Showing 39001 words to 42000 words out of 54222 words
Chapter 14 - A'isha Humaira Hausa Novels Document complete .txt
muje mu ko
Hamma
Ni ban san gsrdama muje mu
Binsa ta dinga yi ya bude wani gida suka shiga ts juyo tana kallon sa a ranta tace ikon Allah
Daki ya shigar dakin ya sa ma dakin key yana kallon ta ita ma shi take kallon dan karin bayani take nema daga gurin sa
Biris ya mata ya shiga toilet dan yayi wanka zaunawa tayi zugum tana kallon kasa
Wayarta ta dauko ta kira amira taji ta a kashe bata da carji
Tsaki tayi yafi a kirga ya fito daga shi se towel ta juya masa baya ya bude drower ya dauko short da singlet ya zura ya fesa turare ya shafa mai me tsada ya kalleta ki je kiyi wanka
Ni ba wani wanka da zan yi gida xani
To nan a daji kike ?
To ni dai ksna ganin danuwana yaxo memakon muyi hira seka wani dauko ni nan
Kefa aisha naga alama baki da tausayi baki da imsni ko
Ni mena ma
Ba kya tausayina dubi yadda kike kiba ni kuma dubi yadda nake ramewa shekaru nawa ina kallon ki kawai kamar hoto bazaki ji tausayina ba ki bani abunda nake so ki maidani namiji ko!
Hamma ai ban da wannan karfin
Mtsw kin san Allah bazan barki ba yau ki gama tsaretsaren ki da kumbiya kumbuyiyar ki amma kin gama zuwa hannu
Yau sena amshi sadakina kums na nuna miki *sakomakon kauna*
Aisha humaira dai kawai kallon sa take yi kawai cike da mamaki
Da tsoron masdook din.
Ke banda abunki abunda kike gudu ai a ksn sa auren ya ta'allaka dashi ya dogara
Hawaye suka zubo mata a kuncin ta
Ki daina kuka muyi addu'a Allah ya barmu tsahon shekarun da zamu ga jikokkin mu
Kice amin.
Ta masa banza
Kinga ki je kiyi wsnka ki zo muyi sallah
_bayan wasu mintuna_
Wankan tayi tasa wata riga da ya bata ta fesa turare sallah suka yi ya ksma kanta ya mata addu'oi sannan ya mata tambayoyi
Daukarta yayi cak ya dora kan gado ya dinga raba ta da kayan jikin ta ita kam idan ta a kulle yake taki kallon sa se hawaye da take zubowa
Rungumeta yayi ya dinga aika mata da sakonni kala kala masu rikitarwa da rudarwa da rikita wanda ake yiwa numfashi kawai yake fitarwa ita kuma kuka kawai take dan ba karamin gurzuwa take yi ba a gun sa gaba daya ya gama kashe mata jiki tun dare ake sbu daya be barta ba seda yaji kiran assalatu shima dan sallah ba dan ya gaji ba
Da ya dawo ma gun ya sameta ya ita ko tunani take yi girman daren farko duk yadda zata fassara daren farko bazai fassaru ba wata irin kauna da soyayya da ba a taba sanin bil adama yana yiwa dan uwan sa bil adama ba,ita ce yau hamma ya nuna mata.
Tun farkon daren har zuwa karshen sa .
Ji tayi ya rungumeta a kirjin sa cike da wata kauna ,ta sa hannu tana goge hawayen ta ya na taimaka mata yana mata fatan alkhairi .
_ina son ki aisha humaira kin yadda ke din zuciyata ce ,my heart kin yadda?_
*a sanyayye ta amsa ,na yarda*
Murmusawa yayi ya dada rungumeta
Ta hankada shi
Dubi fa iriyar wahalar da ka ba ni ,kalli fa ciwon da ka mini.ni don Allah ka bari na warke .
Janyota ya dada yi gaskiya kam naga alama kin sha wuyar ,kiyi hakuri kin ji ko !
