Showing 6001 words to 9000 words out of 80508 words

Chapter 3 - Inda Rai Book 1 Complete By Aisha Aliyu Garkuwa.pdf

06 Jul 2025

3614

kuma ta kalli Garkuwa dake cewa.
“Aa ki ɗauka mana, har ta tsinke”.
Juyo fuskantar wayar tayi ga mamakinta sai taga hoton.
Wata kekkyawar Babbar mace ce, mai tarin kwarjini da haiba kana an rubutu.
Fist Love a saman hoton nata,.
Sai kuma tayi kasake ganin kiran ya tsinke sai kuma poton gaban wayar ya bayyana.

Wannan matar ce a zaune sai kuma Taj da yake durƙushe a gabanta ta daura hannunta a kashi
tana Murmushin dake bayyana tsananin soyayyarsa a ranta sai kuma wasu mata dake kewaye
dashi.

Da sauri Maryam data leƙo tace.
“Laaa ikon Allah wannan hoton pilot ɗin nanne fa da yayi mata addu'a ta nitsu a jirgi, Aunty
Garkuwa ganifa”.
Ta kare mgnar tana nuna mata fuskar wayar.
Ita kuwa Aysha jakar tata ta fara laluba wai ko zata jiyo wayarta, jin wayam ba wayar ne yasa ta
kalli Garkuwa dake cewa.
“Ikon Allah tofa inaga kunyu canjin waya da bawan Allah nan”.
Dai-dai lokacin kuma wani....!




By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/3, 2:13 PM] Fa'izatu Tsohuwa: ✈️

*INDA RAI*

*BOOK ONE PAGE 2*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*



Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Kayana sun iso lfy. Aikin su ya kankama, komai
ya zama Available. Duk abinda kake so a cikin wanda zan sako a nan akwaisu Available,
kayane masu zafi da tururi kayane da ban taɓa jibgo kamar su da irinsu ba. Ku matso iyayen
amare, da amaren da yayun amare da ƙannen amare da ƙawayen amare, Uwar gidaye gareku,
tsakar gidaye kuma ban barku a baya ba, mai jego sabon haihuwa ko tsohon jego wato barden
goyo, amarya Budurwa ko Bazawarara duk ku taho kowa da zazzafan haɗinsa, ina araha kam
duk ɗan karen tsadan da kayan suka ƙara Amman fa ina hana bashi. Idan kayan ɗa'a kikeso ga
number da zakuyi min min da ita 08069423567.


*Littafin INDA RAI na kiɗine, yanzu munayin free pages ne, ki biya ki karanta cikin aminci, 1k ne
kacal, 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki kuma ta
wannan number 09097853276. Ku ma mutan Niger 1000fc ne zaku biya wato jaka ɗaya rak. Ta
wurin Mommy zaku biya.+22790899076*

Kiran ne ya ƙara shigowa da sauri Maryam ta miƙa mata wayar.
Atake hoton fuskar wani kekkyawan dattijo fari ƙal dake zaune a tsakiyar zaratan maza manya
da ƴan saffa-saffa wanda sun kai takwas zagaye dashi sai kuma Taj dake gabashin zaune ya
ɗaura kanshi bisa guiwowin Dottijon,ya bayyana wanda aka rubuta. Yah Abana.
Bisa alamu duk mutanen Ethiopia ne, domin su kalar fatarsu da farinsu ke nunasu a duk inda
suke a faɗin duniya wanda kalar ƴan Sudan na ɗan ɗibi da suɗin.

Kasake tayi har kiran ya tsinke.
Sai kuma ta kalli fuskar wayar ganin babu matakan tsarone yasa ta sauƙe numfashi tare da
kutsa kai ta shiga.
Wurin Contacts ɗinsa sabida tabbatarwa, da sauri ta fara bin sunayen mutanen da yafi mata
kama da sunayen larabawa da rubutun da yafi kama da na larabawa da akayi amfanin dashi
wurin rubuta sunayen.
Cikin sauri tace.
“Tabbas ba wayata bace gashi komai ba nawa bane”.
Kai Maryam da Garkuwa suka jinjina tare da cewa bai lura bane ya dauƙi taki wayar ya bar Miki
tashi.”
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Ok bari in kira layin nawa in gaya mishi ya mana canjin waya”.
Ta ƙare maganar tana sa number ta.
Kana ta danna kiran.
Dai dai lokacin kuma Afif Taj yayi wani gajiyeyyen miƙa, tare da gyara kwanciyarsa bisa
tattausan katifar gadonsa na masauƙinsa mai alfarma, wani irin mayataccen bacci mai gauraye
da gajiya yakeji, ji yakeyi tamkar kanshi zai rabe gida biyu, so yake ya watsa ruwa ya sauƙa
ƙasa ya tafi Harami, Amman ina bazai iya saboda tarin gajiyar dake tattare dashi. Sassayan numfashi mai sanyi ya fesar tare da miƙa, hannunshi ya jawo ɗaya daga cikin
woyoyinsa biyu daya aje akan bedside drower, ya sani Ummenshi bazata yi bacciba har sai taji
ya isa Lfy.
Haka kuma Yah Abananshi sai yaji sauƙansa Lfy yake samun nutsuwa.
Yana mai ware idanunsa da bacci ya fara cin ƙarfinsu ya ɗan shafa fuskar wayar.

