Showing 15001 words to 18000 words out of 21093 words
Chapter 6 - TA DABAN BOOK COMPLETE By AMMEY LAYLERH.pdf
b...... "Zeynab!!!"
Abba ya wani irin ƙira sunanta a mugun tsawacen da ya sanya kowa rawan jiki a wurin. Don
ba abu bane daya taɓa faruwa a zahirance duk kuwa irin tijara da jalalar da Annie'n keyi akan
duk wani abu daya danganci Meesherh ɗin. I'm sorry Abban jur..."
Ta furta muryan ta na rawa.
"I said get out my friend!"
ya sake buga mata wata uwar tsawar da tafi ta farko ba shiri ta haɗiye maganar da bata
ƙarasa taba tana barin wurin don A yadda ta ji muryarsa a kausashe kam ta tabbata babu wasa
a cikinta.
Jiki a sanyaye kowa ya shiga darewa banda Mah da jikinta har wani jijjiga jijjigan ɓacin rai da
baƙin cike take yi, Sa'ar ta ɗaya sunan ALLAH ne ya fara zuwa bakinta kafin komi shi yasa ta
dinga nanata sunayen ALLAH'n a bakinta.
Meesherh kuwa tana fitowa compound na gidan ta tsaya tare da ɗan sa hannunta na dama
tana riƙe ƙugunta. Nainarh ce tsaye ƙaramar autarsu Sheikh juraij jingine da jikin motar ta. Wani
irin kallo Nainerh take watsama Meesher'n tare da furta. "Har ke wa ce ce a cikin gidan nan da
har zaki ringa mahaifana meda yawu akan ki gaban mutane?"
Wani kalan sheƙeƙe Meesherh ta mata "Kin ga kenan ke da kanki kin ba kanki cikakkiyar
amsarn cewa Ni ɗin wata aba ce me girma a cikin gidan nan, Idan kin gama bani hanya ta zan
wuce"
Tay maganar tana kama murfin car nata tana ɗora haɓarta akai, ta buɗe baki kenan da nufin
sake watsoma Meesherh ɗin wata rashin kunyar idanunta ya sauƙa akan babban yaya wato
Sheikh juraij thabit Jedaans. Babu shiri ta gimtse bakinta tana haɗiye sauran maganar data
saura a cikin bakinta. Tamkar kiftar ido haka Nainerh ta ɓace a wurin. Zuciyanta a cunkushe ta
shige Motan tana zama mazaunin Driver yayin da ya zauna gefen mai zaman banza. A natse
tasa hannunta farare ta kunna motar cikin yanayin nutsuwa take driving nata, Yayin da shi
kuma yake gefenta zaune. Ahankali yake ƙarema zara-zaran yatsun hannunta dake kan
stearing tana juyawa kallo,me kama da kalan nashi don sosai abubuwan su suke ɗibar kamanni
harta da sawayenta kalan nashi ne futiƙ,wani ɗan numfashi ya fesar tare da furta.
"Bani motar nan b.... Ji yay ya tsinta kansa da kasa ƙarasa sunan Babyn da yay niyar faɗi.Se
ma lumshe idanunsa dayay tare da shaƙan ƙamshin humranta daya cika motar. Ita kuwa bata
kawo komi a ranta ba sema kallon yanda ya lumshe idanunsa tay se taga ba ƙaramin kyau ya
mata ba. A jikinsa yaji kallonsa take se kawai ya gyara fuskan da kyau yana jingina kansa da
jikin motar, Kamar kuma ba zai yi magana ba buɗe lips inshi a hankali yay tare da furta. "Kallon
fa?"
