Showing 48001 words to 51000 words out of 80508 words
Chapter 17 - Inda Rai Book 1 Complete By Aisha Aliyu Garkuwa.pdf
*BOOK ONE PAGE 10*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
í ĵí½í ĵí½í ĵí½í ĵí½í ĵí½í ĵí½í ĵí½í ĵí½í ĵí½í ĵí½í ĵí½
*LITTAFIN INDA RAI NA KUĈINE, 1k ne cal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki
turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853278, ku kuma mutane Niger 1000fc jaka
Éaya kenan rak zaku biya ta wurin Mommy +22790899076, ku biya mu tafi tare domin mun kusa
gama free pages*
Tsaya-tsaya fa kiji yar uwa.
Zuwa yanzu na gama nazari da fahimtar Ĉorafe-Ĉorafen wasu daga cikinmu mata da kan zomin
da kukansu ire-iren hakaí ½íħ.
Garkuwa mijina baida kuzari!
Garkuwa mijina yana fin sati biyu ko uku bai buĈaceni ba!.
Garkuwa mijina baya gamsar dani in an fara 2 minute yakeyi.
A'a Garkuwa wlh abin oga yana ĈanĈancewa.
To ku taho ku kuma yi shiru.
In sha Allah, da yardar Allah da kuma izininsa da faÉinsa bai sauĈi ko wanne ciwoba Saida ya
sauĈi maganin cutar, sai dai in ba'a ganoshi ba.
Yar uwa kizo da yaĈini da yarda in Sha Allahu kukanki ya Ĉare.
Domin akwai haÉin maganin maza.
Na basir da sanyi.
Domin mafi akasari matsala biyun nanne ke sasu wannan matsalar.
Bayan maganin matsalar kuma, akwai zazzafan haÉin maza.
Mai magance matsalar ĈanĈancewar gaba, mai Ĉara masa kuzari, da girma, gami da iya juriyar
daÉewa lokacin raya sunna, da samawa iyali gamsuwar da zata Ĉara zaman lfy da inganta farin
cikin dararen ma'aurata.
Akwai maganin na gargajiya da kuma na Bappa Nasara...
âLaylah najin daÉin garin nan fa, ita cewa ma tayi wai in koma in bar mata keâ.
Murmushin tayi tare da ruggume Laylah data faÉa jinkinta.
Cikin sanyi ta Éan lumshe Idanunta tare da cewa.
âToh Allah ya kaika lfy y dawo da kai lfy ni ina nan tare da Laylah naâ.
Ameen ya amsa. Yana mai kallon Minat da saboda kamar ta da Ishmah yasa yake jinta har
ransa.
Washe gari da Asbah can cikin bacci Ishmah ta fara jiyo sanyayyan sautin muryan sa na ratsa
dodon kunnenta daga Masallacin Ĉofar gidansu yana karanta Suratul Juma'a.
Cikin sauri ta buÉe idanunta tare da miĈewa zaune sai yanzu ta tuna ashe fa yau juma'a ce jin
yana karanta suratul juma'a miĈewa tayi tare da tashin Laylah da Minat, kana taje tayi alwala,
suma sukayi.
Bayan sun idar da sallah sukayi Azkhar sai kuma ta kalli Laylah dake gaisheta amsawa tayi
kana ta riĈe hannunta.
Yayinda hannunta Éaya kuma ta shafa kan Minat tare da amsa gaisuwar ta, daga nan suka fito
falo hannunta na dama na riĈe da Carbi tana Istigfari...
Acan gefen Taj tare da Abba da Yah Muhammad suka fito daga Masallaci suka nufi gefen Abba
da kullum suke zuwa shan tea cikin nutsuwa Abba ya kallesa kana yace.
âMuje mu duba mutuniyar taka dan jiya da daddare tana ta rakin cewa hannunta ya Ĉoneâ.
Da damuwa Taj yace.
âSubhanallah amma da dare sosai ko?â.
