Showing 75001 words to 78000 words out of 106121 words

Chapter 26 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

01 Jan 2025

7549

wanan ba na dai dauka yawan jin zafin shi ne yasa bai iya kwana a cikin gida ashe munafuki dawata manufa yake min hakan.
Ranan ko da na fito da dare sauro ya damay mu sai ban gashi ba wurin da yace yana kwanci din abin ya ban mamaki sosai a raina.
Da safe daya shigo nake tambayan shi ina ya kwana an dauke wuta bamu da maganin sauro na fito da dare ban ganshi ba.
Yace cikin dakewa ai wajen gida ya fita inda samarin unguwa ke kwanci da dare can yake kwana tare dasu sai ban kawo komai a raina ba danaji ya fadi hakan.
Ranan ina zaune na gama girki da rana sai ga matan yayan shi din nan sun shigo gurina na tare su tare da basu ruwa da abincin dana gama.
Sunci sun sha nake tambaya su ina suka fito suke ce min sun fito duba watace a cikin unguwan nan sai ban mai da hankali in san ko wacece suka zo gani ba .
Wai ashe guri Ruth suka zo duba bata da lafiya sai bayan kwana biyu nake ji a gurin wata yar unguwan mu wai ta gansu ranan sunzo gaida Ruth tayi fama da zazzabi.
Abin ya matukar bata mi rai naga yadda muke dasu wai ace sun zo duba farka miji na kuma gashi banda gidan zuwa sai nasu idan na tashi fita unguwa.
Ban kyale su ba har gidan su na samay su suna faman yi min rantse rantse wai ba can suka fito ba ban wani tsaya ba na dawo gida.
Wanan abin sai da ya hadamu fada da jamil yake cewa wai bakin kishi zai kashe ni idan banyi hankali ba nan dai muka kwasa dashi ranan sosai.
Sai banda wani damuwa yanzu sosai don ban gama turmuje yan kudaden dake hannu na ba lokacin don haka yake bina a sannu.
Mijin yar uwana ya samu aiki koyarwa a university da ke kano don haka ya tafi ya barta a nan inda take dan zuwa wurina tana debe min kewa a gidana.
Nan take fadin ba zata yarda ya barta a garin mu ba bin shi zatayi idan ya samu wuri banga laifin ta ba, da take fadin hakan lokacin don zaman mace kusa da miji yafi.
Sai dai ida bata samu anje da ita din ba tayi hakkuri zuwan shi biyu yana komawa inda suke daukan rikici dashi.
Har dai ya yarda zai tafi da ita bayan iyayyen sun sa baki a cikin maganan nan ta fara shiri sai dai bamu fada a gida ba duk shirin da takeyi sai daga baya muka je tare muka fada masu batun tafiyan nata.
Sun yi murna da farin ciki sosai don sam babu bakin ciki ga alamarin su damu sai nuna kulawa da kauna a gare mu.
Wanan abin wani lokaci yana samu jin kunya har da muka fito muke maganan nan dai take fada min wallahi inbi yan uwa in daina bin zancen Jamil da yan uwanshi.
Sosai taimin magana a cikin natsuwa yadda zan fahince ta na kuma fahinta da abinda take nufi don banyi sanyi a gwiwa ba na fara zuwa kai da kai ina ziyaran su.
Tun kan Summaiya ta bar garin sai dai wani abu daya bata muna lamarin shine ita kanta summaiya tayi abinda har ni ya bata min rai da ita sosai.
Don kaya dakin ta gaba daya har kujerun da muka canza ta sayar ba tare da ta fadi a gida ba bayan munce gyara muke son yi a gurin baba kabiru da iyalan shi.
Don sun muna komai da akeyi a duniya nan gaskiya wanan abin da tayi ya bata ran mutanen gidan baba kabiru din sosai don ta fifita uwar mijin ta gare su.
Kayan dakin nata ma karshe akace uwar mijin nata ke amfani dashi kin san abu ga mai kishiyoyi su suka kwarmata ma gidan mu wanan zancen.
Ba yadda zasuyi damu dole sukai hakkuri suka bar zancen duk ko da ransu ya baci ga hakan da tayi masu din don sun fahinci dai bamu dauke su a maysayi iyayyen mu ba.
