Showing 27001 words to 30000 words out of 113548 words

Chapter 10 - DANA SANI BY AMNAH EL YAQOUB .pdf

bamuda
wannan dabi'ar ahmad"

yafada yana goge qwallar idonsa

Ahmad yace "tahir nayi asara, wallahi na cuci wadda ta yarda Dani sosai"

Tahir yace "to Amma menene sanadi? Meyakawo hakan?"

Ahmad yace "Allah ne masani tahir, nayi DANA SANIN daukarki feenah har zaki fita nahanaki,
wallahi nayi DANA SANI Akan abinda na aikata miki feenah"

Tahir kawai kallansa yake, shi kanshi ahmad din yabashi tausayi,
Tahir yace "ahmad toko akwai abinda ita yarinyar tayima har hakan ya kaika ga aikata hakan,
Dan nasan kaide wannan ba halinka bane,"

ahmad yace "tahir wallahi batayimin komai ba
Kawai de nasan kalau nafita daga gida, nayi nisa ne ahanya naji cikina yana murdawa, haka
marata tanamin ciwo kadan kadan, to saida mukai nisa da ita ahanya shine al'amarin yafaru
wanda nide a wannan halin ji nayi bazan iya hakura ba, inde bansamu abinda nake soba, "

Tahir yadago cike da mamaki yace" to kaci abinci ne kafin kabar gidan? "

Ahmad yadago kansa yace" banciba, banci komai ba tahir.... Tunanin sa ne ya tsinke dayaga
lemon dayasha kafin yabarshi Akan fridge kafin ya fita
Tsaye ya Mike yana nuna just din da hannunsa, tahir ya Mike yace "me kake nufi?"

Ahmad yace "nasha... Tabbas nasha wannan, shine last abin danasha nafita,"

tahir cup yaje yadauko, ya tsiyaya lemon aciki, nan su kaga kalar lemon ta sauya kadan
Tahir yace "kagani ba?Ahmad tabbas ansama wani Abu acikin lemon nan, kabani kwalin lemon
zanje gida gobe zan bincika duk abinda nagani zan fadama"

Ahmad kawai yazama mutum mutumi

"Aikuwa akwai rashin mutunci agidan nan, 🤣inde nagane dasa hannun wani aciki, wallahi duk
wanda yayi silar bacin ran feenah to tabbas shima saiya tabbata cikin bacin rai,"

juyowa tahir yayi yana kallansa Jin irin furucin dayake futowa daga bakinsa





Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] â£ï¸DANGI DAYAâ£ï¸: 🌱DANA SANI 🌱



Writing by Amnah el yaqoub



Dedicated to my family



24



Baba naganinsa yatashi tsaye cikin ladabi yace" sannu maigida, yakarfin jikin Naka? "

"lafiya baba yauwa nace kwanaki kuwa lokacin danake rashin lafiya bakaga yaran nan sun
shiga part dinaba?"

Baba maigadi yace "yara kuma ranka ya Dade, ai yanbiyu da auta basa shiga su batama kofa"
Ahmad yace "eh baba basu ba haka de Babu wanda kagani yashiga?
Yara ko manya"
Baba maigadi yace "gaskiya banganiba ahmad"
"OK" ahmad yace zai juya yatafi
Sai yaji baba maigadi yace "saide ko in kafin rashin lafiyarka de nake tunani"

Ahmad asukwane ya juyo yace "wacece? Wakaga ta shiga?"
Baba maigadi baiboye komai ba ya kwashe komai yafadawa ahmad
Yaci gaba da cewa tabbas naganta da idona tana gyaran firinji (fridge) ta futo da lemuka tana
maidawa
Huci ahmad yake kamar wani tsohon zaki
Har baba maigadi yace" lafiya kuwa? "
Ahmad baice komai ba yajuya ciki, walaya tasaki labulan data rike ahannunta jikinta yana rawa
ta tsaya Ajikin window
Kawai shawara ta yanke tahada kayanta tabar gidan, saide kafin ta juya taji taku abayanta,
yanayin dayaganta shiya tabbatar masa dacewa itace ta aikata masa wannan aikin kai tsaye
yace Mata "zo"
Moper hannun ta tayar Garin sauri kafarta tana hardewa ta tuntsirar da ruwan da take moping
din, tabishi abaya har part dinsa
Bakin gado ya zauna itama ta zauna aqasa kanta asunkuye
Ahmad yace "menamiki kika cutar Dani walaya?"
Walaya shiru ba amsa
Yasake tambayarta cikin tsawa "nace uban Mena miki kika cutar Dani?
Kudi ko?
Nawa aka baki kika zabi ki lalatamin rayuwa?"
Walaya cikin kuka tace" Dan Allah kayi hakuri, wallahi bazan sake ba "

