Showing 69001 words to 72000 words out of 80508 words
Chapter 24 - Inda Rai Book 1 Complete By Aisha Aliyu Garkuwa.pdf
kayi magana ka faɗi abinda ka sani kuma yake
shine gaskiya.”
Idanunsa da suka sauya launi yayinda jijiyoyin dake cikinsu suka yi jajaye ya ɗago ya kalleta,
lips d’insa ya d’an cije kana ahankali yace.
“Ba abinda na sani da zan iya cewa”.
Da yanayin damuwa Aunty Maryam ta kallesa kana cikin sark’ak’iya tace.
“Kamar ya ba abinda ka sani Tajj? wani irin maganane wannan? wacce iriyar magana kake
zaka ce mana ba abinda ka sani?”
Ta ƙare maganar cike da jin tsoron anya kuwa Taj bai shiga tarkon shaiɗan ba.
Dai-dai lokacin Zakiyya ta fito hannunta riƙe da waya tana hawaye wanda bisa alamu da Aunty
Halima take waya.
Ita kuwa Aunty Halima shesh-sheƙan kuka take Ummey ta mika wa wayar.
Ummey na amsa tace.
“Toh Halima ya zamuyi addu'a kawai zamuyi masa amma lallai muna cikin ƙalubale, muna gab
da fuskantar wani kalubale mafi muni a rayuwarmu, muyi ta addu'a Allah ya kawo mana da
sauƙi, ni da Abbanku jiya kwana mukayi ba muyi bacci ba, sannan yau da safe naje na samu
Dr. Abbas na duba shi BP d’insa ya hau.”
Jin hakan yasa Taj sunkuyar da kansa ƙasa tare da d’an yunƙurawa ya miƙe ahankali.
Kallonsa Ummey tayi tare da faɗin.
“Ina zakaje?”.
Ƙwayar idanunsa ya risinar ƙasa kana atausashe cikin had’iye tarin damuwarsa yace.
“Zanje duba Yah Abana”.
Ya ida maganar yana mai jin ƙaunar iyayen nasa acikin ransa.
Yana shiga ɗakin kuwa ya samu kusan baki daya yayunsa Mazan suna nan sai kuma ya ɗan
tsaya jin Yah Hafiz na magana cikin sanyi da taushin lafizi da biyayya yana cewa Mahaifin su.
“Abbah kafin ayi komai a nutsu abi abin ban Ahankali, Abba kaine mafi sanin halayen mu gaba
ɗayanmu mu ƴaƴanka. Allah ne ya tarbiyyantar damu amma kaine ka daura mu kan hanya
Abba ka sani cewa Taj baya ɗaya daga cikin irin mutanen daya kamata ace wannan zargin ya
hau kansu, kuma ka tuna cewa Taj mutum ne ajizi dan girman Allah da Manzonsa koda an
sameshi da ajizanci a cikin maganar nan ayi mishi uzuri a sassauta mishi”.
Cikin sauri Yah Yusuf ya karbi maganar da cewa.
“Sosai ma Abba dan Allah asan abinda za'a yi akan maganar nan, ni inaga Maganar nan anyi
masa bahagon fahimta ne yarinyar nan Meymey ita kanta batasan mai take faɗa ba”.
Ahankali Yah Abana ya ɗago gajiyayyun idanunsa dake nuni da damuwa ya kalli Tajj sai kuma
ya sunkuyar da kansa.
Tajj kuwa lokaci ɗaya yaji hankalinsa yayi masifar tashi fiye da wanda yake ciki zuwa yanzu ya
fahimci mahaifinsa kamar baison ganinsa ne jiki amace ya isa tsakiyarsu kana ya zauna a
gaban Yah Abana tare da faɗin.
“Yah Abana Barka da safiya”.
Batare daya amsa gaisuwar nasa ba yace.
“Menene gaskiyar abinda Meymey ta faɗa?”
