Showing 87001 words to 90000 words out of 113548 words
shiga mutafi kosaina bigeki?"
Tace" nide anty Allah da uncle zan tafi "
Ganin Zata batamin lokaci ne yasa nadauketa nasata agidan baya, sannan nashiga naja motar
muka tafi
Ina driving ina goge hawaye
Ashe shiyasa gabana yake ta faduwa, ashe da wannan azzalumin zan hadu shiyasa
Ina parking agidan husna na futo, nacemata "idan kinga dama ki futo, in kuma wajansa zaki
koma saiki ja motar kije" 橙提
da sauri ta futo ta riqeni, tace "to anty yaushe zaki mayar dani wajan uncle din?" 橙提
Nace "baby Dan Allah kimin shiru"
Cikin gida kuwa husna tayi tayi yafada Mata wacce matsala yake nufi, yace babu komai,
yadauki hannu ya rafka uban tagumi 踫潤蕃踫董橙提
Shi kansa tausayin kansa yake, bare idan yatuna ahmad, ko yaya zasu qare da feenah? 橙提
Suna wannan halin nashigo falon nida baby ina kuka
Sallama nayi muryata ciki ciki, ina Zuwa nafada jikin husna nasaki wani uban kuka mai ciwo
Tahir kasa magana yayi cikin ransa yace shikkenan tafaru ta qare, 橙提 ruwa yaqarewa Dan kada
Dagani har ahmad din Yau babu me wata dabara, kawai inma zagi ne ayi mana, in hakan zaisa
a huce
Husna tace "me yake faruwa kika taho da babyn?"
cikin kuka nace " anty husna shine, wallahi shine azzalumi"
Husna tace "wai menene hakane? Kai kacemin akwai matsala ba yar qarama ba, ita tacemin
shine,"
baby ta kalla tace "ke baby me yake faruwa? Me akayi Mata?"
Baby tace "nima bansaniba, nide naga ta mari uncle,"
tahir cikin ransa yace "ai kadan ma kenan, nayi Zatan abin zaifi haka" 橙提
Cikin mamaki husna tace
" mari!"
"Feenah, tahir wai kuyi min bayani mana,"
feenah tace "anty husna ashe mutumin dayaci mutunci na, ya keta min haddi na, shine wanda
su Abba suka dauki baby suka bashi"
Husna tace "subhanallah" 橙揭潤蕃
Tadubi izdihar tace "baby jeki wajan su mama suna daki kuyi wasa"
Tana tafiya husna tace
" innalillahi, mun shiga uku!" 踫潤蕃
Sannan Ta kalli tahir tace
"Tahir!!! "
Tahir yakasa magana, sai can yace "shiyasa nace miki akwai matsala babba, Amma meyasa
kika cemin nafeesa batasan baban baby ba?"
Husna tace "haka tace mana ai, gatanan ka tambaye ta" ,
cikin ransa yace wato saboda soyaiyar datake masane yasa takasa tona masa asiri,
afili yace "ai ni yanzu bana buqatar dogon bayani, nasan komai
Itama kuma tasani"
Husna ta dubi feenah tace " hakane?"
Gyada kai nayi kamar kadangaruwa nace
" nasanshi anty husna,"
Husna tasake maida kallanta ga tahir tace "wai kana nufin itace wadda kabani labari kace
ahmad yana Santa harma yakasa sauraron kowa saboda ita?" 橙提
Cikin sauri nace "wallahi anty husna karya yake
Mayaudari ne, bayan saida na yarda dashi yaci amanata karshe yaje yayi auren sa" 橙提
Tahir ne yace "am feenah kingane ahmad bashida laifi anan idan kika tsaya kika saurari abinda
zai....."
"Ni kadena min maganarsa yaya tahir, wallahi na tsaneshi"
Husna ma tace " to Amma ya ahmad zai Mata haka?"
Tahir yace "kamarya ya zai Mata haka, kin tsaya kinji yayi miki bayani ne?"
Wayar feenah ce ta dauki qara,
New Number tagani, tana dagawa taji ance
" nafeesa"
Cikin nutsuwa ta amsa, yace "mahaifin mukhtar ne,"
cikin ladabi tasake gaida shi, yace "kema sun turo miki saqon ta layin mukhtar dinko?"
