Showing 12001 words to 15000 words out of 21093 words

Chapter 5 - TA DABAN BOOK COMPLETE By AMMEY LAYLERH.pdf

25 Apr 2025

1963

ci gaba da sipping coffee creamer ɗin ta. A
cikin zuciyarta ayyanawa take ehhhhhh lallai Pa'apanta na daban ne kuma me kyau ne da
kuma tsafta. Wanda indai magana ake ta wanka yabi jiki to kuwa ba tantama tasan pa'apanta
ƙarshe ne. Sam babu ko ɗigon annuri a kyakykyawan farar fuskan shi haka babu wasa ko
alamarsa a saman fuskarsa nashi da tai wani kalan fayau, wanda kai tsaye ita tasan dalilin
daya haddasa may hakan.
Don kamar yadda yasan duka halayensa haka itama ta san duka halayensa da kuma kalan
damuwan da yake shiga ko akasin hakan. Kowa dake parlour'n wani kalan shiru yay har ya
gama saƙƙowa,kallon kowa baiyi a cikin parlour'n ba saima ta bayan parlour'n daya zaga yana
shigewa cikin balcony in da kai tsaye nan ake jera may abu mara nauyi duk daren duniya ba
tare da su yake yin lonch ba. Wayane maƙale a kunnensa wanda da dukkan alamu wata
wayace yake yi muhimmanci.
yana yin wayar ne kuma hannunsa na ɗauke da wani haɗaɗɗen glass cup mai ɗauke da
Whipped cream a ciki yana sha. Gefensa kuma Mohan ne da bay jima da biyo bayansa ba
shima zaune saman sofa se woyansa da yake aikin dannawa wanda alamu suka nuna kai
tsaye chatting ne yake yi. Shima nashi hannun ɗauke da Extreme milk shakes ɗin dake a
saman ɗan table ɗin dake gaban Sheikh juraij ɗin.
★ Bayan ya kammala woyan kai tsaye ya maida kallonsa ga Mohan ɗin. "Yaya abubuwa
sosae suke yin kyau game da binciken sirrin da muke yi kamar yadda ka buƙatan ama. To
Alhamdulillh se dai mu ce Masha Allah" Gefin lips nashi ya ɗan ciza kaɗan se kuma ya furta
"don't worry zamu magana daga baya ina buƙatan hutawa yanzu" kansa ya gyaɗa may yana
miƙewa harya fara tafiya kuma ya tsinkayi muryan babban yayan nasu yana ambatar sunan shi
kai tsaye da *Mohan Sameer* chakk ya tsaye tare da waigowa alamar gaskata in ƙiran ne ya

koma. nodding Kansa yay alaman ehhhhhh ƙiran yay, baya ya dawo yana zama inda ya tashi.
Magana yake son may game da Meesherh amma bakinsa ya masa nauyi se kawai ya fiddo da
wani kyakkyawan ƙaramin kwali me kyau da ɗaukan hankali "Na lil juraij Mohan ne" amsa yay
fuskansa ƙawace da murmushin jin daɗin kulawan da Sheikh ɗin kema yaron san, duk da
yasan kome yake da buƙata shima a cikin duniyar yakan iya narka kuɗaɗen sa wajen siyan ko
miye se dai ita kyauta ɗaya ce kuma daban take. Duk yawan tarin dukiyar da kake da to fa idan
wani ze ciri wani abu ya baka as matsayin kyautatawa wani kalan jin daɗi kake. Kwarai kyauta
Rahma ce kuma takan sanya mutum yaji daɗi da shauƙin kyautan da aka masa. Godiya ya may
cike da fara'a yana barin wurin gaba ɗaya don bashi space ɗin kamar yadda ya buƙata.