Kanta ta ɗauke wani munafikin murmushi ɗauke saman fuskanta. "Pa'apahh!!!" Ta ƙira hasalin
ainihin cikakken sunan shi gareta tun yarinta.Hakan ne ya sanya Idanunsa dake lumshe ya
shiga motsasu ahankali yana son buɗe su tare da faɗin. "Buddies kiyi abinda ke gabanki, ko
kiban motan!" Buɗe idon ta da yanzu ne ta lumshe su dama tare da juyowa ta kalli inda yake zaune, iyaka
muryansa kaɗai da taji ya sauƙar mata da samun nutsuwa. "Pa'apahh to kace ka yafe min pls"
tay maganan da alamun rauni sosai tattare da ita. "Da ki kamin me kenan fa?" Yay maganan
cikin ko in kula. "Everything forget itt" Kansa ya dauke a kallonta yana maida shi can kusa da
closed windown motar, Itama se bata sake furta komai ba don tasan bayi son maganar
kenan.Nuvel script ɗin ta dake gefe ta ciro me ɗauke da photon'nta tana budewa ta ɗaura shi
saman gaban motar. A duka sassan jikinsa ya soma jin banbancin yanayi.
Sake buɗe idanunsa calmly akanta yay, wacce ta nutsu wurin driving nata a kuma daidai
loƙacin suka kawo ƙofar get na wani makeken ƙaton get. nitsatsassun fararen idanuwan ta da
suke nan sakk nashi kawai ta zuba akansa. tamkar wacce bata da wata matsala a rayuwarta
tamkar babu abinda ke damun zuciyarta ta furta. "Pa'ap.... Bai bata wani dama na ƙara sa
ambatar sunan shi da tay shirin yiba ya fi ce a motar. Wani irin shiru tay tana me binsa da kallo
da raunatattun idanunta. dan Shiru tayi na wani loƙaci kana taja kan motar ta tay reverse tana
shan kwanar da zata bi. Cikin son shanye komi cike da nitsuwa take ci gaba da tafiyanta kamar
daga sama taga wata babbar mota tayo kanta. Tamkar wacce aka bugama guduma haka taji
amon muryansa cikin wani shuɗaɗɗen lamari yana furta "Babyyyyyy.....
A wani irin tsiyace ta taka wani mahaukacin birki tare da juya kan motar ta zuwa ɓangaren
gabas, wannan babbar motar da tayo kanta na bugar wata motar daban ba ita ba.
★★
Slowly ta shiga buɗe idanunta da taji sun mata nauyi loƙaci guda, ɗan lumshesu ta sake yi tana
ƙoƙarin saita kanta dan koda wasa batai tunanin zerewa motar ba. Wata ƙatuwar Ajiyar zuciya
ta sauƙe me nauyi. Tana ambatar sunan ALLAH cikin rai da ruhinta. ★ Ɓangaren Sheikh juraij
kuwa a natse ya sanya kansa cikin ƙaton parlour'n gidan, da gwaggo Haleemah wacce ta
kasance kaka a gareshi ya fara cin karo. Gwaggo Haleemah yaya ce ga Ama kuma ita kaɗai
take da ita ƴar uwa anan kusa idan ka cire dangin su dake saudia. "Aaaahhh lale marabu da
babban angona, Juraij yau kuma kaine da kanka?, Kodai ɓatan hanya kayi Ni Ko nace banda
wajen zaman masu ɓatan hanyar?" Tay maganar da murmushi kwance saman fuskarta. Zama
yay daga saman 1str ɗin dake kusanta. Zamansa babu daɗewa kamar an cillota Samha ta
shigo cikin parlour'n zaram tamkar ana tunkuɗota.
