Showing 75001 words to 78000 words out of 80508 words
Chapter 26 - Inda Rai Book 1 Complete By Aisha Aliyu Garkuwa.pdf
A hankali ya ɗan gyara zamansa tare da kallon Tajj ɗin ta mirror.
So yake yayi mishi cikekken bayanin akan tarbiyya da halayyar Adaya to Amman ta ina zai
fara? More especially yanzu da yaga ubangidan nashi yana cikin yanayi mai wuyar fahimta,
saboda zurfin cikin sa da haƙurinsa da jumriyarsa, yasa bazaka iya tantance halin da yake
cikiba.
Shi kuwa Taj.
Numfashi mai zafi ya fesar dai-dai lokacin da yaga sun ɓullo kan titin nan da bazai taɓa
mancewa a rayuwarsa ba.
A hankali ya dire ganinsa kan masallacin da ƙaddarar auren Adaya ya riskeshi a ciki.
A hankali ya ɗagawa Abu Hashim hannu jin yana faɗin.
“Sir lamarin yarinyar fa, ba daɗi a bisa binciken da...”.
Sai kuma yayi shiru ganin Taj ɗin ya ɗaga masa hannu tare da jujjuya mishi kai.
Shi kuwa Abu Hashim a hankali ya sauƙe numfashi tare da fuskantar gate ɗin gidansu Adaya,
kana ya matsa hon.
Da sauri maigadin gidan ya leƙo, ganin dantsatsetsiyar motar dake tsaye tana zuba ƙyalli ne
yasashi saurin buɗe musu gate ɗin.
A hankali ya yayi parking, tare da buɗe marfin motar ya fito yana mgnar zuci.
Nazari yau kusan kwana ashirin da biyar kenan da yin wannan binciken Amman ya rasa ta ina
zai fara faɗawa ogan nashi sabida ganin tun ranar da aka ɗaura auren bai sakeyi mishi
mgnarba, gashi ya roƙeshi mgnar ta kasance sirri a tsakaninsu.
Da sauri ya ɗan miƙawa Maigadin hannu tare dayin mishi sallama yana mai mmkin wani irin
kallon da maigadin ke binshi dashi.
Shi kuwa Maigadin cikin nazari da tuno fuskar Abu Hashim ɗin da dan farin sani gani da yayi
mishi a ranar da yace ya aura wa ɗansa Tajuddeen Adaya, cikin tsananin jin daɗi yace.
“Mahaifin Tajuddeen mijin da ka aurawa Adaya ko!”.
Da sauri Abu Hashim ya gyaɗa mushi kai yana mai mamakin yadda akayi bai mance fuskarsa
da sunansa ba harma da sunan Tajuddeen ɗin.
“Kai Masha Allah, yau mai gidan zaiji kekkyawan labari da yake fata”.
Ya ƙare maganar yana murmushi.
Shi kuwa Abu Hashim cikin sanyi yace.
“Masha Allah, to kayi mana sallama dashi, kace dashi yau ga mijin Adaya na kawoshi”.
Gyara tsayuwarsa yayi tare da ɗan jim kaɗan cikin sanyi jiki yace.
“Baya gida, yau kwanansa biyu a asibiti, ciwonsa ya tashi”.
Cikin sanyi da alamun damuwa ya ƙare maganar, shi kuwa Abu Hashim cike da tausayawa
yace.
“Ayyah Allah ya bashi lfy, to Ma'aruf fa?”.
Yana ɗan sauƙe numfashi yace.
“Duk basa gidan sai Adaya itama yanzu ta dawo, daga asibitin da ƙaninta to shi yanzu ya fita”.
Shi kuwa Tajj shiru yayi cikin motar tamkar ba kowa, haka nan yakeji duniyar na juya mishi.
Ji yake yi tamkar ba'a raye yake ba, haka nan yakejin ƙasar Ethiopia tamishi zafi da ƙunci, to
me zai yi a cikin ƙasar tunda Yah Abana ya barrantar dashi da kowa nashi.