A ƙalla seda ya debi wasu ƴan lukuta masu tsayi kana ya miƙe yana bin ƙofan fita wajen
parlour'n ta baya.
Ji yay a jikinsa tamkar ana kallonsa loƙacin da yake tafiya domin nufar ɓangaren sa, tana
tsaye cikin kayan shan iska amma ba masu nuna tsiracin mutum ba kanta babu cap hannunta
riƙe da woya tana daddannawa. Ido biyu sukai tay saurin janye nata tamkar dama can ba shi
take kallo. Se hakan ya Hasko wani abu daga cikin memory'n baya cann. Ko me ya tuno kuma
oho amma kome ya tuni me girma ne dan wani kalan tattausan Murmushin gefin baki ya saki
yana wucewar sa kai tsaye. Wani kalan luuuuuuu da nata idanun itama tayy tana yin
bayaaaaaa......

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

More Information
08104493215








https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D

༺༻
*♡ ��☆*
༺༻
_ҽcⅈɑʟ_

����� Naseer ɱⅈɑһ

_AMMEY LAYLERH_

Page

7&8

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Ƙafar benen tay hanzarin kamawa tana sakin wata munafukar ɓoyayyar ijiyar zuciya ta saki
acan ƙasan ranta. Juyowar da zatai tay ido biyu da Mammanta wacce ta tsarera da ido, Ɗan
faɗuwa taji gabanta yayi ganin yadda Mah ɗin ta wani kalan tsareta da idanunta."Me ki ke yi
anan?" kai tsaye Mah ta cilla mata tambayar fuskanta babu alamun wasa don ita mace ce
bame son ɗaukan wargi ba ko daga yaran natane kuwa. "Ina shan iska ne maah" Rolex watch
ɗin dake daure a tsintsiyar hannun ta Mah ɗin ta kalla tana furta. "Kalla ki gani ƙarfe nawa
yanzun da kike nan tsaye har yanzun baki kwanta ba?" Kanta ta ɗan rausayar gefe ba tare
data ko sake furta wata magana ba Mah ta kama hannunta tana kaita har bakin ƙofar parlour'n
ta.
Ita kuwa Meesherh Koda ta shige room ɗin nata ma bata shige bedroom nata ba kwance
kawai tay anan bisa 3 str daga ita sai wata yellow ɗin doguwar rigar baccin dake jikinta irin
me santsin nan me kuma bin jikin mutum.Sai wata tattausar hular sanyin dake kanta yellow,
yayinda himilin gashinta yayi luf luf yana kwanciya har gadon bayanta se dai ba can ba, don da
kaɗan ya zarce kafaɗunta. Sosai tay wani kalan masifar kyau duk da kasancewar kayan bacci
ne a jikinta,kasancewar ita ɗin me kyau ce wanda shi wannan kyaun ya haɗu da aji da kuma
tsantsar hutu da jin daɗin Rayuwa. Har ta kama doorhandle na ƙofar parlour'n ta seta juyo da
baya tana jin kamar ba daidai ba, kodan kasancewar ta auta ne ya sanya duk daren duniya
bata taɓa iya bacci ba tare da ita taga baccin babyn nata ba. Kamar yadda take a kwance a
parlour'n haka Mah ta tarar da ita kwance hankalin kwance kuma take baccin abinta.Gashin
kanta dake ɗaure cikin jan riboms ƙwara ɗaya ya zame yayi nashi wuri, se hakan ya bama
gashin damar bajewa akan 3 str ɗin da take kwance akai.Se sheƙi da walainiyar kyau yake
gwanin birgewa. Zama tay gefenta farar fuskanta irin ta Mahaifinta Sameer Jedaans sak ta ɗan
shafa,sauƙe ajiyar zuciya tay tana zuba mata idanu sosai, A natse kuma ta shiga tashinta ba
yadda zata firgita kota tsorata ba. Idanunta ta baccin sosai ya fara cin ƙarfin su ta ware akan
mahaifiyar nata. Ɗan Murmushi me laushi ta sakar mata tana kamata ta mikar da ita tsaye.
Kasancewar ta bame nauyin bacci sosai bace ya sanyata miƙewa Mah na taimaka mata
wajen soma tafiya da ita. Akan lallausan gadonta ta kwantar da ita haɗi da tattare mata gashin
tan wuri guda tana sake ɗaure mata shi da ribboms ɗin cen ƙasan ƙeyarta don karya dameta
wajen baccin. Adda'an barci ta mata haɗi da neman tsari kafin ta tsareta da ido a cikin ranta
kuwa faɗi take {ya Allah ga baiwar ka nan Meesherh ka kula min da ita cikin amincinka da
buwayarka, kaci gaba da tseratar min da ita daga duk wasu masu nufarta da mugun nufi. Na
bayyane da na ɓoye, ya Ilahi ya mujibud da'awati karkaci gaba dabe kowa damar sake
cutatarmaka da wannan bewar take me raunin zuciya!!! Ya Allah} Se kuma A hankali ta ja abin
rufa ta rufe mata daidai saman ƙirjinta haɗi da ɗan ɗukawa tana manna mata kiss a goshinta.
"Ya Allah kamar yadda ka raba tsakani idan har babu Alkhairi karka kuma jarabtar wannan
baiwa taka da wani abu na daban" wannan karon kam a bayyane tay maganar Jiki sanyaye ta
juya tana barin bedroom ɗin. Itama jikinta sanye da kayan bacin dogon wando da riga sakake

