Showing 69001 words to 72000 words out of 106121 words

Chapter 24 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

01 Jan 2025

7531

tsakanin su take bude mai bakin aljihun ta yake shagali shi dashi don iya yaudaran shi da karyan shi.
Da farko yaje gun Ruth ne ya tatsi banza ya gudu sai ya hadu da yar duniya dama tana neman wanda zata kama sai ta daure shi har kafa baida daman dogon motsi ya gudu gareta.
Don ta dade da asirice shi yaje cin banza banza ta ciyo shi ga masifana a gida da nake aza mai tunda nasan bai rabu da ruth din ba na sashi gaba da fitina.
Har ya fito fili ya nuna min ban isa in rabashi da ita ba wallahi haka muke zaune bani na samu kaina ba dashi sai da kudin da muke bin gwaunati ya fito na wata hudu sannan ya nemi shiri dani don yaci kudina.
Ya ko ci don nan ya kawo min kabali da ba,di bamu da kaza ya kamata mu sai kaza na amfanin mu shi nashi bana lalurar gida bane sai nawa idan sun zo ake sakawa a gaba a cinye anga banza.
Niko ban gane shi ba har yanzu ina dauka sona yake tsakani da Allah sai nake sakar mashi komai idan yai min dadin bakin su na maza.
Na ramay na lalace ni ragga diyana ragga duk mun bi mun kanjamay don wahala gashi dan aikin da nake kuri dashi an dakatar da yin shi yanzu.
Sai abin ya taru yai min yawa sosai a kaina dole naje gida wurin anty don ta taimaka min tasa baki ga kanne na su bani dan wani abu in sai ko kura na ruwa dan kwabo ya dinga shigo min.
Da kyat da boni anty ta yarda zata sa mun baki gare su duk ko da tasan abune mai wuya a banbare su kudin da nake so.
Amma haka ta daure zatayi masu magana idan sun shigo shikan baffa tana tun karan shi da zancen yace ba zai bayar ba.
Sai dan karamin mu ne da anty ta titsiye yace zai bani dubu goma tace bai yi ba don Allah su tausaya min idan basu koyi bani ba yanzu yaushe zasu koya.
Haka dai har ta ciwo kanshi yace zai bani sha biyar lokacin daidai kudin baron ke nan nayi ta murna da ta fada min.
Inda ta zaunar da kanne na tayi masu nasiha sosai mai ratsa jiki duniya ke nan wace Jamil ya cusa muna ra,ayi mu guje ta itace kuma yau na komawa ta taimake ni.
Ba tare da tayi duban baya ba ga komai ta tausaya wa hali da nake ciki tasa ai min wani abu a tallafa ma rayuwana don Allah.
Baron ruwan da na saye baiyi wani tasiri ba duka duka baifi wata ba na kadar dashi na fara sana,an kayan mata da dan kudin.
Wai ni a gani na zaifi sana,an ruwa kawo min kudi a cikin lokaci kwana biyu muka turmushe kudin babu ko labarin su kuma.
A cikin haka ne su maman Ahmed yan hayan gidan mu suka tashi don zaman mu yaki dadi dasu ga matsin jamil akan shi fa sai dai su bar muna gida.
Do sune ke zugani ina wani abin don shi bai kaunar yaga nayi wayau a rayuwan shi yafi son ya gannin ko yaushe kamar wawiya yana juyani yadda yake so.
Tashin su ba a dade ba aka sa wata amarya a dakin da suka tashi ciki amaryan matar abokin Jamil ne yasa muke kuma dan shiri da ita.
Wanda hakan yasa na dan samu sauki wasu abubuwa a gidan yanzu don yana ganin yadda abokin nasa ke kula da matar shi.
Sai dai abinda ba halin mutum ba bai iyayin kamar kowa don bai saba yin hakan ba tun farko ina dai zama zamana hakkuri dashi.
Shiko yana holewar shi waje da matan banza yau ma kamar kullun na tashi babu ko sisi a hannuna ga yara na har sun fara min kukan yunwa.
Na rasa yadda zanyi dasu a daki can dai dabara ya fado min wanka nayiwa yaran babu ko sabulu na shirya su muka nufi gidan mu dasu.
Bayan mun gaisa ake tambayana inda na fito da sanyin safiyan nan nake cewa gida ganin yanayi na baisa sun matsa da dogon bincike a kaina ba sai abin karyawa aka gabatar min dashi.
