Showing 6001 words to 9000 words out of 21093 words
Chapter 3 - TA DABAN BOOK COMPLETE By AMMEY LAYLERH.pdf
yake gudana a tsakan kaninsu.
soft Fararen hannuwansa ya miƙama yaron daya kasance me sunan shi, domin Mohan
Sameer Jedaans kai tsaye sunan Sheikh juraij ɗin ya sakama yaron. Wanda Sheikh kema wani
kalan mahaukacin so na tashin hankali,Yes shi kansa yasan yana son yara sedai tayaya me
zeyi auren bare har a haifar mishi yaran?
A kullum kwanan duniya shine tambayar dake addaban zuciyarsa. So da Ƙaunarsa a gun
mace ɗaya yake baida feelings akan ko wacce irin macece koda kuwa zatay yawo tsirarane a
gabansa. Sedai a yanzu yasan wannan ɗin ya zama kamar tarihine don ko kyauta aka bashi
baya jin ze ko iya kallonta a matsayin mace, macen ma kuma ta aurensa. tun iyayensa na
damuwa da rashin aurensa har suka tattara lamuran suka miƙa buƙatunsu wurin me du ka me
kowa me komai wato ALLAH. Ɗan gyaran muryan da Mohan yay a karo na biyu ne ya dawo
dashi daidai ɗin sa. Magana ne sukai akan zaman meeting ɗin da yake da shi da ƙarfe 11:30 na
yau. Daganan suka ɗan tattauna maganganu akan yadda al'amuran kasuwancin nasu yake
tafiya.
★Araund 7:50 kowa na gidan ya gama kammala kansa a babban dining room na gidan inda
room ɗin yake ɗauke da rassa daban daban na dining table. Meesherh itane ƙarshen fitowa
kuma dama kusan kullum itane last, zama tafi fuskan nan ta kan daren jiya kan wayewar yau ta
sake yin fiyau. Bata ɗaga kanta ta kalla kowa ba bare ma woni yay tunanin kawo mata wargi,
kamar kuma yadda bata gaida kowa dake room ɗin ba.
Annie ce ta dubeta cike da jin zafin da bata san kona miye ba ta furta. "To Ishashshiya
tunda babu tarbiyyar girmama na gaba dakai se a tashi ayi saving namu dinner,Mutum kuma in
yaji haushi ya ajje aikin shirmen da yake ya koma Islamiyya kodan sanin yadda ake girman na
gaba dakai" Idan ƙasar dake wurin tayi motsi to kuwa tabbas Meesherh ɗin ta yi itama. Don haka wurin ya
ɗauka wani kalan mugun shiru kowa na kissima abubuwa maban banta a cikin rayukansu.
Papiey' ne kawai yay ƙarfin halin duban inda Meesher'n take bawai don beji zafin maganan da
annien tay akan gudan jinin nasa ba. A ahhh sedai kara da kawaicin da ya saba ma yayyensa
iyayen su juraij ɗin kenan. kasancewar shi autan su kuma mutum mafi haƙuri da jure ko wanne
kalan ƙalubale daga Ahalin nasu. Ɗan zafawa yay tare da furta.
"Mamana bata ji ana magana ba ne?" Prof Sameer Jadeens yay maganan yana duban inda
Meesherh ke zaune. Cike da rashin haƙurin da mijinta Sameer Jadeens yaga ta kowa take
dubansa, domin kuwa ita ɗin ba sakar ya bace da zata ji ana muzanta jinin ta kuma tai shiru,
"Amma ai Papiey'n Meeshel kadai fi kowa sanin cewan Meesherh bata da lafiya? Ko duk ba
gasu Nainerh nan ba, su Aysha su Nanameerah su Salma ba se ita kaɗai za'a kalla ace tayi
saving namu dinner"
Ya buɗe baki kenan da nufin mata magana Jedaans turaki ya katse shi ta hanyar masa nuni
da eat kawai don wannan loƙacin dinner nasu ne. Kafin kowa ya miƙe Annie ta miƙe ranta na
mata suyar ƙin tanka tan da Meesherh tayi. Hakan ya sanya cike da fusata ta furta, "A dai koma
Islamiyya ko a samu rabon kusanta kai ga Allah" wani irin shiru mai saka duk wanda ya shiga mutuwar jiki gurin ya ɗauka, Don hatta metres
sarvice ɗin dake ta aikin kai da koma a wajen tsit sukai.Kallo ɗaya Maminsu Moh Saif Ameen
tama ma'aikatan wurin suka tare duka a take.
