Showing 12001 words to 15000 words out of 82249 words

Chapter 5 - A DAREN FARKO COMPLETE Book by Rabi'atu Nasidi Abubakar .pdf

yawa sannan yaran danake
dasu ba kowane yakeda amana ba, sannan ina
samun matsalar rashin masu sa ido a kan
abubuwa dukda kokarin danake da ganin na basu
hakkokinsu gudun samun matsala irin wannan
toh amma matsalata ba za tasa in ki taimakon
al'umar musulmi ba, na hakura da amfanuwar da
kasuwancina zaiyi dakai kaje kayi wannan karatu
don ka taimakawa al'ummar musulmi 'yan
'uwanmu.
Mama tace "to amma abba kafin yatafi yanada
kyau yayi aure yatafi da matar ko?
Dr. khalifa tadafe 'kirji tare da fiddo ido yace
"aure mama? sghekaruna duka duka ashirin da
biyu ina ni ina maganar aure? don Allah karki
'kara wannan maganar mama ni tun da nake ma
ban ta'ba ganin wata mace da zuciyata ta ta'ba
so ba, wadda har nakejin zan iya aure.
Mama ta ta'be baki tana harararsa tace "kai da
Allah rufe mana baki ni za kacewa ba wata mace
daka taba so, duk 'yammatan dake biyoka har
gidan nan ba 'yan matanka bane? kokuwa kana
zaton ba ni da masaniya kan abinda kake?
Yalangabar dakai yace 'Alah mama ba budurwata
ko daya aciki? su duk wacce kikaga ta zo gdan
nan nemana kawata ce ina nufin abokan karatu.
Abba yayi murmushi yace "to ko ma dai meye za
katafi germany a haka ba tare da aure ba amma
idan Allah ya dawo dakai lafiya za ka yi aure
insha Allahu ka fahimta ko?
Kansa na kasa bai ce komi ba shi kan baya so ko
zancan aure a yi masa don ba batun soyayya a
gabansa ama batun kawaye wadanda ake debe
kewar rayuwa dasu ai babu wadda babu.
Bayan fitar khalifa abba yabata rai yana kallon
mama yace "ba na son kina matsawa yaron nan
kan batun aure tunda ba shi da ra'ayi har 'kwara
nawa khalifan yake da za ace dole sai ya yi aure.
Mama tace "Alhaji ai kaine dai bakasan abinda ke
faruwa ba, dukiyar daka sakarwa yaron nan tasa
yanayin abinda duk yaga damar yi masa auren
shi ne abinda yafi dacewa.

Ya kara tsuke fuska yace "ni fa ba na son zargi
irin wannan muci gaba da dagewa da addu'ar
damuke masa insha Allahu Allah zai tsare mana
shi.
Tace "shikenan alhaji kuma bayan haka kana
sane da maganar yarinyar nan zainab tana
matukar son khalifa amma 'ki'ri'kiri yake nunawa
ba ya son ta ka ki yin wani abu a kan wannan
maganar dakayi inason kabani goyon baya ne don
ayi auransu da zainab har kunyar mahaifiyarta
nakeji yadda fa yake d'angata itama 'yar gata ce
mahaifiyarta na sonta kaga......
Abban yace "Don Allah kihutar da bakinki da
fad'in abinda ke kanki kinsan ba zai yiwu ba.
Daman na ce miki mahaifiyar zainab ba ta son ta
ne, kokuwa kin ta'ba ganin wanda yahaifi d'ansa
yace ba ya so? kawai dai kud'i ake nunawa da
so? kinfi kowa sanin cewa ba zan ta'ba
tursasawa d'ana auran matar da ba ya ra'ayi ba
don muna da dangantaka da iyayanta, kamar
yadda nima ba zanso a tursasawa wata d'iya ta
auri khalifa ba alhali ita ba ta so.
Inaso idan khalifa yatashi aure ya auri matar
dayake matukar so itama tana matukar sonsa,
insha Allahu zanyiwa khalifa bikinda za a jima a
garin nan ba a ga biki na d'an gata irin sa ba.
Farin cikina da kwanciyar hnkalina bai wuce
auran soyayya bane don hka idan khalifa yanason
zainab zai aureta a lokacin daya nuna yana son
aure, idan kuma ba ya sonta zai auri wadda yake
so ne bbu dlilin dazaisa don tana son shi ace
dole sai ya aureta, hkan na nufin ita an mata
adalci shi kuma an tauye masa hakki nsa knan?
Tace "shknan ya wuce.
A DAREN FARKO
8
Ummi d'iya ce ga Hajiya Hauwa yayar Abba
wadda take bin babbar yayarsu Hajiya jummai
duk da cewa kafin tasowar ummi hajiya Hauwa
ba sa shiri da mama don tana cikin masu zakewa
'yan gaba gaba a kan sai abba ya yi aure tunda
ita maman ba haihuwa take ba, in banda hajiya
jummai datafi karfinsu ita kuma tana matukar son

