Showing 66001 words to 69000 words out of 106121 words

Chapter 23 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

01 Jan 2025

7528

Tun wanan lokacin ya sa wana mutumin da matar shi agaba gidan da anyi abu zai fara fadin ba mutumin arziki bane dama ya kamata su tashi su bamu gida.
Sai dai wanan karon baiyi nasaran haka ba kaina don ban bashi hadin kai yadda yaso ba yake min a baya kan yan hayan mu.
Sannu a hankali na samu na biya kudin bashin da ake bina koshi da taimakon dan abin da nake samu a wurin baba kabiru aboye bai sani ba na biya.
Don daya sanin karbe kudin zaiyi ba wani wuyan aiki bane a gurin shi don haka yanzu na fara boye mashi komai nawa nima saboda yanzu na fara fanhintar shi.
Don a gaba shi maman jinior zata aiko batun kudin ko tazo da kanta yana ji bai cewa komai idan kuma na mashi magana sai yace idan ta samu zai bayar.
Ko hakan da yake fadi don mahaifin shi wanan karon ya fita bayan shi yayi mashi fada sosai har ranshi ya baci shine yake fadin wai zai biya da baki don baida niyar biya din.
Tun da yaji baba yace yana nema na yana daki kwance yaron yana fita zubur ya fito daga dakin yana tambaya ko lafiya baba ya aiko yans nema na ?
Nace ban san ko may yake nema na dashi ba in dai na gama zanje in ji dalilin kiran yace ki tafi ni zan karasa sauran akin daya rage din.
Ban ki nasa ba na gyara jikina na nufi gidan namu inda na samu baba na gida bai fita ba baya mun gaisa ne yake fada min zancen kudin mu ne ya taso bayan long proces da akayi yanzu ranan monday zamu je muyi signing din documents din a Abuja.
Wani irin farin ciki ne ya turnuke min zuciya ta idan mai karatu bata manta ba na fada maki kudin an kasa su uku ne kadan kadan suke zuwa muna ke nan.
Murna a gurina ba a cewa komai hakama dana koma gida da zumudi Jamil yake tambayana lafiya dai ko ?
Ba bata lokaci na labarta mai abindake faruwa ya wani washe baki yana murna tare da fadin wai Allah dai ya jikan baba.
Karo na farko danaji yayiwa mahaifina addu,a ke nan ita mahaifiyar mu ba a magana kanta.
Nan wuyan talaucin da muka fito ne a ciki yasa yai wanan addua,an haka da bai ma san yazo mashi a baki ba a lokacin.
Nan ya fara haba haba dani bai fita yawo sosai sai lokaci lokaci yakan dan fita ya dawo ana jiji dani da yarana lokacin har fita yake da yaran wurin fira kofan gida inda suke taruwa.
Yanzu idan mun zauna baida magana sai na tsara yadda za,ayi idan kudi sun shigo hannun mu har da fadin zai fito dani gari don zai sai min babban waya irin na kowa ni da ko nokia banda shi.
Sai yan uwa idan sunji haushi rashin wayana ya damay su zasu dan sai min yar nokia in rika bai kai wata daya a hannun na idan matsi ya kama mu in sayar in sai wani abin.
Gashi nima bakina yasaba da dadi irin na jamil yanzu ba ko wani abinci nakan iya ci ba in ba yan kayan kwalama ba da sauran su.
Ni dai ina jin shi yana ta tsara yadda yake so abin ya kasance wanan karon dariya nakan yi a raina kawai do ko da tsiya sai na gyara dakina wanan karon.
Nagaji da rufe kofa da boye boye wa kawayena idan sun zo gidana har kunyar yadda dakina yake nakeji don ko na wata tsohuwa yafi shi dadin kallo.
Ranan mondaya shi da kanshi ya rakani gidan baba kabiru tunda asuba don asubanci zamuyi mubar garin don mu isa da wurin during warking ahours.
Sai dai bai yarda mutanen gidan mu sun gashi ba yana isa kofa saida yaga na shiga ya koma shi bai shiga ba lokacin.
Nasan nasa wayau do kada aga zalaman shi a fili ne yasa ya boye hakan ya labe daga kofan gida yaki shiga daga ciki.