Sai alokacin tatuna da saqon da mukhtar ya turo mata, tace " baba, naga anturo de, Amma ban
budeba,"
muryarsa na rawa yace
" kayya sun saceshi nafeesa, abinda suka fada kenan, wai bazasu sake Shiba har sai yace
yabarki "
Wani ihun kukan naqara sakawa, bansan yaushe baba yakashe wayarba
. Nace "na shiga uku na, wannan wacce irin masifa ce ne?"
Husna da tahir ne suka hada baki wajan fadin "menene?"
Nace "ansace shi, wai wasune suka sace mukhtar"
Husna tace "Yau munga ta kanmu
Satar ango kacokam" 踫潤蕃
** *** **
"Momy Dan Allah kiyi hakuri, kiyafemin, daddy, mamy kuma kuyi hakuri Dan Allah, banyi hakan
da niyya ba, nasan duk abinda zan fada muku bazaku fahinceniba"
Daddy kawai kallansa yake, saida yagama bayaninsa, yace
" kagama? To tunda kasan bazamu fahimta ba karma kasake kayimana maganar"
Ahmad yajuya ya kalli Momy yace "Momy Dan....."
itama cikin sauri ta katse shi, tace "karka cemin komai ahmad nikam na zare hannu na acikin
al'amarinka," mamy hakima ita kanta wannan al'amari baiyi Mata dadiba, itada take Dan goyon
bayansa, shiyasa itama tayi shiru
Rana zafi inuwa quna, Yama rasa ina zaisa ransa, Dame zaiji? Ita waccan taqi kula shi, suma
iyayan nasa sun kasa fahimtar sa
Tashi yayi, zuciyarsa nayi masa zafi, idonsa jajir
Kofar fita ya nufa, yana Zuwa bakin Kofar, yaji kirjinsa ya riqe, yakasa numfashi, cak yaja ya
tsaya, daga baya su Momy sukaji qara, suna juyawa su kaga ahmad a kwance shame shame
babu alamar numfashi
Gaba dayansu sukai kansa da gudu
Daddy yafi kowa shiga cikin rikici, da sauri yace
"adauko mota,"
nan da nan suka tafi asbiti
Kai tsaye asbitin tahir sukaje
, gashi bayanan, Dan haka mamy hakima takirashi awaya tace yazo asbitin sa yanzu ahmad ba
lafiya
Cikin sauri yafuto, husna tace "ina zakaje?"
Yace "ahmad ne wai bashida lafiya, kuma nasan hakan baya rasa nasaba da wannan rikicin
Zanje asbitin yanzu, ki kula da nafeesa"
Nikuwa ina daki ina kuka, ina hada kayana, husna tashigo tace "mekikeyi hakan?"
Nace "gida zan tafi anty husna, duk Garin yaficemin akai,"
Husna ta rungume ni itama, tana share qwallah, tace " kiyi hakuri, insha Allah, Allah zai
bayyanashi kinji, kiyi hakuri"
Nace "to sister"
Tace " shima tahir din yatafi asbiti yanzu wai ahmad din bashida lafiya,"
yatsina fuskata nayi, nace "shiya jiyo"
Ina Gama hada kayana, nacewa anty husna na tafi, gara inje in sanar da Abba abinda yake
faruwa dangane da mukhtar, ita kuwa baby daga Yau tadena zama agidan wannan mayaudarin
Babu yanda ta iya Dani, dole ta rabu Dani na tafi, baby tana dayan seat din, ina driving
mukadau hanyar zaria, munyi nisa ahanya Zahra ta kirani tace " feenah Amma kin fasa Zuwa
ko?"
Nace "Zahra ainakoma zaria ma," tace
" subhanallah Allah yasa lafiya," nace "lafiya Amma ba kalau ba, Zahra naje ganin baby
Wai ashe ahmad aka bawa baby bansaniba,"
Zahra cikin firgici tace
" wai wanne Ahmad" 橙提
nace "ahmad de nawa"
Zahra tace "innalillahi to tayaya?" Nace "ina nasani Zahra, nikam wallahi nadauko yata nabar
musu gidansu,"
Zahra tace "matsala!"
