Showing 33001 words to 36000 words out of 106121 words
Chapter 12 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt
zancen zuwana makaranta ba ai idab son samu ne shi ya kamata da yake namiji ya tafi karo ilimi.
Ganin ranshi ya baci sosai akan tafiyan hankalina ya daga sai dai babu yadda zanyi don dole in tafi din don ba zan iya musa ma iyayyena maza ba a lokacin.
Ganin ban da mafita do ko ranan da zan tafi din da dare sai da muka kai ruwa rana dashi inda muka gama yanke sharawa na kamo hanya da safe zuwa birni.
Na samu baba ya gama min sayayyan komai da zan bukata a karatuna har abinci da kayan girki komai ya saya min da na iso washe gari ne zamu tafi.
Da dare washe gariin ne aka nemay ni aka rasa a gidan baba kabiru din inda hankalin su ya gama tashi sosai da nema na a garin sai dai babu labari na ko ina.
Ran baba ya mugun baci ya buga gida ance banzo ba abin ya kara tayar mai da hankali sosai gashi nursing ba gurin wasa bane da za a dan daga min kafa .
Basu ganni ba sai kwana biyu na dawo masu kamar wata gigitatta dani ina fama da matsanancin ciwon mara dake addabana.
Gashi ban son in zauna a gurin da mutane suke zaune nafison in kebe gurin daya indinga tunanen halin rayuwan dana tsinci kaina.
Anty tajini shiru tazo falo don ta dubani don kowa na cikin daki suna kallo wasu ma sunyi barci a lokacin halin tashin hankali ta samay ni ciki don ni ban san ta tsaya ba a kaina ina zaune sai buga kafa da rike mara da nakeyi ina ciza baki.
Hankalin ta ya tashi da yanayin da ta riske ni din daki ta koma hankali a tashe tana fadawa kanwa ta summaiya da suke matukar dasawa da ita anya ba ciki yar uwarki ta zubar ba kuwa.
Hankalin shamsiya yayi matukar tashi dajin zancen inda ta samay ni a falo hankali tashe tana tambayana may damuna na dai boye mata komai .
Abinka da dan uwa take fada min abinda anty ta fada mata a kaina wanda jin hakan yayi matukar girgizani don ban sauka kowa ya fahinci halin da nake ciki ba.
Ashe abin ba haka bane duk wata uwa ta gari tana saka ido akan yarta tasan duk takon da yarta ke takawa nan dai na hau fadan karya inda nake shiga ba nan nake fita ba sai da sumaiya ta taushe ni a kan zancen kada aji ace kuma wani abu.
Ido kawai baba ya saka min don bai iya cewa dani komai ba sai idon da ya saka min a gidan sai dai banyi zaton bacin rashin yakai haka dani ba sai lokacin dana tashi komawa kauye yace ai na dawo nan ke nan don babu inda zan tafi kuma mutane suna zagin shi.
Hankalina ya daga sosai da jin hakan na shiga jin haushin kowa har kannena takaicin su nake ji a raina kan wanan zancen.
Dole ina ji ina gani zama na ya dawo a hannun baba kabiru na bar kauyen da sana,ata na dawo muka hade da yan uwa na wanda hakan yayi wa umma dadi a ranta sosai.
Don tana ganin rabuwana da Jamil yazo ke nan a lokacin don taji komai ta kuma san halin da ake ciki sai dai zaman ta na kaka a gare ni ba yadda zatayi ne ga tsufan da ya kamata a lokacin .
Zaman dai gashinan ba wani dadi har lokacin da yar uwata ta kare karatun ta muna zaune tare inda muna samun manema sai dai ni har lokacin ba wanda ya kwanta min a raina kamar Jamil dina.
Kwatsam sai jamil shima ya tattaro ya dawo birni da zama gidan wanan abokin mahaifin nasa haka yai min dadi so sai a raina don masoyina da ke zaune yanzu a kusa dani.
Tsagumi bai kare ba ga bakunan yan kauyen mu don har nan din ma basu barmu ba don maganan dayace koda yaushe shine su baba kabir sun cinye muna gadon kudin mu.
Maganan bai yi zafi ba sai lokacin da dan kudin birnewan da gwaunati ke bayarwa na mahaifina da ya fito inda aka raba muna aka ware ma mahaifiyar shi nata.
Nan mutane suka shiga tofa albarkacin bakin su wai kudin yafi haka yawa an dai san yadda akayi dasu ne inda mu kuma jin hakan ya fara daga muna hankali.