Mun isa lafiya mun samu wanan kudin a yadda sukai muna bayani suna da yawa sosai don haka zai fi na farko dana baya yawa ke nan .
Murna fal a zuciyana baki har kunne muka dawo gida da farin ciki zuciyar mu fara kal da jin wanan zancen.
Na samu ya gyara daki ya dafa abinci ya jera min yana jiran dawowana kamar ance mai da kudin zamu dawo dayani daga zuwan mu.
A gidana baba ya sauke ni suka tafi ina shiga na samu yana zaune yana jirana a cikin duhu duk da babu wuta a lokacin amma haka yake zaune kamar maye shi kadai a falon mu.
Nan yai muna sannu da zuwa ya karbi goyo na yana tambayan ta ya hanya kamar yarinyar ta iya magana lokacin.
Yace bari yai mata wanka don kada gajiyan hanya ya hanata barci shi yai mata wanka ya bata abinci taci ta kwanta tunda dama a gajiye muke.
Ya fara tambayana yadda akayi ina labarta mashi yayi wani irin ihun murna tare da fadin kice zamu faso gari ke nan sosai wanan karon.
Da yakw dan duniyan namiji ne bai barni na huta ba duk ko da gajiyan dana debo a hanya sai da ya kusanceni ranan .
Don kawai ya kara gyara min rai niko ina jin dadi a raina ga miji na tatali na ana sona don sai ka dauka ya daina halinshi ne yanzu na bariki.
Tun wanan ranan suka shiga yin meeting dashi da mijin kauwata wai idan kudi sun zo ga yadda zasuyi muna dashi .
Zakace abin na Allah ne ake shiryawa lokacin don sunce bazasu yarda su baba kabiru suna muna wayau ba ko wani lokaci duk da fa su baba basu karban ko kwandala daga cikin kason mu din.
Amma sun ce wai wayau suke muna kawai don sun dauke mu yara kanana suna yi muna yadda sukaga dama da hakkin mu .
Muko mun hau munga ga masoyan mu na asali masu kaunar mu da zuciya daya don Jamil yana cewa.
Da ke nan da baisan ciwon kan shi ba suke cinye kudin ba abin kwarai da mukeyi dashi yanzun kan tanadi sosai za a yi muna gaskiya.
Fadin haka da yakeyi yasa na kara yarda dashi sosai don na dauka talaucin da muke ciki yasa yanzu yayi hankali ne.
Mun dauka wani sati kudin zai fito a yadda aka nuna muna a can da mukaje abuja sai gashi shiru har mako uku ya share ba wani labari kuma na kudin .
Nan dai ya shiga kuma sake magana yana fadin kila ma su baba ne da sherin su kudin an sako basu fada muna ba kai ba dai abinda bai fadi kan kudin.
Har turani gida yayi in koma in tambayi baba cewa munji shiru baba dai yayi dariya yace hadiza banda abinki ko wancan karon ai haka akayi ko ?
Sai lokacin da muka ji su kin san gwaunati ba ayi mata dole tunda ba abin mutum daya bane abu ne na taro kowa dake cikin system din jira yake yi kamar mu.
Na dawo gida na fada mai abinda baba yace ya ja tsuki don takaicin da yake ji a lokacin yana fadin wanan shegen gwaunatin basu da tausayi wallahi.
Yakan yi maganan kudin nan kusan sau uku ko hudu a wuni shi dai ina ganin lokacin damuwan shi bai wuce yaji ance kudi sun shigo muna ba shine nasa.





ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU.
5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Ranan dai ban iya aikata komai ba a gidan ko abinci ban dafa ba duk jikina ya mutu ina jiran shigowan jamil din gidan inji inda kayana suke.
Wanda nasaye da hakkina na rufa mai asiri dashi na dawo yanzu ban samay su dakin ba kuma ai dole hankalina ya tashi sosai fiye da tsamani.
Kamar yasan ina jiran shi sai ranan kuma bai shigo gida da wuri ba sai can cikin dare sosai ya dawo lokacin har barci ya fara sata na a inda nake zaune a falo.
Jin karan bude kofan shi na mike zubur dani yace may ye haka ban bari ya rufe baki ba nace Jamil ina kayana suke don babu komai a cikin akwatunan ga baki daya dana bude.
