Showing 18001 words to 21000 words out of 21093 words

Chapter 7 - TA DABAN BOOK COMPLETE By AMMEY LAYLERH.pdf

25 Apr 2025

1962

yanxun idan bata koyi ƙarfin hali ba se yaushe kike son ta koya?" Papah ya
bata amsa da hakan yana hayewansa sama. Mohan Sameer da shigowansa kenan parlour'n
shima yama kansa mazauni akan É—aya daga cikin expensive chairs da suka ma parlour'n
ƙawanya. Yana ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana fuskantansu su duka cike da farin cikin
ganinsu su dukansu. Aunty Ummeterh ya fara gaisarwa kana ya sake gaida Maamah duk da
kuwa cewan babu jimawa suka Hausa ɗin. Lil juraij dake riƙe da hannun Mohan ɗin ne ya zame
cikin wayonsu irin na yara kai tsaye ya nufi inda Meesherh take, duk kuwa da yadda take
ƙoƙarin ɗauke fuska daga yaron,cikin muryan gyaranci ba sosai ba ya ce "Otty kin ga ni paap ne
ya bani kuma yace karna fatawa kowa ma" yay maganan cikin gwaranci ba sosai yana mata
nuna da wani Rolex watch na diamond gold me kyau kalan na yaran nan me shegen tsada da
kyau. Ɗan taɓe baki Maamah tayi tana juyar da kanta daga kallon yaron tana maidawa kansu
Ummeterh da Mohan da suke wata maganar daban.
Miƙewa tayi da niyar tafiya amma lil juraij ya maƙale mata duk yacce ta so data yagar dashi
kuwa. Gashi zuwa loƙacin kanta sosai taji yana juya mata gashi wasu masallatan harsun fara
ƙiran sallah, dole dashi ta tafi sama yana maƙale da ita. Duk da ido suka bita kafin Mohan ya
kalla Maamah tare da furta "Maamah don ALLAH Meesherh ta dakata da aikin nata don yanzu
kamata yay ace tana gidan aurenta, Ki duba fa tana age na 24 year's ba ai yaci ace ma tana da
nata babay'n itama" tunda ya soma maganar Maamah ta kafe shi da ido ko ƙiftawa batayi seda
ta tabbar da ya gama ta furta.
"To sannu ubana da wannan ai kamata kawai yay ka bani umarni, ka ga Mohan ka fita ido
na In rufe idan har kaima ba zaka iya bin Meesherh da fatan Alkhairi ba to kamata yayi kaima
ka janye idanuwanka daga gare ta" ta ƙarasa maganan a fusace tana miƙewa tare da barin
parlour'n baki É—aya, don Maamah irin iyayen nan ne masu shegen S0n Æ´aÆ´ansu wanda basu
ganin laifinsu ko kaÉ—an, se dai sammm bata barin ko waye daga cikin yaran nata ya aikata ba
daidai ba kuma ita mutum ce da bata iya ƙunbiya ƙunbiya da abu ba ita ɗin karan tsaye ce ƴar
kai tsaye me gaɓa². Ko waye ya taka ta to kuwa lallai itama zata taka shi don bata ɗaukar raini
kamar yacce itama bata raina kowa se har in mutum shi ne ya fara shiga hurumin ta da wata
sigar ta daban, to kuwa lallai anan ne zaka gane ko kai É—in wane ne.
Ajiyar zuciya me tattare da damuwa Ummeterh da Mohan Sameer suka sauƙe kusan loƙaci
guda kan kalaman mahaifiyar nasu, duk kuwa da cewan ba yau bane suka saba fuskantar
hakan daga gareta. kawai abinda suka sani suke kuma so shi ne suga sun inganta rayuwar