A kuma dai-dai lokacin Aysha ta kalli Garkuwa tare da cewa.
“Wayarfa switch off”.
Tana zama bakin gadon ta, tace.
“Toh ko ya kashe wayar ne”.
Numfashi ta ɗan fesar tare da lumshe idanunta kana tace.
“No dama nasa wayar a Airplane mode. Wata ƙil shi baima lura ba wayarsa bane”.
Sai kuma tayi saurin jiyowa ta kalli Maryam tare da cewa.
“Ni Allah ma ya rufan asiri yasa ba'a jirgin nabar wayata ba”.
Sai kuma tayi saurin kallon fuskar wayar jin tana ringing ga mamakinta layinta ne.

Shi kuwa Afif Taj, manna wayar yayi a kunnensa yana mgnar zuciya mai haɗe da nazari.

“Yah Salam na ɗauki wayar mai aljanun nan kenan na bar nawa a wurinta.
Ayyah Ummeei na tayi ta kira kenan bata sameni ba”.
Sai kuma yasa hannunsa ɗaya ya jawo ɗaya wayartashi.
Yess yasamu kiran iyayen nasa kuma, sai dai kasancewar wayar na silent kasancewar itace,
wacce yake yawan amfani da ita, waccar ta wurin Aysha iya Family inshi kaɗai yake kira da ita,
a Family inma mafi kusanci dashi.

Ita kuwa Aysha a hankali ta amsa kiran, saboda jin Garkuwa na cewa.
“Ki amsa mana”.
A kunneta ta liƙa wayar, cikin sanyi murya tayi cikekken sallama.

Cikin son yakice nannauyan baccin dake danneshi ya amsa sallamar tare da cewa.
“Kina ina!?”.
Cikin sauƙe numfashi ta lumshe manyan Idanunta masu masifar haske da ƙyalli tare da faɗa
mishi sunan masauƙinsu da room number insu, ta ɗaura da faɗin.
“Ka ɗauki wayata ka bar, min taka”.
Ta ƙare maganar cike da tsananin mamakin to ya akayi ya samu ya cire pin ɗin wayar tata har
ya kirata, nazarin nata ya katsene jin yana cewa.
“Yah Abana, da Ummeei na sun kira ko?”.
Da sauri tace.
“Eh Yah Abana da Fist Love ne, suka kira Ummei bata kiraba”.
Ɗan gudun numfashi ya fesar kana yace.
“Ok kada ki amsa kiran kowa idan an sake kira.”
Da sauri tace.
“Ton ni kuma waye da waye suka Kirani!?”.
Cikin lumshe idanunsa yace.
“I don't know”.
Cikin fahimtar shi mutum ne mai taƙaitattun kalamai ta ɗan yamutsa fuska tare da cewa.
“Please idan Barrister ya kira kada ka ɗaga, in kuma Dadeey na ta kira ka ɗaga, ko Abba na
kace musu munyi canji wayene.
Kuma kace musu ina lfy”.
Cikin ƙosawa da surutun nata yace.
“Bazan iyaba”.
Yana faɗin haka ya katse kiran, tare da cilla wayar gefe,
Kana ya kira Ummei shi da ɗaya wayar tasa.
Bugu ɗaya ana biyu ta amsa bisa dukkan alamu tana cikin haramine dan yaji sowan dubban
jama'a, wacce tafi ta kullum saboda ƙaratowar ranar arfa yasa gaba ɗaya mahajjata sunata
hallara cikin Makka.
“Afifff”.
Ta ƙira sunansa cikin mabayyaniyar so irin ta uwa da ɗanta.
Cike da gajiya kana da magagin baccin yace.
“Ummeey na mun sauƙa Lfy”.
Cikin jin daɗi tayi hamdala tare da cewa.