Yace cikin dakewa wasu kaya kuma nace kayan sunana da muka saye yace suna ciki mana ina ruwana da kayan ki tunda muka saya.
Nace abar maganan wasa ina kayana suke yace wai bai sani ba yana kokarin shigewa daki na mike da sauri nasha gaban shi ido rufe na kara tambayan shi.
Yace wai kina haukane ko may ko kin mai dani barawo ne da zaki tsare ni kina tambayana kayan ki ko kinga ina zama a gidan ne ni ?
Hannu na dora a kai na fara zunduma mashi ihu a dakin ina fadin wallahi ban yarda ba don babu wanda zai shigo min daki bai bar alama ba.
Ganin zan tayar da mutane gidan yasa yace ki bari zan maki bayani da safe don Allah yana fadin haka ya shige daki ya kwanta abinshi .
Haka na kwana ina juyi duk tunane ya hanani barcin kirki washe gari ma da wuri na tashi don kada barci ya dauke ni ya gudu.
Ina cikin aiki ya fito na bar abinda nakeyi nace Jamil ina sauraren ka yayi kamar bai jini ba yana kokarin ficewa dakin.
Nayi sauylrin tarewa ina fadin wallahi ba inda zaka sai ka fada min ko inyi karan ka ya wani juyowa yana fadin ni zakiyi kara akan kayan ki hadiza ?
Nace wallahi kuwa idan baka fada min inda kakai min kayana ba yau a gidan nan ganin da gaske nakeyi yasa shi fadin suna wurin dinki.
Cikin zaro ido nace duka kake nufin kakai dinki turmi talatin da wani abu , yace bake kika ce a dinka ba shiyasa na kai dinki duka.
Wani wawan ajiyan zuciya na sauke ina fadi yanzun naji magana dai sai dai har yanzu zuciyana bai yarda cewa duka kakai din ki ba gaskiya.
Yace yanzu dai na gane abin hannun ki ya fara rufe maki ido da har kike son tayar min da hankali akan zanuwan banza naki ki jawo min mutane.
Nace ai dole don kudin nan kaima kasan ban ci komai a cikin su ba don may ko ba zan tayar da hankalina ba akan su.
Kowa ya sai abin kwarai da kudin shi sai nice zan banzatar da kudina a sakani a baki gashi dama mutane na fadin nice banda arziki cikin mu da an bani kudi ka cinye.
Yace inji uban wa ke fadin haka ya wani gayayyako ni yana fadan karya har ya samu ya fice daga gidan dama abinda yake so ke nan ya samu hanya ya sulale ya fice.
Ashe shi wayau shi daya kwashe kayan ace sata aka shigo akai min da bana nan shine hikima shi na turani gidan su in yi kwanaki acan.
Sai kuma wani abinda ban sani ba mai ban mamaki da daure kai da lamarin Jamil shine ashe wai hayan kaya nan sukayo dashi da Ruth a shago.
Sukayi alkawarin zai dawo masu dashi da zaran an gama suna danawa da na baby din ga baki daya har akwatinan gaba daya na hayane.
To ina yakai min kudin da ya karbe a hannu na din daya karba wanda yasa na sayar da filin mu a wani gari daya matsa muna sai da muka sayar.
Duk abinda nakeyi yin shi kawai nakeyi hankalina bai kwanta da zancen kayan ba don tun ranan da mukai maganan ya shiga wani tsare gida yana daure fuskan shi gare ni.
Kyale shi nayi sau da aka cika sati biyu na kara tuntubanshi kan zancen dinki yace yaji kawai ya fita bayan kwana biyu mm a sake tambayan shi kuma.
Ranan dai fada mukayi dashi sosai kan kayan inda nasha kuka na sosai don na fahinci babu dai kayan kwana kwana kawai yake min kan kayan.
Washe gari tun da safe na shirya sai gidan mu gurin iyayyena inda na samu dama irin ranan da suke jira gare ni ke nan yazo.
Sai da suka gama saurare na suka dora a inda na tsaya baba bai gida a lokacin sai da ya dawo ne anty ke fada mashi ina nan na zo gida mun samu rikici da Jamil.
Yasa a kirani nazo ina kuka nake fada mai komai har na gama murmushi baba yayi tare da fadin ni dama ban shirya ma zuwan irin ranan nan bane a rayuwana.