Samha ƴa ce ga Surayya ƙanwa ga Annie kenan wacce kuma suke ƙoƙarin haɗa aurentane
kuma da juraij ɗin, sedai sam yarinyan bata da kamun kai amma su basa ganin hakan babban
burinsu kawai auren ya haɗu. Se data ta shigo kuma cikin mugun bariki da kisisina ta wani
sinne kanta ƙasa tana furta. "Laaaah dama uncle kaine? To sannu da zuwa Bara a kawo maka
juice" da hannu ya mata halaman bai buƙata. Dan faɗa fuska tayi tare da duban gwaggo
Haleemah tana furta, "Gaskiya gwaggo ki ma Uncle juh magana! Shikenan yazo shi kullum ba
zai ci abincin mu ba inda Ni ce na ce zan kawo mishi"
Dan murmushi irin nasu na manya gwaggo Haleemah ta yi tana furta "Yo in banda abin kima
Samha kwana nawa ya rage miki, ku ce kan kita masa girkin kalan wanda yake so, kuma dai
kinsan juraij bai fiye son komai a sake ba, amma idan da gake se shi ne seki ta lallaɓa kayanki
ko" ta ƙarishe maganan da Murmushin nan ɗauke saman fuskarta. Dariya ta saki tana rufe
idonta wai ita ala nan dole an bata kunya.Daga haka ta shige dayan parlour'n dake kusa da
wannan ɗin shi kuwa a natse yaja fruits ɗin dake gaban gwaggo'n apple ya ɗauka ya ɗan ci
kaɗan. Bayan bata saƙon da yay ya miƙe da shirin tafiya. Suraj ne ya shigo parlour'n da yake
shima jika ne ga gwaggo Haleemah'n. Gefensa ɗan wani matashin saurayi ne suna tafe gwanin
birgewa. "Ahhhh yau wa nake gani kamar babban malami" ya fadi a washe hakwaronsa farare
tasss waje, Bai bi ta kan iya shegen da suraj ɗin ya soma mashi ba yana bama matashin
hannun suyi masabaha. Don ya san idan ya biye ma suraj ɗin babu ruwansa kunya ne kawai
ze bashi.
Ita kuwa gwaggo Haleemah bin bayan Samha tay, zama tay gefenta suka soma fira cikin
dabara gwaggo take dan son lurar da Samha'n kan lamarin Sheikh juraij ɗin da ake shirin aura
masa dap. Sedai maganan bawai tama ko fita bane iyaka yasu ya sune suke ƙusƙus dinsu
tsakani. Sosai firan da gwaggo take mata akan juraij ɗin ke mata daɗi da sanyata nishaɗi
♡
Rasss gabanta ya mugun buga mata don ganin drector Muhsin Aliey Yahaya tsaye da wasu
yara wanda kana kallon su kwanyarka zata Hasko maka cewan ƴan daba ne. Sedai shanye
tsoron nata bayyanuwa tay tana karasa fitowa a motar nata kai tsaye ba tare data kalla inda
yake ba ta shigewanta inda zasu gabatar da shooting film ɗin ta na. ★TAURARUWA♡
Film ne da take son yin cleaning up nashi Kan yadda waɗanda taurarinsa suke Haskawa a
cikin duniyar suke wulaƙanta mabiya dama masoyansa. Tana shiga hall ɗin Hotels din da za'a
gudanar da shot ɗin suka dauki sowa da ihun ƙiran sunanta.
Kanta ta ɗauke daga kallon Moh Ameern Saif daya kafeta da ido. Nan aka soma gudanar da
shirin cike da birgewa.
Ba itane ta sama kanta ba se wajajen 5:40 pm. A matuƙar gajiye lilis ta fito daga cikin hall ɗin
tana jin matuƙar haushin kanta na kin tahowa da ko gurds ɗaya da batay ba. Jingina da jikin
Railer'n dake gaban hall ɗin tay idanunta lumshe. Ko dinner gaza yi tayi haka har wata actress
me suna Khadija Yobe ta fito itama ta sameta. "Meesherh lafiyan ki kuwa?"
"Hummm kedai Khadijah kyaleni wllh duk a gajiye nake jima nake kamar bazan iya driving ɗin
nan bane ma wllh"
"Me zai hana idan har babu damuwa na miƙaƙi gidan" ɗan numfashi ta fesar tana furta "No ba
ma se kin hawal da kanki ba na kira ayrah amoh nace ta biyo ta nan ta tafi dani"
"Kuma kina ganin har loƙaci bazai ƙure miki ba kanta ƙara so?" Khadijah yoben ta tambaye ta
ko kafin ma ta bata amsar sega wata arniyar farar Roy *R* Rayce nan na danno Kanta cikin
Hotels ɗin.
Har gab dasu motar ta ƙaraso kafin a natse aka soma yin kasa da glass na motar, wani kalan
zaro fararen idanuwanta woje tay don ganin..............
