanarda iyayyenmu domin su ne kadai a halin da
Haleesa take ciki za su iya tankwarata ta amince da zance aure.
Habeeb bashida matsala Juwairiyya duk abunda nakeso shima yanasonshi bamu ta6a samu
sa6ani ra'ayi, Haleesa ta d'aga hankalinta tana buk'atar ganin Ammi karki hanata tafiya ni kuma
zanyi amfani da wannan damar naje Yobe na nemawa Habeeb aureta.
Ba matsala mommy duk yadda kika ce haka za'ayi'
"Madam tayi murmushin farin ciki tace kira min Haleesa mu yi sallama, Juwairiyya ta mik'e tsaye
tana washe hak'ora kamar mai talla toothpaste Haleesa na kwance Abba na bisa cikinta yana
wasa doki, Juwairiyya tana dariya tace wannan k'aton yaro za ki aza bisa ciki yana doki sai
yafasa miki ciki, Haleesa ta mik'e zaune tace Abba naa ba k'ato bane, Juwairiyya ta tabe baki
had'e da cewa ki taso Ku yi sallama da "mommy za ta wuce Haleesa ta mik'e tsaye suka fice
tare Madam nagani Haleesa ta'kara fad'ad'a murmushinta tace Haleesa ni zan wuce ki gaida
Ammi kafin nazo mu gaisa.
"To mommy zai taji na gode sosai da d'ibin alkhairi ki agareni madam ta zuge zip handbag d'inta
tafito da bundle na dubu d'ari ta mik'awa Haleesa gashi Haleesa ki yi wa su Ammi tsaraba
Haleesa ta girgiza kai had'e da cewa hidima da kike yi da ni mommy tayi yawa ba zan kar6i
kud'inki ba. Madam ta mik'e tsaye ta mik'awa Juwairiyya kud'in Juwairiyya takasa k'ar6a kad'a kai "madam
tayi batare da tace komai ba ta ajiye kud'in bisa hannu kujera, tajuya tafice cikin sanyi jiki
Haleesa da Juwairiyya suka Mara mata baya da sauri Aderwale yafito ya bud'ewa madam mota,
tashiga Haleesa ta dafa k'ofa tace mommy narasa da wance kalma zaiyi amfani da ita wurin

gode miki, banida abunda zan saka miki da shi mommy saidai, zan cigaba da yi miki addu'ar
fatan alkhairi ke da zuri'arki.
Madam tayi murmushi da ke nuna taji dad'i kalamai Haleesa daga bisani tace ba komai Haleesa
ni na d'auke ki tamkar Hannah, Haleesa da Juwairiyya suna tsaye har motar madam tafice daga
gate d'in gidan sannan suka juya zuwa cikin gida, Haleesa tafad'a bisa kujera ta ja wata
doguwar ajiyar zuciya Juwairiyya ta zauna kusa da ita cikin sanyi murya tace Haleesa meyasa
kike so komawa Yobe alhali da bakinki kika ce sai kinyi _3 week's_ za ki koma gashi _1 week_
kawai kika yi kince za ki koma ko anyi miki wani laifi ne"?
"Ba abunda akayi min kawai dai nagaji da garinan
Shikenan bara na shirya na rakaki kasuwa gobe sai ki bi morning flight"
Murmushi Haleesa ta yi, cikin zuciyarta tace hakan shi zai saka Habeeb Lamido yagano
kwakwalwa da zuciyarshi sun cuce shi da suka haska masa cewa na zo Lagos ne saboda shi,
ta yatsine fuska a baiyane tace _disgusting_ Juwairiyya ta zaro idanu tace lafiya kike Kuwa
Haleesa"? "Yes am absolutely fine
Murmushi Juwairiyya tayi ta mik'e tsaye had'e da cewa ki je ki d'auko mayafinki mu tafi batare
da ta jira amsar da Haleesa za ta bata tashige bedroom d'inta.
Yinin ranar sun k'arace shi ne a yawon siye banza siye wofi ba su ne suka dawo gida ba sai ana
kiran sallah magariba, don haka a gajiye suka shiga cikin gida kaitsaye kowane su yanufi
bedroom d'inshi Haleesa ta jefarda mayafinta bisa bed tanufi bathroom tayi alwala bayan ta
gama sallah ta zabga tagumi tasoma tunani Habeeb Lamido zuciyarta cike da mamaki shi wai
ina bibbiya shi to me zan tsinta a wurinshi mtss mahaukaci kawai marar tunani, da kyar ta samu
ta rinjaye zuciyarta tabarta ta gabatarda sallah isha dawowar masa'ud yasa tafito parlour ba
rarrashin da banyi mata akan tayi zamanta koda _1 week_ ne ta'kara musu amma Haleesa ta
k'ek'ashe k'asa tace ita dai tafiya za tayi dole masa'ud ya kyaleta......
[15/09 8:00 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```�NI DA YAYA HABEEB�```

_�the sweetest love_�

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```50```

```WASHE GARI ```


Da wuri Haleesa ta tashi ta yi wanka tana jiran fitowar Masa'ud yakaita airport, saida yagama ja
mata rai sannan yace tafito su tafi koda tafito _10:30am_ ta buga gashi flight d'in da zata bi zai
tashi k'arfe _11:30am_ sai faman complaints take mishi ya6ata mata lokacin Juwairiyya sai
faman dariya take yi gani yadda Halee take zumud'i tafiya saida suka ga tashin jirgin su
Haleesa sannan Masa'ud da Juwairiyya suka nufi gida.