Kai Abba ya gyaÉa suna cigaba da tafiya yace.
âEh kusan Ĉarfe goma sha Éaya Naji tanata raki anzo wajena karÉan Zam-zam ta Ĉone kasan
Ishmah da raki sai da naje nayi mata tofi kafin ta samu bacci, yanzu ma muje nayi mataâ.
Ĉan murmushi yayi tare da cewa.
âToh Abbaâ.
Kana sukayi gaba su Yah Muhammad na biye dasu bakinsu Éauke da sallama suka shiga falon
zaune a tsakiyar Parlour suka samesu...
Kamar yanda Abba ya sani tana riĈe da hannun tana hura masa iskar bakinta kana tana Éan
yarfewa.
Anutse ta Éago kanta tare da amsa sallamar sai kuma tace.
âYawwa Abba ayi min tofi hannun raÉaÉi yake min ya hanani bacciâ.
Sai kuma ta maida kallonta kan Khadijah dake cewa.
âUmmmâ.
AshagwaÉe tace.
âToh me zakice wani ce Ummm?.
Keda kike ta baccin ki baki sani ba ya hanani bacci da kyar na samu nayi bacciâ.
Murmushi Abba yayi cike da kulawa yace.
âShiyasa ma naxo na Miki Tofi Mamanaâ.
Ya Ĉare maganar tare da zama kan kushin kasancewar tana kasa ya kamo hannunta yana mata
Tofi su Yah Muhammad sai dariya suke suna faÉin rakinta yayi yawa Taj kuwa kallonta yake cike
da tausayi da kuma yanda take shagwaÉe fuska kallonsa tayi sai ta sake kwaÉe fuska shima
fuska ya kwaÉe kana ya Éaga mata girarsa Éaya. Abba kuwa bayan ya gama yace.
âToh ki matso mana Taj ma ya Miki addu'a kinsan kowa da dafa'in bakinsaâ.
Juyawa tayi ta kallesa sai kuma ta miĈa masa hannu ya mata tofi tare da cewa.
âToh Allah ya sawwaĈaâ.
âAmeenâ.
Ta amsa tare da gaishe da Abba kana ta gaishe da Yayunta da Taj.
Har zasu fita tace.
âAbba in zo musha shayin tareâ.
Kai ya gyaÉa tare da faÉin.
âZo mana Mamanaâ.
Mikewa tayi tabi bayansu
Atare suka sha shayin da ita.
Ĉarfe sha Éaya dai-dai Jirginsu ya tashi daga Yola zuwa Maiduguri borno birnin kanuri bayinmu
Fulani.
*Sirati sirta moÉa, toh saldori tagga moÉa* kasancewarsu bayi ne a garemu yasa suka koyi
karamci da martaba bako, Borno gidan karamci da girmama baĈi tarba na musamman Taj ya
samu daga Manyan Malamai Tabbas yaga karamci awajen Kanurai A jiddari aka sauĈe sa
bayan ya huta yayi wanka yaci abinci kana akayi masa jagoranci zuwa babban Masallacin
Jumma'a Al-Ansar.
Kusan a tare suka shiga yana tsakiyar
Al Sheiky Zharma..
Imam Muchmah. Da kuma Al Sheiky Idee sun sashi a tsakiya yayinda. Dubban musulmai ke
dandazon shiga ciki masallacin
shi yayi musu limancin Sallar juma'a na wannan ranan.
Koda aka idar tuni matasan Borno suka zagayeshi nan sukayi ta gaisawa dashi tare da yin
hotuna da vidios suna yaÉawa a social media, tuni Nigeria ta Éauka cewa Sheykh Afif
Muhammad Taj na cikin Ĉasar.
Washe gari Asabar bayan an idar da sallan asuba ya wuce garin Zamfara, nan ma yaga
karamci.
Kamar yadda ya alĈawaranta haka ya limamcesu kamsusul salawat.
Daga Zamfara ya wuce Kano ta dabo tumbin Giwa.