Autar nasu, sun gaji da ce ce kucen da ake akan Meesherh É—in daga media harma da nan cikin
gidan nasu kuwa. Tabbas hakan na masu ciwo da kuma matuƙar ƙona musu zuciya.
†
*Sheikh juraij*
Tunda yabar wurin kai tsaye cikin garden yay shigewansa, sanyi da kuma iskan dake kaÉ—awa
a wurin na ratsashi wanda har yake jin kamar fatar jikinsa ce ta bude kai tsaye sanyin yake
ratsa masa ko wanne sassa na jikinshi yana daskarar da duk wata magudanar jini ta jikinsa,
kamar kullum yana sanye cikin shigar farin yadi me azabar laushi da tsada É—inkin jumper cables
irin na zamanin nan amma kuma ba masu sherp da yawa ba irin na matasan yanzu. Sumar nan
tasha gyara na musamman se fidda daɗdan ƙamshin take yi gami da daukar ido. Sajen nan yay
luf luf abunsa har wani kalan shine blue yake bayarwa daga nesa.
Sanyi haÉ—i da daÉ—in iskar ne ya sanya shi kasa zama wuri guda don haka ya shiga zagaye
cikin garden ɗin,Hannuwansa goye a bayansa daga can ƙasan zuciyarsa kuwa yake furta.
_Subhanallah,wal hamdu lillah, wala'ila ha ilallahu wallahu akhbar³_

Da dai duk sauran adda'o'in da duk suka zo bakinsa, kai tsaye ba zaka taɓa fuskantan tasbihi
yake ba sedai ka kalla fatar lips nashi kaÉ—an tana motsawa. Sammm yama rigada ya manta da
abinda ya farun yanzu ko na ce dazu. Ganin loƙacin ƙiran sallah yayi ne ya sanya shi fita, se da
ya fara shiga bedroom nashi kana ya fito kai tsaye yana shigewa cikin babban masallacin dake
cikin anguwarsu. Shi ne ya ƙira sallar ya kuma ja jami'i cikin wannan daddaɗan sautin nashi da
sauraran yanda yake fidda tajweed nashi yake sanya mutane cika masallacin duk kuwa kalan
girman da yake da.
Dama shi ka'idan sane baya shigowa se bayan sallar Isha'i sosai shi yasa kowa na gidan ke
riga shi kammaluwa a dining room É—in,duk da kasancewar tonight baya zaman dining room É—in
amma kuma hakan jiran shigowarn nashi ya zama kamar al'adan kowa.
Iyayensu mata kawai ya gaida kasancewar sun gaisa da iyayensu maza tun a can cikin
masjid ɗin.Nan ƙannashi maza da matan suka gaida shi shima,A natsensa ya amsa su yana
kallar bakin Meesherh da kuma Moh Ameern Saif da babu su a cikin jadawalin gaisuwar.
Directly balcony É—in da ya saba zama kai tsaye wuce maids É—in dake aikin shirya dinner É—in na
binsa da tea plask É—in dake É—auke da zazzafan tea wanda duk daren duniya shi ne kawai yake
sha. Jere mishi tay daga inda yake idanunsa lumshe yana ambatar sunan ALLAH acan ƙasan
ranshi. Se da ya tabbatar ta bar wurin kana ya buÉ—e idon yana jan tea plask gabansa. A natse
yake sipping tea É—in abinsa daga gefe dashi kuma System nashi ce yake aikin sarrafa ta.
Yau be daÉ—e a wurin ba kamar kullum ya tashi ya tafi don yana da abinda zeyi a daren. Ga
yawan bugun da zuciyarsa ke mai akai akai yana jin tamkar wani abu mara daÉ—i na dab da
faruwa dashi, Amma sosai yay ƙoƙarin danne hakan se adda'o'in sa da yaci gaba dayi yana
adda'an koma miye zai faru dashi to Ubangiji ya kawo shi cikin sauki ya kuma takai ta ma masa
É—in, da haka yanar wurin yana daura alwula tare da fara jero nafil fili wa mahalicci'nsa...