mama sbda kirkinta yayin dasu hajiya hauwa gani
suke duk kirkin dasu jummai ke cewa tana dashi
na kissa ne da munafunci don ta mallakesu su da
d'an uwan tare dacewa babu abinda alhaji
muhammadu ba ya musu hatta saudiya shi yakai
hauwan ita da mijinta kasancewar duk cikin 'yan
uwan nata ma itace ta auri mai karamin 'karfi sai
dai tsananin soyayya, kayan abinci da kudi akai
akai yake musu aike dukda haka hajiya hauwa ba
ta gani kawai sbda ba ta son matarsa hajiya
maijidda, yan biyu hajiya hauwa tafara haifa
sannan tahaifi wani namijin mai suna
Abdulrasheed tahaifi wasu 'yan biyun su kuma
mata ummi ce d'iyarta ta biyun 'karshe inda taci
sunan mahaifiyar abbansu ake cemata ummi
daga ita sai dan autansu umar.
Hajiya hauwa na matukar son ummi
kasancewarta mai halayya irin ta ta, tun tana yar
karama take abokiyar shawara gareta ,ba laifi
itama tanada kyau da d'an gwargwadon abinda
yasa ake dad'a ganin kyaun ummi bai wuce
yanayinta ba da kuma bkin tsiwarta tsiwar kanta
tan yi mata kyau, tana burge mutane da dama.
Bata fiye zuwa gdan abba ba sai ana wani
sha'anin sbda ba shiri take da mama ba, tanada
d'abi'ar duk wanda hajiyarsu bata shiri dashi
itama baza tayi shiri dashi ba, tana biyewa ra'ayi
da son zuciyar hajiyarta shi yasa ra'ayinsu ya zo
d'aya.
Ummi na aji hud'u na secondary Allah yayiwa
mahaifinsu rasuwa kuma a gun zaman makokin
ne wata irin soyayya tashiga zuciyar ummi da Dr.
khalifa farat d'aya a lokacin ummin shekarunta
goma sha shida kacal a cikin 'yan maan ma bata
ri'ka ba shi ne lokacin dasuke tasawa.
Ranar da aka kwana bakwai da rasuwar suna
zaune a d'akin hajiya hauwa ita da babbar
aminiyarta kuma makotansu wato jidda khalifa
yashigo tare da sallama fuskarsa a tsuke yake
amsa musu gaisuwa yace "ina hajiya? "
Jiddah tace "tana gaisawa da ba'ki a sit room
d‹in baba.
Yace "to idan ta fito kice mama ta ce maganar