Jallabar hausa. Ya Salam shine abun da yake faÉa a lokacin da ya dira a malam Aminu Kano
international airport, sabida ganin taron masoya mabiya karatuttukan.
Bisa jagorancin Malam Aminu Ibraahim Daurawa da tsaron hukumar Hisba suka tarbeshi har
zuwa masauĈinsa na musamman da aka tanadar.
Taj yaga karamci iya ka wurin kanawa.
Dole kwanan sa biyu a Kano.
Ishmah ce zaune bisa kujera riĈe da cup Éin da da Khadijah ta dama furar mata ta kasa sha,
Éan kwafe fuska tayi lokacin da ta kurbi damun, domin ba daÉi kam to Amman akan ya lalace ai
gwara ta shanye musamman in ta tuna gargaÉin Garkuwa gyara riĈon da tayiwa wayarta tayi
tare da cewa. âYanzu dai ai yau zaku wuce Bauchi koâ.
Yana mai Éan sunkuyar da kansa kasancewar wayar na aljihunsa ne domin rashin samun
lokacin kansa yace.
âEh yanzuma zamu tafiâ.
Cikin kula tace.
âTaj anya kuwa kana cin abinci yadda ya kamata Allah naga videos Éinka ka Éan rame, gashi
kanawa nan yan al'barka sun zagaye min kai yadda kake ta musabaha da mutane a gajiyeâ.
Yana Éan lumshe idanunsa dake cike da tarin gajiya yace.
âSuna da karamci Amman yawan su da yawan son da suke min yasa sun kasa barina in hutaâ.
Cikin sanyi tace.
âBari in Barka dan naji yanzuma cikin mutane kakeâ.
Cikin sanyi yace.
âIn sha Allah jibi zan dawo dan yau in munje Bauchi da dare zamubi jirgi zuwa Abuja.
Duk zaman da zamuyi gobe zamu gama a Abuja jibi da sassafe zan iso Yolaâ.
âToh Allah ya kawoka lfy Amman Please ka kularwa Meymey da kanka da Adayaâ.
Da sauri ya rumtse idanunsa tare da katse kiransa saboda tsinkewa da zuciyarsa keyi a duk
sanda ta kira mishi su more especially Adaya.
A ranar suka wuce Bauchi.
Sha biyu dai-dai suka isa Bauchi Yakubu.
Kai tsaye suka wuce gidan, Sheykh Tajuh Usman Bauchi, dottijon malami kuma sannane a cikin
Ĉasar mu da kewaye baki Éaya, Shekh Tajuh Usman Bauchi dottijon mai tarin limin addini da
yawan shekaru kana da zugar zuriya Ĉ´aĈ´a da jikoki da jikokin jikoki, malami ne na Ĉarika
tsakakkeyiyar Éarika. Wanda yake da good understanding da manyan malaman kasarmu na sunan, shiyasa tafiyar
ma dasu akayi suna shiga harabar gidan Taj ya lumsh idanunsa tare da sauĈe wani irin
amintaccen ajiyan zuciya da fesar da sassayan numfashi kana ya buÉe idanun a hankali yana
karewa tsarin gidan da yafi dacewa da a kira shi da fada ko masararuta ilimi isilam domin
girmanshi ya wuce ace dashi gida, tsaruwarsa kuwa yafi karfin ace dashi ko sangaya sai dai
masarautar.
Isarsu ba wuya akayi musu iso cikin asalin sashin Sheykh Tajuh Usman Bauchi.
Kusan a jere a jere suke tafiya cike da kamala da nitsuwa da ilimi addinin Musulunci ya sakar
musu, yayinda yan agajin da kuma jami'an hukumar Hisba ke zagaye dasu.
Kusan duk a tare suke sauĈe sassauke numfashi a hankali da tsuka ratsa tsakiyar wani
mashahurin Parlour na alfarmar.
Sai kuma duk suka Éan tsaya saboda, ganin Éaya daga cikin masu yi musu jagoran ya Éan
buÉe musu wata babbar Ĉofa tare dacewa Bismillah.