sosai da riga buɗaɗɗiya sosai irin fararen nan masu faɗi dai haka sosai. Kamar yadda ta fita
haka ta dawo ta tarar da prof Sameer Jedaans yana nan zaune gaban System nashi sai faman
aikin sarrafata yake idanunsa sanye da farin gilashi, bare daya ɗago ba ya furta "Se yanzun
kike dawowa? Kin gama lallaɓa Babyn taki kenan har tayi baccin!" Murmushi kawai ta yi ba tare
da tace komai ba ta wuce Bathroom don haɗa masa ruwan wanka me ɗumi da ƙamshi. Don
al'adansane baya taɓa kwanciya har se yayi wanka. Zama tay kusa dashi tare da ɗan Murmushi
ɗauke saman fuskarta. Kanta ta kwantar da kanta saman shoulder nashi, "Papiey'n Meeshel
ruwan wankanka is ready"
Kansa kawai Papiey'n ya ɗan girgiza yana lumshe idannuwansa ƙaunar matarshin abin sonshi
na sake ratsa shi. Kayan jikinsa ya rage yana faɗawa bayin.
Bayan ya fito ɗaure da alwulan da al'adan gidan ne ba'a kwanciya ba tare da alwulan ba,
sedai wasu sukan yi wasu kuma basu yi haka nan tsarin yake. Ko kafin ya fito tuni Mah ta sake
gyare bed ɗin daga nan suka kwanta abinsu se bacci.

☆☆☆☆

Ance wai dare mahutar bawa, kamar ko wanne rai me numfashi ke kwance domin samun hutu
ga rayuwarsa cikin kwanciyar hankali yana barcinsa, Se dai a dai-dai wannan loƙacin Sheikh
juraij thabit ke zaune saman darduma yana rera karatun Al- Qur'ani mai girma,Cikin wani irin
amo madaidaiciyar muryarsa mai daɗin sauraro da sanya ma zuciyoyi nutsuwa yake raira
karatun. Idanunsa lumshe suke daga can cikin ƙasan ƙasan zuciyarsa karatun ke fitowa.

Wani kalan Nunfashi mai nauyi Abba dake tsaye tun da jimawa a ƙofar shigowa parlour'n yaron
nasa yaja. kana ya fesar tare da cike da sanyin jiki ya turo ƙofar ya shigo a natse. Jin motsin ne
ya sanya Sheikh juraij buɗe idanunsa da suke a lumshe har zuwa loƙacin. Akan Abbansa ya
sauƙe ganinsa kai tsaye, saurin tashi tsaye yay yana me nufo abban. Sanya hannun sa masu taushi yay yana kama na sheik ɗin cikin nashi, bakin bed ɗin Sheikh
ɗin Abba ya zaunar dashi shima yana zama kusa dashi. Se daya ɗan ja wasu second haka
kafin cike da tsananin tausayin yaron nashi ya furta.
"JURAIJ akwai wata alfarma da nake nema awajenka!" Cike da wani Irin baƙon yanayin da
zuciya ke ɗauka a bazata ya ɗago kansa yana kallon Abban cike da girmamawa ya furta.
"Abba kawai kace wani Umarni zaka bani amma ba alfarma zaka nema daga gareni ba.
Saboda kafi ƙarfin neman alfarma awajena sai dai ka bani Umarninka kawai, Ni kuma a koda
yaushe me biyayya ne ga dukkanin umarninka"