“Alhamdulillah tun ɗazu na kiraka baka ɗauka ba,
Malam ma ya kiraka duk bakayi picking calls inmu ba, kana lfy dai kam ko?”.

Tamkar yana gabanta ya gyaɗa kai kana ya ɗaura da cewa.
“Alhamdulillah Ummeey”.

“Zaka shigo Harami yanzu ne?”.
Cewar Ummeey.
Yana gyara kwanciyarsa yace.
“Sai asuba”. Kai ta gyaɗa tare, da miƙawa Malam Muhammad wayar, amsa yayi tare da kaiwa
kunne cikin tattausan lafazi da irin soyayyar nan da bata ɓuya a kan fuska dottijon yayi sallama
tare da ɗaurawa da cewa
“Abana”. Dan haka yake kiransa, kasan cewar sunan mahaifinsa garesa shi kuwa Afif yana
juyawa gefen damanshi yace.
“Yah Abana”. Murmushin mai sauti dottijon yayi, kana suka gaisa tare dayi mishi sannu da gaji.

Jin yadda muryar ɗan nashi yayi ƙasa sosai alamun bacci ne, yasa ya sallameshi, daga nan
sukaci gaba da ibadunsu.

Su Aysha kuwa bayan sunyi wanka sun ɗan ci abinci.
Suka sauƙo ƙasa kasan cewar masauƙinsu ba nisa da Harami.
Daga nan suka fara gabatar da aikinsu.

Shi kuwa pilot Afif Taj, lumshe idanunsa yayi tare da karanto addu'ar kwanciya bacci yayi,
saboda yana da al'walansa. Yana gamawa ya shafe jikinsa kana ya kwanta tare da fuskantar
alƙibla, yana mai tasbihi, cikin second nin da bazasu gaza 23 ba bacci yayi awon gaba da shi.


Gaba ɗaya Mahajjata, basu da wani tunanin ko, nutsuwa da ya wuce gabatar da aikinsu.

Alhamdulillah kuma komai na tafiya, bisa tsari na addini.
Yau kwanasu uku kenan, kuma jibine, arfa. Hankalin Majjata duk na can.

Aysha ce dake sanye cikin wani Maroon Abaya mai manyan flowers da yayi masifar yi mata
kyau sai kuma Maryam dake ɗan tafiya cikin alamun, gajiya, suna ɗan sassarfan bin Garkuwa,
domin, so suke su koma gida su samu su ɗan rumtsa, kasancewar a Harami suka kwana.

Cikin damuwa Aysha ta kalli Maryam tare da cewa.
“Mutumin nan fa, yauma na kira shi, bai ɗaukaba, nagaji da rashin wayata a hannuna, yau
kwana ukufa kenan bai amsa kirana, ko su Dadeey na sai dai muyi waya dasu ta wayarki.”
Ta dire ayar mgnar dai-dai lokacin da suka shiga lifter da zai kai su masauƙinsu.

“Kada ki damu fa ai dole zai nemeki, dan na tabbatar wayarshi tafi taki mahimmanci, kuma

Kinga tashi babbar takice, kawai collor insu ne ɗaya”.
Maryam ta faɗa mata cikin kula.
Kai ta jinjina tana ɗan lumshe Idanunta tace.
“Ni da katin nashi bai ƙareba ai ko a jikina bakiga da wayar tasa naketa kiran su Dadeey naba”.
Ɗan murmushi Garkuwa tayi tare da cewa.
“Okay Shiyasa tun jiya kika buwaye mu, ashe katine, ya ƙare, da shiru kikayi, kinata bin cike mai
waya, da duba abubuwansa”.
Fuska ta ɗan ƙwaɓe wanda yasa ainihin kyawun fuskarta bayyana tare da cewa.
“Yoh shi mema a wayar tashi ba komai fa.
Ko pictures babu sai irin wanda in an kiranshi suke ɗan fitowa a fuskar wayar. Sai dai tarin Apps
na Qura'an da hadisai da abubuwa su na pilot, da kuma Doctors”.
Kai Maryam ta jinjina kana tace.
“Gaskiya dai gwara ya ɗauka a samu a amshi wayar, Kinga cewa Yah Barrister mukayi wayarkin
ta faɗine, kuma naji yana cewa zai saya Miki wata.”
Tayi mgnar cikin tausayawa ɗan uwanta.

