Showing 114001 words to 117000 words out of 137467 words

Chapter 39 - NIDA YAYA HABEEB COMPLETE BOOK By Hauwa Shehu Aliyu .pdf

12 Apr 2025

9410

idanunshi a tsawace yace ke tashi"!
"Da sauri Hannah ta mik'e zaune ya nunata da yatsa banta6a, sani Hannah munafuka ce ke
ba yau.
Uhm......uhm.....yaya Habeeb me nayi maka da za ka kirani da munafuka"?
"Zan wanka miki mari in ki ka k'ara tambyana abunda ki ka yi mun tsabar munafucin irin naki
Hannah, ki ka ce da mom nace banaso leesa sha'awarta nake yi domin nasan leesa
tana da kunya bara ta ta6a tunk'arar mom da wannan magana ba saidai tafad'a miki ke kuma
da ki ke fitsararriya shine ki ka fad'awa mom.
''Jikin Hannah yadauki rawa ta yi wuk'i-wuk'i da idanu gani haka yasa Habeeb yarik'o
kunnenta ya murd'e da k'arfi Hannah tasaki ihu azaba yasoma kashe mata gargad'i muddin ki
ka sanarda mom na shigo d'akinan sai nayi miki dukan tsiya tashi ki fita.
''A lokacin d'aya Hannah da Haleesa suka mik'e tsaye saboda ko Haleesa ta tsorata da
lamarin Habeeb ganin take yi da yagama da Haleesa zai juyo kanta.

''Da sauri Habeeb yasha gaban Haleesa kallo-kallo suka shiga yi wa juna eyes balls d'inta
suka yi mugun tsorata Habeeb sakamako yadda suka yi kwancin jini ga layin yatsunshi kwance
akan kumatunta.
"Nan take Nadama yak'ara lullu6enshi sonta da tausayinta suka k'ara samun muhalli a
zuciyarsa.
''Sautin kukanta ne yak'ara dawo da shi natsuwarshi hannunta yarik'o da k'arfi tafincike
hannunta tara6a gefenshi za ta Wuce yak'ara shan gabanta I'm so sorry leesa Dan Allah ki
saurareni nasani ni mai laifi ne a gareki shiyasa nakeso ki bani dama na goge laifina.
"A fusace tafara magana had'e yarfe hannayenta Nagaji yaya Habeeb nagaji da wahala da
ka ke bani kafita hanya ta banaso ka k'ara zuwa idan nake ko wannan zaman da nake yi anan
gidan don inajin kunya mom ne da tuni na kama gabana.
"Habeeb yadawo kalar tausayi, yak'ara sausauta murya leesa ko ubangiji da ya halince mu
muka sa6a masa idan muka rok'eshi yana yafewa mana ballantana mu 'yan Adam.
Kowane d'a Adam ba ba ya wuce kuskure leesa ki tausayawa rayuwata kiyafemin.
"Batare da ta tanka masa ta nufi gefen gado ta zauna tadafe kanta tsaye Habeeb ya yi yana
kallonta daga bisani ya baro inda yake yanufi wajenta ya zube gabanta ya yi kneeling yad'ago
fuskarta.
"Ta runtse idanunta gam...... Ko kusa bataso kallon fuskarshi domin zai iya karya mata
zuciya, har ya yi nasara gano ta yi zurfi a sonshi.
"Narasa kalma da zan yi amfani da ita "to express my feeling for you leesa but I really love
you bara iya cewa ga takamame lokacin da sonki yashiga zuciyata ba amma kisani ina miki so
da bana yi wa kaina.
"Ina rok'onki, ki amince da ni zan koyo miki yadda za ki so ni leesa ke ce mace ta farko da
zuciyata tafara so tsawon rayuwa da nayi da aunty salma banta6a jin kwatankwacin abunda
nakeji akanki leesa.
"Haleesa tarasa sama take ko k'asa take takasa amincewa da abunda kunnenta yake ji daga
bakin Habeeb Lamido dama akwai ranarda da arrogant kamar Habeeb Lamido zai k'ask'antata
kanshi a gareta sai yau tak'ara yarda da nasiha da Ammi take mata _Haleesa ki yi hak'uri Ki
kasance mai tawalkali Allah da ya kar6i Habeebu shi zai kawo miki Wanda yafi shi komai na
rayuwa_
''A lokacin da Ammi take mata wannan nasiha jin ta kawai take sai take gani kamar Ammi tana
fad'a ne don ta kwatar mata da hankali sai gashi Allah ya nuna mata shi mai rahama da jinkai
ne ga bayinsa ya had'a ta Wanda yafi margayi yaya Habeeb komai.
''Ita kanta tasan samun Habeeb Lamido a matsayin mijinta Rahama ce ta ubangiji Haleesa
tayi ajiyar zuciya mai k'arfi tana ware idanunta akan fuskar Habeeb tak'ara jin wani Sabon
sonshi yana kwarara a zuciyata.
''Wata zuciyata tace What are you waiting for Haleesa just tell him you love him, nan take
wata zuciya tace Haleesa za ki zubarda ajinki ne ki yi amfani da damar da ki ka samu, ki latsa
shi kamar yadda shima yabaki wahala.
"Yatsine fuska tayi kaga bawan Allah nace bana sonka ka kyalleni ka fita daga rayuwana idan
kace za ka cigaba da matsanta mun za ka nemi ni karasa, kuma karka yi tsanmani zan tafi Yola
uwa duniya zan shiga idan har ka mutu bara ka samu Wanda zai ce ya ganni, ba don haka
karka yi wa iyayyena asara ta domin su ne suke min soyayya ta gaskiya ba pretending ba.