Nace "ina kikaji matsala Zahra, wai ansace mukhtar, dazu dazu babansa yakirani yake
fadamin," Zahra tace
" munshiga uku, wata sabuwa," nace "Zahra bana cikin nutsuwa ta yanzu, mayi waya daga
baya,"
wayar na ajiye muka ci Gaba da tafiya
** *** **
Yana Gama dubashi yafuto daga Dakin din, yasamu su Momy awaje a tsaye, yace "Momy ku
qaraso daga ciki,"
Babu musu dukansu suka shiga office dinsa
Tahir yace "daddy saide kuyi hakuri, Amma ahmad ayanxu kulawar ku yake buqata, yana gab
da kamuwa da ciwon zuciya, kuma kunsan hakan, Amma bakwa kiyaye damuwar sa
To maganar gaskya, abin nasa yayi girma dayawa, yakamata a kiyaye abinda zai dinga bata
masa rai"
Daddy yace "Amma tahir kasan abinda yaron nan kuwa ya aikata? Zinafa tahir
Ina hankalinsa yake? Har menene zai debeshi yaje ya aikata wannan mummunan aikin,?"
Tahir ya nunfasa yace
" hakane daddy, Amma kuma bakusan menene abinda yasa yaje ya aikata hakanba
Ninasan ahmad, kuma nasan abinda ku Baku saniba nasa
Abinda yake faruwa shine ahmad yanada zurfin ciki, bai futo lokaci daya yayi muku bayani ba,
Amma nasan yayi muku bayani Akan maganin da laila tasa masa
To daddy laila bawai tamasa illah bane wajan hanashi haihuwa ba, a a, asanadin wannan
maganin dayasha ne yasa yaje yayi raping wannan yarinyar, alokacin shida ita suna soyaiya
Wannan dalilin ne yasa kai tsaye ya yiwa laila saki uku,
Alokacin da abin yafaru ninaje nataho dashi daga asbiti, wanda anan aka tabbatar da qwayar
dayasha ne yasa shi aikata haka
Damuka zo gida duk kunyi bacci, auta ce kawai bata kwanta ba, kuma wannan yarinyar itama
shaida ce Akan halin dataga ahmad aciki
Haba Momy, daddy, mamy ku yiwa zancena kallan fahimta, anan ina ahmad yake da laifi?
Laifinsa daya yaci amanar soyaiyar dasuke da wannan yarinyar, shima kuma idan ya nemi
yafiyarta Zata yafe masa,
Maganar yarinyar nan baby kuma, ni kaina danake auran yayar ita nafeesa wallahi bansan
yarinyar nan yar ahmad bace, saida suka fadamin dazu
Ita kanta nafeesa batasan agidan su ahmad aka bayar da yarinyar ba, "
Momy taja numfashi dajin wannan zance kamar almara
Tace" eh naji tace datasan agidan yakema da bata zoba
Haba nifa ince, wannan yarinya tunda tazo gidan nan kowa yadauki son duniya ya dora Mata,
ashe jinin muce
, Amma yanzu tahir ace wannan babban al'amari yafaru ahmad yakasa Bude baki yayi mana
bayani,
Yanzu ba Dan Allah yakawo wannan yarinyar ba, munsan gaskya, aida anyi batacciya, domin
kuwa kullum Muslim bashi da aiki sai cewa yake yana San baby"橙提
Tahir yayi murmushi yace
" Momy soyaiyar jini ce kawai"
Mamy hakima tace "kace munkusa kashe danmu batare da munsan gaskiyar magana ba"
Daddy yace "to Allah yarufa asiri," Gaba dayansu sukace " amin"
"Yanzu abinda za'ai, tahir kayi mana jagora gobe muje gidan iyayan ita yarinyar nan mu basu
hakuri kuma mu nemi yafiyarta"