Ajiyar zuciya me ɗan ɗumi Sheikh ya sauƙe a natse, se kuma ya miƙe tsammm a wurin se
dayay taku ɗaya ana biyun a dakata. Cikin wannan natsatstsen low tong voice nashi ya furta.
"Kiyi haƙuri Annie Amma kai tsaye daga yau na soke duk wata magana da zata fito daga
bakin ki akan baby da Mah, Indai bame daɗi bace kai tsaye da yawun bakin Abbie nay magana"
daga hakan ya sanya kansa yana barin room ɗin baki ɗaya, yanajin hankalinsa na dawowa
jikinsa kodan umarnin abbiensa daya cika akan annie'nsa.
ɗago idanuwanta rinannu tai da sukai laushi ta kalla Eng Thabit Jedaans wanda shima juyowa
yayi ya kalleta da idanuwansa da suka nuna babu wasa ko wargi a cikinsa.wata bahaguwar
ijiyar zuciya ta sauƙe ahankali tana matse hannuwanta duka biyu a wuri guda.Ga Wani kalan
shegen sanyin da taji yana ratsa ilaihir gangar jikinta. Wani kyakykyawan murmushi tsohon ya
saki wanda ya fito da ƙananun teeth nashi farare tasss kamar ba na tsoho ba. Kai tsaye zaratan
magidan tan ƴaƴan nashi suka bishi da ido. Wani murmushin ya sakar musu na badai zaku
fahimtar komai ba. Daga haka ya miƙe tsaye da ƴar sandarsa ta narkakken zinare me sheƙi
yana barin parlour'n baki ɗaya ma. Daga haka suma kowa ya miƙe kasancewar sun san lalle
kenan akwai abinda tsohon yake shirin aikata koma yana dap da aikatawar.
*Sheikh juraij*
Kai tsaye katafaren dogon ginin sa ya nufa ba hasalin wanda yake a ciki yanzun ba. A cikin
can ƙasan zuciyarsa yake furta. "Hamdan,khathiran,ɗayyuban barrakhallahufihi!!!" Domin ma ya
rasa abin magana akan Anniensa ya kuma rasa wanda kalan tunanin ya kamata yayi.
Nosemask ɗin dake cikin aljihun farin dogon yaɗin jikinsa ya ɗauko yana sakayawa a face
nashi.
duk rabin face nashi a rufe da nose mask ɗin se glass ɗin daya sanya. Amma hakan ba shi ne
zai hana ka gane cewan shi ɗin kyakkyawa ne ajin farko ba, Yana da murɗaɗen jiki haɗi da
murjewan fata,yana da wani irin faffaɗan ƙirji tamkar irin India actor's ɗin nan.Damtsen hannun
san nan tamkar sa fashe saboda training gym da yake yi a ko wacce safiyar duniya. duk girman wajen shiru babu motsin ko wanne rai me numfashi, dama haka yake sau da
dama yakan zo sa'i zuwa sa'i don kaɗaita kansa daga kowa musamman idan yana hali na
damuwa.zaune yakai kan wata fara tas ɗin sofa. jikin nan nasa se glowing na ƙyau da kyau
kawai yake kai ka rantse da Allah bai taɓa taka koda ƙasa bane, Saboda tsananin laushinta da
kuma yadda take ɗaukan ido na tsantsan kyau. Gashin nan a kwance luff luff tamkar wani
renon larabawa ko turawa.Duk inda kaji an ce Sheikh juraij thabit Jedaans to ana nufin wannan
Kyakkyawan farin matashin malamin ne mai jini a jika, sosai yake da hasken fata da kallo ɗaya
mutane suke bashi sunan ko .
dogone cikakken namiji me cikqkkan wayewa na addinin Islama daya gama ratsa jinanen
jikinsa, yana da faffaɗan ƙirji wanda yasa kai tsaye muscles nashi bayyanuwa sosai.