Murmushin Aysha tayi tare da cewa.
“No nima bazan barshi ya sai min wata ba.”

Dai-dai lokacin kuma suka isa masauƙin.
Bayan sun shiga, ne suka nufi ɗakinsu.

Murmushin mai yelwa Barrister yayi tare da nufosu.
Cikin yanayin dake nuna yaƙinin soyayyarsa gareta, ya amshi goran Zam-zam ɗin dake
hannunta.
“Baby kinyi mana addu'a ko?”.
Kai ta gyaɗa mishi tare da nuna mishi Maryam da Garkuwa, cikin mutumtaka suka gaisa kana
su suka shiga ciki.
Shi kuma da ita a Corridor ɗin suka zauna bisa kujerun dake wurin.
suka ɗanyi hira kana ya miƙe suka shiga ciki.
Kuɗi ya basu baki ɗaya sun.
Kana ya fita ya tafi.

Yana fita suka ci abinci da suka shigo dashi kana, suka ɗan watsa ruwa, suka kwanta bacci.

A hankali yake kimtsa kanshi, cikin wani tattausar jallabiya fara ƙal, sai kuma hiramin daya saka
sky blue daya yafa a saman kafaɗunsa, sai kuma yar tattausar hular fara mai ratsin sky blue ɗin
ya murza a kanshi, turaren Hubban shadidan, ya feshe jikinsa, dashi, kana ya zira tattausan
silifas, shima sky blue. Bakin gadon ya zauna yana shafa fuskarshi da hannun dama, yana jin alamun tofowar sajen da
baya barinshi ya bayyana a jikinsa, dan shi saje baya cikin, ababen da ya damu da bari, dan
gani yake zai dameshi.
Numfashi ya fesar yana mai tunanin, yana gama aikin, Cheving face ɗin nashi zai fara yi.

Wayar Aysha dake kan pillow ya jawo, tare da ɗan taɓa ƙasan fuskantar wayar kaɗan da
babbar yatsarsa,
Ido ya zuba wa fuskar wayar, cike da mamakin yadda yatsarsa kan buɗa wayar da ba tashi ba.

Kauda tunanin yayi tare da kiran wayarsa.
shiru yayi yanajin yadda wayar ke ringing Amman ba'a ɗaga ba har ya tsinke.
Sake kira yayi a karo na biyu, still ba'ayi piking call ɗin ba, har ya tsinke.

Ita kuwa Aysha cikin baccinta da yayi nisa, take jiyo ringing ɗin wayar, sai dai tana farkawa
kiran na katsewa.

Ɗan tsuka ta ja, tare da gyara kwanciyarta ta cigaba da bacci.

Shi kuwa Taj, time ya duba, ganin, ƙarfe takwas ne na safe, yasa ya miƙe tare da zira wayar a
aljihunsa, dan Ummeynshi tace tana son su shiga Oriental Abaya House.
Dan tana son sayawa yar autarta Zakeeya, wata Abaya data fitineta da kira dominsa.

Wannan tunanin ne, yasashi miƙewa tare da fita.
Yana tafe yana mgnar zuci.
“Wannan ina ta shiga ina kira bata ɗagawa, kada kuma inje masauƙin nasu in samu bata nan,
bari dai in fita da wayar, in na dawo in fara zuwa wurinsu in amshi wayata, in bata tata adena
takura min rayuwa da kiraye-karayen naci”.
Ya ida mgnar tare da shiga ɗakin da iyayensa suke,
Daga nan suka shiga ɗakin Addawa, wacce kakace a garesa mahaifiyar Ummeynshi.

Malam kuma dama tuni yana Harami.
Daga nan suka nufi inda zasujen


Ƙarfe goma dai-dai Aysha ta farka,
Ido ta zurawa gadon Garkuwa saboda ganin bata nan.
Zama tayi a bakin gadon tare da kallon ƙofar bathroom dan jin motsin ruwa, sai kuma ta kalli
Kofar shigowa,
“Yauwa masha Allah, Aysha kin tashi, Please yi sauri mu fita, ga Uncle Ali, yazo mu fita tare
dashi, zamufi zararshi”.
Cikin alamun bacci tace.
“Wayeshi ɗin”.
Tana mai kallon Maryam dake fitowa wanka tace.
“Uncle nane ƙanin mamana kuma shine Amirul Hajj namu”.
Da sauri Maryam tace.
“Kai haba tunda muka haɗu nake ta Miki kallon kamar nasan fuskarki, ashe fuskar shi nake
tunawa, gsky kuna kama wlh”.
Kai ta jinjina tare da cewa.