Dauuu kakeji ahmad ya wanke ta mari, kafin ta dago yaqara Mata wani,
Idanunsa sunyi jajir yace" uban waye yasaki, "
cikin kuka tace" wallahi wani ne nima bansan Shiba, kawai cewa yayi na temaki shi, "ahmad
yace" owk shine kuma kika temakeshi kuka hadu kuka cutar Dani
Nayi DANA SANIN zaman ki agidan nan walaya,
Bazaki fadamin waye ba,? "
Cikin kuka tace" wallahi bansan Shiba, "

belt dinsa yacire yafara dukanta dashi
Ganin yana neman illatata ne yasa tace" ga wayar danake magana dashi, "

karbar wayar yayi ya dokata da qasa
Nan take ta tarwatse
Ihun ceto walaya take nema, Amma ahmad ko ajikinsa, su momy ne da mamy sukaji kamar ihu
ake agidan, aikuwa dukansu suka futo afalo suka hadu momy tace" me yake faruwa ne,"
bukhari ne yace" a bangaren yaya ne," aikuwa suka tafi Gaba dayansu
Zuwansu yayi daidai da Suman walaya, salati momy tafara tana tafa hannaye" anya kuwa
ahmad kanka daya?" Jin sunan data kira shi shiya tabbatar masa da cewa ranta yabaci, kuka
yafashe dashi yace" momy wallahi Yau ko ni ko wannan yarinyar," momy kawai saita fara
hawaye, wannan wacce irin masifa ce ace danka kuma ma babba mai hankali yakama mace
yana duka, hawayan idan ta ta goge tace" shikkenan gatanan kakashe ta ahmad "
tajuya tayi waje, suma yan biyu ganin tana kuka abinda basu taba ganiba sai suma suka fara,

sukabi bayanta, mamy hakima tace" my son me yayi zafi hakane?"
Ahmad cikin kuka yace" mamy wannan yarinyar ta cutar Dani, Allah ya'isa tsakanina dake
walaya," mamy bata kula shi ba, taje ta debo ruwa a fridge ta shafawa walaya, nan take tafarka,
ai tana ganin ahmad ta tashi Zata gudu, yace" basai kin gudu ba, "

janyo ta yayi kamar kayan wanki, yayi waje da ita, mamy tana" ina zaka kaita? Ahmad dakai
nake fa,"
Amma ko juyowa baiyi ba, haka yajata har compound din gidan yayi wulli da ita, kowa kallansa
yake yana ganin ikon Allah, shigowarsa gidan kenan saura kadan yabi ta kanta da mota, da
sauri yafuto yana gyara malun malun din dake jikinsa,� a daidai lokacin ahmad yana nunata
da hannu "karna qara ganin kafarki agidan nan, ko ahanya karki nuna kinsanni, fice ki barmana
gida mayaudariya, azzaluma,"


"saboda gidan Kane? To Babu inda zataje" inji daddy daya tsaya yana ganin wannan karfin Hali
Danme zaka kama yar mutane kayi da duka kowa yanajin kukan ta agari, irin tarbiyar danama
kenan? "
Ahmad cikin share hawaye kawai yajuya Yakoma part dinsa, daddy yajuyo da nufin ya yiwa
walaya magana Takoma ciki, saiyaga wayam ba ita ba alamar ta, maigadi ne kawai yaga fitar
ta, shikuma yasan maigida yanada gaskya shiyasa yabarta tafi ce, inba neman magana ba ina
ita ina shiga bangarensa? Daddy ne yayi ciki, suma su saudat dasu mamy suka bishi abaya