To ai Shikenan muma semu gimtse
*BY AMMEY LAYLERH*
Chat mee view
My phone
07085041758
Or
08104493215
Don son magana dani AMMEY LAYLERH chart Mee or call a wannan No ɗin 08104493215
Masu neman *MIKIYA* ma har yanzun ƙofarku a buɗe take har yanzu yana nan akan farashin
sa na ₦ 500 ban ƙara ba kamar yacce na ce a baya.
https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D
༺༻
*༺♡ ☆༻*
_ҽcⅈɑʟ _
♡
a ɱⅈɑһ
_ _
a
9&10
✯ * JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
(J.W.A)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159
6987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa
su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
*
001*
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Don ganin Papiey'nta da tai zaune cikin car ɗin, duk da cewan ba abin mamaki bane a wurinta
amma na yau ɗin se ya fi koda yaushe bata mamaki. Wata kyakykyawar ajiyar zuciya ta sauƙe
me ɗan ƙarfi tare da nufo car ɗin ita da jaruma Khadijah yobe. Itane ta buɗe mata gaban motar
kusa da Papiey'nta ta, car key nata ta miƙa mata bayan ta gaida Papiey'n tare da cewa tayo
dropping car ɗin zuwa gidan su tun da dama ba sa da woni tazara sosai. Itama Khadijah yobe
ƴar masu hannu da maiƙo ce sedai idan dasu Meesherh Jedaans a wuri babu Powerful ɗin
kowa da ke aiki a kafff ma faɗin garin Kd da zagayenta.
"Papiey yau ka tuna dani kenan?" Shi ne tambayar data fara jefa ma mahaifin nata Duk da
tasan cewan tasan kwanan zancen ba zai wuce sake kwantar mata da zuciya da zai yi ba. Left
hand nashi da baya driving dashi ya sanya yana kama nata tafin tare da jimƙewa a cikin nashi,
cikin tsananin jarumta da ƙarfin hali da kuma son kwantar mata da hankali ya furta. "Baby ita
Rayuwa da kike kallo komai yana zuwarma bawa ne ga bisa umarnin abinda ya tsara a cikin
tarin Rayuwarka! Ina son kici gaba da shanye komai da zakici gaba da fuskanta daga can gida,
amma ba ta yadda komai ɗin ze zama illa wa taki Rayuwar ba. Insha Allah wannan karan komai
ya kusa daidaita da yardan me du ka wato Ilahu Sarki ALLAH, Sarkin da babu kamarsa buwayi
gagara misali ina..jin... Ina...jin...ina.........jin matuƙar ciwo sosai da ɗaci kan aibantamin MY
BABY'n Papiey da ake...
Muryan shi ce ta soma rawa da ƙoƙarin karyewa dan haka yay shiru yana sake damqe
hannuwan Meesherh ɗin da ɗan ƙarfi yana qasa da idanuwansa da suke neman cikowa da
hawaye. Don sosai Maganan Anniey ya buge shi se dai samm baya taɓa damuwan komi akan
face nashi kan duk wani mahluki dake cikin estate ɗin nasu koma na ce family. Jin rauni ya wanzu a cikin muryan papiey ne ya sanya ta itama ɗin sake kame hannuwansa
cikin nata ta na kasa cewa komai dan tasan kuma ba zai iya ci gaba da maganan ba kenan.
Ɗan lumshe fararen idanuwanta tayi A bayyane kuma ta shiga furta adda'ar "Rabbi inni
lima anzalta ilayya min khairin faƙir³ Ra rabbi inni magalubun fantasir³ la haula wala quwwati illa
billahil aliyal azeem³, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ³" haka ta shiga ambata tare da sauran
adda'o'in da duk suka zo cikin bakinta. Ajiyar zuciya me sanyi papiey ɗin ya sauƙe a natse
yanajin hankalinsa na dawowa jikinsa take yaji dacin zuciyarsa ya ragu sbd yadda adda'o'in
data karanto ɗin suka ratsa shi sosai tare da zuciyarsa.
slowly kuma ta shiga ware idanunta tare da sake sanya hannunta tana jinginar da kanta jikin
papiey ɗin nata, daga haka tafiyan nasu ya koma na kurame har suka ƙara so mahaukacin
estate ɗin su, Shi ya fara fita jikinsa duk a wani kalan amma yadda yake tafiyan cikin nutsuwa
kai kace babu abinda ke damun Rayuwar sa nan. Lugagge bag na papiey kawai ta dauke se
handbag nata tana bin bayan mahaifin nata. tana tafiyar ne kuma tana ɗan shedding tears nata
zuciyan ta na ƙara yin nauyin abubuwa da yawa da suka kanainaye cikin rayuwarta.