Bamuyi kallon irin fadi tashin da baba kabiru yakeyi akan komai na mahaifin namu ya fito ba sai dai burin mu muji ina dukiyan iyayyen mu ya shiga.
Wanda Jamil na daya daga cikin masu hasasa muna wuta akan hakan har takai zugan su ya shiga kawunan mu sosai mun fara dauka don haka muka tafi kauye muka samu umma kan muna son jin inda motar mahaifin mu da sauran dukiyan shi suke.
Wanda hakan ba shawaran kowa bane sai nawa ni dake daukan zuga sai kanina Baffa da yanzu ya tasa shima burin shi na akan son jin komai don mun zugu da yawa a gurin mutane.
Kakan mu batayi sanyi a gwiwa ba ta aika iyayyen mu maza suka zo ta tara su inda ta fito masu da maganan da muka zo mata dashi.
Kai baba kabiru ya jijiga yana fadin Allahu akabar da yaran nan sun san komai akan dukiya da basuyi muna wanan fahintar ba sai dai yanzu a kira su muyi masu bayanin komai don suji su sani.
Umma tasa a kiramu muka shigo idona ya bushe banjin nauyi kowa a cikin su a lokacin ni dai burina kawai in san inda dukiyan mu ya shiga don Jamil yace idan mun samu zamu iya rufawa kan mu asiri muyi aure da dukiyan.
Ga wautana da rashin wayona da mahaifana suke kiramin kullun a lokacin da suke a raye sai nake ganin ai yin hakan shine daidai a gare mu.
Baba kabiru ne ya fara da addua tare da fadin umma ta fada muna maganan da kuka samay ta dashi sai dai ina son ku sani mu bamu ci kwandala a cikin dukiyan mahaifin ku ba.
Abinda bamu son ku sani yau ya zama dole gare ku ku sani don mahaifin ku ya mutu da bashin banki a tare dashi.
Wanan nauyin ne muke ta kokarin ganin mun sauke a kanshi da abinda kuke hasashen mun ciye maku din nan dai ya shiga yi muna bayanin inda ya dora da fadin yanzu kuma Alhamdullahi don mun sauke mashi wanan nauyin a kan shi mun biya bankin bashin shi da kudin gida da motan da muka sayar nashi.
Da fatan zaku fahince mu yanzu tsuru tsuru mukayi a dakin babu wanda ke iya magana a cikin mu lokacin ga nauyin da mukaje nasu kan kokarin da suke akan mahaifin mu din.
Baba musa ya dora da fadin ban taba tsanmanin zakuyi wa wanan bawan Allah butulcin ba kabiru akan irin kokarin da yake a kan ku.
Hakkuri muka shiga bashi muna fadin ya yafe muna munyi a kan kuskure da zufan mutaje ne don bamu san haka zancen yake ba ai.
Muka mike simi simi don barin sakin don shi baba kabiru bai iya furta komai ba a lokacin sai baba yushau yace ai ba tafiya zakuyi ba.
Ku zauna muka dawo a inda muke yace yanzu ku bakuji nauyi da kunya ba kan rikon da bawan Allah nan yake maku don mu din nan badon shi yana a cikin mu ba ina zamu shiga zuwa nemawa mahaifin ku dukiyan shi a kasan nan.
Umma ne ta karbe da fadin duk wanan tsegumin yana gurin wanan mai shegen idanuwan kanana da kuke gani ba kowa ke zugata ba kuma sai wanan famfararen yaron da ta lakanta Jamil.
Na fada maki ko mutuwa zakiyi sai dai ki mutu don ba zamu aura maki shi ba muddin ina raye sai dai ki mutu naji haushin wanan maganan da umma tayi a kaina a gaban iyayyena maza da suke da Alhakin daura min aure koda kuwa ace iyayyena suna raye ne sune dai din ma daura aure na a duniya.
Ban iya cewa komai ba haka muka bar dakin a cikin bacin rai muna shiga daki kanwata sumaiya ta hauni da fada sosai tana fadin sai da tace muna kada muyi wanan maganan muka zo mukayi.
Budan bakin Baffa sai cewa yayi da ita ke dole fa mubi ba ba,asin dukiyan mu don muna da gaskiyan mu yanzu ba cewa akayi wanan gidan da baba kabiru din yake ginawa ba yana cewa nasa ance da dukiyan mu ne yake gina sa ba.
