Showing 90001 words to 93000 words out of 113548 words
na duba text din da aka turomin ta layin mukhtar
"bazamu sake Shiba har sai kinyi alqawarin zaki rabu dashi, shima yayi wannan alqawarin "
Mama na nunawa tace "Allah yarufa asiri," nace "mama bari nakira naji,"
Ina kira nasa wayar a handsfree
Nace "Dan Allah kuyi hakuri ku sakeshi,"
"Wacece kedin?"
Nace " ni kuka turowa text Akan in rabu dashi
Naji zan rabu dashi, Amma Dan Allah karku taba lafiyarsa, Dan Allah ku rabu dashi, banaso
komai yasame shi"
Qit aka kashe wayar batare da ancemin komai ba
Mama na kallah da mamaki tace "wannan yaro ko a wanne Hali yake ciki, nasan iyayansa
hankalinsu ba a kwance yake ba"
Nace "hakane mama, Allah yasa suyi hakuri su sake shi," tace "amin"
Batamin zancan ahmad ba, nima banyi mataba
** *** **
Next day, maqota da yan'uwa ne suka cika gidan kowa yana fadar albarkacin bakinsa Akan
dawowar mukhtar
Wasu gulma ce take kawo su, wasu kuma jaje
Iyayansa sunfi kowa murna da dawowar dansu lafiya batare da komai ya sameshi ba
Saida suka kebe da iyayansa ne baba yake tambayarsa babu de abinda suka masa ko? Yace
babu komai
Ko zaginsa basuyi ba, kawai sude fatansu na rabu da ita, baba yace ikon Allah to ai Allah yafisu
Inna ce tace nikam Malam yaron nan daya hakura da al'amarin nan, tunda Abu yafara Zuwa da
matsala
Baba yace "a a haba de zainabu
Yaza'ai mu zama qananan mutane a idan iyayen yarinyar
Bayan kuma suma kansu yaran sunason junan su"
Tace "Toshiknn, Allah yashige mana Gaba"
** *** **
Ina kwance adaki ina waya da mukhtar sai farin ciki nake saboda futowarsa
Nace "wallahi naji dadin yanda ka futo lafiya mukhtar," yace "Allah ne abin godia feenah tah,
kinsan yanzu fa baba yahanani fita ko ina
Banda masjid babu inda nake Zuwa, kullum ina gida ina tunanin feenah tah"
Daria nayi nace" wallahi gara haka, tunda ai bazasu zo har gida su daukeka bako, mukhtar abin
nan yana dauremin kai, narasa waye yakesan rabani dakai
Basusan cewa duk wani farin ciki na yana tare dakai ba
Fatana da burina shine ka kasance uban 'ya'yana"
Mukhtar yace "me kika ce? Please Dan Allah maimaita"
Kashe wayar nayi ina daria, daga cikin blanket na futo, baby duk ta yaye jikinta anatashan
bacci, falo na futo da murna ta nace "mama ansakeshi!"
Turus nayi ganin Ammu da Abba da mama ne afalon, ko yaushe yazo oho
Rissinawa nayi na gaida shi, yace "nafeesa kiyi hakuri fa Akan abinda yafaru, ni nasan ahmad
bawai haka kawai yayi ba, dole nasan akwai sanadi, saboda wannan ba halayyarsa bane"
Nide bance komai ba nakoma daki, mama tace "zonan ina zakije kuma"
Dawowa nayi tace "yaushe aka sakeshi," nace cikin murmushi "yacemin de dazu ne da safe"
Abba yace "to alhmdlh, bari nima nakira iyayan nasa"
Ammu yace "eh gaskya kam, Allah yaqara kiyayewa Gaba," cikin murmushi nayi daki na
** *** **
Wandon jeans ne ajikinsa blue, sai baqar Riga body hug, daidai jikinsa
Sai yar sama daya dora kalar jeans din jikinsa mai laushi
Sumarsa tasha gyara
Agogo yasa qirar plaget
Sai zuba qamshi yake
Falo yatafi kai tsaye, yana Zuwa yaga iyayansa suna break
Har qasa yagaida su, mamy hakima tace "yajikin Naka?"