"Dafe kai yayi had'e da furta Omg! Wani tuk'uk'i yake ji a zuciyarshi ran 'yan maza yafara 6aci
shi dai gashi ba gwanin surutu ba amma yak'ure malejinshi yadawo tamkar parrot duk don
Haleesa ta fahimce irin mugun sonta da ke d'awainiyya da shi takasa fahimta sai wani banza
zance da tashigo mishi da shi wai yana ,pretending. "Habeeb ya mik'e a sanyaye ya zauna kusa da ita ta matsa da sauri yak'ara matsawa ita ma
tak'ara matsawa haushi ya turnuk'e Habeeb ya d'ank'i hannunta yashiga murza yatsunta da
k'arfi ihu taje kurmawa da sauri ya had'e bakinshi da nata tsawon lokacin suka, dauka a haka
daga bisani yasaketa ya had'e goshinshi da nata yad'anna mata cizo a hanci ta runtse idanunta
hawaye, yasoma gangaro mata ban yarda ba yaya Habeeb baka sona yaudara ta ka ke yi za ka
cuce ni ne watakila har yanzu da raguwar sona wata a zuciyarka
Can! K'asan mak'oshi yafurta meyasa bakida tausayi leesa"?
''Ko makaho ya dubi zai gano I'm in love with you leesa.
"Yatsine fuska tayi tace watakil ni makauniya, ce shiyasa nakasa amincewa da kai.
"Habeeb ya girgiza kai yace mu ajiye wannan zance a gefen banaso ki amince ki ta kallona a
matsayin Wanda baya sonki, don ma kinsamu ina rarrashinki kidaina gani mom tana cewa sai
na sake ki fad'a ne kawai take yi don taji dad'in bakinta tasaki nishad'i amma wallahi koda za ta
aza mun bakin bindinga aka zan furta mata inasonki ba wai kalma saki ba yanzu ki yi favour
d'aya za ki yi min kitash mu tafi hospital a duba min idanu nan naki banaso wani abu yasame ki.
"Murmushi takacin Haleesa tayi tace ae ba wannan ne karo na farko da kasaba mari na
idanuna su yi kwancin jini yatsunka su sami muhalli a kumatuna karka damu kanka wannan ba
bako bane a wurina
"Murmushi Habeeb yayi had'e da d'anke yatsunta, uhm...leesa yanzu abunda yafaru almost
3 years ashe baki manta ba"?
Harara ta zuba masa ta kauda fuska.
Duk yadda Habeeb yaso Haleesa ta saurare shi tak'i daga karshe ma ta yi mik'e tanufi k'ofar
fita da sauri yadawo da ita da kyar ta amince ta zauna.
"Cikin tsawa tafara magana nace bana sonka yaya Habeeb ka kyalleni kai ka manta irin
wulaqancin da ka dinga zuba min eyeee"?
Ko angaya maka banida zuciya a kirjina to ina gargad'inka kafita harkata I don't love you
anymore banaso ganinka please stay away from me tak'arasa magana cikin sautin kuka.
"Habeeb ya ja iska cike da takaici yake kallonta ahalin yanzu kalamai bakinshi suna daf
takarewa.
"Tsawon lokacin suka dauka ba Wanda yak'ara magana Habeeb ya kai dubanshi akan wrist
watch d'in hannunshi zaro ido yayi cikin kaduwa yake kallon Haleesa daga bisani yace ki dubi
tsawon lokacin da na dauka a d'akinan ina miki magiya wannan kadai bai isa ya gansar da ke
inasonki ba. "leesa ba abunda nake ba wa mahimmancin irin lokacin domin da yawuce ba zai dawo ba
amma gashi throughout ba inda naje ina zube a gabanki ina miki magiya ki ji tausayina leesa
kiyafemin.
"Haleesa ta yi shiru kamar tana nazari daga karshe brain d'inta ya nazarto mata mugunta da
za ta yi wa Habeeb yadda za ta yi hurting nashi very badly tad'ago idanunta fuskarta d'auke da
wicked smile, tafara magana tana yatsina kamar yadda Habeeb yake mata a da zan amince na
kar6i tayin soyayarka amma a bisa sharad'i d'aya ta d'an suke numfashi tana jiran ta ji ta

