Showing 54001 words to 57000 words out of 106121 words

Chapter 19 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

01 Jan 2025

7532

fili.
Haka dai na gaiyaci yan uwana kan suzo akwai maganan da zamuyi dasu a gidana ranan kaza da yake mukan hadu ba wanda ya sani mu dan tatauna dasu.
Da farko sunki ban hadin kai kamar yadda naso sai daga baya ne da na sa masu kuka jikin su yayi sanyi suka yarda a sayar da filin don na fada masu abinda nake son inyi da kudin filin.
Tunda wancan mai yawan baida ranan fitowa gare mu yanzu abinka ga dan uwa duk sai suka tausaya min suka fara fadin suma suna da abinda zasuyi idan kudin sun samu.
Nan muka aje ranan da zamu samu baba kabiru da zancen filin kowa ya koma inda ya fito sai ranan da zamuje wa baba kabiru da zancen kuma.
Jamil ya dawo yana tambaya na yadda mukayi dasu nace sun yarda nan ya hau yin dadin baki irin nasa har da fadin yadda kudin filin zai kai idan mun sayar din.
Ya shiga tsara abinda zai saye na suna da wanda ni zanyi tun lokacin da yaji yan uwana sun yarda don ni yanzu ina kallon shi ya daina harkan bariki gani kadai ya dogara a gidan.
Bukin yar uwanshi za ayi a kauye ya shiga min shiri wai yana son in fito wurin bukin dani da Amira yai muna dinki fita buki kala biyu duk da bamasu tsada bane niko sai rawan kai nake zan fasa taro da kayan idan naje.
Ina ruwan dan baka saba ba nake ganin ai ba wanda zai kaini fita a gutin yadda yake dada kayan a gabana da yadda zasuyi min kyau.
Mun samu baba da zancen fili baba yayi mamaki kwarai may zamuyi da kudi haka mukace muna dai son a sayar a bamu kudin mu ne lalura zamuyi.
Yace mu bari zai tuntubi yan uwan shi idan sun yanke shawara zamuji daga baya abinda suka yanke.
Kwana biyu na wuce wurin buki a kauye wanan karon ban dade kamar yadda yake turani in dade ba saboda zancen kudin da yasa ma rai din ya matsa akan in dawo.
Tun da na dawo ya sani gaba haka nikuma na sa yan uwana a gaba muka tayarwa baba hankali akan fili baba musa yace wa baba kabiru a sayar kawai tunda matsin yayi yawa yaran nan idan ba munyi da gaske ba suna da ja sosai damu nan gaba.
Haka dole aka sa fili kasuwa kan sayarwa shiko gogan kulun ya dawo tambaya yake yaya babu wani magana a bangaren babane har yanzu.
Idan nace a,a sai yace ya gane mutanen nan cutan mu suke son yi idan ba haka ba fili ne za a ce yayi wuyan sayarwa a gari kaza.
Shi idan basu samu mai saya ba shi zaije ya samo wanda zaisai fili a bamu kudin mu don ga lokaci yana karasowa na haihuwa na ni bani tunanen hakan shi idan na haihu baida yadda zaiyi gaskiya.
Nikuma jin hakan sai na kara hasa ma yan uwana wuta muka matsama baba kan zancen fili mudai a sayar ko nawa ne a bamu kudin mu shine burin mu.
Baba yace indon ta nasa ne a bari nan gaba fili zaifi kudi sosai don yanzu ba lokacin kudi bane ga mutane don damanane yanzu .
Mukace mu dai a sayar duk wanan abin mu uku ne masu hasasa wutan komai shi karamin mu baya cewa komai sai yadda mukayi dashi.
Da yake yana jin maganan mu shi dai bai cewa damu komai sai yace duk yadda muka yanke yayi mai don ko kudin farko da aka raba nasa Baffa ne ya kalalamay yaki bashi wai don kada ya halaka kudin.
Ko dubu daya yake so dole sai baffa ya sani zai cire ga account din shi don Atm da komai nasa yana hannun baffa don bamu yarda da iyayyen mu ba saboda zugan su Jamil dake aiki a kan mu lokacin.
Wani tsana da kiyayya ne ya fara shigowa tsakanin mu da yan uwan mu da farko muke daukan kan mu duk abu daya yanzu irin abinda suka ga muna nuna ma mahaisu sai tsana da rashin yarda ya fara shiga tsakanin mu dasu.