sa'kon nan zatayi mata waya yanzu dai bai samu
ba ni sauri nake ba zan iya jira tafito ba.
Bai saurari abinda za suce ba ya fice su ma
basuyimagana ba ya ga toh dasuka hada baki
suka fada lokaci guda.
Bayan Fitarsa jiddah tadubi umi tana murmushi
tace "Oh ni tunda nake ban taba ganin mutum
mai jin kai da isa irin yaya khalifa ba ko dan yana
ganin ya had'u ne.
Ummi tayi ajiyar zuciya tace "lallai kam ba abinda
yake sashi ta'kama wanda yawuce haduwarsa sai
kuma dukiyar mahaifinsa wadda yake takama da
ita kina ganin duk tsadar mota khalifa zai hauta
da zarar an shigo da mota sabuwar yayi 'kasar
nan komi tsadarta abbabnsa zai siya masa ya
hau, kuma dan wani karin jin kai da alfahari ma
ba zai yawo a mota d'aya ba sai ya jera motoci
goma yana tsakiya tare da abokansa yana homa
daga bisani ne surutu yayi yawa a dangi da
abokan abbansa ya tsawatar masa a kan yadaina
fita da motoci da yawa haka shi ne yanzu yake
fita da motoci biyu ko uku.
Jiddah tace "duk abinda yayi ya yi daidai don ya
isa yayin, ni kam yaya khalifa yana matukar
burgeni ina mai ba ki shawara ummi in har za ki
iya shiga zuciyarsa kada kibari ya subuce miki.
Ummi tayi ajiyar zuciya tace "jiddah kin san dai
yaya khalifa kuma kinsan yadda rayuwarsa take,
nima kinsan gwargwadon wayewata da fahimtarki
da rayuwa kina ganin zan iya shiga xuciyarsa ina
nufin kina ganin ina da nagartr da zai so ni?
Jiddah tace ummi kina da kyau kuma kina da
wayewa, meye zai gagareki idan kika bar wannan
damar tawuce miki za kiyi nadama.
Ummi ta jima tana nazari kanta na 'kasa tace
kada kijefa min damuwa a zuciyata kan abinda
samuwarsa gareni zaiyi wahala.
Jiddah tace "idan kika sa wa zuciyarki damuwa
akan samuwar khalifa gareki to lallai wahala zai
zame miki, yayin da idan kika sa wa zuciyarki
abu ne mai sauki mai sauki ne kada kidamu da
jin kan yaya khalifa ko haduwarsa da takamarsa
kina da hanyar da za ki iya mallakar zuciyarsa

cikin sauki mata irinmu da ba mu da alaka ta jini
tsakaninmu shi ne zai mana wahalar samuwa ke
kuwa uwa daya uba daya iyayanku suke gdanku
gdansu ne haka gdansu gdanku ne, kitashi tsaye
ki mallaki miji na fita kunya mijin da za a iya
shiga dashi ko ina a kalleku bayan kyau ga dukiya
ga uwa uba ilimi ba jiya kikace min zai tafi
germany karatun likita ba?
Cikin sanyin murya ummi tace "jiddah na yi
mamakin wannan magana ta ki sai jace kin shiga
zuciyata, wlh jiddah tun kafin in mallaki hankalin
kaina insan waye namiji insan menene so nake
matukar so da sha'awar yaya khalifa duk sanda
na ganshi nadinga kwatantashi a matsayin mijina
abinda yas nakasa kusantar kaina gareshi sbda
miskilancinsa kina gani ko gaisawa akayi sama
sama yake amsawa, ban taba gaida khalifa ya yi
min murmushi ba al'amarin har tsoro yake ba ni,
amma khalifa shi ne nakema son dana tabbTar
babu wani d'a namiji da zanwa ko da rabin son
danake masa, tabbas a wannan rana kin fama
min inda ke min 'kai'kayi a da na kwantarwa da
zuciyata soyayyarsa dake raina amma yau kin
tayar min da ita insha Allahu sai inda karfina
yakare xan nemi soyayyar yaya khalifa bakin raina
zanyi duk abinda zan iya don ganin na mallake
shi ba zanyi sakaci wata d'iya mace tarabani
dashi ba ko ta halin 'ka'ka.
Tami'ke a hankalin ta tsaya gaban madubin dake
bango tana kallon kanta tun daga sama har kasa,
doguwar rigace a jikinta wadda tafito da zahirin
suffar jikinta, gashin kanta ya sauka har gadon
bayanta, kamar yadda take doguwa mai kyau siffa
tana daga cikin abinda yake dauker hankalin
maza tare da ummi shi ne gogewar fatarta, ba
fara bace 'kal 'kal amma tana da haske sosai,
fuskarta tanada daukar hankalin mai kallonta,
sannan tana da daukar dressing in dai za tasa
kaya sai sun amsheta sbda ba zai yiwu tasa
kayan dabasu dace da kalar jikinta ba, haka duk
d'inkin dazatayi sai ta tabbatar zaiyi mata kyau
sbda ita Allah ya yi ta da iya zabar kaya dan shi
kanshi telanta daban ne shi yake mata tsala