bakinshi.
"A Rikice Habeeb yad'ago muryarsa na rawa yace menene sharad'in naki"? muddin za ki
amince da ni zan iya.
"Wani shu'umin murmushi Haleesa ta yi tace............


Jeeddah Aliyu🌹

[10:42PM, 15/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [15/12 5:23 pm] aliyujeeddah: ```�NI DA YAYA
HABEEB�```

_�the sweetest love_�

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

_this page dedicated to only you my sweet Mrs Umar Billions words can't ever exprees how
much I love you but I wants you to known that Fatee you're very special person to me
remember that & always saying KE D'AYA CE FATEE_

```93```

~~Ta d'ago da sauri ta dube shi, ta yi fari da ido cike da mugunta tafara magana anyya kuwa
yaya Habeeb za ka iya?
"Murmushi ya yi had'e da lumshe ido wannan ba matsalarki bace, ke dai kawai ki fad'i
sharad'in naki matar na tuba ae bata rasa mijin aure.
''Ta tabe baki uhm......sharad'in na ba wani mai zafi bane inaso in tabbatar da soyayya da ka
ke kirarin kana yi min ta gaskiya ce ko kuma pretending ka ke yi domin kasami damar cigaba da
kawarda sha'awarka akaina.
Da sauri ya kalle ta ya kawar da kai wannan ya ba wa Haleesa damar cigaba da cewa indan
har da gaske yaya Habeeb kana sona ba sha'awata ka ke yi ba daga yau karka k'ara zuwa inda
nake kuma karka kirani a waya, na har tsawon watanin 3 idan da gaske kana sona za ka iya
jure wad'annan watani batare da ka waiwaye ni ba indan kuma sha'awa ce na tabbata kwana
d'aya tak ba za ka iya ba batare da ka zo inda nake ba yanzu dabara taragewa mai shiga rijiya
za ka iya"?
"Sai lokacin Habeeb yad'ago ya yi mata, kallo lalle yarinya nan kin zare da mugun mamaki
yafurta _3 month_ fa ki ka ce leesa"? Ina laifi ki ce 3 day's su d'in ma zan yi sune adaddafe
haba gaskiya I can't do this!
Haleesa ta ya mutsa fuska idanuta suka ciko da kwalla cikin muryar kukan kissa had'e da

shagwa6a tafara magana, ni dama nasan baka sona yaudara na ka ke yi idan da gaske
soyayya gaskiya ka ke mun miye _3 month"?_
''Please leesa ki fahimce ni irin son da nake miki ba zai barni na d'aukin tsawon wannan
lokacin batare da nayi tozali da kyakyawar fuskarki ba indan nace zan tilassawa kaina hakan zai
iya cutar da ni ina miki so na hak'ik'a dai-dai da second 1 banaso na nisata da ke yak'arasa
magana cikin sanyin murya. "Juya masa baya tayi shikenan yaya Habeeb za ka iya tafiya amma kafin katafi kasani a
kowane lokacin za ka iya nema na karasa domin ba zan iya cigaba da zama da mutume da ba
zai iya jajircewa akan farin cikina ba Wanda hakan yanuna mini har yanzu zuciyarka tana
wasiwasi da soyayyata. ''Zuwa wannan lokacin Haleesa tafara k'ular da shi ya mik'e a fusace I can't leesa ni da nake