Wannan kyakykyawar Innocent face ɗin nashi ɗauke take da dogon hancin da ya ƙara wa
fuskarsa wani kalan kyau da zati, ɗan karamin bakinsa ɗauke yake da kyakkyawan Pink lips
kalan masu shining ɗin nan tamkar wanda ake goga musu lipstick. Wanda hakan ba ƙaramin
kyau ya ma ɗan ƙaramin bakinsa ba ta hanyar masa ƙawanya. A hankali ya ɗago da dara daran fararen idanuwansa masu kama da ana musu ɗuren
madara masu shegen kyau kamar yasa musu ƙyalli, kwayar idanuwansa da ta kasance light
irin me tsananin hasken nan mai ɗaukar ido, idan kayiwa idon na shi kallo a fusge sai kaga
kamar ruwane suka tarun masa a cikin eyes ɗin nashi. Don kuwa sedai a fisgen don da matuƙar
wuya kace ka taɓa iya haɗa ido dashi koda na tsawon 1 mints ne. Don wani irin kwrjinine dashi
na Zati da kuma girman da musulinci ya bashi, kai tsaye idan da za'a faɗa maka yawan
shekarun Sheikh juraij thabit Jedaans to lallai tabbas zaka Musa ne. Don wani kalan
kyakykyawan ginannen jiki me kyau da tsada Ubangiji ya ba shi, kai bakace wannan first born
ɗin bane na JEDAANS wanda yake matakin girma na shekaru ɗai ɗai har shekaru 47 year's.
Kai tsaye kai a naka lissafin zaka iya bashi shekaru kamar irin 31/32 ɗin nan ne. Kai bakace ma
ya haura 30 year's ba shugaban .
A hankali ya fara motsa idanuwansa da suke a ɗan lumshe har dogayan eye Lashes ɗinsa na
motsawa suma sosai ,wanda hakan ya sanya sosai girarsa take a cike itama motsawa da
haɗewa sabida cikarta ya sanya motsa fuskan nashi dayay suka haɗe da juna, gefe da gefen
fuskar sa duk gargasar gashi ne da yasha gyara irin me luff luwai ɗin nan kuma veey mood for
anything, A natse ya ɗan kai hannunsa ya shafi kyakkyawar dark brown hair nashi fuskar nan
ɗaure take tamau kamar bai san me dariya ba ma a duniya.Wani irin ƙamshinsa ne baki ɗaya
ya gama gauraye ilahirin gurin hutawan. Wanda kai tsaye kowanne hanci dake shaƙan
ƙamshin yake masa laƙabi da na musamman, don tsadansa da kuma ƙamshinsa ya banbanta
da wasu ƙamshin sbd kai tsaye shi nashi ƙamshin cikin sanyi me nutsuwa yake shiga ya wuce
zuciya mutum kai tsaye.
Jin motsin shigowar Personal person ɗinsa wato Al-Ameen Hafeez gurin ne kuma ya
sanya buɗe idon kai tsaye yana sauƙewa akansa. Waya ya shigo yana yi wanda kai tsaye akan
zuwan su Lagos ne da zasu wanda wasu manyan malaman can ɗin suka turo masa gatin
gayyatarsa ta cikin email address nashi dama saƙon kai tsaye. Tun kamin ya ƙara so inda yake
ya kashe wayarsa ya ƙaraso har inda Sheikh ɗin ke zaune, Nuni ya masa daya zaune daga
kujeran hutawan dake gefen sa, System nashi ya buɗe directly a gaban Sheikh ɗin nan ya shiga
gabatar masa da yadda tsarin tafiyan nasu ze kaya da booking flights ɗin daya riga tun daren
jiya ya musu. Sosai ya gamsu da jawaban Al'ameen ɗin kuma nan da 45 minutes jirgin nasu ma
ze tashi kasancewan a yau ɗin suke zon zuwa Lagos ɗin kuma su dawo a yau ɗin. Daga nan
Personal person ɗin nashi ya fice shi kuma ya miƙe yana shigewa zuwa ɗaya daga cikin
ɗakunan palonsa ya zauna ahankali akan 2 seater ta turkish luxury sofas dake palon ya zauna,
wanda ƙamshi da sanyin ac/n suka gama ratsawa.Wayarsa dake gefensa ajiye ya kai dogon
hannunsa fari tas ya ɗauka yana cireta daga flight mode ɗin daya sata kai tsaye yana calling
wata No.