“Eh haka dai ake cewa Amman ni ban yarda ya za'ayi mace tai kama dana miji”.
Ta ƙare maganar tana kamo hannun Aysha tana tsayar da ita tare daci gaba da cewa.
“Mu tafi. Yanafa jiranmu yace, shekaran jiyama yazo ya samu, kuna bacci baku gaisaba dan
haka yau in tasoku”.
Cikin sanyi Aysha tace.
“Bari in ɗan watsa ruwa”.
Da sauri Garkuwa ta jujjuya mata kai tare da cewa.
“Please kifi, kada kice sai kinyi wanka, kafin muyi baccifa duk munyi wanka”.
Kai ta jinjina kana tace.
“Toh bari inyi al'wala”.

Bayan tayi al'wala ta fitone, ta kimtsa, cikin tattausar Abaya Black collor mai masifar sulɓi, tayi
rolling kanta da ɗan kwalin, kana ta zura takalmin snicker nevy blue, tare da ɗaukar ƴar hand
bag itama nevy blue wayarta ta zura a ciki kana, ta rataya a wuyanta, irin rata yawar nan ta kai
duka.
A jere suka fito.
Cikin kulawa Uncle ya sakar musu murmushi tare da cewa.
“Yaran albarka ya ibada”.
Cikin jin daɗi sakin fuskansa suka amsa da.
“Alhamdulillah Uncle komai lfy Lau”.
Kai ya jinjina tare da yin gaba yana faɗin.
“Masha Allah”.
Suna sauƙa suka samu mota a tsaye driver na ciki bisa dukkan alamu su ake jira.

Gaba ya shiga ya zauna, yayinda su kuma suka zauna a baya.
Kana motar taja suka tafi.

Cikin kula yace.
“Aysha ya kewan gida”.
Kai Garkuwa ta ɗan jinjina tare da cewa.
“Gaskiya dai kam Uncle ina missing su yan uwa sun samu duk kusan ɗakinsi ɗaya suke ni
kuma. Ni ɗaya, irin Maman Khairta kam ma tunda nazo bamu haɗuba. Gwara Mami, Maman
Sayyid, da Aunty Nanee su mun haɗu.”
Sai kuma tayi shiru jin Maryam na cewa.
“Toh ba gamu ba, muna ɗebe miki kewarsu”.
Murmushi tayi jin Aysha na cewa.
“Kuma mu jinki muke kamar yar uwa”.
Da sauri tace.
“Wallahi nima haka nake jinku”.
Uncle Ali kam sai murmushi yayi.

Sha ɗaya da rabi dai-dai suka isa bakin.

Riyal Abaya shop.
A kuma dai-dai lokacin Aysha ta ɗan gyara zaman jakarta, tare da zaro wayar dan duba Time,
sai kuma tayi arba da miss calls har biyu, da layinta, da sauri ta kira layin nata.
Kasake tayi tana jin yadda wayar keta ruri Amman ba'a dagaba, ƙara kira tayi a karo na uku
tana mai sauraron Uncle Ali dake cewa Garkuwa.
“Yauwa shiga ku ɗauki duk abinda kukeso, in kun gama ki kirani ki gaya min, zan biya kuɗin
kuma zan turo Usman yazo ya ɗauke ku da kayanku.
Ya ƙare maganar yana miƙa musu.
kuɗi, Dukansu uku kana ya haɗa da cewa.
“Wannan ku ajiye ne, Amman na sayayyar da zakuyi, in kun gama kawai kuyi min mgn”.
Cikin jin daɗi Maryam da Aysha sukayi ta godiya tare da yimishi addu'a.

Da sauri Aysha ta maida hankalinta kan wayar jin, an amsa kira na huɗu data sakeyi.
A takaice yace.
“Kina ina?”.
Da sauri ta ɗago kanta ta kalli rubutun gaban saman wurin tace.
“For naw dai Ina Riyal Abaya shop, kaifa kana ina?”.
Yana mai dudduba jallabiboyin dake gabansa yace.
“Oriental Abaya House”.
Jin haka yasa tayi sauri ta kalli Uncle Ali tare da cewa.
“Ayyah Uncle dan Allah ta ina Oriental Abaya House yake”.
Kai ya dan juyo ya kalleta tare da cewa.
“Can kuke son zuwa ne”.
Da sauri tace.
“Eh Uncle dan zan amshi wayata ne a wurin wani yace min yana can”.
Kai ya gyaɗa kana yacewa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login