fatar yau d'inan mom tabarki ki koma gidana mu fara shinfid'a kyakyawar rayuwa shine za ki
tsiro da wannan shirme"?
''Kafin Haleesa tabashi amsa madam Hindu ta turo k'ofa tashigo tana rafka salati cikin kad'uwa
Habeeb da Haleesa suke kallonta.
"Ohh...ohh....son dama har yanzu kana cikin gidanan"? Shine ka kad'a mun yarinya a parlour
kai kuma ka zo nan ka kasa ka tsare uban me yashigo da kai nan shin ba nace banaso na k'ara
ganin k'afarka a gidanan ba"?
"Cikin sark'ewar halshe Habeeb yace ni fa ba wani abu ne yashigo da.........
''Kai dallah! Saurara wannan tsayin da na tarar da kai kana yi karatu ne ka ke koya mata ko
me"?
Huh......sweetheart hak'uri ne nake bata.
"Ae yanzu bakada sauran kalma da za ka yi amfani da ita wajen bata hak'uri tajuya wajen
Haleesa tace hukuncin da ki ka zantar ya yi mun dai-dai ni anawa ra'ayi so nayi yabani takarda
ki kowanenku Allah ya had'ashi da rabonshi.
"Habeeb ya hadiye wasu yawu masu mugun d'aci yana kallon madam Hindu a tsorace yana
mamakin yadda take k'ok'arin shiga tsakaninshi da farin cikinshi, Iya saninshi Sam baya laifi a
wurinta, amma sai gashi yau ta zo mishi da abunda bai saba da shi ba.
''Daga yau karna k'ara ganin k'afarka a gidanan har sai watanin 3 sun cika maganar madam
ce ta katsiwa Habeeb tunani yayinda Madam tacigaba da cewa idan kuwa ka kuskura tsautsayi
yasa ka tak'o k'afarka gidanan to kasani a bakin aurenka ko ba haka ba Haleesa"?
''Da sauri Haleesa ta gyad'a kanta.
Habeeb ya yi sororo yana kallonsu Madam ta galla masa harara tace kama hanya katafi cikin
zafin zuciya yanufi k'ofa ya bud'e da k'arfi yafice a downstairs parlour ya tararda Hannah tana
kallo rankwashi mai zafin gaske ya zuba mata aka _wayyo Allah mom yaya Habeeb zai kashe
ni_ Ke! Munafuka yafad'a a tsawace shiru ko na wanka miki mari duk gargad'in da nayi miki bai
shige ki ba da yake ke munafuka ce saida ki ka fad'awa sweetheart ina d'akinki tare da leesa
koh"?
"Allah yaya Habeeb bani na fad'a mata ita ce da kanta tagane.
Harara ya watsa mata yanuna ta da yatsa yayi kyaci yafita yana huci cikin zafin rai da baqar
zuciya yanufi parking lot ya bud'e k'ofar mota yashiga Bala yagani ya kwa6e seat yasaki Ac
yana sharar bacci hadda su dogon minshari.

Wawan duka Habeeb yakai masa a kafad'a kai! Dallah tashi a rikice Bala ya tashi ya gyara
zaman seat yayi hamma had'e da mik'a cikin murya mai d'auke da alama bacci yace "Boss wai
kana nufi duk tsawon wannan lokacin munan gidan"? gaba d'aya na manta da inda nake.
Hararashi Habeeb yayi yace ae dole ka manta da inda ka ke saboda hankalinka a kwance