Momy suka gani afalo tana zaune yan biyu suna gefenta, daddy ya zauna yana cewa "meyasa
mu wannan yaron?"
Momy tace "aida ka barshi ya kasheta, shima sai akashe shi,"

"haba hajiya wai meyasa kike hakane?"
Inji mamy

daddy ne yace" ke mabaruka kiramin shi "

Part din taje, yana zaune agefen gado yarike kansa da hannu biyu "
Tace yaya Dan Allah kayi hkr, kabarwa Allah komai," dagowa yayi yaga mabaruka ce, cikin
tsawa yace" ke tashi ki fita, "

Tace" to daddy yace kazo,"

wuf tayi waje tun kafin itama yahada da ita

Tashi yayi yaje, duk suna falon, ya zauna aqasa idonsa jajir, daddy yace." ina jinka metayima? "

Ahmad shiru, aransa yace Tome zance musu magani tasamin nasha naje nayi wa yar mutane

fyade?
Kansa ya girgiza yace" ba komai daddy, "
Daddy yace" au haka kace toshkn, tashi kaje kahada yanaka yanaka katafi Cairo, da tafiyar ka
jibi ne Tona fasa, kaje kahada kayanka katafi yanzu, banasan tashin hankali "

Auta ce tafashe da kuka tafara birgima" Allah daddy a a, nide bazai tafi ba"mamy hakima tace"
maryam kin rufe min baki kosaina bigeki anan?" Momy tace" kyaleta mana hakima, haba
yarinya cefa "

Saudat ce ta dauki maryam tana rarrashinta sukayi sama, suma sauran yaran mabaruka da
twins suka bisu,
Mamy hakima cikin sigar rarrashi tace" my son kayi hkr kayi mana bayani menene tayima? "
Ahmad kansa aqasa yace" mamy Babu komai "
Momy kuwa dama bata tambaye Shiba, yaje can yaqara ta

" Tashi katafi, Allah yakiyaye, zanyi waya yanzu anemama ticket na kowanne jirgi ne inde zaije
masar, ka gaida abi, Allah yatsare," inji daddy

Ahmad baice komai ba, yatashi yayi part dinsa, kayansa yadauka kala uku, sai su singlet,
yadau trolly dinsa Babu wanda ya yiwa sallama agidan yatafi "mad'aar" (Airport)
To dama zaman me zaiyi aqasar ma, feenah taqi tsaya wa yayi Mata bayani, iyayensa sunajin
haushinsa, gara ma Yabar qasar ya huta




** *** **




Yadade yana faman kiranta Amma wayar akashe, Amma Yau cikin sa'ah sai gashi ta shiga,
yana zaune afalo baidade da dawowa daga hospital ba, yana tsiyaya ruwa a glass cup yaji ta
daga

"Amincin Allah yatabbata agareki, ma'abociyar nutsuwa da kamala"

Sake duba wayar tayi, anya kuwa da ita yake? Itade tasan batada biye biyen samari balle tace

Husna tace "pls wake magana?"

"Kina tare da doctor tahir"

Tace "doctor tahir kuma?"

"Yes wanda yayi muku lecture kwanaki harna hanaki shiga" 🤣

Husna ta zaro ido tace" Dan Allah kayi hkr, wallahi bansan kai bane "
Murmushi yasaki yace" no karki damu, dama zan gaisheki ne kuma nabaki hakuri Akan abinda
nayi miki "🤣

Husna tace" Babu komai na gode "

Yace" cewa zakiyi nayafema, "

husna da mamaki yagama cikata tace" to komai ya wuce "

Yace"good girl, dama inasan tambayrki,"

husna tace "ina jinka" yace "kina sona?"

Husna cikin kaduwa da kalamansa tace "so kuma?"

