Showing 93001 words to 96000 words out of 106121 words

Chapter 32 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

01 Jan 2025

7527

Kira naji ta kwala min daga dakin na dauka na wani abu ne sai na shiga tana cewa dani ina gadon ki anty ta tsare ni da idanuwan ta.
Kasa amsa mata nayi lokacin take fadin yanzu har gadon kwsncin ku sai da wanan mayaudaron mijin naki yasa kika sayar wai may kika mayar da kanki for god sake ?
Wallahi ban ganin laifin shi naki nake gani yanzu don kece mai bashi kwarin gwiwan yayi maki duk wani abinda yake maki..
Haka nazo nake jin wanan kangon da muka saya don gaba mu samu madogara wai ya sayar da naki ya tafi da kudin .
Tsaye nake daga kofa ina sauraren ta ban san lokacin da na tafi baya ba suuuu zan fadi tayi saurin rike min hannu daga ciki.
Falo ta fito dani tana fadin wai may ye haka ko dama baki da labarin ya sayar da kangon gidan da aka sai maki ne tana fadi tana kokarin zama a kusa dani lokacin.
Wasu hawayen da sukaki tsayawa suke zubo min dafa idanuna lokaci guda na kasa controling din su in mata bayani.
Taci gaba da fadi dama tunda nazo naji wanan zancen hankalina ya tashi gaki da yara mata a gaban ki yanzu kin san lalurar diya mace da kashin kudi ne komai na ya mace kudine tun tana yarinya.
Duk bayanin da takeyi ban iya bata amsa ba ko daga kai in kalle ta banyi ba asalima na lula wani duniyan tunane ga baki daya.
Sallah ta tayar har ta kare ina gurin a zaune ban iya dagawa ba waya ta dauko daga jakkar ta ta kira baffa kanina yazo ya samay mu agidan.
Bai jima ba ya iso nan takw fada mai abinda ke faruwa dani numfasawa yayi tare da girgiza kanshi yace shike nan yana murmushi .
Maimakon in ji haushin mai laifi Jamil sai haushin ya koma ga wanda baiji ba bai gani ba Baffa.
Ban san lokacin da nace zakayi dariya mana tunda ba kai aka cuta ba yace nikan ai ya gama cutana wallahi .
Sai dai ke ki zauna watarana sai ya sayar dake da yayan ki kuna zaune za a ce kuzo ku tafi ya sayar daku ya amshi kudin ku.
Nikan yanzu wallahi kar nake kallon shi duk wani sallon yaudaran shi na sani tunkan ya min shi sai dai ke da yake tsarawa zai cuta amma bani ba.
Ya mike har ya fara tafiya ya juyo yana dadin kuma bari kiji wallahi sai ya biya kudin wanan gidan daya sayar maki ko muyi sharia dashi wallahi .
Yana fadin haka ya fice abinshi ya barmu zaune kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi zagi kan ranan ya sha,shi kwado kwado ba wurina ba wurin kanwata ba da tafini ma jin takaicin shi lokacin.
Bai dawo gida ba har ta tafi kamar yasan muna jiran shi har ta tafi abinta sai dare sosai ya dawo ban jira ko ya zauna ba nace.
Jamil may kake so da rayuwana ne wai Jamil may nai maka kake bina da cicin duduge na hakane ?.
Ke ya fada cikin wani tsawa ya jiyo yana kallona tare da fadin wani irin magana kike fada min haka wai ?
Na fada maka mayaudari kawai azzalumi na yarda da kai nabar kowa nawa saboda kai amma kazo ka cuce ni dan gidan da nake barazanar ina dashi don yaudara ashe ka sayar ban sani ba.
Wani irin kallon mamaki yai min a lokaci guda yana mamakin yadda naji wanan maganan da yake ta boye min wata da watanni.
Jin ban yi shiru ba yasa yace na sayar din idan ban sayar ba kina da kudin da zaki karasa ginashi ne komay.
Ranan kaca kaca mukayi dashi har da dukana yayi kan abina saboda irin kalaman da nake fada mai masu daci duk abinda yazo min a baki fada mai nakeyi.
Sai da yan hayan gidan mu suka rabamu a cikin daren nan abinda ba a taba yi muna ba wani yaji mu muna rikici irin haka.
Asuban farko na nufi gidan iyayyen shi duk da yanzu ba shirin nan da mahaifin shi ke yi dashi irin baya can tunda ya yaudare shi kan kudi.