A bakin entry na babban parlour'n gidan sukayi kiciɓus da Moh Ameern Saif inda ita ta tura
shi kuma ya turo. Kin sakin ƙofan tayi tana kuma ƙin kallonsa, sake murɗa handle door ɗin yay
yana jan ƙofar baya ya kuma ja ya tsaye yana ƙare mata kallo tun daga samanta zuwa ƙasa. A
ɗan kausashe ta furta "Moh Bani hanya" Ɗan girgiza kai yayi kawai tare da ɗan taunar lisp nashi, Wani shegen killer smile yayi tare
da ɗan shafar gashin ƙeyarsa yana me furta "Ohh Ohhh beb wai cikin sauƙi haka?" Yay
tambayan cikin ɗan iskan salon jan hankali da kuma rashin mutumci. Chakkk ta tsaya daga
ƙoƙarin raɓa gefen Moh Ameern ɗin da take niyar yi. Sakamakon tausasan hannuwan da taji ya
raba tsakanin su ta hanyar janye ta daga niyar shigan, ko bata juyo ba ZUCIYAR TA ta riga da
ta gama sanar mata ko wa ne ne. Hakan yasa ta jan idanunta ta lumshe su gaba ɗaya. Moh
Ameern daya ƙame cike da tsoro da kuma kafe Sheikh juraij ɗin da ido yake kallonsa, Shima
idanuwansa da suke a rufen ya buɗe tarrr akan Moh Ameern. Kafin ya saki wani murmushin
rainin wayo tare da zamar da ƙasan lips nashi ya furta. "Shi kuma wannan ko a cikin wanne
hadisin ne ko sura ohooooo, amma ko ba komi abin ya bada gitta da ƙyau Sheikh babban
salo!!!"
Haka muryan juraij ɗin ya dake shi Sheikh juraij ɗin. A natse ba tare da garajen komi ba ya
rabata da jikinsa yana jefawa Moh Ameern ɗin wani kalan mugun kallo me tattare da cikakken
gargaɗi. Ita ne ta fara barin wurin tana jin yadda ƙirjinta ya ɗan ƙare mata tare da mata wani
kalan nauyi wanda dama har yanzun bawai ta gama warkewa bane rass.
★A ƙaton parlour'n su wanda yake ɗauke da duk wani nau'in jin daɗin rayuwa ta tarar da
duka su Maamah har dama ƙarin babbar yayarsu ummeterh. Da sauri ummeterh ta nufo ta tare
da riƙe hannunta fuskanta ɗauke da kyakykyawan Murmushin da ya sake fidda tsananin
kamanninsu kasancewar su duka Ukun kamanninsu ɗaya. "Ma sha ALLAH Dear lallai jiki yayi
sauƙi tunda har aka iya fita shooting yau" ɗan murmushin yaƙe tayi tana shafa kan baby'n
nuwaira da ita ma ta nufo su fuskanta cike da farin cikin ganin Aunty Meesherh ɗin. "Dama ay
duk laifin Maamah ne banda haka ai naji sauƙin sosai!" Maama'n da itama ta taso daga idda
take zaune ne ta dawo ɗayan gefen Meesherh'n ta zauna ahankali tare da dafata fuskan ta da
ɗan murmushi ta furta "Ko yanzu nasan babay'n papah ba ta da cikakken lafiya kawai dai kina
danne hakan ne na sani"
"To banda abinki Mamman'su Karfa ki manta Meesherh fa ita ma ce ce wata rana haihuwa
zatay, tun daga