Sai kuma ya rumtse idanunsa da ƙarfi saboda wani irin ƙunci da zuciyarsa keyi masa, so yake
yayi tunanin ta ina zai fara bawa wannan kamilin dottijon haƙuri akan abinda yasan in yayinshi
dottijon zaiji ƙuncin zuciya da rayuwa.
Shi kuwa Abu Hashim a hankali yace to.
“To ayi mana iso da ita ɗiyar tawa ace mata ga mijin ya iso”.
To yace jiki a mace ya nufi cikin gidan domin ya san wacece Adaya da kuma yadda take ƙin
batun aure, dama yadda take wargaza duk aurenta da mahaifinta ke shiryawa, da wannan
nazarin ya nufi size ɗin Ummin Adayan inda yake jiyo kiɗa na tashi.
Bakin motar Abu Hashim ya dawo, tare da ɗan leƙawa ta ciki kaɗan.
Ganin haka ne yasa Taj ɗin ɗan sauƙe glass ɗin kaɗan tare da zuba mishi ido.
Cikin girmamawa ya gaya mishi yadda sukayi da Mai gadin.
Kai kawai ya jinjina mishi.
Ita kuwa Adaya da ɗan sauri ta miƙe tsaye daga zaman da take a gaban dressing mirror bisa
dukkan alamu yanzu ta fito wanka.
Dan Towel ne a daure a ƙirjinta.
Jin yadda ake ta buga ƙofar ne, yasa tayi saurin jawo hijabin dake gifenta ta zura shi kana ta
nufi ƙofar.
Ido ta zuba wa Maigadin nasu lokacin data buɗe ƙofar.
Shi kuwa ɗan rusunar da kanshi yayi yana maijin kiɗin data sake yana buwayarsa.
“Lfy meke faruwa?”.
Tayi tambayar tana girgiza ƙugunta, saboda haka take bata taɓa iya nitsuwa.
Ita a zatonta su Ummi ne suka dawo.
“Kinyi baƙi ne!”.
Ya faɗa yana ɗan jan baya.
“Toh kace su iso mana, ya za'ayi ka barsu a waje, su Asina ne da Izzin suka zama baƙi kuma”.
Tayi tambayar da alamun tana tsumayin jiransu ne, zasu fita su tafi wurin ibadar rawar da suka
ɗaurawa kansu.
Cikin sauri yace.
“A'a basu bane!”.
Tana mai ɗan juya ido tace.
“Toh su waye ne?”.
Cike da tsoro yace.
“Bawan Allah nanne daya aurawa ɗansa ke, to shine yazo da mijin naki”.
Wani irin murmushin mai sauti ta saki tare da juyi a tsakiyar Parlour kana tace.
“Da gaske?”.
Da sauri yace.
“Wallahi kuwa gasu can a harabar gidan”.
Ya ƙare maganar yana mai kafeta da ido da mamakin yadda fuskantar ta cika da farin ciki.
Ita kuwa Adaya cikin Tsananin jin daɗi samun damar yadda zata watsa auren ba tare da wani
mushkila ba, kasancewar ba kowa a gidan babu mai taka mata birki da fesa mishi salon tijarar
da zatasa dole a yau ɗin a yanzu ya saketa ta samu damar cimma burinta cike da jin daɗi tace.
“Alhamdulillah”.
Sai kuma tayi maza ta wuce ta gefenshi tare da cewa.
“Bari in kawo maka key ɗin BQ kaje ka buɗe mishi kace ya isa”.
To yace kana ya bita da ido.
Da sauri ta dawo tare da miƙa mushi key ɗin.
“Yauwa Baba ya yanayinshi yake?”.
Yana ɗan lallonta yace.
“Toh gsky dai ban ganshi ba, Amman zan iya nazartan yanayin mahaifin nasa mutumin kirkine,
kuma shima ɗan hakanne domin naji Muryar karatun Sheykh Afif Muhammad Taj ne ke tashi a
cikin motar tasa bisa alamu mutanene managarta ne masu kamala”.