Manyan malaman sunan a gaba, yayinda suka sa Taj a tsakiya sai yan agajin dake baya, kusan
duk a tare sukayi sallama
Ya Salam.
Shine abinda Taj ya faÉa a lokacin da suka iso tsakiyar Parlour da yafi dacewa da a kira shi da
holl, sai kuma ya lumshe idanunsa saboda hango Sheykh Tajuh Usman Bauchi dake zaune a
tsakiyar Ĉ´aĈ´ansa da jikokinsa gami da kuma amintattun Éalibansa duk sun zagayeshi tamkar
sarki a tsakiyar waziransa. Haka nan sai yanayin yayi mishi kama da yadda suke sa Yah Abana a tsakiyar duk ranar
jumma'ar Ĉarshen ko wanne wata, komai na zaman da tsarin gidan yayi mishi tuni da gidansu.
A hankali ya buÉe idanunsa tare da diresu kan kekkyawan farin dottijon.
Kusan a tare shi da Dottijon suke rufe idanunsu Saboda wani irin fitinenne bugun zuciyarsu da
yayi a tare.
Yayinda sauran kuwa duk sun zube a tsakiyar Parlour a gaban dottijon da duk ya girme su,
yana haifesu wasuma yayi jika dasu.
Yayinda sauran yaransa kuwa duk suka juyo suna kallon inda mahaifin nasu ke kallo.
Malaman Sunnan kuwa da sukazo cike da girmamawa suke gaida Sheykh Tajuh Usman
Bauchi.
Amman ina hankalinsa baya kansu.
Ido ya zuba wa Taj tamkar zai mannesu a jikinsa.
Shi ma Taj idon ya zuba mishi yana mai Éan matsowa kusa da abokan tafiyar tasa.
Sai kuma duk taron jama'ar da suka samu a Parlour suka juyo da sauri suka zubawa Dottijon
idanu jin yana mgna cikin muryar girma da nitsuwa da tsufa mai nagarta yace.
âInajin Ĉamshin Mahmoudu na, Ĉamshin Mahmoudu nakejiâ.
Ya Ĉare maganar da miĈawa Taj hannunsa tare da cewa.
âAfif Muhammad Taj ne yau a sangayataâ.
Da sauri Taj ya miĈa masa hannunsa.
Jawosa kusa dashi,
Da sauri Taj Éin ya Éan rusuna tare da direwa bisa guiwowinshi,
Shi kuwa Sheykh Tajuh Usman Bauchi, kan Taj Éin ya Éaura bisa cinyarsa, sai kuma ya sunkuyi
tare da cusa hancinsa cikin sumar kan Taj, tare da shaĈar Ĉamshin jikinsa.
Numfashi mai sanyi ya fesar tare da Éago kanshi ya kalli baĈin nasa tare da cewa.
âIzala Ĉanwar Éarika yau kun kawo min baĈo na musamman, bakon da nake jin jini da zuciyata
sun aminta dashiâ.
Sheikh Jabeer sani Maihula ne yayi Éan murmushi cikin sokkotancinsa yace.
âMalam ai ayanzu Sunnan ce abbabba Éarika ce aĈĈarama, kawai kui mubaya'a ku yarda mune
ag gaba garekuâ.
Murmushin Dottijon yayi tare da cewa.
âYoh aiko Éan hodiya mancewa yayi a sauka Sokoto da Bauchi zaizoâ.
Dariya sukayi mai sauti sai kuma duk suka fara gaisawa, har lau dai Sheykh Tajuh Usman
Bauchi bai saki Taj ba, yayinda Ĉ´aĈ´an da jikokinsa kuwa kab idonsu na kan Taj.
âTo Alhamdulillah sannu ku da isa lfyâ.
Sai kuma ya Éan kalli gefen damansa tare da cewa.
âKu isa kusha ruwa kuzo muyi muĈabalaâ.