Maganan seconds sukai ya ma kashe woyan baki ɗaya a natsensa ya miƙe bedroom dake
palon ya faɗa. Minti kaɗan ya fito cikin wata shigar ta daban, Ta can wata sihirtacciyar hanya
yabi domin sauƙaƙama kansa tafiyan. Apartment na iyayensa ya yaje ya musu sallama don tsaff
yake da shirinsa na tafiya Lagos ɗin. Adda'a Abbiensa ya may Annie'nsa kamm ko inda yake
bata kalla ba, Se kuma yaji duk babu daɗin hakan har yaji tafiyan ma nason fita masa a rai
gaba ɗaya, ganin yanayinsa take ya sanja ne ya sanya Abbie ƙarfafa masa gwiwa harda ma
daɗin yar nasiharsa bayan anniey tabar palon.
♡ Kai tsaye inda manyan jibga jibgan motocin sa suke a Parker ya nufa,da guda ɗaya ya fita
kasancewar airport ne kawai zasu kaishi. Sedai hakan be hana wasu daga cikin securities na
gidan rufa masa baya ba. Suna zuwa befi da 3 mints ba girginsu yay landing zuwa garin Lagos.
A Wani babban wuri wanda ake tanajarshi kawai domin yaɗa aikin ALLAH suka sauƙa.
Fuskansa da tsananin haiba da kuma tsananin kwarjinin dake firgita magautanshi ya fara tafiya
akan sawayensa. Yana Sanye cikin shigan nan ta al'farma shigar dake nuna nasabarsa ta
kowacce sashi,Wanda madarar ilimin addinin daya gama kwankwaɗar romansa. A natsensa ya
zaune a inda aka tanajar masa se gefinsa kuma Personal person ɗin sane tsaye cakk tamkar
woni dogari. Cikin rahama da ni'imar da ubangiji (S.W.T) yau ma wannan bayan nashi ta iya sarrafa
harshe da tausasan laffuza, ya soma da gabatar da adda'o'in zaman lafiya wa ƙasar mu
Nigeria. Wani kalan Shiru mutanen dake cike da wurin suka ɗauka kamilallar muryan san nan
na ratsa musu har jinin jikinsu. Bayan ya kammala tarin Adda'o'in sa A hankali kuma yasa hannunshi yana gyara zaman
Microphone ɗin dake maƙale wacce ta zagayo harta bayan ƙeyarsa, wanda hakan ya zamewar
kamar ƙarin ƙawata adon nashi ne. A hankali ya lumshe idanunshi kana yayi ƙasa da kanshi
cikin yanayin nitsuwarsa ya buɗe pink lips nashi cikin zazzaƙan sautin muryarsa bayan ya
gama kawo jawabansa akan *MUTUWAR ZUCIYA* yaci gaba da furta.
"Idan kana karanta littattafan tarihi to tabbas za ka ga a kowane zamani bayin da ake
bautatarwa sun rabuwa kashi biyu ne!. Akwai bayin da ake azabtar da su!, Kana akwai kuma
bayin da suke jin daɗin kasancewarsu bayi a ƙarƙashin wasu, waɗanɗa zuciyarsu ta gama
mutuwa murus,ba sa tunanin ƴancin kansu Alal misali...... Zamanin da aka kwashi baƙaƙen fata daga nahiyar Afirka zuwa Amurika da Turai da sunan
bayi, ana bautar da su.Wanda Bayin sun kasu kashi biyune, Bayin Gona da kuma bayin gida.
Bayin Gona su ne masu yin aikin noma da sauran ayyukan wahala,kai tsaye su ne waɗanda
ake azabtarwa Su kuma bayin gida su ne waɗan da suke gidajen masu gidansu fararen fata,
suna yi musu aikin bauta suna cin abincin da suka rage, da sanya tsofaffin tufafinsu. da kwana
a gidajensu suma waɗan nan bayin gidan suna jin daɗin bautar sune har ta kai ga ba sa tunanin
samun ƴancin kansu da kuma rayuwarsu.