Daddy ne yabata amsa da fadin " kya tambaye shi jiki, mutumin dayayi irin wannan wankan"
Kansa ya sunkuyar yana Sosa qeya, yace "mamy jiki yayi sauqi"
Tace "alhmdlh ga break fa"
Tasowa yayi, yana zama qannansa suka fara gaida shi, auta ce tajefo masa tambaya
"Yaya yaushe baby Zata dawo?"
Mabruka ce ta doketa
Momy tace "a a Mabruka kya daketa?
Dan tayi tambaya? Ai yanada kyau taji, "
Ahmad ne yahade ransa, ya kalli Mabruka yace "idan kika sake dukanta saina tsinka miki mari"
Momy tace "daga tambaya sai duka? A wanne dalili?"
Shiru kawai yayi, yaga alama Momy so take ta dora masa laifin komai
Maryam yaja, yamaidata cinyarsa yace "kiyi hakuri Zata dawo, kinji?"
Hawayen ta ta share tace "to yaya"
Sun Gama kenan tahir yayi sallama yashigo, yasa yadi fari mai kyau, Amma baisa babbar
rigaba, yayi kyau sosai
Yana gaidasu Momy da da daddy, dukansu sukai haramar tafiya
Har sunzo shiga mota, ahmad yace "tahir kawo key din saina kaimu"
Daddy da haushi yacika shi, yace "kakai suwa?
Saide kakai wasu, Amma mukam bazaka bimu da wannan shigar ba, haba kullum mutum cikin
qananun kaya," yadubi tahir yace "ka dinga yimasa fada, tunda naga kai ka fishi Dan hankali"
Sunkuyar da kansa yayi yace "daddy "ma'alesh" (kayi hakuri)
Juyawa yayi cikin sauri yaje yasauya kaya, shima farin yadin yasa, tahir sai daria yake masa,
mota biyu sukayi suka tafi
Suna Zuwa zaria guards suka Bude musu mota
Tahir ne yakira Abba awaya yace sunyi baqi
, ahmad kuwa kasa futowa yayi daga motar
Daddy ya kalleshi yace tunda mu mukai laifin aimune yakamata mu futo
Sai a sannan yafuto, Gaba daya jikinsa yayi sanyi, yarasa tayaya zai fuskanci wadannan bayin
Allah
Haka de yafuto kansa asunkuye
Su Momy kai tsaye cikin gidan suka shiga
da Abba suka hadu suka gaisa ba yabo ba fallasa
Kofar gidan ya qarasa ya yiwa su daddy iso
Abba cikin mamaki yace "haba alhaji, harda kai ake tafe ashe,"
daddy yace "ah babu komai wallahi, ai takamane"
Dukansu Abba yace ku shigo mana, su Momy suna Zuwa suka zauna afalon, nan su Abba da
daddy ma suka shigo falon
Gaba dayansu, ahmad da tahir ne aqarshe
Mama tace "nafeesa tashi kikawo musu ruwa mana,"
Dan kwalina nafara lalube
Ina dagowa karaf muka hada ido dashi
Da sauri na janye idona
Cikin ransa yace masha Allah gashin ta de yana Nan da yawanshi
Da kallo yabita kamar zai hadiyeta
Saida tahir yalura, ya mintsineshi, sannan yadawo hayyacinsa
Kallansa yakai kan Momy, ta balla masa harara
Shi kam Yau yaga ta kansa
Abba ne yace "tahir ku zauna mana"
Kansu aqasa kamar munafukai, suka shigo aqasa suka zauna
Ina kawo ruwan da lemuka, nafara zuba musu
, su kuwa ko kallansu banyi ba, mama ce ta harare ni, afakaice
Aikuwa na matsa nakai musu
Idonsa kyar akaina
Kamar bazan Bude bakiba nace "yaya tahir gashi"
Tahir yace " yauwa autar mu, mun gode"
Shikuwa Dan qaramin bakinta yake kallah yanda take budeshi kamar bataso
Baby ce ta futo daga daki, tana kallan mutane afalon ta tafi da gudu wajan daddy
Tace "ga daddy"
Daddy yace "izdihar, ashe kina ciki,"
saikuma Takoma wajan su Momy, tana ganin ahmad kuma sai Takoma wajansa da gudu
Saita bawa yan falon daria