Da sauri Sheykh Daurawa yace.
âA'a Malam zafa kayi mubaya'ar nan da baka sonyi in mukayi muĈabalaâ.
Sai kuma suka kalli Sheykh Janeer dake cewa
âAwoh haÉimai Gsky dai, domin hujjar aggaremu gaba gareku, kuna gani da ajjiyarku zaku
dawo baya garemu, ko ku zam kuna Éumiâ.
Dariya sosai sukeyi musamman sokotancin da Sheykh Jabeer ke zubawa.
A hankali ya yunĈura tare da fara kiciniyar miĈewa, da sauri Taj ya tallabeshi tare da taimaka
mishi ya miĈe, sai kuma yayi saurin amsar sandar da mutumin dake gefensa ya miĈa mishi.
Amsa yayi tare da bawa dottijon shi kuwa Sheykh Tajuh Usman Bauchi cikin tarin girma da isar
kamala yace.
âNi bana gaisawa da baĈo har sai na bashi abin sha da ci yaci ya sha, dan haka Bismillah ku
iso nan ya Ĉare maganar yana nuna musu Dinnin area.
Wani tamfatsetsen Dinnin table ne na alfarmar wanda ke da kujeru goma sha huÉu.
Yayinda saman table Éin ke cike maĈil da kayan marmari da kuma manyan womers na alfarmar
sai plates, bowls, mugs, and spoons.
Sanin YESS bazai tsaya yayi mgn ba sai sun sha wani abune yasa suka nufi Dinnin area Éin
bisa jagorancin babban Éansa.
Sheykh Tijjani.
Ga mamankisu kuwa sai gani sukayi yaja hannun Taj.
Sun bi wata Ĉofa ta musamman sun tafi.
Kusan duk yayansa kallon kallo suka farayiwa juna, fuskokinsu Éauke da maÉaukakin mamaki.
Su Sheykh Jabeer kuwa.
Bayan sun ci sun shane, duk sukayi al'wala saboda jin an kira salla.
Daga nan suka wuce masallacin sangayar.
Murmushin Daurawa yayi lokacin da suke tsaye a sahun forko sai kuma ya kalli Sheykh Musa
Yusuf Asadussunah na faÉin.
âToh yau maji ma gani wa zai limamce, izala zata limancin Éarika ko Éarikace zata limancin
izalaâ.
Murmushin Sheykh Isa Ali Pantami yayi tare da cewa.
âMu mun basu damaâ.
Da sauri Sheykh Janeer yace.
âAnya ko munefa gaba garesuâ.
Murmushin Sheykh Tijjani yayi yana kallon mahaifinsa ganin yana jawo hannun Sheykh Afif
Muhammad Taj.
Ga mamakin duk al'ummar Annabi dake cikin yankin jin Dottijon yana faÉin.
âYau ba ni zan ja sallaba
ya faÉa tare da Éan matsawa gefe kana yaci ga da cewa.
âAlhamdulillah dai ga Afif Muhammad Taj, a Ĉasar Nigeria a kuma jahar Bauchi a tsakiyar
tsagayata a kuma sahun limamcin masallancimu.â
Ya Ĉare maganar yana jawo hannun Taj ya tsaida shi da'irar limancin kana ya koma ya tsaya a
sahun forko.
Shi kuwa Taj zuwa yanzu al'amarin dottijon ya daina bashi mmki kawai dai yana jinsa har cikin
jini da tsoka Ĉashi da bargo jiki da zuciyarsa, wani irin son dottijon yakeji yana game jiki da
zuciyarsa.
Cikin sanyi ya gyara tsayuwarsa tare da gyara maek Éin cikin nitsuwa gami da cikir kamala ya
Éanyi gyaran murya tare da cewa.
âSahoohhhh! Sahoooohhh!! Sahooooooohhhhh!!!â.
Kusan gaba Éaya mamun nasa lullumshe idanu sukayi saboda yadda sautin Muryasa yake
ratsadu, sai kuma duk suka gyaggyara tsayuwar sahun.