Babu magana mai dadi haka ma su anty duk sun tsamay hannun su ga zancen mu yanzu a hankade suke kallon mu idan munje gidan.
Haka yasa muma mukai shawaran daina zuwa gidan wurin su sai an dauki lokaci mai tsawo bamu taka gidaba da sunan zuwa gaida baba.
Don shi baba kabir mutum ne mai wuyan sha,ani baka gane bacin ranshi a lokaci daya don bai nuna muna komai dake faruwa a tsakanin mu dashi sai dai su iyalin nasa.
Anty ma tun abinda mukayi wa iyayyen mu maza muka rasa gane kanta ta daina muna komai sosai da take muna a baya yanzu ta rungumi diyan ta kawai.
Duk da tana dan iya kokari wurin nuna muna ba komai amma mun ja baya ga al,amarin ta sosai yanzu haka dai ake zaman kadaran kadaham damu dasu.
Ranan dai na samu baba da kuka ina fada mai ina cikin matukar bukatan kudi ne don haka don Allah a sayar da filin nan ko nawa ya samu.
Ba a fi sati ba aka sayar da filin namu ina kwance gida baba ya aiko inzo yana neman mu Jamil yana jin haka yai zubur ya fito daga daki yana fadawa dan aiken yaje yace gani nan zuwa.
Bayan fitan dan aiken yake fadin in tafi zai karasa min aiki na kafin in dawo don haka na shirya a gurguje na nufi gidan namu wurin kiran da baba kabiru ke muna.
Ban dade da isa ba yan uwana suka hallara a gurin nan dai baba yai muna jawabin yadda filin ya kama inda za, a fitar da gadon mahaifiyar su sai a raba muna sauran.
Idan akwai mu abinda muke ma bakin ciki shine ace za a raba gado a warewa mahaifiyar mahaifan mu gado tunda yanzun bata darai ai.
Gani muke kuma da yadda Jamil ya lurar damu ai zalunci ne da ha,inci ake muna a hakan da komai za a ce wai a cire kason mahaifiyar su duk da bata raye wai a raba da ita don dai kawai su samu kason wani abu daga ciki.
Yau ma kaman kullun bayan sun gama muna jawabi sai kanina baffa yace shi yana da magana wai duk da hajiya umma bata raye, may kesa ake cire mata nata kason ko yaushe idan anzo rabo.
Kai baba kabiru ya girgiza yana murmushi yace yanzu kai baffa waye bare a cikin uban nan, nan naka , sai baba musa ya dakatar dashi da fadin ba wanan ba don na gane dan kason mahaifiyar mu da muke ci daga cikin arzikin su suke wa bakin ciki don yau kun fito fili kun baiyana muna manufa ku akan abinda kuke nufi.
Baba kabiru ranshi ya baci sosai damu bai iya magana a gurin ba saboda bacin rai sai na koma tun a wurin ina jin nauyi da kunyan kanmu sosai na abinda mukaiwa baba kabiru da yan uwanshi sai dai murna da dokin samun kudi a lokacin bai bari mun rokeshi gafara ba.
Kamar yadda muka saba idan mun saba mashi muke bashi hakkuri ya huce damu sai yau bamu samu yin haka gare shi ba don doukin samu kudi da mukeyi.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: Yau da gobe na Allah ne abinda muke jira tsawon shekaru sai gashi Allah ya nufa sun shigo gare mu nan hankali mutane ya dawo gare mu.
Don suji yaya za ai rabon wanan kudin namu an kasa kudin gida uku muka fara samun kashin farko ranan jamil shi da kan shi ya shirya min yarinya don inyi sauri mu hadu a gidan baba kabiru inda aka bukaci muje har.
Har kusa da gidan ya rakani yana fadin idan kinji ki maida hankali ki saurara da kyau don kada a samu matsala nace insha Allahu mukai sallama na yaju ya koma gida yana jiran dawowa na daga gidan mu din.
Na samu su baba musa da baba yushau sun shigo garin inda na karasa ciki da sallama na ina gaida mutanen gidan namu da kwana.
Aka ce ni ake jira in karasa ciki kafin yar uwata tazo an bude gurin da sallama tare da addua kamar yadda musulmai keyi idan sun hadu a gurin yin abu mai muhinmanci.
Baba musa da yake babba ne ya fara magana yace to Alhamdullahi yau dai Allah ya nufa wanan kudin da aka dade ana jira sun fara shigowa gare mu.