Tace "yauwa uncle, ashe kazo tafiya Dani
Anty to kema debo kayanki saimu tafi Gaba daya"
Nikam ko inda suke ban kallah ba
Daddy ne yayi gyaran murya, anan aka sake sabuwar gaisuwa
Daddy ya dubi Abba yace "alhaji munzo ne Akan abinda yafaru tsakanin yaran nan, Dan Allah
Dan annabi kayi hakuri
Kuyafewa yaron nan
Dan Allah alhaji," saukowa daddy yayi yadawo qasa, Abba Da sauri yatashi ya tareshi yace
"haba alhaji
Ni danasan zaka zo da kanka ma, dana hanaka wallahi
Babu komai ai Dan Adam baya wuce qaddarar sa"
Daddy yace "hakane
Tahir kayi musu bayanin abinda yake faruwa, kamar yanda muma kayi mana bayani"
Aikuwa tahir tiryan tiryan yabada labarin komai
Abba yace "babu komai, adade nayiwa zancan mummunar fahimta, Amma ayanxu dana gane
komai, to alhmdlh nikam komai ya wuce awajena, wallahi har cikin raina, nida mahaifiyar
wannan yarinya, mun yafe masa"
Cikin sanyin murya Ahmad yace" Nagode Abba, Allah yasaka da alkhairi"
Abba yace "babu komai ahmad karka damu, Allah yakiyaye Gaba kuma"
Gaba daya falon a kace
" amin"
Abba yace "saide ita, gatanan saika bata hakuri, ku sasanta kanku, tunda Allah yanufa da rabo
atsakanin ku, koba komai kudinga gaisawa ma, albarkacin wannan yarinyar Allah yasa mufi
karfin zuciyar mu"
Aka sake cewa "amin"
Momy da mamy ma, sun nemi yafiya, kuma anyi musu, anan de aka fahinci Juna
Daddy ne yadubi Abba yace "alhaji ina neman alfarma awajanka, idan bazaka damuba,"
Abba yace " haba alhaji aikafi karfin komai awajena, kasauke mulkin da Allah yadorama kazo
nan da kanka saboda abinda yafaru ai kayi komai"
Daddy yace "hakane Nagode sosai, dama inaso ne ka temaka kabawa yarona auren yarka
Kaga shikkenan saisu riqe yarsu, batare da kowa yasan halin da ake ciki ba"
Abba ne yace, "wallahi alhaji nafi kowa San wannan al'amari, Kodan izdihar ma, Amma hakan
bazai iyuba"
Gaba daya falon akai shiru dajin furucin daddy
Musanman ahmad
Abba yace "saboda anriga anyi Mata miji, yanzu haka saura wata daya da yan kwanaki yarage
bikinta"
Kansa ne yaji yasara
Idonsa yakada yayi jajir lokaci daya
Daddy yace "Toshiknn alhaji, ai duk daya, dama haka Allah yatsara"
Mama ce ta cewa su Momy, "hajia ku shigo daga ciki"
Babu musu suka bita, baby ma tabisu
Daddy ma fita sukai tare dasu tahir,
Wajan yarage dagashi sai ita
Mrs Usman ce ✍️
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: DANA SANI
Writing by Amnah el yaqoub
Dedicated to my family
55
shiru ne yabiyo baya, kanta asunkuye takasa dagowa ma bare ta kalleshi, ada kam yanda
zuciyar ta take yi Mata zafi, gani take Zata iya yimasa rashin mutunci
Saide gashi kuma gata gashi, Amma kuma tama kasa dagowa bare ta kalleshi
Shine yayi karfin halin tashi daga inda yake ahankli, cikin nutsuwa yaqarasa dab da ita ya
zauna, duk da yana tsoron yimata magana saboda baisan mai Zata maida masaba, Amma
kuma wani bangare na zuciyarsa yana qara qarfafa masa gwiwa
Cikin muryarsa mai dadi da sanyi, yace
"My feenah"
Har cikin qwaqwalwarta taji sunan, meyasa takeji ahmad yafi kowa iya fadar sunan ta? Meyasa
duk lokacin daya ambaci sunan ta take jinta cikin wani yanayi na daban?