☆ Meesherh kuwa koda ta koma bedroom nata wanka tayo ta shirya kanta cikin singlet ta mata
da wando. Army green da farar singlet inda tayi stocking singlet É—in cikin wandon ta É—aure da
beld. Sai light green ɗin top wadda ta ɓalle duka maɓallanta ta barta a buɗe, Iskar da ake
kaÉ—awa a gurin na diban rigar nata tana kamar zata cire,gaba É—aya rigar tabar jikinta sai singlet

ɗin kawai, tsaye take daga jikin window na bedroom ɗin ta tayi crossing ƙafafunta suna a
harɗe. Sosae iskar dake shigowa ta cikin window'n ɗakin ke mata daɗin shaƙa tare da ƙamshin
flowering dake ata bayan window nan suke sake bata nishaÉ—i da jin cikakkiyar nutsuwa, saima
taji ta nema ciwon kan data shigo dashi ta ne meshi ta rasa.♡ Shi yasa most especially Idan
tana cikin yanayi mara daÉ—i idan bata son fita balcony takan tsaya a wurin ne ta yaye duka
labulayen wurin nan take samun cikakken nishaÉ—i sosai.
☆
Lumshe fararen idanuwanta tayi tare da faÉ—awa wata duniyar ta daban, tunani take akan
baya idan tace baya tana tunanin Baya cann da dadewa kafin rugujewar komi. A cikin idanunta
dake lumshe komai daya faru yake dawo mata daki daki tamkar komai daya faru ne a waÉ—an
can loƙutan haka komai ya Shiga zeroying mind nata. Saurin dawowa hayyacinta tayi sakamon
zuciyan ta da taji tana son maido mata da hannun agogo baya, Bayan nan da har gaban abada
bata fata da burin dawowarta cikin rayuwarta koda a matsayin mahaifin ne a gareta. Domin
mahaifiyarsa ta rigada ta gama ɓata komi tun a wancen loƙacin. A yadda ta tashi ta tashi ne ta
buɗe Ido da shi, Shi ne mutum na farko data fara ƙira da pa'apahh...........
Akan shi ta fara koyan magana tana yima kowa ƙyuwwa amma banda shi ciki kuwa har da
Maamah'nta. Domin matukar Meesherh tana wurin juraij bata yarda da kowa bata kuma zuwa
wurin kowa se pa'apahh'nta juraij. Ta kai ta kawo ko bacci zatay se da shi a gefenta, shi ke
maga wanka ya wanke mata fufu idan tayi, ya goye ta a gadon bayansa da zani irin yanda uwa
kewa ɗan ta, a loƙacin shi yana da shekaru sha bakwai a duniya ita kuma tana da 1 year's a
cikin duniyar, Shi ne ya Renata yaci kashinta yaci fitsarinta har zuwa sanda ta shekara biyar a
duniya, A kuma daidai loƙacinne abubuwa suka soma Sanja kansu, suka kuma soma samun
saɓani wanda shi ne farkon jinin tubalin da har ya kai su ga irin wannan matakin da suke kai a
yanzu. ♡
Duk wasu É—abi'iu kalan nashi take yi masu kyau a da can baya kai takai ta kawo ko cima
bata cin abinda baya ci, iyaka abinda pa'apahh'nta yake ci itama shi take ci. Saɓanin farko da
suka fara samu a cikin rayuwarsu shi ne tun da ta ɗan ƙara wasu shekaru a cikin shida zuwa
tara/goma ya fuskanta ita ɗin mayyar jin kiɗe-kiɗe da waƙe waƙe ce, ga shegen son kallon tsiya
a wurin ta kamar me, duk yacce zeyi don ganin ya cire mata hakan abin yaci tu ra. Har yakai ga
ya dena shiga lamuranta na wasu ƴan loƙuta haka zata zo ta shige jikinsa tayi ta masa koke
koken banza har se ya dawo ya kula ta, Amma hakan bazai hana gobe ta sake kunna casunta
ba, haka zata sa ata sawo mata irin kayan indiyawa sune kayan sawanta. Ya tattare ya ƙone
amma haka Maama zata sake sawo mata wasu. Kai har takai ta kawo Meesherh ta dena shiga
cikin duk wasu lamura na Juraij ta dena tsoronsa ta dena ƙiransa da sunan data bashi na
pa'apahh wanda a da yayyenta shi kuma ƙannensa koda mutum ne yay kuskuren ƙiran sunan
shi da sunan da ita kaɗai take son take ƙiransa da abinda to kuwa ranan wunin rigima zata wuni
tana yi. Amma se gashi sannu a hankali komi nasu na sake samun saɓanin ra'ayi.
Se kuma a karo na biyu loƙacin da ya fahimta Film ta karanta, wannan shi ne tushen komi...
Shi ne tubalin dayay sanadiyyar rugujewa da watsewar komi don a nan ne Mahaifansu suka
samu babban saɓani na farko kowa ya nuna nashi na shi ne. Daga nan komi ya tsaya musu
cakkkk kowa ya fita a rayuwar kowa fita wacce suke jin fita ce ta har gaban abada abadan.
☆
★Wani gauron numfashi ta kawo me kyau lokacin data tuno kaɗan daga cikin wani sashi na