Na dan tsaya basarwa mama ta matsamin akan in dai karya din don ban samu anty a gida ba lokacin tana gurin aiki sai mama ne a gida kawai.
Nan dai na fara labarta mata halin da muke ciki a gidan ina kuka tace in daina kuka nawa kaddaran auren ke nan yazo min a haka.
Hadiza kina da hankali da ilimin ki zaki zauna kullun miji yana cutan ki kin kasa wayau ki fahinci abinda yake nufi dake.
Fada sossi mama tayi min ban iya magana ba sai kukan da nakeyi har barci ya daukeni a gurin ban koma gida ba anan naci na safe dana rana har anty ta dawo daga aiki ta samay ni a gidan.
Kallo daya taimin ta gane halin da nake ciki bayan ta idar da sallah la,asar ta fito ta samay mu nan dai ta shiga min nasiha inda duk laifin a kaina ta dora inda ta kare da fadin idan naga dama in koma in kara bashi kudin don yanzu ba abinda ma yarage ai.
Na samu ta hada min abubuwa na koma gids na girka muna abinda zamuci da dare dani da yaya na sai gashi ya shigo dauke da dan leda a hannun shi.
Lemon sha ne ya zauna ya bare ya min mikawa yayan shi bari ya shiga shan abinci sai da ya gama yayi gyatsa yana kaiwa kwance saman kujera ya mimike sallah na idar idar na jawo kullan abinci ina zubawa don in ci yace ina kika samu abinda kikai abinci ?
Ban saurare shi ba saboda haushin shi da nakd ji a raina yaya nami zai fita tun safe bai damu da yasan iyalin shi sunci ko basu ci ba.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Kamar yadda Jamil ya damu da isowan kudina haka mijin yar uwata ya damu da zuwan su shima sai dai bai yarda ya nuna zalaman shi a fili ba kamar yadda nawa mijin ya nuna .
Don ya fishi shekaru da ilimi da ma wayewa sosai don ni nawa mijin iya secondary ya tsaya shiko wanan har masters yayi a karatun boko.
Wasa wasa har aka share wata uku ba labarin kudin sai abubuwa suka fara canzawa ga matsi da yai muna yawa na talauci .
Mahaifin Jamil har gida yazo ya saka min magana wai sunji rigi rigi sakwat mana ance ga kudinan tafe sunji shiru kuma.
Nace baba lokacin zuwan su ne baiyi ba tukun aida sun sunzo abinda bana mutum daya ba ai sai hakkuri kamar yadda kowa yayi.
Allah karimun rahimun a ckin wata na hudu sai ga kiran baba wai kudi sun sauka muna a cikin dare ya kirani yana fada min haba kamar in jawo safiya a ranan.
Don lokacin Jamil baya gari na kirashi ina fada mai ya yanka wani ihu a waya yana jin dadi kamar wanda ya biyo dare sai gashi koda goma tayi yana cikin garin.
Ina tsaka ga gyara gida ya iso ina yana shiga daki yake fadin to yaya an raba ne nace har yanzu baba bai kirani ba yace kaji ko ?
Kin ga halin yaudara ko in ba haka ba kudi sun zo araba aba kowa nasa mana an tsaya jan rai sallon ayi yaudara da aka saba kuma.
Kallon shi nake da manaki yadda ya hakikance yana fada kan kudin da baida kaso a ciki koda yake shine mai kason nawa wanan zuzudin da yakeyi haka.
Misalin sha daya ya kasa hakuri yana kwance a daki ya kwala min kira na amsa na shigo yake fadin kije gidan nan kiga abinda ake da idon ki zaifi gaskiya.
Ke ma banda abinki an kiraki tun cikin dare an fada maki ba sai kiyi sakkon zuwa gidan ba amma kin tsaya kina shininiki irin wanda kika iya.
Ba abu mai wuya bane gare su su rage yawan kudin kuma nace a a gaskiya yaya za a rage yawan su abinda ke rubuce.
Sai fa baba yaba kowa waya munga yawan kudin ake fara rabawa yace ke dan Allah ja can ke may kika sani don Allah.
Haka ya matsa min dole na shirya na tafi gida naje na samu baba baya gida lokacin don haka na tsaya jiran shi har ya dawo ban raba dayan biyu tunda na tambayi kani Baffa akace sun fita da baba nasan banki sukaje tare cire kudin.