Mun fi fifita mazan mu a kan su dole kowa yanzu ya kawo ido yasa muna aga iya gudun mu da mazajen namu da muka dauka uwa uba a gare mu.
Sai bayan wucewan su magana ya fara tashi wai da kudin ta mijin ta ya nemi aikun daya samu wai wanan kangon da muka saye babu nata a halin yanzu.
Waya na nema na kirata na fara mata korafi sai bata bari nakai ayya ba ta hau fada tana fadin wai ni a ina naji wana zancen wanan magana ba gaskiya bane duk wanda ya fada mun kuwa.
Haka dai magana ke faman yawo kan mazajen mu sun cinye muna kudaden mu duk wanan maganan da ake fada baba kabiru baice damu kala ba kan zancen mazajen namu.
Kuma ya hana iyali shi suyi muna magana don haka ne zancen bai daga sosai ba yadda wasu suka so cikin dangi a dauki mataki akan mu.
Yakan ce kubar yaran nan inda kuka gansu idan masara taji wuta da kanta zatai kara ai ba sai an tambaye su ba duniyace.
Don yanzu ana magana zasu ce kuna son ku kashe masu aure ne don baku kuka haifesu ba sai yan uwa suce kwarai kuwa Alhaji kabiru.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Na samu wannan kawana dake makwabtan mu tasa mijin ta ya dauko muna manja da garin rogo a can inda yake da zai dawo.
Ita nata zata aika dashi ne gidan su a sayar ni kuma tace in saida nawa a nan cikin unguwar mu din tabar min sai idan mun sayar zamu tura mai kudin ya kara sayo muna wani.
Alhamdullahi don sana,ar ta karbu min a cikin unguwar tamu da farko da Jamil ya gani ya fara tambaya a ina na samo kudin da na sai wanan abin ?
Ban so in fada mai ba amma danaga matsin yai yawa yana tambaya don zargina yake ko na samu wasu kudine naki fada mai don har bugun cikin baffa kanina yayi a waje bai ji komai ba.
Dole na fada mai inda na samu kayan ina sayarwa din nan ya hau fada wai yarabani da wanan matar don ta fini wayewa shi bai son rikici da dauko magana.
Na dai kyaleshi yayi fadan shi ya gaji ya sa mun ido mutane sai shigowa suke dare da rana suna fadin abasu manja ko gatin kwaki da sugar.
Dadi dadi na hada kudin farko don a cikin sati biyu komai ya kare muka tura ya sake turo min da wani don ita ma an sayar mata da nata acan gida da ta kai.
Wanan ma yayi saurin karewa da wuri don yanzu mutane sun sanda ina sayarwa kuma a cikin sauki na hada kudin mijin kawata cif da sunan washe gari in kai mata ta tura muna wurin mijin nata.
Washe gari tun da safe Jamil ya fita kan zai tafi wani kauye yace min a can zai kwana don haka sai dana gaba duk aikin gida na shirya na nufi inda na aje kudin don in shiga in mika mata.
Kudi yace dauke ni inda kika aje sai da na dafe kirji na nakai kasa don capert nake dagawa na aje ba wanda yasan inda nake aje kudi a dakin idan na hada su.
Don gudun haka tunda nasan halin shi da kudi ni kadai a daki sai zufa ke karyo min a lokacin don nasan babu wanda zai dauki kudin nan sai Jamil din don ba mai shiga dakina har kurya.
Ko baki nayi a falo nake ajesu basu shiga min daki, don kunyan dakin da nake ji ni kaina ban son wata mace yar uwana ta shiga min dakin.
Don haka ban zargi kowa ya shigo min daki ba na rasa yadda zanyi a lokacin sai daukan diyana nayi na nufi gidan da mahaifi shi yake.
Duk da nasan abu mawuci ne ya goyi bayan dan nasa a lokacin sai banda yadda zanyi dole in je gurin shi da wanan maganan.
A gigice na isa gidan muka gaisa dasu sai na fashe da kuka na fara fada masu halin da ake ciki budan bakin mahaifin nashi tun ban karasa ba shine.
Kina nufin Jamil ke nan yai maki sata ko wa da kika zo nan din ranan matar mahaifin nashi tayi min abin kwarai don kafin in magana tace .
Haba malam idan bata zo nan ba ina kake son taje da wanan abin kunyan kai kullun danka bai laifi itace mai laifi haba a rika yin abu don Allah mana.