Da sauri tace.
“To je kayi mishi iso”.
Ta ƙare maganar tana komawa ciki.
Wayarta ta ɗauka tare da dannawa Asina kira bugu ɗaya ana biyu ta ɗauka.
“Ke wai dan Allah kuna inane har yanzu baku iso ba?”.
Cikin juya ido Asina tace.
“Gani nan ban fito Bama Izzin nake jira yazo ta ɗaukeni”.
Wani dogon tsaki taja tare da cewa.
“Kai Izzin na mana wulakanci wlh rashin mota na damunmu, Amman ba komai nasan in sha
Allah muna dawowa gasar rawar nan, motoci sai wanda mukeso zamu hau, ke dai muyi fatan
Allah ya bamu sa'a”.
Cikin ƙwaffa Asina tace.
“Wlh kuwa Kinga nayi ta kiranshi ma baya ɗauka.”
Tana gyara wuyan hijab dinta tace.
“Dan Allah ki fito ki hau taxi ki taho, Kinga wai yanzu wannan wai Tajuddeen da Abpu keta cewa
mijina, ne yazo so kuyi sauri kuzo mu tace mishi mutunci dan naji alamun ustadz ne so da
makircin karuwaci zamu sa ya sakeni yanzu”.
Cikin sauri Asina tace.
“Kan bala'i gani nan fitowa yanzu kice zamu goge haddar kan ustadz”.
Cikin jin daɗi tace.
“Fes ma kuwa.
Yauwa maza kiyi sauri bari in kira banzannan kuma, dan kin san dashi abin zaifi tafiya zaifi
zargin Izzin ɗin Guy ɗin dake ɗebe min kewa ne Kinga saki dolen doliya kafinma su Ummi su
dawo munkorasu”.
Da sauri Asina ta miƙe tsaye, tare da katse kiran kana ta fitowa Parlour inda ta samu tsohuwar
kakarta wacce tsufa ya cimmata.
“Yanzu Asina bazakiyi kanki faɗa ki raba kanki da wannan shegen yaronya ku kama kanku ke
da Adaya kusan cewa akwai mutuwa da kwanciyar ƙabari da hisabiba.
Tana yamutsa fuska tace.
“Ni Kinga tafiyata ki rufe ƙofarki, dan acan zamu kwana, saboda rihazal ya fara zafi”.
Taƙare mgnar tana fita, da ido tsohuwar nan ta rakata ido na cikowa da hawaye.
Tace.
“Yah Allah kaine mai shiryawa ya Rabbi ka shiryi yaran nan shirin musulunci.”
Ita kuwa Adaya Parlour ta fito waya na maƙale a kunnenta.
Cikin wata iriyar muryar dake nuna Izzin ɗin yana tare da macene yake mata mgn.
Tsaki yaja tare da cewa.
“Please kayi sauri kazo gidanmu, zamu kora mijin da Abpu ya aura min. Wai yau yazo, karka
biya Asina ita ta fito”.
Da sauri yace.
“Ok gani nan zuwa”.
Ya ƙare maganar da raba jikinsa dana arniyar ƙaruwar tasa.
A hankali ya iso gefen Abu Hashim tare da cewa.
“Bismillah ku isa BQ na buɗe, Adaya nan fitowa”.
“To mun gode”.
Ya ƙare maganar da bashi hannu.
Kai ya gyaɗa kana juya ya koma bakin gate wurin aikinsa wanda yake da ɗan rata daga inda
motarsu yake.
Da sauri ya buɗewa Taj marfin motar tare da cewa.
“Bismillah ka isa”.
Cikin sanyi ya ziro ƙafarsa waje tare da fitowa yana mai rumtse idanunsa.