Ajiyoyin zuciya suka rinĈa sauĈewa tare da bubbuÉe kwayar idanunsa lokacin daya fara tada
iĈama.
Da yawa sunso ace jam'in sallama Magrib ko Isha ko asuba zai jasu dan suji zaĈin muryasar.
Bayan an idar da salla suna sake koma ciki.
Nan suka tattauna duk abinda ya kawosu.
Kasan cewar Sheykh Afif Muhammad Taj da Isa Ali Pantami da Sheykh Jabeer Sani Maihula da
wasunsu Abuja zasu wuce, kuma sai tara na dare jirginsu zai tashi ne yasa suka kai dare.
Saura kuma tun bayan la'asar suka juya suka koma Kano.
Sit kakaji masallacin da lokacin da yake jansu sallan Magrib babu abinda ke tashi sai sautin
muryarsa bayan ya karanta suratul Fatiha kana ya Éaura.
Daga forkon Suratul Yoosuf
â(Aliflamrah tilka ayatu alkitabi almubinu)â.
Daga nan yaci gaba da kawo ayoyin har yaje aya ta 10 kana sukayi sujjadar forko, kana suka
miĈe dan.
Cikin aminci ya karanta suratul Fatiha kana Éaura da Suratul Yusuf Éin ya Éauka daga aya ta
11.
(Qaloo ya Abana ma laka la tamanna Aaala Yoosufa wainna lahu lanasihoonaâ.)
Wasu irin tafassasun hawayene suka zubawa Sheykh Tajuh Usman Bauchi, Dottijon mai cike da
wani miki a zuciya, yayinda shi kuwa Taj haka nan yaji tsoro na diro mishi cikin danne rauninsa
ya kawo aya ta 12.
â( Arsilhu ma'AAana ghadan yartaAA wayalAAab wainna lahu lahafithoonaâ.
Numfashi mai nauyi ya fesar a hankali tare da baddashi cikin taĈib kana yaci gaba da kawo
ayoyin Saida yaje aya ta 20. Kana suka tafi ruku.
Haka dai sukayi sallan cike nitsuwa da amcin mu'ujizar Alqur'ani mai girma.
Koda suka idar basu fitaba sai da sukayi isha, anan ma duk a Suratul Yusuf ya jasu, wanda duk
aya goma goma ya rinĈa kawowa haka yasa aka samu ayoyi 40 kenan
Ĉarfe tara dai-dai jirginsu ya tashi zuwa Abuja.
Cikin alfarmar darajar Alqur'ani mai girma. Aka Éaukesu kai tsaye gidan Sheykh Isa Ali Pantami
suka wuce.
Taj yaga kara da mutumci iyaka a wurin wannan Bagombe ya nuna mishi kuma lallay Gombawa
Éiban farine, ba'a kwana dasu ba a tashi dasu.
A dare ranar yaga karrama.
Washe gari da safe, cikin mutuntawa Sheykh Isa Ali Pantami ya shiga masauĈin baĈon nasa.
Shi kuwa Taj a dai-dai lokacin waya yakeyi da Ummeey ya kuma haÉa comfrence call ne da
Ishmah sai dai Ummeeyshi bata saniba.
âBabana wai sai yaushe zaka dawo ne? Ko ka mance cewa ka tafi ka bar mararka ne, yau fa sai
nan tazo muka kwana, tace gaba Éaya Ĉasar Ethiopia batayi mata daÉi in baka nanâ.
Sai kuma ta Éanyi shiru.
Shi kuwa Taj a hankali ya gyara tsayuwarsa tare da Éan gyara zaman hular kansa yana mai
nazari kan wasu ababen sauye-sauyen Meymey da sam a zuciyarsa bai aminta da itaba.
âHello Babana kayi shiru, Éazu munyi waya da Laylah tace wai bakusa ranaba me haka ke
nufi?â.
Cikin sanyi murya can Ĉasan maĈoshinsa