Mahaifin shi ke nan balle ni haka dai na daure na tafi gidan nice na tayar dasu da barci ranan na shigo da kukana wiwi .
Cikin tashin hankali suke tambayana ko wani abu ya samu dan nasu ne a cikin dare zama nayi nai masu bayanin komai dake faruwa.
Sai tsuki mahaufin nashi yayi yana fadin wanan ai ba yanzu kuka fara ba ko don haka kije ki hakkuri ku shirya kan ku.
Don ko biya akace yayi baida kudin biyan wanan gidan kin sani tunda ya mayar da kanshi mutumin banza a cikin yan uwa.
Ban gane komai ba haka na juyo na dawo gida raina bace ina danasanin zuwa wurin mahaifan nasa.
Ina dawowa gida na samu wani rikici a gida mu don kanina Baffa ne ya bugo sammako zuwa gidan mu ya samu Jamil din da tashin hankali kan maganan.
Rikici sukayi sosai da kanina din kan sai ya biya wanab kudin shiko yana fadin ina ruwan Baffa din cikin magana mu.
Shima ya rikice mai sunyi fitina sosai ranan tsakanin su sai da Jamil din yaje ya kira mijin kanwata suka zo tare aka hade nan tare aka aje magana yace zai biya idan ya samu kudi.
Haka aka aje maganan rayuka dai basuyi dadi ba don Jamil din yan uwana sun bashi mamaki sosai ranan don basuyi mai ragowa ba.
Haka dai muka hau sama muka fado yana ta faman fushi dani da kowa nawq da yazo min yawon sallah bai sakewa dasu koda sun gaida shi sai kace bashine mai laifin ba.
Abinda ban sani ba shine jamil ya na zaman rayuwa can da wata yana yaudarana anan shine yake kwasan dukiyana yana karya dashi.
Kanwata diyar baba kabir ke fada min wanan maganan da tazo gidan mu gaidani da sallah maimakon in kwantar da hankalina in fahinci may take nufi.
Sai na tare ta da masifa kuma ina fadin yace wanan karya ake mai don yace duk wanda yaji yana wanan maganan sai yayi kotu da mau shi.
Tace tau tau nayi shiru anty hadiza dama nima naga abindai tayi yawa ne yasa nace haka tana kokarin tashi tsaye tana saka hijabin ta a jiki.
Haka ta tafi tana tsaron in kwashe in fada mashi bata san bamu cikin dadin raima dashi ba lokacin.
Don bayan kanne na da muke ciki daya dasu lokacin ban yarda na fada wa wani wanan maganan dake cina ba kaf a cikin dangin mu.
Waini ban son kowa yaji aimin dariya da gwai tunda naki uban mu na zabi mijina fiye dashi din yanzu ashe abin ba hala bane.
Abin duniya baya boyuwa don kowa kallo na yake da maganan har baba kabir yasan da zancen sai da kangona da Jamil din yayi yanzu.
Sai yanzu nake jin zafin aikina da baba kabir ya sama min nace aba Jamil ni yar dadi aure gashi yanzu dan wanda aka samo min ina dan samun rufin asiri an dakartar damu shekara biyu da wattani.
Shine dalilin da nake cikin matse sosai ga sana, a ina son yi ba jari mai kwari da zanyi sana, ar dashi hakana.
Sana,a sai da jari mai kwaro don idan baka da jari abin bai kai ko ina sai mutum ya cinye kwana biyu da farawa.
Zaman jiran tsamani kawai muke na sauran kudin mu kullun ko zai fito mu dan samu sa,ida a gurin gashi shiru har yanzu ba labarin komai.
Ashe ban sani ba mijin yar uwata ganin Jamil yaci bulus shima daya tashi sai ya sayar da kangayen kanne na gaba daya su uku ya sai mota dashi da mahaifin shi.
Sai dai nasa akwai banbanci da nawa don da niyar idan ya samu sai ya sai masu wani nan gaba yayi haka kunga ke nan akwai banbanci sosai da nawa matsalan.
Sai dai lokacin da kanina ya samu wanan labarin hankalin shi ya tashi yasa mijin nata a gaba dole ya samu kudi su sai dai saida ya bashi lokaci.
Daya samu ya biya su nasu matar shi ce bamu san yadda suka kare da nata ba har yau don banji tai min maganan komai ba akan hakan.