tsalan dinkuna nagani, duk kayan daza tasa sai
an tabbatar an yi matching dan a birge ai kuwa
tana birgewar, ko a salon iya tsara magana aka
tsaya musamman ummi za tatafi da imanin
mutum yatsaya yasaki baki yana kallonta yadda
za kaga tana tsara xance daya bayan daya mai
shiga cikin wannan ne yasa takeda mutane a gida
da makaranta, hatta malamansu sun santa kan
tsananin iyayinta da son gayu duk kudin da
hajiyarta tasamu akan sayawa ummi sutura mai
tsada da kayan kwalliya suke tafiya kowanne kya
sai an hada mai mayafi, takalmi da fashion don
ace dai an yi kyau.
Ummi tana matukar jin kanta ba kowani d'a
namiji take kulawa ba duk da dumbin masoyan
dake nuna mata zahirin kauna ba wani d'a namiji
daya taba burgeta sai yaya khalifa.
**************
Jidda ce kawai ta 'kud da 'kud kuma aminiya ga
ummi tun suna yara ba ajin kansu kasancewar
katanga ce kadai taraba gdansu kafin rasuwar
mahaifin ummi baida abokin shawara kamar
aminin daya wuce babansu jiddah shi ne dalilin
dayasa zumuncin na su yakara kwari, duka
makarantun dasuke zuwa guda uku a kowacce
rana duka ajinsu daya kullum tare suke wuni babu
abinda yake rabasu sai bacci, kullum shawararsu
daya banbancinsu shi ne jiddah ta fi ummi tanada
tsiwa da jin kai da raina mutane, yayin da jiddah
ke da girmama mutane da gudun zuciya.
Iyayan jiddah hamshakan masu kudi ne su biyu
suka haifa daga ita sai yayanta Habibullah wanda
yake kasar england karatu, itama jira suke
takammala secondary su fidda ita kasar waje tayi
karatun ta na jami'a dukda cewa ta ce babu inda
za taje sai fa in za a hadasu da aminiyarta ummi,
lokacin data fadi haka mominta ta yi murmushi
ne tace "jiddah manya, jiddah aminiyar ummi,
idan har ummi da iyayanta sun amince za ta
outside karatu mai zai hana dady dinta yabiya
mata insha Allahu indai kinga ummi baku tafi tare
da ita ba ,ita ko iyayanta suka ce ba za ta ba.
Cikin tsananin farin ciki jiddah tashigo gdansu

ummi dagudu ta isketa cikin dakin hajiya tana
kwance bisa gado tana karatun littafin hausa
tafisge littafin ta watsar tace "Albishirinki.
Ummi ta lumshe ido tace "kina burgeni jiddah
sbda koyaushe ina ganin ki cikin nishadi da
wahala mutum ya fahimci wata damuwa a
zuciyarki.
Tace 'hakane ummi ban cika sa wani abu a
azuciyata ba ballantana yadameni ina daukar
raywa da sauki dan kada in dami zuciyata zuwa
nayi in gaya miki insha Allahu idan mun gama
secondary tae za mu tafi outside karatu.
Ummi tayi shiru batace komi ba fuskarta ko
walwala babu ballantana tanunawa jiddah ta ji
dadin maganarta, itama jiddar gimtse far'arta ayi
tace "ummi yaya ni dana taho da batu mai dadi
gareki ina mai gaggawar yi miki albishir sai inga
fuskarki ta ahiga damuwa kamar wadda tazo miki
da labarin tashin hankali ?
Ummi tayi doguwar ajiyar zuciya tace "jiddah ba
wai farin cikine banyi ba ba yadda za ayi ayiwa
mutum albishir irin wannan yakasa farin ciki sai
dai inason kiyi hakuri jiddah na gode kwarai da
gaske da kaunar dakike min wadda tasa har kike
jin ba za ki iya tafiya wani gari kiyi rayuwa babu
ni ba, iyayanki suka amince miki akwai haka tare
Dacewa kudi za su kashe ba na wasa ba, babu
inda za ayi haka sai in akwai kauna mai yawa
kuma kauna wadda take ta gaskiya sbda Allah to
sai dai inda gizo ke sakar shi ne jiddah kiyi
hakuri, zuciyata ta yi nisan kiwo a cikin soyayyar
yaya khalifa, ba zai yiwu bayan kammala
secondaru din mu in bar kasar nan zuwa wata
kasa ba ba tare da na san matsayina a zuciyarsa
ba.
Ba tare dani ba duka hanyar da ta dace nabi don
in nemi soyayyarsa ba don in nemawa kaina
masauki na din din din a zuciyarsa.
Tagyara zama har yanzu idanuwanta na kallon
jiddah taci gaba da fadin "jiddah zuciyata tana
yiwa yaya khalifa wani irin so wanda ban taba
tunanin akwai irin son a duniya ba, ba zan iya
bayyana miki irin yadda nake jin ciwon sonsa a