Don may zamuyi shiru akan abinda yake hakkin mune ba zamu tambaya ba tace yanzun da kuka tambaya ai kunji abinda bai muna dadin ji ba don ashe baba ya tafi da bashin banki ne tare dashi kuke wanan haukan.
Bata bar baba kabiru ya dawo ba sai shiryawa tayi tana fadin ita binshi zatayi ba zata zauna ba don zaman kauyen ya isheta gaskiya.
Dole muma muka shirya muka biyo shi birni har muka dawo bai nuna muna komai na bacin rai ba a tare da mu sai ma dan hiran da yake jan kanne dashi a motar.
Gaskiya baba kabiru mutum ne da yasan hakkin rike maraya sosai don irin kokarin da yake ya yaki zuciyar shi a kan mu da kuma iyalan shi.
Don bai taba yarda a kawo sukan mu a gurin shi koda ko mune bamu da gaskiya yanzun zai ma mashi fada sosai tare da fadakar dashi illan yin hakan gare mu.
Mun dawo haka rayuwa ta ci gaba da tafiya muna inda yanzu shirin auren diyar baba kabiru mace ake yi wanda yaso ace nima a lokacin tunda ba karatu nake ba na samu wani tsayayye na tsayar ya hadamu tare yai muna aure.
Sai dai banda Jamil ban kula kowa har yanzu gashi shi kuma jamil din baida ranan zancen auren mu din don bai aje ba bai ba wani ajiya ba.
Dole haka aka fara gabatar da bukin yar uwata a gidan inda yan uwa da abokan arziki birni da kauye suka cika muna gida.
Ayi lafiya an watse lafiya kowa ya koma gidan shi a cikin farin ciki zuwa lokacin baba kabiru ya karasa ginan shi muna shirin komawa ciki ke nan.
Ranan laraba muka kwashe zuwa sabon gidan mu inda a nan dakin mu daban na yara da muke zama mu yan matan dakin anty amar mu biyar ne nata daya sai mu biyu da wata diyar baba yusha,u da mahaifiyar ta ta rasu a gurin haihu.
Da suka je gaisuwa ta biyo anty muka tashi mu biyar sai kannen mu maza dake zaune da ita da nata biyu muka tashi mu takwas a gurin ta.
Duk da wanan yawan rayuwan mu ba zaka ce ba itace ta haife mu ba don gaskiya babu banbanci a gurin ta da wanda ta haifa damu din haka muke rayuwan mu a cikin jin dadi.
Don yanzu Allah yaiwa baba din budi sosai zaman mu gwanin ban sha,awa a gidan ana cikin haka ne umma ta kawo masu ziyara a garin.
Munji dadin zuwan nata sosai inda muke zama gwanin ban sha,awa babu wani tsangwama a tare damu sai dan dan gulman mutane da ba a rasa ba dake zuwa yana dawowa a tsakani.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:53 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼♂️ KANIN AJALI 🙆🏼♂️
1️⃣3️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
IMANI A ZUCIYA YAKE SANIN ALLAH DA IMANI DASHI YANA SA MUTUM TSIRA DAGA HALAKA AMMA FA SAI WANDA YA DAUKA DA GASKIYA YA KE KAI GA HAKAN UBANGIJI KA KARA MUNA IMANI A ZUKATAN KASA MU FI KARFIN ZUCIYAR MU, , , ,
JUMMA,ATUL HAIRAN YAN UWA MUSULMAI 👏👏👏👏👏👏
Zaman mu da umma a gidan baba kabiru ba tsangwama ko kadan yadda takewa kowa a cikin jikokin ta haka muma muke da ita har ina mamakin ta.
A cikin wanan yanayin ne Jamil ya labartawa wani dan mutumin da yake zaune a gidan shi labarin mu dana mahaifin mu shima yaji yana ra,ayin kanwata summaiya ya samu wanan gara basan na mahaifin mu da jamil ke labarta mai zamu samu.
Haka yayi dabaran daya hada sumaiya da wanan dan gidan da yake zaune dasu yazo gurin summaiya da sunan soyayya a gare ta.
Sai dai shi wanan ba rago bane kamar jamil dina don yana matakin kare karatun digree din shi a lokacin.
Batai wani na,am da shi ba a lokacin don ta gane manufa hakan a gareta don anty amarya ta hasko dabaran su a gare mu bata kuma boye muna ba ta fada muna kai tsaye abinda suke nufi damu din.
Sai dai irin matsin da yaron keyi na zuwa wurin kanwar tawa tare da dadin bakin jamil yasa har take dan sauraron shi don yace da zuciya daya yake sonta a yadda yace mata din .