Haka yasa nasan cikin maza akwai mayaudara da dama sai sa, a abindai ke nan don wasu abin matan su bai ishe su kallo ba balle har su taba.
Sai dai muka bamuyi dace da bagari ba gaskiya musanman ma ni da komai ci yake babu biyan bukata gare ni ko kadan banda riban kwana dashi da nake samu kawai.
Nakan tuna maganan anty da takan fadi kafi auren mu da cewa sun hada bakine su aure mu do sun ga akwai ci cikin al,amarin mu nan gaba.
Gashi ko maganan nata yana zama gaskiya akan mu yanzu muna ganin ishara kala kala daga mazajen namu.
Muda kan bamuji dadin aure ba ko kadan wallahi musanman ma ni dai baka saye kobo a gidan miji sai dai ga wata na wanan bai kan damay ni.
Nidai bukatana shine mu zauna lafiya dashi hakana tunda naji na gani ga auren shi sai dai hakan bai samu ba gare ni tundai yanzu da yasan banda komai da zai kadar nawa.
Sai zaman ya koma kamar na dole yake dani don inda sabo na saba da zaran yaga banda komai ya shiga min wulakanci ke nan kala kala a rayuwan mu ina shanyewa ni kadai.
Babu wanda zan iya fadaw don zurfin cikine ko may ye ban sani ba do ban iya fadawa kowa halin da nake ciki dashi waini may rike sirin aurena .
Haka ma yar uwata take bakajin zancen ta a gurin kowa garama nawa ana gani ana fadi tunda a garin nake zaune tare da yan uwa.
Ita ko ba, a ganin ta ma balle a fadi sai ita ke gani tana shanyewa gara ita idan tazo tana zama da anty da ta yarda da ita su zauna ta fada mata matsalan ta ta sama mata mafita nan take na yadda zarayi.
Niko ko nazo na fada yanzun anty zatace ba ruwanta inje in hakkuri ko an fada min zuwa zanyi in fada ma mijina ya kama masu rashin kunya.
Raina kan baci idan tace haka dani har nazo na daina fadi don ba anty ba duk wanda nakaiwa kukana haka ake ce min kada mutum yace wani abu in kwashe in fadawa mijina.
Ranan ina gida da rana ina wanki sai ga baba ya aiko yana nemana wani tsale na daka ina murna don nasan baba baya nema na a banza saida dalili mai karfi.
Kafana kawai na wanke na jawo kofana zuwa gida tare da dan aiken muka koma gida wurin kira baba din da yake min.
Aikuwa zancen kudin mu ne baba ya nemo ni nan yake min bayanin mutanen sun kirashi akwai wasu takarda da zamu saka hannu a cikin shi kwanan nan don haka in zauna a cikin shiri ke nan .
Nafi kowa murnan zuwan wanan kudin duk da kowanan mu a matse yake kan zancen kudin nan dama a cikin mu.
Sai dai ni nawa yafi na kowa don ga Amira ta isa shiga makaranta mahaifin ta yace shi sai priravert zai sakata bai kaita na gwanati.
Har kaita babban wan mu yace zaiyi wani makaranta dake kusa damu na gwaunati amma ya hana hakan.
Wai sai lokacin da ya samu kudi zai kaita makarantar kudi irin na yayan masu shi karya da burgan aiki irin nasa.
Wai isan baka isa irin na dan tallaka daya dauki duniya da fadi kamar jamil sam shi baison yin abin kananan mutane.
Bai gida ko da baba ya kirani sai da ya dawo nake fada mai kiran da baba yai min din har ya fara fada yana huci wai na fita ban fada mai ba.
Saida nace akan kudin mu ne kuma ka bani baki ko baka nan idan an kiranika ace udn in tafi.
Sai naji yace yanzu akan kudin ne suka neme ki nace eh baba yace sun kira kudin zasu iya samuwa ko wani lokaci.
Sai naga ya kai zaune yana fadin saboda Allah yausje ke nan nace yadai ce zasu samu ko wani lokaci daga yau za a iya kiran mu.
Nan fira ya kaure a tsakani mu duk akan kudin da zasu zo muna ya fara sabon tsare tsaren shi ina kallon shi harda tsuki yana fadin.
Sai dai tsiyan kudin naku kuma sai anjawa mutane rai dashi kafin ya fito mm nace ba dai in ya fito ba za a mu samu.