rayuwar da suka shuɗe na baya. Tsaye ta miƙa daga zaunen data kai gefen bed nata zuciyarta
na wani kalan bugu very slowly ta miƙe. Waƙar (pareshanura ) ta cikin film ɗin Dhruva na
jarumi _Ram Charan_ Wacce sukai da _Rakul preet_ ta kunna tana ƙure volume ɗin. Waƙar na
sata shiga wani yanayi mai wuyar fassara tare da É—ebe wan can tunanin nata tana ta rawa tana
juyi abinta. Ita ta bari on repeat tayi ta kuma dawowa daga nan ta koma waƙar *BAD BOY* ta
cikin film É—in _Saaho_ wacce jarumi _Prabhas_ tare da _Jacqueline fernandez_ kai da kaga
yacce take rawan zaka tabbatar da cewan ehhhhhh lallai wannan dole a ƙira ta da TA DABAN
ɗin, don kai tsaye kai baka isa cewan ba ita ne ta hau waƙoƙin ba kai tsaye bare kai duba da
kalan shigar dake jikinta. Shigowan Maamah'nta shi ne ya katse ta don loƙacin 11:30 na dare
harya gota. Kwantar da ita Maamah tayi bayan ta tofeta da adda'an bacci,seda ta ƙara kamar
15 minute kana ta fita a daƙin a tunaninta bacci Meesherh'n ta samu, sedai bata sani ba idonta
biyu tana fita ta tashi zaune wani abu na mata suka a cikin zuciyarta. Wanda take yawan jin
hakan a da a yanzu ma shike ƙoƙarin gaza control nata.

☆Around 11:30.