Ahankali ya motsa Lips ɗin sa zuciyarsa na wani irin mummunan bugawa yace.
“Ban saniba Yah Abana”.
Kai Yah Abana ya kawar batare daya sake bi ta kansa ba.
Murya na rawa ya ɗan zuba masa Idanu ganin yanda lokaci ɗaya ya ya faɗa, asanyaye kuma
yace.
“Yah Abana ya jiki?”.
Ƙin amsawa yayi sai ma rufe idanunsa da yayi.
Ganin haka yasa ahankali Taj ya zauna kana ya sunkuyar da kansa ƙasa tare da sa hannunsa
da nufin kamo ƙafar mahaifin nasa dan yi masa tausa.
Saidai hakan baikai ga samuwa ba yayi sauri janye hannunsa sakamakon Yah Abana da ya
dakatar dashi ta hanyar janye ƙafarsa.
Kafaɗarsa Yah Abdurrahman ya dafa tare da faɗin.
“Afif kai namiji ne fa ya kamata ace kana da ƙarfin zuciyar da zaka iya yaƙi da komai.
Ya kamata ace zurfin cikin ka ya tsaya iya kan hakuri bakan abinda zai cutar da kai ba kana ya
cutar damu”.
Sai kuma duk sukayi shiru suna kallon Aryaan dake cewa.
“Akan komai dai ɗan Adam zai iya zurfin ciki mun shaida Afif nada zurfin ciki amma dai akan
wannan maganar in dai yana da gaskiya yasan ƙazafi akayi masa dole ya fito ya wanke kansa”.
Ya ƙare maganar da iya yaƙinin gaskiya yasan dole in dai Afif yana da gaskiya acikin maganar
dole ya fito ya wanke kansa.
Taj kam shiru yayi batare daya tanka kowa ba...
Dai-dai lokacin kuma Meymey ta shigo hannunta riƙe da Laylah da kuma sauran Matan Yah
Abana duka su huɗun suna shigowa Hajiya Babba tace.
“Ni yanzu ma an tabbatar da cewa shin akwai cikin?,ko yaya?”.
Cikin sauƙe nannauyan ajiyar zuciya Yah Hafiz yace.
“Batun ciki kam tabbas akwai shi domin likitoci sun gwada an gani cewa akwai ciki harna wata
2”.
Cikin sauri Ummu Aryaan tace.
“Aje dai asake gwada wa shine kawai abinda yafi dacewa”.
Cikin sanyi Meymey dake zaune a gefen Mom Amal tace.
“Wani gwaji kuma ya rage Umma? ai ba gwajin daya rage, likitoci nefa sukayi gamayya a kan
gwajinta kuma suka tabbatar da cewa tana da ciki.”
Kai Ummu Aryaan d’in ta girgiza tare da cewa.
“Ai shima Taj ɗin likita ne yaje ya gwada da kansa a tabbatar mana”.
Cikin sauri Meymey tace.
“Toh Umma in dai da kansa zai gwada ai bazai taɓa fadar gaskiya ba, tunda yasan abinda yake
tafiya, nifa nasan cewa shi ya aikata duk wannan abun kuma shima ya sani.”
Cikin taɓe baki Aryaan ya karbi maganar ta hanyar cewa.
“Toh dama ya za'a yi wanda ake tuhuma ya zama shine mai yin gwaji? kamar fa Shari'a ce ace
an bawa mai laifi alƙalanci, kawai Idan ba'a yarda bane sai asake tafiya wani waje aje a gwada”.
Cikin sauri Yah Yusuf yace.
“Toh shikenan asake ayi wani gwaji a tabbatar”.
Asanyaye Yah Abdurrahman yace.
“Toh shikenan bari na haɗa ku da abokina Dr Sonail Khan ɗan Indi'a ne amma anan yake aiki ”.