Tahir yace "to daddy babu damuwa, yanzu ma zaku iya tafiya insha Allah zan kula da ahmad
din"
Saida suka koma suka sake duba jikin ahmad din, daddy ne harda tattaba fuskar sa, aikuwa
nan take yafarka, yana dora ido Akan daddy yace, "daddy Dan Allah kayi hakuri"
Daddy yace "karka damu my son, tahir yayi mana bayani, Amma karka sake boye mana komai
nan Gaba kaji, Allah ya yafe mana baki daya," Momy tace "Allah yasawaqe mu zamu tafi, tahir
yace zai kula dakai,"
yana murmushi yace "to Momy Nagode," mamy hakima ma saida tashafa kansa tayi masa
addu'ah sannan suka tafi
Suna fita ahmad ya cewa tahir "kai meka fadawa mutanan nan kuwa? Naga kowa sai nan nan
yake Dani,"
tahir yace "ai abinne saida siyasa, cewa nayi ciwon zuciya ne yake gab da kamaka, kana
matakin karshe, ingayama nan da nan suka rikice," 橙提
ahmad yasaki daria yace
" kai Amma kai dinnan bakada dama wallahi"
Tahir yace "wallahi saina koma nafada musu gaskya,"
ahmad yace "haba abokina yi hakuri mana,"
tahir yace "har labarin abinda yahadaku da feenah nafada musu, kuma alhmdlh sun fahinceka,"
ahmad yace " babu abinda zance ma tahir saide godia,"
Tahir yace "karka wani damu, ai yiwa kaine, danna yiwa qanina abinda yadace" 橙提 橙提
Ahmad yace "yauwa wai meyasa ka kirani ne dazu kake min tambayoyi Akan feenah"
Anan tahir yabashi labarin komai
Yaci gaba da cewa "yanzu saide muje gidan kabata hakuri"
Ahmad yace "wa? Ni?踫董 Wallahi ni tsoron tama nakeji"
Tahir ya kwashe da daria yace "ah haba kamar ba ahmad din dana saniba?"
Ahmad yace "wallahi tsoron ta nakeji, idan tahuce Zuwa gobe naje nabata hakuri"
Tahir yace "aikuwa su daddy ma sunce zasuje subawa iyayan ta hakuri,"
ahmad yace "shikkenan ma saina bisu nima
Amma yanzu kam
Inaaa wallahi bazan iya Zuwa wajanta ba, yanda naga lokaci daya ta rikide dinnan Takoma wata
daban kamar ba my feenah taba"
Tahir yace "ai tunda naji baby tana cewa anty ta mari uncle araina nace ai abinma da sauqi" 橙提
Ahmad yace " infadama ban zataba wallahi kawai naji tasss
Kaga kuwa yanzu idan naje ai saide duka"
Gaba dayansu suka sa daria
** *** **
Ina parking gida nashigo ina kuka, ko motar ban rufe ba, baby ce a bayana tana janyo jakarmu
daqyar 橙提
Abba dayake alwala atsakar gida yace
" subhanallah, uwata me yake faruwa haka?"
Ina kuka nace "Abba babu ansace mukhtar
Wai bazasu sake shiba saina rabu dashi
Shikkenan Abba so suke su rabani da mukhtar"
Kamani Abba yayi muka shiga falo, mama tana tambayar abinda yake faruwa
"Abba zoka dau jakar nikam bazan iyaba nakasa" 橙提 橙提
Sukaji muryar baby tana wannan maganar
Abba yace "a a ita kuma wannan daga ina haka?" 橙
Kukanane yaqaru nakasa yin magana
Baby tace "mama kinga ko anty ce ta wanke uncle da mari, kuma tace masa yaci Amana,
Wai nima yarsa ce" 橙提
Mama ce ta rafka uban salati
Abba yace "innalillahi, uwata kina nufin ahmad...."