Karfin halin dagowa nayi nace, "meyasa zaka fadamin wannan sunan? Alaqar datake tsakanin
mu ai ina tunanin tariga data qare
Nasan maganar yafiya ce, zakamin, tona yafema
Shikkenan zaka iya tafiya"
Kansa ya sunkuyar, Yama rasa maizai fada Mata, tsareta yayi da idanunsa dasuke sumar da
ma'abocin qaunarsa musanman feenah
Furzar da iska yayi,yace
" Nagode da yafiyarki agareni, duk nasan cewa abune mai wahala hakan, Amma bayanin da
tahir yayi muku nasan zai gamsar dake, ni tunda nake babu mutumin dana taba zalinta saide
cikin rashin sani, bare kuma abar danafi Santa fiye da kowa aduniya, bayan iyayena, "
Kallansa nayi nace" ok inka Gama nizan shiga ciki "
Miqewa nayi da nufin tafiya, caraf naji ya riqe hannu na, yace "meyasa feenah?
Meyasa koda yaushe kikesan ganinmu cikin tashin hankali ?"
Shima tasowa yayi yaci gaba da fadin
"Yanzu shi wannan lusarin ya zaki dashi? Dan nikam ban taba sawa araina zan rasaki ba, kuma
bazan fara yanzu ba,"
Takaici yacikani, wai mukhtar ne lusari
Fizge hannu na nafara, Amma riqon dayamin yasa nakasa qwacewa, kallansa nayi cikin ido,
nace "karka sake aibatamin abinda nakeso
, koma abinda yafi lusari ne naji inasan abina, ina qaunarsa haka"
Wani zafi ne yaji ya ziyarci zuciyarsa, kansa ya sunkuyar
Yana dagowa taga idonsa yayi jajir, ita kanta saida ta tsorata
Kallanta yayi babu alamar wasa atare dashi, yace "karki qara cewa kinason wani a gabana
Inba haka ba wallahi zaki gane kurenki"
Kuka ne ya kufcemin, cikin shagwaba nace
"nafadadin, nima cikani, kuma koda babu mukhtar babu abinda zanyi kai"
Cikin tsawa yace "nace karki sake ambatarsa a gabana ko!!"
Gyaran murya sukaji akansu, atare suka juya, tahir ya kallesu yace
" daddy yace kafuto mutafi," sannan yamaida kallansa ga feenah yace
" auta, ki turo su Momy, kice su futo mutafi"
Sai a sannan ahmad yacikata
Yana sakinta tashige ciki da kuka
Atare suka futo da tahir, kirjinsa banda zafi babu abinda yake, tahir ya fuskanci halinda yake
ciki, Dan haka kawai ya bubbuga kafadarsa suka qarasa wajan daddy
Suna Zuwa yashige baya ya zauna, tahir naganin haka aransa yace Yau kuma saita Allah,
shiyasa shima baiyi masa maganar driving ba
Su Momy sosai sukai sallama da mama, inda mama tace izdihar tana Gama hutawa Zata dawo,
Dan tasan kawaici suka Mata, suma suna son tafiya da yarinyar
** *** **
Kuka nake Sosai adaki,
" meyasa sai yanzu ahmad ya baiyana agareni? Meyasa saida na mallakawa wani zuciyata
sannan ahmad zai bayyana?
Dole ne inyi maganin wannan matsalar tunma kafin ayimin aure in shiga gidan wani da soyaiyar
wani a zuciyata, mukhtar yamin komai, bai qiniba alokacin dayaji dukkanin labari na, wanda a
wannan zamanin ba kowanne saurayi ne zaiyimin ba"
Share hawayena nayi, nafita falo, nafara tattare kayan da sukai amfani dashi namaida kitchen
Ina kaiwa nakira mukhtar awaya, mukasha firar soyaiyar mu, duk Dan in manta da abinda yake
damuna
** *** **
Su Momy sai firarsu suke a mota, suna tuna shirman baby, mamy tace "nikam hajia banji dadin
wannan al'amari ba, wallahi Naso wannan yarinyar ta auri ahmad, sun dace da Juna sosai,
Naso kasancewar ta cikin family n MARZUQ"
Momy tayi ajiyar zuciya, tace "wallahi hajia nima haka"
Mamy tace "ko yaya ahmad zaiji?"