zuciyata ba.
Kullum dashi nake kwana in tashi kullum
soyyayarsa karuwa take a zuciyata ban kuma
samu mafita ba akan yadda zan bullowa lamarin
har gashi tafiyarsa germany ta matso.
Tun a yanxu ban samu mafita ba inaga in yatafi
tafiyar dazata dauke shi shekaru hudu.
Ina matukar tausayawa rayuwata jiddah ban san
halin da zuciyata za takasnce ba yayin dana rasa
yaya khalifa.... .
Jiddah takamo hannunta cikin tausaya wa tace
"ki kwantar da hankalinki ummi in dai yaya
khalifa mijinki ne da izinin Allah za ki aure shi, in
har baki auri khalifa ba to Allah ne bai kaddara
aure ba ba za ayi ba, shi ne amfanin daukar
rayuwa dasauki.
Ummi hakika na san yaya khalifa miji ne abin so
gakowacce irin d'iya mace kowa cece ita kuwa,
ko ni kaina din nan abinda yasa nake nesanta
kaina daga burgewar da yake min na san ya yi
min nisa ne ba zan same shi ba, ke din ma
bansan za ki tsanantawa zuciyarki matsananciyar
soyayyarsa har tashafi duk rayuwarki ba, da tun
farko ban zungure ki da maganarsa ba, ko
dacewa kina sonsa daman chan a baya tun kafin
in tuntubeki da maganar amma tuntubar danyi
miki ita tajefa ki a wannan damuwar.
Ummi ina mai ba ki shawara ta gaskiya akan ki
dauki rayuwa dasauki duk abinda kika zafafa shi
zafi zaiyi gareki Kuma ba wanda zai dagawa hnkli
sai ke din.
Ki cigaba da fafutuka akan neman soyayyar yaya
khalifa har kiga kin aure shi amma dan Allah
kada kibari damuwa ta lalata miki tunani ki
dogara ga Allah sai komi yazo miki dasauki.
Ummi bata kara cewa da jiddah komi ba har aka
fara kiraye kirayen sallan magriba tayi mata
sallama takoma gdansu, dakyar tatashi tayi
sallah taci gaba da zama a daki kan daddumar
datayi sallah tana jan carbi tayi tagumi idanunta
sunyi jawur.
Hajiya hauwa taahigo dakin ta sha adon ta kamar
yadda tasaba kai bakace ita ta ajiye manyan

samari irin su hassan ba, mace ce mai son gayu
shi yasa ummi ke samun daurin gindin gayu da
kece raini a gunta.
Tayi sororo tana kallon diyar tata tace "ummi wai
lafiya kike kuwa kwana biyun nan kin sauya ko ba
ki da lfya ne?
Ummi tadago ido zuciyarta ba dadi tace "hajiya
zauna kiji wata magana.
Dasauri tazauna ummi tace "hajiya barin kashi a
ciki ba ya maganin yunwa, yau zan fayyace miki
damuwata dan kisamo min mafita a cikinta,
hajiya zuciyata ta kamu da tsananin son yaya
khalifa inaso kigaya min hanyar dazanbi yasoni.
Hajiya tadafe kirji tare da fiddo ido tace "ummi
kinsan maganar dakike fada kuwa? a duniya kirsa
wanda za ki so sai khalifa?
Kara gaya mini ko dai ba khalifan dana sani ba
kika ce kina so?
Ummi tamatso kusa dai tadora kanta akan
cinyarta tace "hajiya babu wani khalifa dazan yi
magana akansa wanda yawuce na mu ba zan iya
raba zuciyata da son sa ba kuma ba na bakin ciki
da son da zuciyata ke masa insha Allahu ba xanyi
nadama ba mafita ce ban sani ba ita nakeso
kisanar dani hajiyta.
************
Maganarta tadamu hajiya hauwa yau dai ba ta
son mahaifiyar khalifa haka shi kansa khalifan ba
kaunarsa take ba, a daran takira kanwarta hajiya
sauda wadda ita ke binta ko gaisawa bata bari
sunyi ba tace "saude tashin hankali ne ya saman
a daran nan.
Hajiya saude tace "har gabana ya fad'i "meya
faru yaya hauwa?
Tace "wai ummi tarasa wanda takeso sai wannan
yaron mai shegen girman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login