Tun kafin Abba ya qarasa cikin kuka nace "hakane, shine Abba"
Nan da nan Abba yacire hularsa yafara firfita da ita
Mrs Usman ce 踫
[5/6, 3:32 PM] 儭DANGI DAYA儭: 潤摹DANA SANI 潤摹
Writing by Amnah el yaqoub
Dedicated to my family
54
"Mama zoki janyomin wannan babyn acikin jaka" 橙提
Mama ta kalli izdihar ita ko ajikinta ma, ta abin wasanta take
Dauko Mata tayi, tana karba tayi Dakin mama da gudu
Abba yadubi feenah yace "tashi kishiga ciki"
Ina goge hawayen idona nayi ciki, Abu yahadu yazamemin goma da ashirin, ga haduwa ta da
ahmad ga batan mukhtar
Harara na zubawa bangon dakin kai kace ahmad dinne awajan, nace sai wani qiba ma daya
qara dakyau kamar bai zalinci yar mutane ba 橙提
Kaina ne yasara, alamun ciwo, Dan haka kawai na kwanta tare da rufe idona
Mama ta janye ta gumin datayi ta dubi Abba tace "alhaji kayi shiru"
Abba yace "Tome zance maman nafeesa, ban taba tunanin yaron nan zai iya aikata wannan
abun ba, abin baqin cikinma yanda yazo yashige mana, muka yarda dashi kamar dan'uwa, nine
mai cewa ko bayan raina ban yarda akarbi baby daga hannun sa ba, ashe shinema uban
yarinyar "橙提
Mama tace" to taya kuwa za'a ce zai aikata alhaji, yaronda saboda tsananin kunya bayama
yarda kahada ido dashi
Har garama tahir zai zauna ayi fira dashi, Amma shifa wannan gim yake zaune, bazakace zai
aikata wani Abu naqi ba"
Abba yace "ai shikkenan, bamu ya yiwa ba, kansa ya yiwa,"
mama tace "hakane, Amma nikam banda nafeesan tafada da bakinta babu wanda zai fadamin
wannan maganar na yarda, wannan yaro bai kyauta mana ba"
Abba yace "jeki ga halinda ita nafeesan take ciki"
Tana Zuwa Dakin taga nayi bacci tajuya, nikuwa batasan idona biyu ba, a wannan halin wanne
bacci zan iya
Abba ne yakira Ammu yace "hassan idan kasamu dama kazo gobe da safe inasan magana
dakai,"
Babu musu Ammu yace
" insha Allah zai shigo"
** *** **
"Yanzu de damuwa da kuka da tunani duk sun qare tunda kaga feenah"
Ahmad yace "wallahi tahir kalau nake jina yanzu, banajin ciwon komai, kai farin ciki ma nake
ciki, Tsawon shekarun dana dauka ina nemanta Yau naganta, tazo har gida tasameni"
Tahir yace " kawai dande haka Ubangiji yatsara ne, Amma ai haduwa kam kun kusa haduwa"
Ahmad yace " kamarya?"
Tahir yace " wai kasan anan asbitin ta haifi baby?"
Cikin mamaki ahmad yace "bangane ba"
Tahir yace "tonima alokacin bansan taba, Dan ko ita husnan banma hadu da itaba alokacin
Da'aka kawo ta batada jini, ga kuma haihuwar tazo kusa,kuma anrasa irin jinin ta, in bazaka
manta ba, kaine kace adebi naka abata, batare dakai koni munsan itace feenah ba, ni bansan
taba, kai kuma bakaje wajanta Bama bare kaganta"
Ahmad yace "wai kana nufin feenah nabawa jini na tahir?
Ashe alokacin aka haifi baby na
Ashe nima na temaka wajan zuwanta duniya"
Tahir yace "abin de kamar almara
Itace fa wadda nake cema nayima budurwa qanwar matata
Kacimin mutunci Akan feenah, ashe ma itance"
Ahmad yace "to aide kaganta, yarinyar tayi tahir, zan iya yin komai saboda ita, har Yau nakasa
manta yanayin danajini aciki, lokacin da wannan abin yafaru, yarinyar tanada...."
Gyaran murya tahir yayi yace "wai koka manta qanwata ce ne? Kaini fa yayanka ne yanzu, yaya
tahir yakamata kace"
"Allah ko yayan zamani," inji ahmad
Tahir yace "kacika baki, wallahi tsaf zanje in zigata," ahmad yace "haba nawan kaifa na hannun
dama nane"
** *** **
Kaina ko dankwali babu sai qananun kalba, mama nasamu afalo ita kadai tayi shiru, kai tsaye
cinyarta nadora kaina, mama tace " kai nikam dagake har baby ne zaku qarasani" 橙提
Murmushi nayi nace "kai mama, dande mu biyun"
Wayata na janyo