Amsawa sukayi saɓanin Tajj da har zuwa lokacin kansa ke k’asa, bayan ciwon da yake ji acikin
zuciyarsa ya gaza iya cewa komai, dan har yanzu ganin abun yake kamar acikin mafarki.
Meymey, Laylah, Yah Abdurrahman, da kuma Khabeer tare suka tafi asibitin.
Bayan awa uku da tafiyarsu suka sake dawowa dai-dai lokacin kuma anyi sallar la'asar bayan
sun dawo sun zauna Kabeer da takardun gwajin ke hannunsa ya miƙawa Yah Abana tare da
cewa.
“Gashi fa tabbas akwai ciki har na tsawon watanni biyu”.
Azuciye cikin b’acin rai me tsanani Yah Abana ya wurgawa Tajj takardun, cikin k’unan zuciya ya
kuma cewa.
“Menene gaskiyar waɗan'nan takardun?Tajuddeen me gaskiyar wannan abin? Me dalilin
faruwan haka? Waye Uban cikin nan?”.
Ya jero masa duka tsauraran tambayoyin ajere Akuma lokaci ɗaya.
Shiru ya kumayi kamar yanda ya saba saboda bazai iya cewa komai ba.
Saidai jin ya sake jero mai tambayoyin a hargitse ne ya sashi buɗe baki hankali yace.
“Kayi haƙuri ya Abana”.
Kusan duk a tare suke kallonsa cike da fara karaya.
Ita kuwa Meymey kai ta girgiza alamun.
“Toh kun ji dai”.
Zazzafan Iska Yah Abana ya furzar daga bakinsa kana akausashe yace.
“Tunda baza ka iya magana ba ka fita bana son ganinka!”
Ahankali ya yunƙura kana lips ɗinsa na rawa cikin wani irin yanayi me wahalar fassaruwa yace.
“Yah Abana kayi haƙuri ka gafarceni”.
Idanu Yah Abana ya rumtse tare da nuna masa k’ofa rai b’ace yace.
“Ka fita sai lokacin da kasamu hujjoji abakin ka kazo ka faɗa min”.
Jikinsa ne gaba d’aya ya d’auki rawa cike da tsananin ruɗani ya miƙe ya nufi hanyar fita.
Yana fita kuwa Ummey tabi bayansa da sauri, tare da riƙo hannunsa murya araunace tace.
“Ina zaka je Afif?”
Kansa dake masifar ciwo ya d’an girgiza kana cikin mawuyacin halin da yake ciki murya can
ƙasan maƙoshi yace.
“Zan tafi gidan Addawa”.
Numfashi ta fesar cikin tsananin tausayin d’an nata tace.
“Toh ai itama Addawan tana nan bari in mata magana sai ku tafi tare, kaci abinci ma kuwa?”.
Kansa ya girgiza cikin lumshe idanunsa ahankali yace.
“Bana jin yunwa".
Addawa kuwa jiyo maganar su ne yasa ta fito, tare da bin bayanshi suka shiga mota suka tafi...
Ummey kuwa direct parlorn ta ta koma sai kuma ta kalli Rashida dake cewa.
“Ummey yayi magana”.
Kai ta girgiza tana kokarin maida hawayen dake kokarin zubo mata tace.
“Um-um baiyi magana ba Rashida, sai haƙurin da yake badawa dake tayarmin da hankali,
Abban ku kuma naga bai fuskanci lamarin nan da fuskar daya kamata a ɗauke shiba yanzu
cewa ma yayi baya son ganinsa”.
Da sauri Aunty Maryam ta girgiza kanta tana maimaita kalmar “Allahumma Ajirni Fii musibati wa
akhlifliy khairan Minha!”
Ummey kuwa araunace ta cigaba da cewa.
“Yace ya fita ya bashi waje In har ba zai yi magana ba, yayi maganar nan kamar ya manta waye
ne Taj kamar ya manta menene halinsa mutumin da tun yana karami baya iya In-kari”.
Atsorace Aunty Maryam ke kallonta cikin tarin damuwa kuma tace.