A lokacin ɗaya a rana ɗaya ƙaddara ta sauya mishi komai, ta kuma sashi zai akata abubuwan
da yafi tsana a rayuwarsa a tun lokacin daya kasance aboki ga Ishmah da ya san sanadin
abinda zai aikata yaune ƙaddararta.
A hankali yake taka ƙafarsa ya nufi BQ ɗin yana mai jin tausayin Dottijon shin ya zaiyi ya zaiji in
yaji abinda zai akaita akan ɗiyarsa to Amman ya zaiyi dole ne ta bar Ethiopia ya kuma nesanta
da ita da duk abin cikinta dan gudun tsinuwar mahaifinsa da kuma tsoron kada ya zama silar
mutuwar auren iyayensa da gudun faɗawa Allah ya isan mahaifinsa akan ƴan uwansa domin
yasan muddin dai in yana cikin Ethiopia to su Aunty Maryam da Rashida dasu Yah Abduraham
dasu Hafiz Yusuf bazasu iya hana kansu alaƙa ko magana da shiba.
Cikin wannan nazarin ya isa BQ ɗin a hankali ya shiga cikin Parlour mai wadace da tsabta.
Sai dai Parlour yana da duhu sosai, kasancewar windows ɗin Parlour a lungu suke kuma a rufe
suke ga kuma labuyen dake sassake.
Shi yasa haske bai wadaci Parlour ba dan iya ɗan hasken bok ɗin dake wajene ya ɗan bawa
Parlour'n haske kaɗan.
A hankali ya zauna bisa 1 setter dake fuskantar 3 sitter.
Ita kuwa Adaya wani irin makirin murmushi tayi tare da sauƙe Towel ɗin dake ƙirjinta ƙasa ta
ɗaurashi bisa ƙugunta, kana ta gyara wuyan hijabinta wanda hakan ya bawa turmusa-turmusan
breast ɗin ta dama sakewa da rausaya wa, a haka ta nufi BQ ɗin.
A hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗesu a hankali,.
Cikin sanyi ya gyara zamansa saboda ganin duhun ya ɗan raguwa idanunsa kasancewar ya
ɗan jima kaɗan a Parlour.
Ƙasa yayi da idanunsa lokacin da yaji sallamarta da shigowar ta duk a tare ta haɗasu,
Murya cike da kamala yace.
“Wa alaikissalam”.
Wani irin numfashin da yafi kama da na jarababbun mata ta fesar.
Wanda haka yasashi ɗago kansa.
Da sauri ya kwaɓe fuska ganin yadda take wani irin girgiza mishi Ballong ɗinta gami da yin wani
fitinenne murmushin mai cike da makirci da fidda ainihin rashin jinta da fitsararta.
Tare da ware idanunta dan ita har yanzu duhun ya hanata ganin fuskarsa.
Shi kuwa Taj.
“Wa iyazubullah”. Shine abinda ya furta a kan lips inshi tare da yin ƙasa da kanshi.
Jin haka ne yasata saki wani sabon sautin karuwanci fahimtar eh lallai plan dinta zaiyi aiki.
A hankali ta matso garesa, tana mai lumshe idanunta tare da shaƙan sassayan ƙamshin jikinsa
da yasata saurin rusunawa.
Allah ya sani bata taɓa jin ƙamshin wani ɗa namiji da yayi matuƙar sauya mata nutsuwarta ba
kamar wannan.
Da sauri ya ɗan ƙara matsawa gefen kujerar.
Ita kuwa Adaya cikin jin feelings ɗin gsky yana diro mata a jiki da zuciyarta ne, ta dire
guiwowinta a ƙasa tare da kife kanta bisa guiwowinshi.
“Innalillahi”. Shine abinda kunnenta ya jiyo mata yana faɗi.
Shi kuwa Taj wani irin tafasa da ƙuna yaji zuciyarsa tana ruɓanya yi saboda ganin lalacewar da
ko a mafarki baya fatan gani.