Ni nasan kina sona ni ne da wawa mara hankali dana tsaya wasa da damata se Allah ya rahamace ni ya fargar dani da mata ta gari ki yi hakuri duk wannan whalar na dan lokaci ne .
Ita dai kuka kawai take yi yace aa heart kukan ki bana so ni kadai nasan me nske ji in kina saukar da hawayen ki
To naji kai ni nayi wanka
Mu koma gida kafin a fara neman mu
Ta kuma fashewa da kuka ni ka cuce ni kowa yanzu ze san me muka yi ka bani kunya ba seka bari se mun koma kano ba
Ke baki da kirki wallahi in bari har se mun koma kano ai kafin lokacin ya rayuwata zata kasance?
Da wa zan kuma lulawa wannan duniyar maji dadin.?
Ta hararesa ,
_cike da shagwaba ta ce to ai ni bani da lafiya baka ga yadda nake ji ba_
To yi hakuri "oh!sorry,
Na gani ayi hakuri a yafewa masdook mijin aisha
Ranar se lallaba ta ya dinga yi ta shirya se azahar yace su zo su koma gida ta dinga surfa masa harara kamar idan ta ze sauko kasa
Yo in kin harari masdook ai kanki kika harara dan kin zama ni na zama ke kima bari kar a mana dariya a ce mun samu sabani saboda na amshi hakkina na shekaru daidai har shekaru bakwai da yan wattani ina fama da ke
Ya shafi mararta Allah sa a kokarin farko na samu na farke wasan dukan hannun sa tayi
_Ayi hakuri hajiyta my heart!_
[6:27PM, 3/14/2017] Kairat Up: ✨✨✨✨✨✨✨
*Aisha humaira*
✨✨✨✨✨✨✨
*Na*
*Khairat up*
*67*
Hajiya
Na'am ahmadu
Hajiya jibi faruk da mubarak zasu dawo fa ah alhamdulilahi naji dadi kace na fara shiri
Jikokina zasu dawo
Wallahi kuwa hajiya ina tunanin zan je gun aunty maryama na sanar mata seta zo ta taya ki wasu yan ayyukan ko kuwa
Ni ba wadda zata zo ta tari dana guda daya rak fa ehe ni da raina ba za a raba ni da dana tilo ba
Wai mardiya yaushe zaki yi hankali
Hajiya ina ganin girman ki kar ki shigo maganar da ba naki ba kin ji ko!
Mardiya wa ya baki izinin zuwan min gida?
Ta ja dankwalin ta gaba ta dan karkace yin kaina ne saboda naji dana zai dawo shi ne nazo na ji takamaimai ran da zai dawo
Ai baki da d'a a gidana!
Tayi shewa,weee ai ko kasuwa ta tashi dan koli dai ya ci riba
Mardiya in kin gama haukan ki kina iya bar min gida na ban yarda dake ba sabida haka yi waje kiyi ta shirmen ki na sani ko bayan fita ta ki lahanta min uwa
Lallai ahmad ban ga laifin ka ba
Ko ki fita kona sa a fitar min dake daga gidana
Dadin abun nima ina da gidan uba
Nagode da kika tuna da haksn seki fita wannan gidan ahmad ne
Tana kumbure kumbure ta yi waje ya yi sallama da hajiyarsa sannan ya fita.
Hajiya ta zauna zugum tana tunani can hawaye suka zubo mata Allah jikan *aisha humaira* yarinyar kwarai me kirki me girmama mutane Allah ksi haske kabarin ki ban da rabon kuma ganin ki amma ina sa ran insha Allah zan ga takwarar ki alfarmar annabi da qurani.
******
Ya faruk!
Na'am mubarak ya akai?
Ya faruk wato ina son muyi shawara dakai muhimiya
Ina jin ka ,
Ya faruk ina ganin in mun sauka a kano zan wuce katsina
Katsina?
Eh katsina
Me zaka yi a katsina?