“Toh yanzu Ummey ya zamuyi?”.
Cikin sanyi Ummey tace.
“Yanzu sai dai ku tashi kuje gidan Alaramma Sulaiman tunda ni kona tambayi Abbanku bazai
barni in fita ba, kuje kuyi masa bayanin ga abinda yake faruwa inada yakinin shi kaɗai ne zai iya
fahimtar da Abbanku wani abu, dan na fahimci Uncle Jibril bazai taba bincike akan duk
maganar da Meymey take faɗa ba”.
Kai Aunty Maryam suka gyaɗa daga nan suka fita suka tafi kai tsaye gidan Alaramma Sulaiman
suka tafi wanda shine Aramman Mahaifinsu mai ja musa baƙi suna tafsir bayan sunje gidan
suka masa bayanin iya abinda suka sani.
Da kansa ya rakosu har bakin mota yana mai jaddada musu cewa in sha Allahu da daddare zai
zo su gana da Yah Abana.
Da daddare Alaramma Sulaiman yazo bayan sun zauna da Yah Abana bayanin da Yah Abana
ya masa da yanda Taj yaƙi yin magana sai jikinsa yayi sanyi hankalinsa ya tashi Yah Abana
kuwa ya ɗaura da cewa.
“Kwanan nan fa da Afif yai tafiya Nigeria yarinyar ya ɗauka kwana goma fa sukayi da ita kafin
suka dawo, na gaya maka cewa acikin lamuran Taj akwai alamun ayar tambaya?”.
Idanunsa ya runtse yana jin wani irin ɗaci acikin azuciyarsa kana ya cigaba da cewa.
“Sannan koda nasan tabbas Taj yana da zurfin ciki acikin al'amarin nan kamata yayi ya fito ya
wanke kansa asalima Taj sai shiru yake duk abinda na tambayesa sai yace bai sani ba ko yace
wai inyi hakuri me haka yake nufi kenan? Taj ya gama ɓata min sunan zuri'a ya gama tozartani
ya gama cimin zarafi kana ya ƙasƙantar min da zuri'a”. Cikin sauri sheik Sulaiman yace.
“Kada kace haka ka bari sai an tabbatar da komai kayi magana akai ”.
Kansa ya girgiza yana mai jin daci azuciyarsa yace.
“Wani tabbaci ne ya rage?na rasa ta ina zanbi in samu tabbacin da zan iya gamsuwa dashi”.
Haka dai sukayi tattaunawar suka gama bayan Alaramma Sulaiman ya sake tunarsa dashi
amma duk da haka basu gano bakin zaren ba...
Wasa gaske haka aka ɗauki tsawon kwanaki biyar ana ta gumurzu Taj ya kasa wanke kansa
kana Meymey babu abinda take sai ƙara jaddada cewa shi yayiwa Laylah ciki.
Ahankali ya shiga cikin gidan yana mai sauke zazzafan Ajiyar zuciya yau kwanansa biyu bai zo
gidan ba saboda koda yazo mahaifinsa daga gaisuwarsa da yake amsawa babu wata magana
da take sake haɗa su.
Ahankali ya ƙarasa shiga Falon Yah Abana zaune ya samu Hajiya Babba agefensa kasancewar
yau girkinta ne bayan sun gaisa ne ya ɗan kallesa kana yayi kasa da kansa tare da cewa.
“Yah Abana zan ɗan yi tafiya akwai Passenger da zan ɗauka daga nan Ethiopia zuwa Malaysia
kwana biyu zanyi.”
Ɗagowa yayi ya kallesa cikin tsuke fuska ya kawar da kansa gefe tare da nuna mishi hanyar
fita.
Jiki amace ya miƙe ya nufi hanyar fita sai kuma ya juya jin Hajiya Babba na cewa.
“Allah ya kiyaye hanya Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya”.