Yarinyar ga dai tana iya kokarin ta wurin ganin ta kyautata mashi amma hakan bai isa ba sai an hada da dauke na mutane da ta dauko kuma yanzu mai kake son tace ma mai kudin do Allah.
Ai sunan danka ne zai baci a unguwar tunda kowa yasa halin shi a gareta ido kawai mutane suka sa masu hakanan.
Naji dadin wanan maganan har cikin raina don yau ta fadi alheri a gamay dani bayi son zuciyan da suka saba ba.
Fada ya hau yi da ita amma bata barshi ba dole tsohon ya sauko tare da fadin nawa ne kudin na fada mai yana gyaran zama yace sai dai ayi raba daidai kije ki nemi saura ki cika masu kudin su.
Ya kirga rabi kamar yadda yace din ya bani na fito ina share hawaye ina zan shiga cikin garin nan in samo rancen kudi in ba mutane kudin su.
Ko dana koma yan gidan mu ke fadin matar tazo nema na sai da gaba na ya fadi lokacin haka na daure na shiga gidan ban boye mata komai ba na fada mata halin da nake ciki da kudin na bata rabin da mahaifin shi din ya bani.
Na bata hakkuri kan zan nemo sauran in karkare mata in an kwana biyu hakkuri ta bani na fito ina hawaye gidan zuwa gidana.
Bai dawo ba sai bayan kwana uku ya dawo in da ya samay ni zaune a cikin tagumi ban ko iya mai sannu da dawowa ba don zakace ba kauye ya fito ba da yace yaje.
Shi sai wani fresh yake karawa ni ko ina figewa banda wani kumari a jikina ko kadan daka ganni, kasan damuwa ya samu gurin zama a zuciyana.
Ganin yadda na fuske shima ya fuske ya shiga daki ko may yayi a ciki can ya fito yana fadin ke lafiya kuwa mutum ya dawo ko sannu da zuwa ba zaki mai ba.
Wani kallo na watsa mashi tare da kawar da kaina daga kallon shi ina fadin azzalumi baiji dadi ba wallahi.
Ka rasa wanda zaka yaudara sai matar ka ta gida mai dawainiya da yayan ka duk wani nauyi da hakkin ka ka rataya a kaina .
Haka bai ishe kaba sai ka hada da kudin mutune ka kwashe ka tona min asiri a gari.
Ya zaro ido yana fadin wa kika mayar barawon ki gida nan nace kai tas ya kwashe ni da mari sai da ba dafe wurin don zafi.
Hakan bai sa na fasa magana ba nace ka kashe ni ka huta dama nasan mutuwa ta kake son ji macuci kawai azzalumi.
Ba wanda zai shigo ya daukan min kudi dakin nan sai kai ba zan zargi kowa ba wallahi don kaine ka kwashe su .
A harzuke yace an kwashe din kiyi abinda zakiyi in zaki iya wawiyar banza kawai kan wasu raggan kudin ki zaki dinga kirana da macuci can kudin da ko mota basu isheni shiga ba.
Nace baka nayi da zakace kada in kiraka da macuci ya kara daga hannun zai mare ni na sa mai ihu sai ga yan hanyan gidan a sukwane sun shigo suna tambayan ko lafiya ?
Ina kuka na fara fada masu abinda yai min don duk cin kudina da jamil keyi wanan din yafi bata min rai sosai wallahi.
Don ya nuna min bai damu ba duk halin da zan shiga da mutane ni na sani ke nan shi ba damuwan shi bane hakan.
Bayan sun gama ji ba mai shiga tsakanin miji da mata sai cewa sukayi inyi hakkuri in kyaleshi mu san yadda zamuyi kudin mutane ya fito.
Haka suka dinga fita daya bayan daya suka barmu a dakin dagani sai shi ya shiga kuryan daki ya fito yana fadin wawiya da bata san ciwon kanta ba.
Da kika fada masu kwatar maki zasuyi ko may ai na dauka zasu sa in biya ki ne dole ina kuka nace Allah dai zai kwatar min hakkina ba wani ba.
Mu kai ta yada ma juna bakaken magana har ya gajibya fita daga gidan ya barni nan ina tukukin bakin ciki da na daman auren shi.