Zama da kyau Abba ya gyara kana ya fuskancesa da kyau cikin raunin zuciya da amincin da
yakeji akan Sheikh juraij ɗin yace.
"Um-um Juraij alfarmar dai kam nake nema" Cikin jin nauyin mahaifin nashi da ganin kimansa
ya sake risinar da kansa ƙasa, muryan sa har na shirin karyewan raunin da tay ya furta. "Idan
har Abbana ya zaman yana nema alfarma daga gareni to ni a gun waye zan nemi ta wa
alfarmar, idan kana faɗin hakan Abba kunya nake ji duk loƙacin da naji kana furta kalmar
neman alfarma daga gareni Abbana"
Kai Abban ya ɗan girgiza cikin sauƙe wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya furta. "Sai alfarmar da

zan nema daga wurinka inason ya kasance iyaka ni da kaine, a iyaka mu nake son maganar ya
tsaya" kansa yake geɗawa Abban tamkar irin wanda bay maganan nan. Kafin cikin wani irin
yanayi mai gauraye da damuwa da rauni ya furta. "Insha Allah Abba a koda yaushe ni me bin
umarnin kane kamar yadda ni me riƙe maka sirrinka ne" "Meesherh!!!, Meesherh itane damuwar juraij tare da Mahaifiyar ka na rasa ta yadda zan
fuskanci wannan al'amari Juraij....." Daga nan suka juye baki zuwa wani yare na daban wanda
Ni AMMEY LAYLERH'NKU banjin duk abinda suke faɗi ɗin kuwa. Sun ɗauki a ƙalla sama da 40
minutes suna magana kuma cikin wannan juyayyen harshen da suka juyemin. Kafin daga bisani
Abban ya miƙe cikin yanayi na ƴar damuwa Sheikh ɗin na biye a bayansa. Da sauri Inuwar da
tun farkon fara zancen nasu take tsaye ta gilma alamar ta kauce. Kafe wurin da ido Sheikh juraij
yay zuciyan sa na beating na ɓacin ran hakan da aka jima ana mai wato laɓe....

*Around 4:20 Am*

Ƙarar Alarm ɗin data sets duk asubahin duniya shi ne ya farkar da ita. A hankali ta shiga ware
lumsassun idanunta da suke cike da barci har yanzun kana suka mata nauyi.da adda'an tashi a
bacci ta tashi a bakinta.
A natse ta ziro fararen santala santalan sawayenta kan tattausan canies carpet ɗin dake
gaban gadon, ɗan miƙa tayi haɗi da shigewa cikin bathroom. Alwula ta ɗauro tazo ta fara
gabatar da raka'atanil fijr,tana nan zaune da Rabbana Arba'in riƙe a hannun ta na Adda'o'i taji
wannan amintaccen sautin nashi na ratsa duka cikin jikinta. Cike da tarin nutsuwa take binsu
sallar subhi ɗin.
Bayan an idar komawarta kwance tay tana sake shigewa cikin lallausan duvet ɗin ta. Ba itane
ta farka se wajajen 11:40 kasancewar weekend ce, Kai tsaye bathroom ta shige tana sakar ma
kanta shower. Se da ta ɗauki sama da 40mins a cikin bayin kana ta fito jikinta sanye da peach
cobbler bathrobe a jikinta, Kanta kuma na cikin fari tass ɗin towel mini. A kan stool in dake gaban 1 mirro'rnta ta zaune kanta ta fara busarwa, kana ta shiga tsane
ruwan jikinta. very expensive lotions ɗinta ta ɗauka take levelling lower skin ɗin nan nata me
kala dana new born baby Wanda hasalin Luxury da Luxury ya gaka ratsawa. Farar powder me
hasalin maiƙo ta shafa a face nata daga haka kuma ta shige cikin closet nata don shiryawa. Sanye ta fito cikin wani mahaukacin milk and coffee colours One Millions all stones yaɗi halp
bubu, Yaɗine me shegen kyau da kuma tsada na manyan yaran ƴaƴan gata. Siririn mayanin
yadin ta ɗora iyaka gefen shoulder nata na dama.Kai tsaye Phone nata dake jikin Rinlight
already ta nufa. Seta cameras na woyan tay ta cikin tiktok nata. Wannan fitacciyar wakar da tay
trend a media ta saki ta Ƴar Arewa. Wacce jarumi Sadeeq sale ya saki, har wani ɗan
lullumshewa idanunta keyi. Tana gama yin Vedio'n tayi posting nata a duka pages nata na
media, take mutane suka ringa likes kan videos ɗin nata kamar kullum.
Daga haka ta nufo ƙasa ta sauƙo kamar yadda ta zata duk iyayentan suna babban parlour'n
gidan ne. Tun kamin ta iso wannan shegen ƙamshin tan nan ya gama sanar musu cewar me
zuciyar j̶e̶d̶a̶a̶n̶s̶ ce gaba ɗaya ke tafe wato ������ ᎷΗƦ ���� ᴰᴬᴬᴺˢ. Daga
gefen Mah ta zauna bayan ta gaida kowa dake dining room ɗin. plate ɗin dake ɗauke da donut,
pizza se picanto taja gabanta tare da ɗauka tana ɗora shi kan cinyarta tare. Metres sarvice ɗin
dake aikin shirya kitchen Meesherh ta kwalama ƙira tana bata umarnin kawo mata fruits. Babu