“Ameen”
Ya amsa kana ya fice, kai tsaye Airport ya nufa ɗakin da za'a masa gwaje-gwaje ya nufa gwajin
farko da akayi masa kuwa aka samu jininsa ya hau 180 kana ga tsananin masifar ciwon kai ga
kuma zuciyarsa dake harbawa da k’arfi, atak’aice dai matsaloli kusan guda biyar aka samu a
tare dashi wanda hakan yasa dole aka soke tashinsa da jirgi wanda dole baza a iya barinsa ya
tafi da Passenger ba nan dai aka bashi magunguna kana Driver’n sa ya maida shi gida.
Har sun kusa gida ya kalli Abu Hashim tare da cewa.
“Ka kaini gidan Addawa”.
Kai Abu Hashim ya gyaɗa tare da nufar gidan Addawa.
Taj na shiga kiran Ishmah na shigowa wayarsa yana ɗaukar kiran kuwa tace.
“Taj”.
Murya sanyaye yace.
“Na'am”.
Cikin tarin damuwa tace.
“Kayi min bayani, gaba d’aya ka sauya cikin kwanakin nan guda biyar zuwa bakwai na kasa
fahimtar ka, sannan ka kasa yimin bayani, Tajj ya kake son inyi da rayuwata hankalina ya tashi
zuciyata ya kasa kwanciya kayi min bayani”.
Cikin sanyi ya girgiza kai tare da taune lips ɗin sa cike da b’oye ciwon da yake ji aransa yace.
“Ma'eesha ba komai ki cigaba da yimin addu'a kinji ko?”.
Kai ta gyaɗa kamar yana agabanta kana murya na rawa tace.
“Toh In sha Allah, amma ya jikin Laylah kwana nawa baka haɗani da ita ba”.
Iska mai zafi ya furzar daga bakinsa gami da cewa.
“In sha Allahu zan haɗaki da ita”.
Asanyaye tace.
“Toh shikenan”.
Washe gari ya kasance ranar Laraba,kamar yanda akasani gidan a cike yake saboda kiran
Family meeting da Malam yayi na gaggawa. kamar yanda aka saba gaba ɗaya family’n sa
dake state ɗin in dai jumma'a ko ya kira taron gaggawan nan gidan suke zuwa maza da mata.
Daidai lokacin da za'a gabatar da Sallah azahar Taj ya tashi daga sahun farko da yake ya kara
matsawa gaba sanin cewa muddin yana ƙasar shi yake jansu sallar Juma'a madadin mahaifinsa
da kuma kamsutSalawat a masallacin su na gida.
Sai kuma ya danyi sauri yaja da baya ganin Yah Abana ya ɗaga masa hannu alamar ya tsaya
ahankali ya koma ya tsaya a sahun farko.
Yah Abana kuwa da kansa ya tada iƙama akayi sallar azahar, bayan an idar da sallar duk gida
suka koma Taj kuwa gidan Addawa ya wuce.
Acan gefen gidan Yah Abana kuwa gaba ɗaya yasa Iyalansa suka taru kasancewar Meymey
bata zoba yasa Yah Abana ya kalli Kabeer kasancewar shine karami atausace yace.
“Kabeer je ka ɗauko min Laylah da Meymey.”
Kai Kabeer ya gyaɗa cikin sauri tare da ficewa ya nufi Parking space...
Motar Kabeer na ƙoƙarin fita na Taj na shigowa cikin gidan ahankali ya fito daga motar bayan
Abu Hashim yayi Parking hannunsa na riƙe da wata sanda me kyau wanda Sheikh Taju Usman
Bauchi ya bashi zuwansa Nigeria yana shiga cikin gida direct Falon Ummey sa ya wuce zaune
ya sameta tare da Yayunsa har Aunty Halima wacce itama ayau ta taso tazo saboda sun
fahimci kiran taron baya rasa nasaba da ɗan uwansu.
Ganinta yasa ya fesar da numfashi kana cikin yanayin sanyinsa yace.