Kwance take saman ƙayataccen bed ɗin ta da ya gama jin haɗuwar duniya da kuma wani irin
gyara na musamman, kai ba kace Mutum ne me Numfashi ke rayuwa a gadon ba.
ÆŠan juyi ba da yawa ba tayi kaÉ—an kafin Ahankali ta shiga ware sleeping eyes nata da suka
mata wani kalan nauyi kana kuma suka ƙanƙance, dishi dishin da take gani acikin su ne ya
sanya ta maidasu ta kulle, sosai taji kanta na wani kalan bala'in sara mata, wanda take da ta
cikakken tabbacin rashin baccin da bata samu ba ne a daren jiya ya haifar da hakan. dan haka
take jin gaba É—aya jikinta yayi weak haÉ—i da kasalan jiki ga kanta da taji ya dawo mata da wani
kalan fitinannen ciwo. Hannu tasa tana É—an dafe kan dake mata ciwo kaman zai rabe biyu,still
idanunta masu kama da na mashayiya ko kalan like irin wanda aka janye su É—in nan, Ahankali
ta ɗan motsa jikinta tare da soma ƙoƙarin ɗaga kanta da takejin yayi mata nauyi sosai,jingina
bayanta da jikin fuskar gadon tayi tare da sakin ajiyar zuciya tana miƙewa da ƙyar tare da nufar
bathroom É—in dake cikin bedroom nata. Shower kawai ta sakarma kanta tare da tokare
hannuwanta duka biyu da jikin toiletry É—in. haka ruwan shower'n ya shiga dukan jiki da kuma
kanta, jin numfashinta na neman sarƙewa ne ya sanya ta janye jikinta da ƙyar. idanunta da
suka sha ruwa sosai ta buÉ—e tana furzar da ruwan cikinsu. Ahankali ta ziro fararen sawayenta
daga cikin bathroom É—in, Sanye da rigan wanka ta fito komi ahankali takeyinsa, Anutsenta
tazauna gaban mirror kan stool, blow drying gashin kanta tayi tai parking nashi a ƙasan
ƙeyarta, ta ɗauki wasu sprays masu tsada da ƙamshi ta feffesa ma gashin,kai tsaye ta nufi
wurin clothing nata da jibgin kayanta ke ciki, walking slowly take tafiyan fuskar nan babu
walwala samm ko kaÉ—an a saman kyakkyawar fuskar tan,Bakar doguwar rigan Arabian jallabiya
ta mata ta sanya. Hannunta riƙe da car key.
Bata tarar da Papiey'n taba ya fita wurin aiki amma kafin ya fita seda ya leƙata a loƙacin tana
bacci kasancewan se dab da asuba bacci gwanin iya sata yay nasararn sace ta. Maamah na
kallonta ta tabbatar ba lafiya ba. Zama tay a kusa da Maamah É—in tana furta
"Maamah kaina kamar ze fashe ciwo ciwo ciwoooo yake min sosai!!!" Saurin tarota jikinta
Maamah É—in tayi jikinta harna rawa wajen furta "Subhanallahi amma kuma shi ne kika kwana a
haka? Meesherh har yaushe kike son zanci gaba da miki magana akan lafiyar jikinki?" Se

kuma ta É—an numfasa tare da furta "Shi ke nan tashi muje Hospital don ni ban woni yarda da
cewan azo gida a duba ki ba nima duk yau haka haka nake ji ma wllh ba daɗi" tsaye ta miƙe a
sanyayen itama tana furta "A ahh Maah kiyi zaman ki bara yanzu zanje na dawo IN SHA
ALLAH" "Ke Meesherh anya kuwa duba fa yanayin ki sosai baki da lafiya kidai bari ko driver ne yayi
driving naki" Dan murmushi tayi tana ficewa da tsokanar Maah É—in. A Parking car na gidan suka
haÉ—u da shi kallo É—aya ya mata ya É—auke kansa yana sake jin bugun zuciyarsa da fitowan nata.
Akan Idonsa ta shige car nata tayi reverse tana janta tare da barin gidan ba tare data ko kalla
inda yake ba.

Cikin nitsuwa shima ya shige tashi motar sanye yake da fararen kayansa kamar kullum.
Security's ne suka hanzarin buÉ—e may mitar ya shige personal person É—insa na jan motar suna
barin gidan.
Dummmmmmm haka yaji zuciyarsa ya buga shan kwanar da zata sada su da inda suka
nufa ganin dandazon mutane fiye da dari kewaye a wuri guda. Cikin bugawar zuciya ya bama
driver umarnin su tsaya. Cikin kamala da tattako ya nufi wurin cikin cikakken takun ƙarfi na
hasali zaka san cewar ehhhh lallai shi É—in Matashi ne mai ji da lafiya irin ta da namiji, se hakan
ya ɓoye yawan shekarun sa don idan ka kallashi befi ka bashi irin 35 year's ɗin nan ba a
duniya, nan kuwa yakai 55 year's a duniyar. Kowa dake wurin ya gaza taɓa komai dake wurin
se jinin dake malala ta ƙarƙashin motar data kife kirif da duk wanda yake a cikin ta. Wani irin jiri
yaji ya ɗauke sa loƙacin da idanunsa sukai masa arba da car ɗin kokkomeɗe a wurin.
Chakkk yaji numfashin sa ya tsaya amma yay ƙoƙarin taro shi domin bazai iya taɓa barin
nashi numfashin ya fita ba tare daya tallafi Tata rayuwar ba.....

😔😔😔😔😔😔

_Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un 3 meya faru? Meke shirin faruwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login