Sai dai zamu so muyi rabo kamar yadda addini ya umurta da ayi yadaiyi yan bayanan shi tare da fadin zasu cire kason umma mahaifiyar su a rabawa magadan ta kamar yadda addini yace.
Nan kanina ya gyara zaman shi da kyau ya kuma dora da fadin zamu cirewa shi Alhaji kabiru kuma kudin shi daya sa na jigila tare da yin wahala kafin kudin nan su fito gare mu.
Sai baba kabiru din yace ba zai karbi kudin duka ba tunda kudin namu bai gama shigowa ba lokacin tare da fadin zai kuma karbi iya wahalan shi rabine.
Nan sukayi komai kamar yadda ya dace ayi kan tafarkin addinin musulunci aka fitarwa maza da kason su sai mu mata mu biyu .
Ganin duk mun bata rai tunda baba musa ya fara magana yasa baba kabiru yin gyaran murya a gurin yace idan mun ga rabon da sukayi bai gamshe mu ba zasu iya kiran malamai ko alkalai suzo su raba muna da kansu idan haka zai gamsar damu din.
Dakatar da rabon kudin baba musa yayi a lokacin da yaji abinda baba kabiru din ke fadi yace assha daga cikin mu nan wa zai cuce su suke gani idan mu masu hali ne ai ko kallon kudin nan da yake gadon mahaifiyar mu ne ba zamuyi ba.
Nan dai muka dan fara kamay kamay alaman nuna haba dai baba aka raba kowa ya dunkule nasa muka fito idanuwan mu mirsisi nayi sallama da mutanen gidan mu muka bar gidan.
Gaba dayan mu gidana muka hade dukkan mu nan kanina ya fara fada akan abinda su baba sukai mu nan dai kowan mu ya shiga fadan albarkacin bakin shi kan su baba din.
Sai baffa ke fadin shi baba kabiru ne yafi bashi mamaki da wai ya karbi kudin da don yayi wahala ya nema muna hakkin ga gwaunati.
Lokacin ko yana UG two ne baba ne mai daukan nauyin karatun shi a makarantar ga diyan shi a zaune bai kai su ba su amma duk wanan bamu gani ko kadan mu kudin mu dai muka sani mu.
Sai Jamil da na samu yana dakon dawowa tun fitana yace yanzu kun fara gane mai nake fada maku din ke nan yanzu shi baiji kunyan fadin wai a bashi wanan kudin ba don Allah.
Mun dai fadi magana a gurin duk wanda yazo muna a baki fadi mukeyi a lokacin don ran mu daya baci kan dan abinda iyayye mu suka dauka wanda iya hakkin su ne suka dauka.
Nan mijin sumaiya yazo shima ya dan dora nasa zancen akarshe a ka yanke shawara Baffa kanina zai rubutawa baba takarda kan abinda sukai muna karshe su sumaiya suka dauki kudin su mukai sallama bayan mun cire wanda zamu rabawa dangin mu kaf daga cikin kudaden da kyat don kowa na fadin kudin sunyi yawa abinda nace a ware din abawa yan uwa da suka wahala damu.
Daga cikin mu dan karamin mu ne kawai bai magana karshe ma da yaga irin shawaran da mazajen mu ke badawa yayi yawa ya mike tsam abinshi yace damu sai da safe.
Nan na gano baya tare damu aiko muka haushi da fada shida bai ce damu komai ba ta fita abinshi yana fadin kudai bi sannu don kudi karewa zaiyi ya barmu da iyayyen mu daga haka ya fice abin shi ya barmu.
Ina mamaki yanzu kwarai da kanwata tafini zakewa akan zancen kudin nan sosai sai daga baya na gane sherin mijin ta ne ya yi mata famfon shedan a zuciya itama ta kumbura fam da iyayyen namu.
Tsakani da Jamil yanzu ko nan wani irin ladabi ya taso ga Jamil din gare ni sai nan nan yake yi dani da yar diyata na zama wata hajiya a guri shi da baya son ko kuda ya tabani a lokacin aka bude wani shafin sabon soyyaya sosai a tsakanin mu.
Tun cikin dare muka fara kasafin kudin da abinda zamu saya da kudaden namu inda yasa na ware ma mahaifan shi nasu kason daga cikin kudin.
Ni yar Dadi aure sai nace ya rike kudin a hannun shi gaba daya duk abinda za a yi sai ayi nan muka shiga facaka da kudi ba wanan, ba wancan, duk kuma yan uwan shi don ni nawa yan uwan ba wanda yazo kaman an tsayar dasu a lokacin daga zuwa gurina.