Zan je gun yar'uwata ne
Amma dea ya muka yi da kai da abba ina cewa mun wuce gurin an bar maganar
Anyi haka amma zuciyata ta daure da yawa yanxu kuma ta.kai makura baxan iya jurewa ba ina son ganin yar'uwata kar na mutu ban ganta ba ko sau daya
Kana tunanin zasu amshe ka ? Zasu gane ka,ko ita xata maida ka wa?
Ya faruk duk ban san wannsn ba amma ina ji a jikina yar'uwata bazata kini ba kuma karfa ka manta jinin mu daya
Ya faruk nasan duk abunda ya faru kaddara ce wadda bawa baya wuce ta abba ma na son ganin diyar sa haka nima
Nima ina da bukatar ganin ta yadda take yar'uwar ka haka take nawa ba sai ka fada min cewa ciki daya kuka fito ba ko ka tuna min *a sanadin* mahaifiyata hakan ta faru
Aa yaya wallahi ban kawo haka ba kayi hakuri
To tare zamu je da kai saboda haka yau zamu yi booking gobe mu tafi yadda zamu yi kokarin komawa da wuri kar abba ya farga yace mun raina shi.
To amma ya xamu fara lalunben gidan?
Shi ne ai
Da sauri yace inna(maryama)
To ya zaka yi tambayar ta fada maka
Uhm shi ne matsalar
Why not mu tambayi baba sunusi
Owk
Wayar kawunun nasu ya kira bugu biyu ya dauka
Hello baba
Hello,faruk ya shirye shirye?
Lfy baba
To madallh baba dan Allah tambaya zamu yi
To Allah sa na sani
Baba dama ina nemsn kwatancen gidan su mama na ne
Amma mesa kk tmby?
Kawai amma in bazai samu ba...
Aa zan turo ma ta text
Tom baba ngd.
Meya ce?
Ze min text din adress din
To alhamdulilahi
Amma Allah sa kar ya fadawa abba wannan maganar amin dai .
**
Amira wai meya ke damun ki naga se amai kike kwana biyu lafiya dai ko
Eh nima dai ban san dalili ba kullim yanzu kasala bacci da amai da zazzabi duk ke damuna
Kin fadawa hamma?
Aa
To ki fada masa a duba jikin naki
Tom bara ya shigo
Aa ba wani bara na kira shi a waya nasan yana kusa ko hamma masdook
Ki barsu fa
Saboda me?
Saboda nasan meke damuna
Ah ah me ke damunki ?
Ciki ne dani fa
Wane irinc.....se kuma ta daka tsalle omg na shiga aljjana ciki oh dear na kusan zaman aunty
Bakin ta ta kulle mata ki daina ihu kar a ji
Aa to ai abun murna me bana tsiya ba
Na sani ina kunya ne
Tab baki ji kunyar daukar cikin ba se kunyar a sani
Ke fa dadi na dake kennan shakiyanci
To bazan fada ba amma zan gayawa my honey bee ya san maganin da za a baki
Kin fiya kafiya wallahi mstw
To naji
*****
Kamar yadda suka fada haka aka yi direct motar katsina suka samu shata su biyu kawai zuwa dikko har inda suke nema .
Tafiyar hour biyu ds rabi suka yi dake me motan gudun tsiya yake yi.
Basu sha wuyar gano gidan ba dan an san su sannannu ne ba boyyayu ba a unguwan.
Su baffa na gona su kuma mazan suna waje dam basu koma gun aikin su ba
Faruk da mubarak suka karasa da sallama
Wa'alaikum sallam
Dan Allah nan gidan mal.mubarak dikko ne?
Eh nan ne kunzo daidai dui jikokin sa ne a nan
To alhamdulilahi mu baki ne
Ai naga alama inji nas
Yanzu gunwa kuka zo dan shi mal din ya rasu tuni sede matar sa *(dada)*
Eh gunta muka zo
To bara na mata iso.
Shi ko yusuf kallon sa kawai yake yi se mubarak yace ina ni'imatullahi?