Komai na baba yana kokarin yaga ya fitar muna da hakkin mu amma huduban su Jamil yasa bamu ganin hakan da yake muna sai ma ganin laifin shi idan kudi sunzo da muke yi.
Nan na zauna ranan ba ko sakin fuska suma yan gidan sai suka share ni suna harkokin su kamar ban gidan.
Nakai kusan awa daya sai gasu sun baba sun dawo duk yayi zufa zufa dashi daya shigo, shima kani ya wani daure fuska a lokacin sai da gabana ya fadi na dauka ba kudin ne da sukaje banki ko kuma wani abin ya faru.
Ashe tsare gidane na irin kada aga walenshi ai muna rainin wayau kamar yadda aka tsara mashi din yayi.
Daga inda nake zaune naji hayaniyar su baba musa sun shigo ana bude masu falo ta baya na sauke ajiyan zuciya nasan kudi sun samu ke nan tunda suka zo.
Araina nake zagin su ina fadin ko kunya basu ji da angansu an san abinda suka zo amsa ke nan wai suce suna cin gadon mahaifiyar su.
Kanwata ta shigo da yar diyar ta suna gaisawa da mutanen gidan mu ana wasa da dariya da kowa sai lokacin naga wautana na gimtse masu danayi da farko.
Nan naso saka baki sai wata kanwata diyan baba kabiru mara kunya tace a, a anty hadiza ke da kika shigo kina daure fuska yanzu zaki ce zaki mana magana kuma.
In dai kudine karewa zasuyi mu zama daya kwana nawa ne ance ma mara mata gwauro raina ya baci sosai da maganan ta.
Ina ganin tun kudin basu shiga hannuna ba tayi min baki aiko nan na hau bakina da fada da ita sai inda na tsaya jin muryana da baba yaji ya kirani tana fadin ashe ma na zo don da ya shigo bai lura dani ba.
Nan muka mike muka nufi falo muka samay su kamar kullun baba musa ya bude da addua sai baba kabiru ya dora bayani kamar kullun tare da miko muna wqyan shi yana fadin.
Ga sakon saukan su nan ga fitarwa yana miko muna wayan ga wautana har zan karbi wayan sai kanina baffa yace ai tare mukaje baba ba sai sun karbi wayan ka ba aci gaba dai kawai.
Nan aka fitar da na mahaifiyar su sai aka fara kasafin namu kuma akayi lafiya aka kare kowa ya kama gaban shi don ko minti ashirin bamu kara a cikin gidan ba muka wuce.
Gidana muka yadda zango kamar yadda muka saba yi idan mun fito wurin su baba din nan muka shiga kullawa da warwarewa a tsakanin mu.
Muka gama shaci fadin mu da komai aka shiga kasafin abinda kowa zaiyi shidai karamin mu wanan karon ma cewa yayi duk yadda mukayi ya fita ya barmu nan.
Kamar hadin baki sai ga Jamil da adam sun shigo gidan a tare da Ahmed mijin kanwata sai wani washe baki sukeyi.
Nan mukai masu bayanin komai tare da fada masu yawan kudin da kowa ya samu da wanda aka fitar kason hajiya umma.
Ahmed din yace yanzu abinda za ayi a cire kudi da zai isa kowa sayen uncomplet building a samu a saya kada kudin su lalace muna.
Saura sai muyi lalurar mu dashi shawaran shi anyi na,am dashi sosai already dama ashe sun yanke hakan har sun cigiya muna ko an samu boyewa dai sukai muna kan hakan .
Sukai muna sallama suka tafi haba shiko gogan nawa kamar jira yake su fita cikin tsare gida yace ina kudin naki nace suna ciki na boye.
Ganin yana kallo na nasan abinda yake nufi yasa na mike na shiga na dauko mashi kudin na kawo mai ya karba yana juyawa tare da tambayan na tabbatar kudin sun kai yadda akace ?
Nace sun kai mana ko a na gida sai da baffa ya sake kirga min yawan su yace to may kike ganin za a saye dasu yanzu in an cire wanda za a sai gidan da ba a kammala ba.
Don dai data nice sai in ce kada asai wanan gina ki fara juya kudin har suyi tsoka daidai sayen gida ginane kinga sai ki zuba yan haya a ciki ko may kika gani ?