Baka jin komai sai kamshin a shiyan mu na soyeye da dafe dafen kayan dani idan mun shige daki yana gida kowa yazo gurina ban fitowa sai dai mutum yayi sallama ya gaji ya tafi don bai bari in fito gurin mai shi.
Ni da kaina naje gidan mu tare da kudin damu ka warewa yan uwan mu dubu sittin kacal da kyat da boni daga cikin kudaden namu.
Banyi mamakin ganin canjin fuska ga kowa na gidan ba sai dai lokacin nima kaina na hayaki sai ban damu ba ashe da safe Jamil ya bayar da wanan takardan daya ce zai rubutawa baba kabir din.
Shine sauyin fuskan dana gani a wurin yan gidan namu a lokacin jin sallama na yasa baba kabir fitowa ya kirani zuwa falon shi.
Inda ya fara magana bayan kara gaisawan da mukayi yana fadin nasan da sanin ki jamil ya rubuto min takarda akan zancen kudin ku don haka na aika kowa yazo don kuji komai da kunnuwan ku.
Ba a dauki lokaci ba naga su baba musa sun iso gidan kowa ranshi a bace damu yake lokacin sumaiya ma ta iso daga gidan mijin ta don unguwan su nada dan nisa da namu.
Ran baba musa ya baci sosai nan sukai muna dala dala karshe suka nuna muna bacin ransu kan sun gane mazajen mu ne suka shiga cikin maganan kudin.
Baba yusha,u yace yanzu kuko nauyi da kunyan wanan bawan Allah baku ji yadda kuka rufe ido kukai mai kan abin duniya shifa kudin gado sai wanda Allah ya nufa ya more zai more mai a duniya.
Zaku iya rama mai irin dawai niyar da yayi dakune koma ince yakeyi dakune a duniya nan don dai mu kun san ba hali muke dashi ba da zamuyi maku.
Cikin fushi baba kabiru yace in don kudin hakkina ne dana karba ya tashi ya mike ya dauko kudin yana fadin gasu na yafe ku kara da naku.
Tunda kuna ganin na cuce ku ne na zallunce ku kuka na fara yi don nice babba kafin in magana kanin mu karami daddy ya mike yana fadin baba wallahi ni kan bada ni akai wanan shawaran ba ban ma san suyi wanan shawaran ba yana fadin haka ta mike ya fice daga fallon namu.
Kuka nima nake ina nema gafaran baba kabir don hankalina ta tashi matuka yadda naga yana kuka akan mu sai abin ya daga min hankali sosai.
Karshe dai muka bashi hakkuri muka fito rayu kan mu babu dadi kan rabon kudin inda kanina baffa da summaiya suka kyankyashe idanuwan su mirsisi basu kunyan kowa.
Mun ba anty wani abu ba wani mai yawa bane don mun san ta wahala da rayuwan mu dubu ashirin muka bata baba ma haka sai uwar gidan ra goma da amaryan ta.
Tace mu barshi ita kan ba zata karbi kudin mu ba gaskiya da kyat na samu na bar mata kudin a dakin ta na fito na tafi inda yaran baba kabir kaf suke muna kallon banza don mun taba masu mahaifin su.
Sai gashi bayan sati biyu banda ko sisi a hannu na dama wurin shi koda na lalabo sai cewa yayi ai kudi sun kare babu komai a hannun shi kuma.
Raina yayi matukar baci sosai da jin hakan ba yadda zanyi dole na kyale shi don banda yadda zanyi dashi kan hakan .
Sai lokacin angulu ta fara komawa gidan ta na tsamiya kuma ya fara tayar da halin shi shikan ya samu ya yi dinkuna na alfarma daga cikin kudaden sosai ya sayi duk wani abinda yake da gurin saye din kafin kudin su shigo a hannun mu.
Dan haka baida sauran takaici kuma yanzu nikan ko kyale da yar diyata bamu samu ba daga cikin kudaden na dai samu na sai wa kaina ledan daki da dutsen guga da wani tsohon tv na hannun don nagaji da shiga dakin yan hayan gidan mu kallo.
Don Anty tasha min fada tana nuna min illar yin hakan da nakeyi na zuwa dakin yan gidan mu kallo wanda a lokacin ban daukan hakan a komai gare ni.
Amma da take nuna min illar yin hakan sai naji abin ya fita mun a raina ko sunce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login