jimawa kuwa se gata hannunta riƙe da plate da yankakkun fruits ɗin a ciki masu sanyi, da
akama yanka ƙananu².
Nanameerah ce ta ɗan kalla inda Meesherh ke zaune ƙanwa Moh Ameern Saif ta furta wallh
Aunty Meesherh kalan yadda kike gudanar da acting naki wurin aikin ku na burgeni wllh" Ɗan
murmushi me faɗi tay tana kallon Nanameerah'n itama tare da furta. "Sosai mutane ke faɗin
wllh aikin mu film na burgesu sosaifa Nanameerah" a tare kuma suka saki murmushi wa junan
su cike da shaƙuwa. Annie ce ta kalla sashin da Meesherh ɗin take tare da furta. "Aikin me? Ke
yanzu har wani abun kirki da alfahari kika ɗauki sana'ar taki, Ko da yake aifa aikin tallata jiki a
yanzun kam shine babbar sana'a a Nigeria"
A rene cikin wani ɗan iskan renin wayo da rainin hankali ba tare data ko kalla inda Annien
take ba ta furta "Nagode!"
Tsaye ta miƙe da niyar barin dining room ɗin. Abba ne ya kalleta da alamun damuwa a ranshi
ya furta.
"Mamana ina kuma zaki bayan baki ko kammala yin dinner naki ba?"
Shafafen cikinta da ba kamar yanzu ta gama cin donut da pizza haɗi da picanto ba sam kai ba
kace ma kwai ƴaƴan hanji a cikin cikin nata ba. Ɗan shafa cikin nata tay tare da furta.
"Alhamdulilah na ƙoshi ne Abba"
"Ok shikenan Mamana Ubangiji yay Miki Albarka, da ameen ta amsa bayan ta sake musu
sallama don yau tana da wani shooting film da za'a ɗauka wanda Film ɗin tane itane da kanta ta
tsara abinta.Har taje bakin ƙofar parlour'n kamar daga sama ta tsinkayi muryawan Ama tana me
furta. "Takwarata taimaka ki sauƙe min yayanku a gidan gwaggo Haleemah" Cike da ɓacin Ran daya kasa dannuwa Annie ke kallon Ama data kasance surukuwa a
gare su kafin cikin hucin ɓacin rai ta furta
"Haba ama bayan batama zuri'armu suna da tay, duk hakan be isheku ba sema ƙoƙarin dan
gan tata da Mutum tsarkakakke kamar juraij da kuke! Don me ake min haka ne eye? Kodan
kawai kina matsayin Yaya ga Mahaifiyata? To ni wllh na gaji nima kawai daga yau ki dawo
yimin kallon surukuwarki ba ƴar ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login