Sai mutum daya ne cikin yan hayan mu ya iya mai magana kan abinda yakeyi din bai kyauta ba gaskiya kudi mutane ne fa ya dauka kuma ya sani yaya yake son inyi.
Don Allah Jamil idan ka samu kudi kaba wanan yarinyar kudin ta don hakan zubar mutunci ne a gurin mace wallahi .
Kaga dai duk cikin matan mu tafi kowa hakkuri yau gashi kakai har ta tona maka asiri a bainan jamma,a haka ai irin haka babu dadi.
Jamil din yace ta dai tona ma kanta tunda bata da wayau don kawai na dauki kudin ta zatai min wanan tonon asirin haka a idon jamma, a.
Mutumin ya sake fadin ai abin ne da cin rai jamil yace malam naga fa kana son shiga hurumin da ba naka ba gaskiya yace a, a niba haka na bane ina dai guje maka hakkin marainiya ne a kan ka.
Kada ka manta matar ka marainiyar Allah ce ta gaskiya kowa kuma nan yasa tare kuke cin kudin gadon ta idan ya samu aiko kaga hakan tayi kokari wallahi.
Don ba ko wace mace bace yanzu zaka samu haka nan yace kada ka fada min maganan banza Nasir ina ruwan ka ne da zancen mu wai da matana.
Basuji dadin juna ba da mutumin nan kowa ya fadawa dan uwan shi bakaken magana ya kulla da wanan mutumin da yake gani wai ya raina mashi wayau shi.
Tun wanan lokacin ya sa wana mutumin da matar shi agaba gidan da anyi abu zai fara fadin ba mutumin arziki bane dama ya kamata su tashi su bamu gida.
Sai dai wanan karon baiyi nasaran haka ba kaina don ban bashi hadin kai yadda yaso ba yake min a baya kan yan hayan mu.
Sannu a hankali na samu na biya kudin bashin da ake bina koshi da taimakon dan abin da nake samu a wurin baba kabiru aboye bai sani ba na biya.
Don daya sanin karbe kudin zaiyi ba wani wuyan aiki bane a gurin shi don haka yanzu na fara boye mashi komai nawa nima saboda yanzu na fara fanhintar shi.
Don a gaba shi maman jinior zata aiko batun kudin ko tazo da kanta yana ji bai cewa komai idan kuma na mashi magana sai yace idan ta samu zai bayar.
Ko hakan da yake fadi don mahaifin shi wanan karon ya fita bayan shi yayi mashi fada sosai har ranshi ya baci shine yake fadin wai zai biya da baki don baida niyar biya din.
Tun da yaji baba yace yana nema na yana daki kwance yaron yana fita zubur ya fito daga dakin yana tambaya ko lafiya baba ya aiko yans nema na ?
Nace ban san ko may yake nema na dashi ba in dai na gama zanje in ji dalilin kiran yace ki tafi ni zan karasa sauran akin daya rage din.
Ban ki nasa ba na gyara jikina na nufi gidan namu inda na samu baba na gida bai fita ba baya mun gaisa ne yake fada min zancen kudin mu ne ya taso bayan long proces da akayi yanzu ranan monday zamu je muyi signing din documents din a Abuja.
Wani irin farin ciki ne ya turnuke min zuciya ta idan mai karatu bata manta ba na fada maki kudin an kasa su uku ne kadan kadan suke zuwa muna ke nan.
Murna a gurina ba a cewa komai hakama dana koma gida da zumudi Jamil yake tambayana lafiya dai ko ?
Ba bata lokaci na labarta mai abindake faruwa ya wani washe baki yana murna tare da fadin wai Allah dai ya jikan baba.
Karo na farko danaji yayiwa mahaifina addu,a ke nan ita mahaifiyar mu ba a magana kanta.
Nan wuyan talaucin da muka fito ne a ciki yasa yai wanan addua,an haka da bai ma san yazo mashi a baki ba a lokacin.
Nan ya fara haba haba dani bai fita yawo sosai sai lokaci lokaci yakan dan fita ya dawo ana jiji dani da yarana lokacin har fita yake da yaran wurin fira kofan gida inda suke taruwa.
Yanzu idan mun zauna baida magana sai na tsara yadda za,ayi idan kudi sun shigo hannun mu har da fadin zai fito dani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login