yake jiya-jiya ka yi wa motar nan ''full tank dubi yadda fuel ya yi k'asa ka k'ure Ac kana sharar
bacci abinka ni kuma ina cikin gida ana mun barazana da rayuwa.
"Tuni Bala ya watsarke ya zaro ido boss wane mai k'arare kwana ne yake maka barazana da
rayuwa"?
"Tsaki Habeeb yaja yace kai banaso shirme banza ja mota mu tafi Bala ya yi wa mota key
yanufi gate maigadi ya wangame musu gate suka fice.
"Madam ta dubi Haleesa tace ina mai k'ara baki hak'uri akan abunda son ya yi miki Haleesa
shiyasa nakeso, ki yi amfani da damar da Allah ya ara miki kema ki rama abunda "son yadad'e
yana miki.
"Murmushin jin kunya Haleesa ta yi tace tun jiya ki ke ta bani hak'uri mom har kinsa nafara
jin kunyarki.
Madam tayi murmushi had'e da rik'o hannun Haleesa tace tsakanina da ke ba, jin kunya
Haleesa ni fa tamkar mahaifiya ce a gare ki shiyasa nake gargad'inki kada ki yi sauri ba wa ''son
fuska har sai yagano shayi ruwa ne.
''Haleesa tayi murmushi had'e da sadda kai k'asa.
Madam tajuya da murmushi tafita Haleesa ta yi ajiyar zuciya ta koma ta kwanta, ta lumshe
idanu wani irin dad'i yana ratsata.

_3 days later_
Habeeb na kwance a parloun'shi kwanaki 3 kacal har yafara fita hayyacinshi bashi da aikin yi
sai tunani gaba d'aya duniya tayi mishi qunci yanaso zuwa gidan madam yana tsoro kada allura
ta tono galma.
Mus'ab da Bala suka shigon parlourn sai faman kyalkyalar dariya Mus'ab ya zauna kujera da
ke facing d'in Habeeb yayinda Habeeb ya watsa masa mugun kallo ya mik'e zaune wai kai
Mus'ab wane irin marar imani ne kai"? Na kira ka ne don kanema min mafita inason matata ba
zan iya jure tsawon watani 3 batare da na ganta ba yak'arasa magana cikin murya tausayi. Mus'ab ya dube Bala suka wani zaro ido kowanensu ya yi murmushin shak'iyanci A fusace
Habeeb yafara magana wannan wane irin iskanci ne ya ina muku magana kuna mini
murmushin munafuncin gaba d'aya Ku na fahimcin farin ciki Ku ke yi da wannan hali da na
shiga yayinda Habeeb rufe ido yadinga zazzaga masifa saida yagaji don kanshi ya yi. Mus'ab ya hadiye dariyarshi yana mamakin zafin kan Habeeb shi dai komai da zafi yake
d'aukarsa yanzu Wanda yake cikin wannan hali ina yaga bakin fad'a da wani.
''Tsanm.....Mus'ab ya mik'e yanufi kusa da Habeeb ya zauna yadafa kafad'arshi calm down
abokina irin wannan tada jijiyoyin wuya har ina"? Yakamata kasawa zuciyarka salama ka
sausautawa kanka wannan saurin fushi domin ba inda zai kai ka.
"Habeeb ya d'age gira ta kasan ido yake kallon Mus'ab daga bisani ya ja iska yace kaga
malam za ka nemo min mafita ko kuwa"?
Girgiza kai Mus'ab ya yi yace akwai mafita guda d'aya chal, yanzu abunda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login