Sai bude baki yayi yana fadin na matsune kudin suzo wallahi don a uzurce nake dasu dama na rasa inda zan samu kudi wallahi ina da lalura mai karfi a gabana.
Nace idan ma kasarai ga kudin nan gara ka fitar don wallahi dakina zan gyara da sana, a wanan karo ba zan bawa kowa ba gaskiya.
Fadin hakan danayi ya kalle ni da mamaki tare da fadi haka kikace nace haka din ne ma wallahi don ni zaman nan haka ya ishe ni.
Wasa wasa daga fadin haka ya fara daure mun fuska yana wani sham kanshi dani tun ma kudin basu iso ba gare mu ke nan.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Wanda baba ya kira a waya ne yake ta faman magana a cikin wayan sai da baba ya tsnkayi muryan kamar daga sama mutumin na fadin hello hello ya karba shi da sauri tare da fadin.
Hello mr Josua mun tashi lafiya ya iyalinka mutumin ya karba wa baba don wayan a handfree take a lokacin kowa najin mutumin a lokacin.
Baba yace mr Josua dama akan maganan kudin yaran nan ne don Allah nawa ne kudin karshe da aka turo masu nan mutumin ya shiga yin bayani dala dala a waya yadda kudin suke a yadda zamu fahinta.
Yana gama bayani yace ihope ba wani matsala aka samu ba dai ko baba yace yarinya tace abinda ta gani matar nan ta nuna mata miliyan goma sha shidda ne .
Jesus mutumin ya furta da karfi lokaci guda tare da fafin ai duka kudin ma idan an hada bai kai haka ba sai kace kudin wani IG ko commitioner.
Nan dai ya kara bayani baba yai mai godiya ya kashe wayan tare da fadin idan ma baku yarda ba ga nomban mutumin zaku iya kiranshi kuji karin bayani a gurin shi.
Sai baffa yace ta yaya zataga abu a rubuce yanzu kuma ace ba hakana bane ?
Innalillahi inji baba kabir Baffa nine kuma zan cuta maku yau kan kudin ku yace baba ba hakana bane don za a iya canza digit din kudin su rage babu abin da ba a iyawa gaskiya.
Hawaye ke zuba daga idon baba kabiru na bacin rai kan maganan da mukayi yanzu a gaban kowa yace cikin wani murya mai ban tausayi ga mai saurare.
Josua ko zaka iya hada ni da wanan matar da ta bamu takardu muka cika ranan Josua yace kwarai kuwa tana nan office din ta ai bara nakai mata wayan.
Dan shiru ya biyo baya kafin ya kai ma matar wayan ta dauka muna ji ta dauka baba ya fara tambayan ta da fadin ko zaki duba muna takardan mu ji nawa muka saka hannu a kai.
Ta duba tace miliyan shidda ne kamar yadda baba ya fada muna din nayi caraf nace ba naka sha shidda a waje farin rubutun kudin ba ?
Dariya mai ban haushi sosai matar ta kwashe dashi sosai muna jin ta a waya tare da fadin amma ke kina da abin dariya fa.
Luckly muna da komai anan a cikin computer mu muna reconding idan zaku iya zuwa kuzo ku duba da kan ku wanan lamban da kike magana.
Shine serial nomba na kudin ku nan ta kara karanto min shi wanda shi din ne na gani a can sai nace bashine kika ce min kudin namu ba.
Tace ke mahaukaciyar ina ne da za a baku wanan kudi haka mai uban yawa kiyi abu na masu hankali mana.
Zaku iya zuwa ku duba komai na nan wurin mu a rubuce cikin computer mu kuzo ku duba shaaa ta katse wayan.
Muryan baba musa ne ke fadin assha wanan hali a ina kuka samay shi ne haka kan kudi ku rufe ido kuciwa kowa mutunci wanan bawan Allah idan baku gode mashi ba bai kamata ku nuna mashi haka a fili ba.
Baffa yace baba ba hakana bane shi sharian kudi idan yazo ds kowa kana iya yin sa ai mu abinda ta fada muna ne ta gani muka sa rai.
Baba kabiru dai bai iya fadin komai ba lokacin sai hawayen da yake sharewa baba yushau yana bashi hakkuri kan maganan.
Nan dai baba musa ya zage mu tas yasa mu bawa baba kabir di hakkuri wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login