Momy tace "Ana can de su tahir ne daganin, bacin rai"
Acan daya motar kuwa, daddy ne suke Dan taba hira da tahir, wasu Akan tituna ne, wasu kuma
abinda yadanganci siyasa, shikuma gogan yayi gim kai kace babu halittarsa amotar
Cikin ransa tunani ne fal, wai bata sansa, mukhtar take so, ko waye wannan gaulan?
Yasan de duk tsiya Babu abinda zai fada masa, Amma kome tagani awajan wani dahar ta iya
budar baki tace shi Zata aura?
Tsaki yasaki cikin ransa baisan afili yayi ba
Daddy ya kalleshi
Yadubi tahir yace "tahir akwai tsakane acikin motar nan?"
Saurin kallan daddy yayi, anan ya gane abinda yake tunanin azuciyar sa yayi, afili yayi
** *** **
"Mabruka bawa Momy wayar mana, kude kullum aka kira waya sai wani acikinku yadaga"
Daria tasaki tace "to ai basanan masu gidan, yanzu mune masu gidan"
Saudat tace "kamarya?"
Mabruka tace "wallahi basa nan sunje zaria dukansu"
Cikin mamaki tace
" lafiya? Me akeyi a zaria?''
Tace" wallahi anty sauda bansaniba, Amma de gidansu anty husna suka tafi, matar yaya tahir,
wai wata yayar baby ce tazo ganinta
Shine fa tana Zuwa taga yaya, tana ganinsa ta tashi, nan suka fara fada"
Saudat tace "fada kuma? Tome yahadasu?"
Mabruka tace "harfa marinsa tayi anty, wallahi muna tsaye sai tassss kakeji ta mareshi, ta
qwace baby tace yarta ce, shima kuma yarsa ce,Dan haka bata buqatar sake ganinsa
arayuwarta, Dan haka yabata yarta,"
Shikuma fa yaqi Rama Marin kawai sai kira yake
" feenah"
Saudat tace "keeee mekikace? Wai kina nufin feenah ce tazo gidan?"
Mabruka tace "wallahi hakade naji yace, Amma kuma ta cewa su Momy sunanta Nafeesa"
Saudat dafe kanta tayi da hannunta
Takashe wayar kawai,
Subhanallah, me yake shirin faruwa ne? Me sister da yaya suke boyewa atsakanin su?
Babu wanda yasan wannan amsar tambayar sai yaya da feenah da kuma yan gidan, Dan haka
Zata jira su dawo taji kan batu
** *** **
Suna Zuwa gida yafuto daga motar baiwa kowa magana ba yayi ciki,
Su Momy ma sukai part dinsu
Suna Zuwa Mabruka tace "anty saudat takiraki Momy, "
tace "ok kiramin ita"
Rufe idonsa yayi ya zauna a kujera, tahir yashigo gamida rufe kofar Dakin
Shima zama yayi, yace
" kayi hakuri ahmad, ni nasan bazakaji dadin wannan labarin ba, shiyasa tun dadewa nakasa
fadama, Amma already nasani
Nasan yanda kake Santa
Kayi hakuri kayi addu'ah idan Allah yayi matarka ce Babu wanda zai hana,
Idan kuma ba matarka..."
"Dan Allah tahir karka qarasa, haba tahir
Yanzu kai har kana tunanin feenah ta auri wanina? Bayan kasan irin dunbin wahalar danasha
akanta?"
Hannunsa yasa cikin sumar kansa ya yamutsata, yace "meyasa ni a koda yaushe banda sa'ah
ne Akan mace?"
Ajiyar zuciya tahir yayi, yace "kayi hakuri mana, insha Allah matarka ce, shikkenan?
Amma kayi addu'ah, nima zan tayaka,