“Aunty Halima me ya kawo ki Lafiya kuwa?”.
Cikin shesh-sheƙan kuka mai cike da tarin tausayinsa tace.
“Taju ka manta kenan?
Tambayata ma kake lafiya?,ka mance halin da muke ciki?”
Adai-dai lokacin kuwa Falon Yah Abana cike yake da ƴaƴansa jikokinsa da kuma Uncle Jibril da
Momyn Meymey saura Meymey sannan Laylah, da kuma Khabeer had’i da ahalin Ummey.
Cikin hakane Aryaan ya shigo falon Ummey tare da cewa.
“Ummey Abba yana neman ku”.
Kai ta gyaɗa kana suka miƙe suka bi bayan Aryaan suka shiga dai-dai lokacin kuma motar
Kabeer dake dauke da Laylah da Meymey yayi Parking.
Yah Abana kuwa hannu ya d’aga tare da nunawa Taj gabansa alamar yaxo ya zauna yayin da
baki d’aya sauran ƴaƴansa kowa yana inda yake.
Dai-dai lokacin kuma Meymey, Laylah da kuma Kabeer suka shigo falon.
Da hannu Yah Abana ya nunawa Meymey da Laylah tsakiyarsu kan su zo su zauna.
Suna zama Yah Abana ya ɗago kansa ya kalli Taj tare da cewa.
“A yau ɗin nan awannan lokaci nake baka dama ta ƙarshe Akuma yanzu ka buɗe baki kayi min
maganar da zan fahimta zan gane.
Wannan itace dama ta ƙarshe da zan iya baka a rayuwata ka faɗa min me gaskiyar abinda ke
faruwa ya akayi Laylah take da ciki”.
Idanunsa da suka kuma yin jawur ya rumtse tare da d’an jijjiga kansa, cikin sanyi had’i da
bugawar zuciya ya jujjuya kansa tare da faɗin.
“Yah Abana kayi haƙuri ban sani ba….”
Jin abunda yace ne kuma yasa baki ɗaya hankalin Ummey, Aunty Rashida, Aunty Maryam,
Aunty Halima, da kuma Zakiyya ya tashi sosai, cikin kid’ima had’i da gigituwa suke kallonsa
hawaye na zuba a idanunsu.
Yah Abana kuwa kallonsa ya mayar kan Meymey dake zaune cikin tsukakkiyar fuska yace.
“Meymey me kika ce ranan?”
Baki ta bud’e cikin zubda hawayen munafurci tace.
“Abbah wallahi Yah Afif shi yayiwa Laylah ciki”.
Cikin sauri Hajiya Babba tace.
“Toh me hujjarki Sannan menene Shaidar ki?”
Cikin shesh-sheƙa ta yi wa Taj da kansa ke ƙasa wani irin kallo kana tace.
“Ina da hujjoji da yawa da kuma shaidu”.
Lokaci d’aya Yah Abana cikin rashin walwala had’i da tsuke fuska yace.
“Menene shaidun ki?”
Tana goge hawayen dake zubo mata tace.
“A tambayi ita Laylah ɗin”.
Da sauri Yah Abana ya juya ya kalli Laylah sai kuma ya maida kallonsa ga Taj.
Taj kuwa juyawa yayi yana kallon Laylah haka zalika duk wanda ke cikin Falon Laylah yake
kallo.
Sabanin Momyn Meymey data zubawa ƴar Tata Idanu tana mai Binta da wani irin kallon
tuhuma.
Laylah kuwa kanta ta sunkuyar ƙasa.
Cikin murya mai cike da damuwa da tsantsar tashin hankali daya bayyana asaman fuska Yah
Abana ya kalli Laylah tare da cewa.
“Laylah”.
Kanta a ƙasa tace.
“Na'am”.
Sake kiranta yayi amsawa tayi batare data ɗago kanta ba.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya ya sake kiranta akaro na uku