Yace, "nasan bakya sona husna, Amma ina neman alfarma awajanki Dan Allah ki aure ni,
wallahi nakasa samun nutsuwa tun lokacin dana fara dora idanuna akanki, zan baki lokaci
kamar kwana biyu kiyi tunani zan sake kiranki inji me kika yanke game Dani"
diff ya kashe wayar Yabar husna da waya akunne kamar photo




** *** **




Text ne yashigo wayarsa, yana dubawa yaga company dayayi apply sun daukeshi aiki, cikin
murna yafuto yazo zai fadawa yayansa wannan labarin
Yana Zuwa falon yaga yana shiri yace" yaya lafiya naga kana shiri cikin sauri haka? "
Abba yace" hassan yayarka ce batajin dadi inaso nakaita asbiti ne,koda yaushe jikin nata ba
dadi, "

" husna! Husna!! "


" Na'am Abba gani nan,"

Ammu ne yace" to yaya kawo key din saina kaiku Gaba daya, "
Babu musu Abba yabashi key din motar suka tafi asbiti dukansu
Gwajin farko doctor ya shaida musu mama tanada jaririn ciki na wata daya

Da murna suka dawo gida bakin kowa yaqi rufuwa, anan kuma Ammu yasake fada musu
labarin samun aikinsa awani company mota sabo da aka Bude a kano, ance ma wani balarabe
ne ya budewa jikansa, haka sukai ta farin ciki ranar




** *** **



After 2 weeks, hannayensu sarke cikin na Juna, saudat na kuka feenah na kuka, saudat tace
"yanzu feenah mun rabu kenan," feenah tace" haba saudat meyasa kike wannan mgnr, "saudat
tace" Toshiknn yaushe zaki tafi zaria?"

Feenah tace" eto sai nanda 3days, "

saudat tace"ki qara sati daya kafin nan yaya yadawo daga masar, kakanmu yarikeshi yace sai
yayi sati uku kafin nan yahuta zai dawo," feenah saita nunawa saudat tasan komai tace" ai
zaizo zaria," saudat tace" nasani duk da haka
Gashi zabe yana matsowa, "

feenah tace" to menene? "
Saudat ta kalleta da mamaki tace" wai kina nufin bakisan babanmu Dan siyasa bane?" Girgiza
kai feenah tayi gabanta yana ci Gaba da faduwa, saudat tace" kiyi hakuri laifi nane daban sanar
dakeba babanmu sanata ne, nasan kema da a kano kike dole zakisan yan siyasar Garin, yanzu
kuma suna neman takarar deputy governor, " hawaye feenah ta share tace" to Allah ya tabbatar da alkhairi sister", saudat rungume ta tana
kukan rabuwarsu, yayinda feenah take kukan bakin cikin abinda ahmad yayi Mata, haka suka
rabu

Tana cikin adaidaita tana goge hawaye, inda tasan ahmad Dan gidan Dan siyasa ne da bata
saurareshiba, domin kuwa tasan yafi karfin ta, yagama cutar ta yatafi wata qasa wai yana
hutawa hawayen idonta ta goge aranta tace nayi DANA SANI ni nafisa

Mrs Usman ce 🖊
[5/6, 3:32 PM] â£ï¸DANGI DAYAâ£ï¸: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family



23



Tahir yace "haba ahmad, meyasa kake neman sauya halinka ne? Bahaka nasan ka ba ahmad,
pls kadauki kaddara mai kyau ko marar kyau wannan shine abinda manzonmu yace"

shiru kawai ahmad yayi
Saida tahir ya tabbatar yabashi kulawar data dace sannan yadauki lemon yatafi gida
Tashin motar sa ne ya farkar da mamy hakima daga bacci, Amma sai tayi zatan ko ahmad ne
yadawo, tayi juyi taci Gaba da bacci



** *** **



Awannan daren ahmad bai runtsa ba, kawai hango kanshi yake yana Dakar wanda yayi masa
wannan aikin, sai gab da a suba sannan bacci ya daukeshi gamida zazzabi mai zafi, hakance ta
faru awajan tahir ma, dakyar yasamu baccin ya daukeshi




** *** **




Karfe 6:48 natashi, kafafuna na ziro kasa, ba laifi jikin nawa da sauqi, banajin komai saide
abinda baza'a rasaba, falo na futo anan naga kaka tana lazimi, tace" sannu nafi, da naga bakya

Jin dadi shiyasa ban tashekiba, "

nace" aikuwa kaka yanzu ma baccin bai isheni ba,"

tace" sannu, aide da sauqi ko? "