```YOBE```

Jirgi na sauka bayan Haleesa tafito batare da 6ata lokacin ba, taja trolley d'inta taxi tashiga tana
gani driven taxi d'in yashiga unguwarsu tasaki sanyaya ajiyar zuciya tasaki iska ta furzar tace
_Home, sweet Home_ har k'ofar gidansu taxi d'in tayi parking cikin zumud'i ta balle k'ofa tafito,
dai-dai lokacin da Hasheem 'kanin marigayi yaya Habeeb yafito daga cikin gida Haleesa ta
tsura masa ido da sauri-sauri numfashinta yake fita saboda sai yau ta'kara tabbatar da tsanani
kama da Hasheem yakeyi da Yaya Habeeb banbanci su kawai yaya Habeeb yafi shi, tsayi gani
yadda take kallonshi yasa yasake mata murmushi yak'araso daf da ita cikin tsokana yace
babylove ya akayi ne naga kin wani tsare ni da ido sai kace yau kika fara ganina ke da kika je
Lagos a maimako ki waye sai kika k'ara kwaso k'auyanci.
"Ko kwakwara motsi Haleesa ta kasa yi da k'arfi Hasheem ya kira sunanta Haleesa!
Haleesa ta dube shi tayi ajiyar zuciya, kafin ta yi magana mai taxi yace malama sallame ni na
tafi Hasheem yace nawa ne kud'inka"?
D'ari uku ne yallabai Hasheem yafito da _N 500_ ya mik'a masa shi kuma ya bashi chaji
yadauki trolley d'inta ya wuce gaba tana biye da shi sai tambayoyi yake zuba mata yayinda
Haleesa takasa bashi amsar ko d'aya daga ciki da sallama yashiga cikin gidan had'e cewa
Ammi fito ga bak'in Lagos da rana tsaka da sauri Ammi tafito daga d'aki tana gyara d'auri d'an
kwalinta tana had'a ido da Haleesa mamaki ya baiyana akan fuskarta da gudu Haleesa
ta'karasa wurinta ta rungume ta tasa kuka Ammi ta bubbuga bayanta, haba! Haleesa meye
kuma abun kuka"?
Cikin muryar kuka mai cike da shagwaba tace Ammi nayi kewarki'
Hasheem da ke gefe ya kyalkyale da dariya yace lallai yarinya nan dad'i ya yi miki yawa ki ce
kukan dad'i kikeyi to ni zan tafi anjima zan dawo na kar6i tsaraba na yak'arasa magana had'e
da yaficewa.

```3 hour's later```

Haleesa na zaune a d'akin Ammi sai labari madam Hindu take ba wa Ammi, kwarai Ammi ta
yaba da kirkin "madam Hindu
Tace duk lokacin da tashigo Yobe zata zo Ku gaisa.
Murmushi Ammi tayi tace Allah yakawo ta lafiya
"Ameen Ammi bara na je na gaida inna mairo ta zari hijab d'inta had'e da ficewa, tana Shiga
gidan zainab ta shek'o suka rungume juna sai da aka fara kiran sallah magariba Haleesa ta
koma gida bayan ta gama sallah tafito tsakiyar gida tasha iska yaya salman ya yi sallama
yashigo, Haleesa ta amsa mishi, ya zauna kusa da ita tana bashi labari Lagos Salman ya
kyalkyale da dariya yace Haleesa manya ke da kika yi _1 week_ kacal a Lagos har wani labari
za ki bayar
Haleesa ta turo baki tace Allah yaya salman nayi yawo saidai ba sosai ba kuma baka ga gidan
da na zauna Allah gidan yahad'u kamar a abroad ae kuwa Salman da kamal suka dinga yi mata
dariya Haleesa ta gallawa kamal harara tace gwara ni na je lagos nayi kauyanci kai kuma kamal
baka ta6a zuwa ba tak'arasa magana had'e da yi masa gwalo har baffa yashigo gida suna

zaune tsakiyar gida suna fira shima ya zauna akayi firar da shi kowane su zuciyarshi cike da
tsan-tsan farin ciki sakamako gani yadda Haleesa take annashuwa da nishad'i sai misali k'arfe
_11:44pm_ kowane su yanufi d'akinshi Haleesa tasuya kaya zuwa wata 'yar k'aramar vest ta
daura zani bisa ta kwanta tana daura kanta bisa pillow ta lumshe idanu nan take face d'in
Habeeb Lamido yafara yi mata shawagi a eye's nata da sauri ta bud'e idanuta _"why Habeeb
why don't leaves my heart to be in peace"?_
Ba gidanku kadai ba har garin Lagos na baro maka _but you still following me_
Hawaye suka ziraro mata a gefen idanu suka sauka bisa wuyanta, kuka Haleesa tayi sosai
daga bisani bacci ya yi awo gaba da ita anan ma bata tsira ba saboda mafalki shi tadinga yi
Habeeb ya zamewa rayuwarta karan tsaye.

```BAYAN SATI D'AYA ```

Haleesa da zainab sun dawo daga islamiyya yamma suna tafiya suna fira, tun daga nesa
Haleesa ta hango mota kirar _KIA cerato_ a Parke a k'ofar gidansu wani matsananci fad'uwar
gaba taji saboda ta ta6a gani Habeeb Lamido cikin irin wannan motar, zainab tace Haleesa bak'i
masu kud'i mu ka yi ne na hango had'ad'iyar mota a k'ofar gidanmu"? Haleesa tad'ago ta dube ta tasauke ajiyar zuciya tace oho! Tafad'a kaitsaye suna k'arasawa
k'ofar gida idanu Haleesa suka sauka bisa number motar _Habeeb Lamido 5_ abunda idanuta
suka hasko mata kenan tsanani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login