Gashi nan shi ne ni'ima
Kawai murmushi yayi nas kuma ya shiga gidsn dan fadawa dada tana da bako
Salamu ailkum
Wa'alaikum sallama
Kai nasiru ya akayi tsohuwa gunki nazo kinyi samari a waje sun zo zance
Jefan sa tayi da dakuwa dan banza su wsye samarin kasan cewa ni din ma fa yar gayu ce
Ah sossea ma kin samo gredin samari
Cene su shigo mana kun barsu a waje dan shashanci
Au daga abun arziki
Ku shigo
To ya raka su har bangaren da dada take tana lazimi ne dama
Yana shiga kawai tsayawa yayi ki kam.yana kallon ta
itan ma shi take kallo
Takalminsa ya cire ya shiga ciki kawai dada ya rungume yana kuka
[6:27PM, 3/14/2017] Kairat Up: [21:30, 01/03/2017] Khairat: ✨✨✨✨✨✨✨
*Aisha Humaira*
✨✨✨✨✨✨✨
*na*
*khairat up*
*70*
*_daga fadar_*
*Hikima writers _*
*_association_*
_wannan page din na ko wanne masoyin aisha humaira ne_
A haka suka koma gida dakinta ta shiga ta samu ta kwanta daga baya kuma zazzabi ya kamata me zafi sossea ita kanta dada bata yi tunanin ta dawo ba tana gun wata kawarta me kalwa a makota
Da kan shi ya shigo bangaren dada ya leka ba kowa ya kara gaba zuwa cikin dakin ta a kwance ya sameta a rufe da bargo jikinta se rawa yake yi.
Jikin ta ya taba yaji zafi rau tsabar zafi taba jikin yayi subahanallahi my _heart_ ya haka naji kina zazzabi
Bata ce masa komai ba se kuma hawaye suka zubo mata ta juya masa fuskarta a ranta tace *kai ka jawo*
Bara ina zuwa dakin sa ya koma ya dauko firat aid ya xo ya auna zazzabin yaga ya kai 120 ya zare idan sa ya kuma aunata da kyau
Bara na samo miki magani kinji
Uhm kawai tace masa yana fita ya hadu da mardiya matar hamma isma'il
Ina zuwa baban mama?
Wallahi humaira ce bata da lafiya zan je chemist na siyo mata magani zazzabi take
Wayyo ina dada?
Dada bata nan
Bara naje to.kamin ka dawo
Da kin kyauta min.
Dakin ta shiga ta sameta sannu aisha sannu kin ji?
Uhm
Meya sameki ne haka
Adda ba komai *(kina ganin ina zazzabi zaki wani tambayeni meya faru)*ta fada a ranta.
Be jima ba ya dawo ya mika mata madarar youghrt bata ta sha se ki bata maganin nsn ta sha
To me baban mama
Ya fice ina zuwa.
Maganin ta kalla ta kalli humaira wai kina nufin se yau?
Hararta tayi a fakaice
Ungo ki sha bara na samo miki dettol da ruwan zafi ki shiga
Ni baxan wani shiga dettol ba yana da effect
To sena sa miki gishiri zaki ji dadin jikin ki
Komai ta hada mata ta shiga ruwan kina yi kinji se gurin ya warke
To adda
Bara naje na turo miki su amira dan basu san kin dawo ba
To
Ki dan ce ma hamma ya kawo min kifi kiyi mini farfesun kifi kinji?
To bara na duba ko yana nan.
Basu jima ba suka shigo dakin amira tana ganin ta tunsurewa tayi da dariya lallai yau bakin wata ya mutu amma hamma ya burgeni yau ya amsa hakkin sa
Cikin rawar murya da kyar tace zan baki amsa duk sanda na samu sauki adda kuma gulma mtsw ni ku fita ma kawai
Tohm.