Wani irin zare idanunsa yayi a lokacin da yaji ta sa hannunta duka biyu ta zagayo ƙugunsa
murya cike da shu'umci ta fara mgna.
“Hi my life, Barka da zuwa”.
Hannunshi yasa da sauri ya fara tureta daga jikinsa.
Da sauri tasa hannunta ta zare hijabinta tare da cilla shi can gefe.
Cikin wani irin tsoron ganin tsananin lalacewar tarbiyyar ta, ya rumtse idanunsa da masifan
ƙarfi.
Sai kuma yaji jikinsa ya saki wani irin fitinenne rawa da tsuma, lokacin da yaji ta kamo
hannunsa ta diresu bisa tamfatsa-tamfatsan breast ɗin ta.
Da ƙarfi ya yunƙura da nufin yin mgn sai kuma ya rumtse idanunsa jin ta zira mishi harceta cikin
bakinsa.
Dai-dai lokacin kuma Ummeey dake kwance bisa gadon asibitin ne takeyin wani irin
maraitaccen kuka mai raunata zuciyar mai sauraro.
Hannun Malam ɗin dake tsaye a gefentan ta ruƙo cikin tsananin rauni tace.
“Dan Allah Malam kada ka nesan tani da Afi...”.
Da sauri yasa hannunsa ya rufe mata bakinta fuska cike da fusata gami da tsana da
hargitsewar tunani yace.
“Kada ki kira min sunansa, wlh muddin kika sake kira min sunansa a bakin aurenki, kuma in har
ya zama sanadin rabuwata dake bazan taɓa yafe masa ba, domin ya rabani da mace mafi
soyuwa da jinƙai a gareni, duk kuma ɗan dake jinina in ya kira min sunansa ko yayi alaƙa dashi
Allah ya isa ban yafe ba, kuma tsinuwata zatabi bayan Allah ya isan”. Da ƙarfu Yah Hafiz, Yusuf, Abduraham, Maryam, Rashida, Zakiya, Halima dama duk sauran
suka rumtse idanunsa.
Addawa kuwa cikin sanyi ta kalli ɗiyartata cikin bada umarni tace.
“Fatima in dai ni na haifeki, kuma zakiyi min biyayya to ban yarda ba ban yafe ba ki sake kira
mishi sunan da yace in kin kira akan aurenki ba”.
Cikin tsoro da tashin hankali Ummeyn Taj ɗin ta kalli mahaifiyar tata tana mai zubda hawaye
masu ƙuna tace.
“Innalillahi wa innalillahi rajiun, Allahumma ajjirni fi musibati wa...”.
Sai kuma ta kasa ƙarasa saboda numfashi daya toshe mata daga ƙasan zuciyarta domin zafin
abubuwan sunyi mata yawa.
Ita kuwa Addawa da sauri ta juya ta fice.
Cikin sassarfa Rashida tabi bayanta.
Shi kuwa Malam cikin zafin zuciya yake mgnar zuci da take iyakar gskyar sace
“Wallahi Allah kenan kab cikin Matana babu macen da ɗanta zaiyi abinda Taj ya aikata, ban
haɗa da ita na sakaba.
Allah kaine mafi sanin irin yadda ka jarabci zuciyata da son Fatima shiyasa ban haɗa da ita na
korata da ɗanta ba”.
Sai kuma ya juya ya fita.
Su Hafiz kuwa zagaye Ummeey sukayi suna bata baki..
Nigeria acan Adamawa kuwa, sosai jihar ke cika tib da baƙin manya malamai da ƙananan
saboda ƙaratowar taron ƙarawa juna sani, da haɗa kan izala da ɗarika da za'ayi a jihar.
Anyi yarjejeniyar yin taron a Adamawa ne, saboda kab Nijeriya Adamawa ne dai muka rage da
tutar Shehu Usmanu danfodiyo, hatta Sokoto da yake tushen Shehu tuni tutarsa daya kafa
musu ta ƙare.