Ya tambaye ni yana tsure ni da manyan idanuwan shi nace ni dai ayi yadda yan uwana sukace kada ya zamo na fita daban a cikin su bayan mun shirya yin hakan da su.
Tun da yamman nan ya ware wasu kudi wai zai sayo abinci ya fita ban ganshi ba har dare ya dawo min babu kayan abincin wai sai gobe idan ya fita zai karbo.
Washe gari ko sai ga kanwata da mijin ta sunzo sunce an samu kangon gida jamil da baffa suzo suje su gani idan yayi masu.
Sun je sun duba kangaye nada dama sosai don gina da aka fara sun tasa sosai kuwa sukace sunyi masu sai Jamil ne yaso kawo rikici wai kangon yayi tsada ga yadda akace kudin shi.
Nan dai Ahmed ya kara fahitar dashi har ya yarda a saye din aka saye bado yaso haka a ranshi ba ba dai yadda zaiyi ne.
Bayan sun dawo sukai muna bayani har sauran kudi sun rage tun nan a gaban su muka fada masu shawaran da muka yake kan zamu gyara dakunan nmu ne.
Jamil bai so haka ba yana ganin an takura mai da yawa mijin summaiya yace zai tambaya muna set din kujeru masu kyau mu saya zuwa gobe.
An ko samu kijerun shi Jamil ya kawo shawara wai a na saka ties a falo na don shima kunyan azo aga dakin babu ledan kwarai yakeyi.
Shawaran shi ya karbu a waje na da tan uwana sukace tunda zanyi gyara ya kamata a sa ties din a falon sai a bar dakin .
Kamar wata amarya haka dakina ya koma ga ties ga tv plastma harda tauraron dan adam da fridge sabo ga su center kafet an saka a dakin.
Duk da jamil yayi na kasa wurin sa ties di dakin ya kara kudi ga abubuwa da dama sosai amma haka aka gyara dakin .
Duk ko da na bashi nasa kaso daga cikin kudin sai dai kuma bai hana shi yin na kasan ba a cikin dan abinda ya rage min din.

Labarin baba kabir kuwa tunda ya bamu hakkin mu bai kara bi ta kan mu nasan don tsage rancin da muka nuna masu ne lokacin rabon kudin da Baffa yace wai dole ne sai an cire na mahaifiyar su .
Sai kuma wanda baba ke bi a ciki na fafitikan neman muna kudin ya fito da yake kai cin hanci da sauran su wurin duk wanda ya dace ayiwa.
Kuma gashi mun sani baiyi shi kadai sai da sanin mu idan za a yi don ko an lalubu mu kudin bamu dashi balle mu bayar din.
Dole haka aka fitar mai da abin shi duk da ma bai cire na jigilan shi ba yace ya yafe muna su amma duk da haka sai da dan hakin shi ya tsone muna ido.
Kada kukaga laifina masu karatu gama in kun tuna na fada maku sai da suka raba mu da kowa namu sai su mazajen namu da kannen mu biyu kawai muke shawaran mu.
Do haka komai sukace sai muga ai sunyi daidai ba ba mu ganin rashin dacewan hakan a gare mu tunda yanzu su zama muna uwa da uban mu a yadda suke fadi ko yaushe.
Don haka muka dauke su da zuciya daya ban ko tuna saura saki daya fa tsakani na da Jamil din duk da dai ban fadi a gidan mu ba kowa ya sani.
Dakina yanzu har zuwa kallo akeyi koda yaushe tv na aiki a falon yan diyana suna zaune suna kallo basu zuwa dakin kowa na gidan da sunan kallo.
Yanzu zamzam muke da Jamil baison ko kuda ya tabani ko diyana a gidan sai dai ban sani ba ashe har lokacin suna tare da Ruth farkan shi.
Ba wanda zai iya fada min don ban iya boye mutum wurin magana shiyasa kowa ke tsoron fada min gaskiya koda an gani sai a kyale ni gashi wanan kawar tawa sun tashi tabi mijin ta can kasa ibo inda yake.
Don da tana nan data fada min idan ta san da hakan ba zata boye min ba kamar yadda mutane suke boye min yanzu.
Duk da na gyara daki yanzu tsiyan daya tsiro min shine sai yace bai iya kwanciya a dakin wai zafi yayi yawa a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login