***
Da daddare suna hira a dakin tsakar gida dake waje maxan su da matan su tare da kamal yana bawa mubarak labari shi ko faruk yana danna computer din sa
Mubark ya ga yadda aisha ke harar masdook shi kuma yana folding din hannun sa alamar tayi hakuri murmushi yayi kawai duk da yana son magana da ita su biyu kawai
Ya gyara murya hakika naji dadin ganin dangina masu hadin kai da sanin ya kamata tabbas nayi.rashi amma ina sa ran da izinin Allah duk abunda na rasa zan same shi a iya dan lokacin nan
Amma gobe zamu.koma kumo
Aisha ta kyabe fuska hamma zaku koma kuma bamu fara hira da kai ba bamu ma xauna ba fa
Eh kamawa tayi kanwata shi yasa kin san abba besan mun dawo ba kuma besan mun zo garin nsn ba
Daga ina kuke to?
Daga cairo muke
Karatu?
Aa aiki muka yi ma abba a can dama gobe ya kamata mu dawo amma saboda ina son ganin kanwata na karya dokar abba na zo nan nida ya faruk
Kennan abba bsya so ka gani shi ma ya gani?
Idanta ya ciciko da hawaye tayi kalar tausayi
Shi kuma ysyi kasa da kansa
Ficewa tayi daga dakin tana kuka
Masdook ya mike ze bita
Mubarak yace hamma can i?
Komawa yayi ya zauna a kasan carpet din.
Shi kuma ya bita
Rabi'atu ta kalli faruk gaba daya burgeta yake yi miskilancin sa ya tafi da ita gaba daya
Fadima ta zungureta me haka?
Ba komai
A kunne tace fada min ko de mr.miskili ya miki ne?
Hararta tayi suka sa dariya
[09:09, 02/03/2017] Khairat: *71*
Shi kuma yana gefen ta yana jin su se ya gyada kan sa yana murmushi dan yaji su sarai ya cigaba da aikin sa.
Humaira a dakalin dake bakin bangaren su baffa ibrahim ta hade kai da gwiwa tana kuka se shassheka ta ke yi
Ya xauna ya mika mata hanky din sa ta amsa tana shsn majina ta dinga gogewa
To kanwata kukan me kike yi kuma?
Bsyan ga wan ki a kusa dake ?
Uhm ni ba wani kusa dani bayan tafiya zaka yi ka bar ni kai baka sona abba ma bsya sona ina zan kama ni kam?
Kiyi hakuri humaira ba haka bsne
To yaya ne?
Hamma babana baya son ku ganni ta kuma fashewa da kuka ta rungume shi tsna kuka
Shi ma hawayen yake yi
Amma yayi sauri ya goge hawayen sa humaira abba ba kin ki yake ba kullum cikin kewarki yake
To amma me dalilin sa na kin zuwa inda nake.kusan shekaru nawa?
Hmm !circumstances ne ya jawo ba laifin kowa ba ne kaddarar mu ce da jarrabawar Allah ki daina cursing din kan ki ko.kina ganin laifin abba a wannan lokacin ko waye aka fadawa wannan maganar zai yarda uwa fa humaira uwa!
Hmm banga laifin ki ba humaira amma ki daure a cikin wani kwana na zuciyar ki ki yafe ma abba bazan ce ki yafe ma umma ba amma zan iya neman wa abba na alfarmar nan inji faruk
Gefenta ya zauna ta zamo tana tsakiyar su ya share mata hawayen ta kinga duk bamu san dadin kanwa ba se yanzu kuma kina ta kuka baki bari mun sha hira ba haka kike so mu tafi ko laifin su abba ne ya shafe mu ko kuma ni ne baza ki kula ni ba saboda umma na
Uhm'uhn ni kukan zaku tafi nake
To ba kya so mu tafi mu dawo miki da abba da hajiya kaka?
Da gaske?
Ya gyada kan sa hmm
Ta yi ihun dadi amma zan yi kewar ku
Muma haka ko zski bimu can?
Wooo ya faruk ai hamma bazai bari ba ai kuma dada tace se abban yazo tukuna zanje kumo se Allah ya kawo ku
Toh kice akwai kewa a gaba
Gaskiya kam
Amma hamma mesa baku zo da matan