Nace" kaka da sauqi sosai ai jiyan an yimin allura nasan shiyasa naji dama dama, "

tace" to sannu, Allah yasawaqe "

nace" amin, "

nayi "hammam" (toilet)
Bayan na idar da sallah awajan bacci yaqara fizgata dakyar de natashi nakoma gado, naci
Gaba da bacci, saide har yanzu bandaina Jin wani Abu a maqogaro naba, hakan kuma baya
rasa nasaba da bala'in dana shiga jiya




** *** **




Da break suna zaune kowa yanacin abincin sa, shiru shiru suna neman tashi basuga ahmad ba,
mamy hakima tace "nifa banga Dan gidanaba, kode har yanzu murnar company din ce, jiya ma
ina bacci naji shigowar motarsa,"

auta maryam datasa indomie dinta agaba tanaci tadago tace

"laaa ai yaya tahir ne yatafi, ba yaya ne ba,"

kowa yajuyo yazuba Mata ido cikin mamaki,
Tace" nima jiya inata jiran yaya yazo naga baizo ba shine naqi bacci, saida naganshi shida yaya
tahir, wai yayama ba shida lafiya "

Momy ce tace" auta"
cikin mamaki
Mabaruka da basa ga maciji tace "kuma Dan iskanci kiyiwa mutane magana shine zaki zauna
kina ma cin abinci ko Ajikin ki?"
Cikin shagwaba maryam tace" to ina ruwanki, Momy kin ganta ko," tafada tana kallan momyn
ahmad,

Momy tace" yi shiru auta, kyaleta keda yaya ai mutu ka raba"

mabaruka harara ta zabga Mata ta tashi tayi part din ahmad,
Akan gado ta ganshi ya takure kansa yana bacci, qarasawa tayi ta yayeshi, wani zafi ya bugota,
tace " subhanallah, yaya, yaya,"
dakyar ya Bude idonsa tace" ashe bakada lafiya, sannu,"
gyada kansa yayi kawai
Ruwa ta hada masa na wanka mai sauqin zafi, tatashe shi yaje yayi wanka, yana shiga wankan
ta gyara Dakin sannan tafita

Komawa tayi ta sanar dasu halin da ake ciki, aikuwa dukansu suka diba yuuuu suka tafi
ganinsa, ita kuma taci Gaba da cin abincin ta

Yana zaune Akan gado harya futo, suka zo suka zagayeshi, idan kagansu anan ne zaka
tabbatar gidan akwai kwanciyar hankali da hadin kai
Saudat, Muslim, bukhari, Momy, mamy hakima, yayinda auta ta dane jikinsa, bata damu da
zafin da jikin nasa yake yiba
Momy ce tace "waladeey ya jikin Naka? Meyasa bazaka kira waya kasanar mana ba?"

"Momy ai ban kwanta da zazzabin ba, kuma yanzu ma da sauqi,"
mamy hakima tace" sannu my son, "

Yace" yauwa mamy,"

" bani wayarka, "

dauka yayi yabata, ta Nemo number tahir
Yana dagawa yace" ahmad ya jikin Naka?"

Mamy hakima tace" pls tahir, zoka duba shi yanadan Jin zazzabi kadan, "

doctor tahir yace" to mamy gani nan insha Allah,"

takashe wayar

Mabaruka ce tadawo Dakin cikin shirin school tace to saiku tashi mu tafi ai, bukhari da Muslim
ne suka tashi, auta ko motsi batayiba, Muslim yace" toki tashi mana,"
tace" nide bazaniba tunda yaya ba shida lafiya, "

saudat ce tace" a a auta, karma ki fara wannan rikicin danba me bullewa bane, oya tashi, "

aikuwa yarinya tafashe da kuka, ahmad ne yace " auta naji sauqi fa, idan kika dawo zamuyi
wasa da jirgi da mota, "tace" to yaya Amma saide in Zata goyeni," saudat tace" wa zai goyeki

yarinya, garama ki warke," maryam tace" Allah saikin goyani," ba yanda saudat ta iya haka ta
goyeta saida ta kaita har mota sannan tajuyo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login