Su kuma bayin gona waɗan da suke cikin azaba sune wanda kullum suna tunani tare da
ƙoƙarin samun ƴanci daga ƙangin bautar da suke cikin ta. Idan bayin gona suka nemi haɗin kan
bayin gida domin gwagwarmayar neman ƴancin kai da kai sai waɗan nan bayin gidan su
ƙalubalance su, Kana su ƙi ba su haɗin kai! sa'an nan kuma sai suje su gaya ma iyayen
gidansu sirrin bayin gona na yin tawaye da neman ƴancinsu. Su kuma sai masu gidan su daƙile
shirin bayin gona na neman ƴancin kai da kai bayan sun sake ninka musu bautar da suke musu
akan ta baya........Su bayin gidan masu moruwa da fararen fata, suna rusa shirin yan'uwansu ne
wajen neman ƴanci ba don wata hikima ko wata manufa ba, a'a, sai don kawai tsoron yankewar
ragowar abinci da tsofaffin tufafin da suke samu daga masu gidajen nasu. Su a wajensu
wannan ragowar abinci da tsimmokarar sun fi ƴancinsu muhimmanci. Irin waɗan nan bayin
gidan su ne musabbabin rashin nasararsu wajen neman ƴanci a duk lokacin da mutanen da ake
zalunta suka yunƙura. Akwai kalar mutanen da sun saba da rayuwar bauta,Waɗan da
zuciyoyinsa suka riga da suka gama mutuwa ƙurmus murus, wanda suke jin kansu ba za su iya
rayuwa ba a ƙarƙashin wani ba, yau da za a yi ruwan ƴanci da da lema za su riƙa yawo. Duk
lokacin da waɗan da ake zalunta suka yunƙura, su waɗan nan bayin gidan ne za su
ƙalubalance su. Sai ka ga azzalumi ya harɗe ƙafa bisa karaga yana kallon bayinsa na gida suna
tare masa faɗa daga bayinsa na gona, don haka ya yan uwana Musulmi ya kamata ace
munbar wannan mutuwar zuciyar da take neman aurenmu, Wanda muke jin ai seda wane ko
wance kana ni zan kai labari!!!......
A ahhhhh ba haka bane kai kanka ba zaka gane hakan ba se loƙacin da kaganka a
tsayayyen ingarman Namijinka sannan zaka tabbatar da cewan lallai ba seda wani wanin yake
rayuwa. Ka sama kanka yaƙini da ƴancin cewar ehhhhhh lallai tabbas zaka iya. To da ga nan
ne se Ubangiji ya jiɓanci dukkan lamuranka da kasa gaba, se kaga ya zaman kama wasu zarra
da nisan kiwon da koda gudun ceton rai aka haɗa shi be Isa kamo koda kamu ɗaya bane. Don
haka har gaban abada zuciyar kowannenmu ta kasance jajirtacciyace me jin zata iya. Ya kori
wannan nakasar dake bisne cikin zuciyarsa domin Ba kasawa bace...."
Ƙiran sallar la'asar da aka ƙirane ya sanya Sheikh juraij thabit tsayawa chakkk, daga ta cikin
zuciyarsa kuma yana me ambatar wannan addu'ar ta ƙiran sallah. Kowa dake wurin be so ba
haka suna ji suna gani sheshin malamin ya kuma gudanar da addu'ar tashi bayan ya musu
alƙawarin Inda Rai da Rabo wata rana INSHA ALLAH zasu ɗora daga inda suka tsaya. Sahu ya
biyo shima kamar yacce al'adansa yake bawai irin al'adan wasu daga cikin manyan malaman
mu na yanzu ba. Ko nace masu mulki da wasu masu kuɗin, Yazo dap da wasu matasa biyu
karaf buɗaɗɗun kunnuwansa suke nan kamar na maciji suka jiyo masa wasu munanan kalmomi
daga gare su.......
.........kunsan dama ance ɗan Adam ba'a iya masa?_
_Yaya kuke tunanin wasan ze kaya?, Gadai sheik juraij thabit Jedaans nan ga kuma waɗan nan
samarin nan_
*BY AMMEY LAYLERH*
08104493215
Byeeee
https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH
༺༻
*♡ ☆*
༺༻
_ °♡◦༺ _ҽcⅈɑʟ_ °࿐_
ᴺᵃˢᵉᵉʳ ɱⅈɑһ
_AMMEY LAYLERH_
ِ
مْسِب_* ِ
هَّللا ِنٰ
َمْحَّرلا