Sai na Yola Adamawan Modibbo Adama Yola dogge doggitore.
To Shi yasa taron ya kasance anan.
Tuni Mai girma shugaban izala ta ƙasa yake amsar tawagar bakwancin malaman suna na kasar.
Yayinda Masarautar Lamiɗo kuma yake mai masauƙin malam ɗarika da sarakunan gargajiya da
suka samu daman halartar.
Kasan cewar yau Laraba gobe al'hamis jibi jumma'a da dare ne za'ayi zaman.
Ishmah ce kwance bisa gadonta, yayinda ƙanwarta autarsu da Hamisu da Adam ke zaune a
tsakiya ɗakin suna hira.
Tun bayan rasuwar Dadeey itace ta meye musu gurbinta, kamar dai yadda Daddy ta bar mata
watsiyar kula da ƙannenan nata.
A hankali Rahma ta ɗan miƙo mata plate ɗin data sa mata kankana tana faɗin.
“Adda lfy kuwa”.
Tana amsar plate ɗin tace.
“Yau fa tun safe neke kiran Taj Amman baya ɗagawa”.
Gyara zama Adam yayi tare da cewa.
“Wata ƙil yana sararin samaniya ne Adda kin sanshi ba mazauni bane”.
Da sauri tace.
“Kuma baifa cemin zaiyi tafiya ba”.
Sai kuma ta amshi wayar ta da Hamisu ke miƙa mata yana faɗin.
“Ga Bappa Kawu na kira”.
Amsa tayi tare da yin piking call ɗin.
Su kuma hirarsu sukaci gaba da yi.
A hankali ta sauke numfashi bayan sun gaisa sai kuma ta ɗan zare ido jin yana cewa.
“In sha Allah ranar Friday zan shigo Yola zanzo cikin tawagar Sarki Abubakar.
Zanzo da cikar shirina in kin amince dani ko a ranar ma a ɗaura mana aure”.
A hankali tace.
“Uhmmm”.
Sai kuma tayi shiru shi kuwa Bappa Kawu cikin sanyi yaci gaba da kafa gwamnatinsa.
A can Parlour Abba kuwa kishingiɗe yake yayinda Yah Abubakar ke gefensa waya yakeyi da
Uncle Bello.
“Toh ai dama rayuwa ta gaji haka, kuma dole Aysha dai aure zamuyi mata.
Domin ko ɗazu da Yamma yaron nan Mukhtar saida yazo min da yayansa da bappansa wan
mahaifinsa. Kuma yace ranar jumma'a zasu zo Yola.
Kaga dole haka zaka daure kayi aure, in dai anyi sadakan arba'in ɗin marigayi ya.”
Cikin sanyi da tarin rauni mai raunata zuciya yace.
“Kayya ni kuma wani aure ya rage min Yah Bello, ai aure kam sai yara ita dai Mamana in samu
tayi sauren shine burina, sai kuma batun auren Adam, kasan jibin za'a kai kefensa”.
Cikin sanyi Uncle Bello yace.
“To Abdullahi zaka zauna hakane, ai zama haka bazai yuwuba. Dole kayi aure ko dan Rahma
da Hamisu”.
Cikin sanyi yace.
“Hummm”.
Littafin INDA RAI na kiɗine karki karanta in baki biyaba dan Allah 1k ne ga account no in da zaki
turo min kuɗinku 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa, ku kuma mutane Niger ga number
Mommy ita zakuyiwa magana ta gaya muku yadda ta inda zaku tura mata kuɗin 1000fc ne haka
ɗaya kenan +22790899076
Ethiopia.
Motarsu na fita daga gate ɗin Asina na shiga ta ƙaramar ƙofar, da kallo tabi motar tamkar zata
liƙe idanunta akai.
Yayinda shi kuma Baba mai gadi bin motar yajeyi da idanun tamkar zai liƙasu a jikin motar, har
leƙawa yakeyi gami da karkata kanshi, saboda wai ko zai samu