Ko ban san wanda na nace sai na aura din bane wai dama sin san abinda zai je ya dawo ke nan sai dai a lokacin da suke kokarin nuna min hakan ganin su nake a matsayin makiyana a gare ni.
Ina kuka nace baba nayi nadaman auren Jamil a rayuwana don ya gama dani gaba daya a rayuwana wallahi.
Baba yace hakuri zanyi in koma don ga zuria a tsakanin mu yanzu sai dai in koma inyi hakuri da halin mijina don su ba zasu taba kashe min aure ba in dawo ina kuka dasu daga baya.
Naji haushin wanan maganan na baba gaskiya sai nake ganin don mahaifan mu basu da rai ne sukai min hakan.
Kwanana uku a gida kafin Jamil yazo da yannan shi maza inda suja samu baba ya aika a kirani da su anty muka samay su a falon shi.
Baba ya bukaci in fadi magana na nan dai na shiga jero magana yan uwan shi sai assha suke fadi tare da fadin su basu san komai ba a kan wanan abinda na fadi jamil din yana min.
Ranan dai ya jishi ba dadi do a gurin yaso yai ma anty da ta zake tana kokarin kwatar min incina a gurin shi don shi baba yana sakaya wani abu don shima nashi ne.
Nan dai anty tayi mashi tas ta zage shi sosai saida ya raina kan shi sosai a lokacin suka dai ba da hakkuri tace zai karbo dinkin idan tellan daya kaiwa ya dawo.
Aka ba da hakkuri ban koma ranan ba sai washe gari inda anty ta saka ai min kitson kaina da kumshi ta bani kaya masu yawa .
Irin su zanuwan gada da kayan aiki da tufafi masu yawa da dare suka mayar dani dakina mun samu bai gidan har suka tafi bai dawo ba.
Sai dare can ya dawo bai kwanta ba yai min dadin bakin shi daya iya yana fadin ya dauka ni mai rufa mai asiri ne ba zanje gidan mu da wanan maganan ba.
Lokacin ne yake ban hakkuri kan kayan nan dai babu su inyi hakkuri idan ya samu hali zai saya min wasu da yardan Allah ya kare cikin dadin baki da bani hakkuri.
Haka na hakkura na shanye zancen kayan a raina na dogara ga dan albashin dake zuwa min wanda yanzu munyi wata uku ba a bamu ko sisi ba na aikin mu.
Haka nake ta faman kama kama ina juya rayuwa a yadda yazo mi din sai daga baya nake jin gaskiyan maganan a makwabtan mu .
Wurin wanan kawar tawa take fada min yadda zancen yake inda take fada min itama a gidan da taje kitso don kawar matar ce bata san suna tare ba take bata labari na.
Inda take fadin maza suna cuta wallahi don abinda akai min din ko da bata sanni ba na bata tausayi sosai raina naji ya baci sosai kafin ta gama bani labarin a gidan ta.
Inda nayi mata sallama na fito ban zamay ko don ko gida ban shiga ba sai gidan da mahaifin shi yake na samay su da kuka ina fada masu abinda naji a gari dan su yayi min don ni yanzu kunyan in koma gida da wanan maganan nakeji.
Budan bakin mahaifin nasa sai fafin yayi ina da aiki idan zanyi amfani da jita jita a rayuwana su masu fadin haka kyashine da hassadan dan shi yasa suke kulla mai sheri.
Don kawai su bata wa dan baidai goyi bayana ta ko ina na fito sai ya tare dan nasa ya kare shi haka na taso da bacin raina na dawo gida naci kuka na ba wanda zan fada ma wanan zancen na takaici ya saurare ni.
Haka ya dawo gida ya samay ni yana wani cika yana batsewa don ma kada inga fuskan yi mai magana ban kula yadda ya dawo min ba.
Na shiga fada mai duk wani kalma daya zo min a baki akan indan har maganan dabaji gaskiya ne na roki Allah ya dubi maraicina ya saka min a gare shi shi da Ruth da duk wani wanda ke da hannu a cikin cutana din da sukayi.
Ruth kan itama bai barta ba don tatsanta yake sosai yayi mata alkawarin zai aure ta idan ta musulunta duk da kusan haihuwan shi da tayi .
Amma haka munafukin yayi mata alkawarin aure a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login