Wai yana jin labarin ta yaji hankalin shi ya kwanta da ita sosai saboda tausayin mune yaji yana matukar son ta a ran shi don rashin mahaifan mu da mukayi.
Sannu a hankali suka kulle dashi har ta fara samun kanta sai dai korafin anty a kan haka da tashin hankalin ta yasa tana dan ja da baya ga zancen shi.
Tafini farin jini don tafini kira sosai don ni irin matan nan ne na fada maku tun baya ni kwalliya ma bai damay ni ba haka mukan ta kwasa da anty akan gyara irin na yan mata kullun muna zaune da daurin zani a gaba a gida wanda take mana masifa akan hakan idan tana gida idan ko ranan aiki ne tana gurin aikinta sai mu zauna hakana a gidan ba wani gyaran jiki.
Don muna ganin ai ba inda muke zuwa banda gida gyaran may zamuyi itako anty yar gayece ta karshe gyara dai na matan zamani ba wanda bata iya ba.
Hakama girki da gyaran muhallinta bata sakaci da wanan don idan mutum yana zaune da ita sai yaso ya ketaci kanshi a kan gyara idan kaji fadan ta damu akan rashin gyara ne da bamu yi don haka muka saba mu tun a can da muka taso.
Dole ta kawo ido tasa muna hakana a yadda ta ganmu kamar wasu yan kauye damu ga yan uwanta daga Niger state suna yawan zuwa gurinta duk yan gayune su amma mu hakan duk bai damay mu ba.
Wata rana umma ta tashi da ciwo mai tsanani a gidan wanda kowa na gidan hankalin shi ya tashi sosai da ciwon nata.
Allah da ikon shi ana treating din ta ta samu lafiya sai kuma gudawa ya biyo bayan samun lafiyan nata nan ma hankalin iyayyen namu ya tashi sosai da ciwon na umma da takeyi.
Kwana uku tana fama da wanan laluran ranan muna barci da dare anty ta tayar damu daga barcin tana fadin mu tashi mu ga halin da kakan mu ke ciki a lokacin.
Abin gwanin ban tausayi mun falka mu samay ta a wani irin yanayi sai sambatun take faman yi haka anty tayi dubaran karantu mata kalman shada sai take amsawa daga inda take din gashi a lokacin baba yayi tafiya don ganin umma ta samu lafiya.
Ba wani shirine tsakanin umma da anty amarya ba don bata ra,ayin ta ko kadan haka dai anty ke shanye halin umma har Allah yasa ta hayyayafa a gidan tare da baba kabiru din don shi yana son matar shi.
Kiri kiri umma zata nuna bata son ta bata son diyan ta data haifa a gidan da baba kabiru din sai uwar gidan ta yar asalin kauyen namu itace mata a gurin umma.
Idan baku manta ba na fada maki haka mahaifiyata ta sha wanan faman da umma lokacin da take zaune a kauye akan uwargidan na baba kabir da umma keji tankar itace ta haifa ta sa cikin ta a duniya.
Don har mutane na fadin ba a banza ta barta ba kan wanan halin da take nunawa da diyan ta ma sune jikokin da umma tafi so a cikin jikoki gaba daya.
Idan anty amarya taji sun shagala da zancen da bata ji daga inda muke a zaune sai ta fadi kalman shahada sai umna din ta karba daga cikin dakin mama din da take kwance.
Hankalin umma yayi matukar tashi sosai ta mike ta fita zuwa makwabta a kwai wani tsoho da muke makwabtaka dashi da wani ba haushe a uguwar duk sauran yarbawa ne da iyamurai don sabon uguwane sosai gurin ba mai kula harkan wani a cikin unguwan.
Tsohon yazo ya duba umma shima hankalin shi yayi matukar tashi sosai da ganin yanayin na umma dayayi yace yanzu dare ne babu yadda za a yi da an kaita asibiti.
Baifi awa daya da fita ba anty amarya kuma bata fasa fadan kalman shahadan da take fadi ba a bakin ta Allah ya karbi ran umma take a wurin .
Wani sabon tasgin hankali kuma a gare mu mun koma ba uwa ba uba babu kakan da muke dan rabawa muji sanyin rashin iyayyen mu a gurin ta.
Haka muna kallo washe gari aka kawar da umma zuwa makwancinta ubangiji yasa sun huta da duk kan musulmin Allah da suka rigamu idan namu yazo mu cika da