Showing 63001 words to 66000 words out of 113548 words

Chapter 22 - DANA SANI BY AMNAH EL YAQOUB .pdf

daria yake, yace "a a
nafeesa angama karatu kuma,"

feenah cikin murna tace
" eh wlh Abba,"

Zahra ce tazo suka gaisa itama tayi wajan yan gidansu Abba yace "a a hassan mu qarasa mu
gaisa dasu mana," har feenah duk sukaje suka sake gaisawa da iyayen Zahra, sannan sukai
sallama suka tafi, feenah tace Mata "sai munyi waya,"
hannu kawai Zahra ta daga Mata

Direct zaria suka wuce, suna Zuwa husna ta futo da gudu ta rungume feenah, Gaba daya gida
de kowa yana ta farin ciki
Mama baki yakasa rufuwa, gata ga feenah, ta kwantar da kanta Akan cinyar mama, Abba yace

" mamana Hali de yana Nan," aka sa daria, takama su mima sai kallansu take, tace "anty husna
basa kama dake yaran nan,"

husna tace "eh da babansu suke kama,"

Taga kowa Amma bata ga baby ba, to ina take,橙 kuma taga babu wanda yayi maganarta,
Batasan lokacin da maganar ta futo ba, kawai de ji tayi tace

" mama ina baby?" 橙提


Mama tace "aiji nake bazaki tambaye taba, tana nursery, yanzu zaki ga tadawo"
Anty maimuna tace "baby ta qwace Mata fada awajan mama kuma yanzu bata ganta ba ai dole
ta tambaya," wannan maganar da anty maimuna tayi, shiya tabbatar min da batasan baby yata
bace, kenan Ammu bai fada Mata ba, lalle wadannan mutane suna kaunata

Aikuwa kamar jira take su Gama magana, sai gata da gudu ta shigo, tana cikin uniform dinta da
school bag dinta a bayanta, kayan yayi Mata kyau sosai, tana Zuwa falon taga baqi dayawa,
batabi takan kowa ba tayi wajan mama da gudu, ta rungume ta, wata sallamar suka sakeji
abayansu, wani yaro ne yashigo yace " mama kice baby tabani kallo kallo na,"
saida yafada sannan mama takalli hannun baby, aikuwa yana hannun ta, mama tace
" bashi abinsa kafin na dakeki," baby tace "to wayace shima ya tsokaneni,"

yaron yace "karyane niban tsokanetaba," mama ta karbi abinsa tabashi, tace " baby nahanaki
rigima, bakyaji ko," turo Dan qaramin bakinta tayi gaba, tace "to mama nadena"
Ammu ne yace "baby ba gaisuwa?"

Wajansa taje suka gaisa, tana juyawa taga husna Takoma wajanta da gudu, feenah tana
kallanta, husna tace " baby ga anty Baku gaisaba,"

kallanta ta maida ga feenah, suka zubawa Juna ido, baby sai kallanta take, tasauri Takoma
wajanta, tace" ya sunanki? "

Feenah tace" baki sanni ba?"
Baby tace" daga ina kike? "
Feenah tace" makaranta," baby tace" Amma zaki zauna damu bazaki gudu ba irin na anty
husna"
Feenah tace "eh zan zauna," baby tace

" to Amma... "

Mama tace "baby barta ta huta tagaji banasan tambaya kinji,"

Abinci mukaci nayi wanka na tafi daki nakwanta, baby ce tashigo Dakin ta tsaya abakin kofa,
tace
" sabuwar anty in shigo?"
Feenah tace " shigo," tana Zuwa tahau jikinta, takama kallanta, feenah tace "baby lafiya?
Wannan kallan fa,"

baby tace "ina sanki,
Nan dinki nake kalla irin nawa," takai hannun ta kan dimple din feenah,
Feenah tace "um nagani, yanzu bacci zanyi, nagaji, tashi kije wasa,"

baby tace "tonima zanyi baccin," 橙提

feenah tace "to kwanta kiyi" , kwanciya baby tayi, feenah tana rufe ido bacci ya dauketa, baby
tatashi a hankali taci Gaba d kallanta, tanata daria ita kadai
Matsawa tayi jikinta tashiga jikinta sosai nan itama tayi bacci

Mama ta kalli husna tace, "kiramin baby nasan tanada home work, yanzu haka wasa take,"
husna na fita ta duba ko ina babu baby, Dakin feenah tashiga, kawai tagansu sunata bacci,
husna tace "mama zokiga" 橙提

, mama nazuwa tagansu aranta tace Allah sarki, uwa da d'a kenan soyaiyar nan de dole saita
wanzu atsakanin su
Juyawa tayi, tace "ashe bacci suke," tabar husna anan
Itakuwa husna kallansu take cikin birgewa

Gab da magrib nafarka, ina juyi naji mutum ajikina, kallanta nayi da mamaki, yanzu yarinyar nan
saida ta kwanta ajikina, kallanta nake da mamaki nashafa kanta, Natashi zan shiga wanka, ina
motsawa itama tatashi, cikin muryar bacci, tacemin "nima natashi," 橙提

nace "to jeki wajan mama," tace "wanka zakiyi?" Nace " eh,"

tace "nima to kiyimin wankan"
Nace cikin raina Yau nagamu da jaraba,橙 nace "jeki mama tayi miki," tace "um um ni kece
zakimin" , girgiza kai nayi nashiga wanka, na shirya nabarta,dataga zan fita nabarta adakin
kawai yarinya tasa kuka,橙提

tace "Allah saikinmin," kallanta nayi kawai, Babu yanda na iya dole saida nayi Mata wankan

da daddare nabawa kowa tsarabarsa yan biyu sai murna suke, kayan su iri daya su ribom su
takalma, saina husna itama kaya, sai na Abba da mama kuma,
Baby cikin sanyin kuka tace" Toni ina nawa?" Feenah tace " ai banda ke"
tajuya wajan mama tace

" wai mama banda ni,"

mama tace "yi shiru mana baby kefa sai ragwanta ko?"
Feenah tayi daria tace
" toga naki," cikin murna izdihar tace "yeeee"

Haka ta ishi kowa da surutun kayanta ranar, washe gari su Ammu suka koma suma da tasu
tsarabar, tare suka koma da husna, gidan ya rage daga su sai su, da yamma su aysha
sukazomin sannu da Zuwa da ita da kala da kaka sai baba Adamu, sun jima sannan daga baya
suka koma gida
Sati na daya agida, ina kwance afalo, ina kallo, dayake da weekend ne Babu school saiga baby
ta futo daga daki tace
" sabuwar anty"
Nace "menene,? Kinfa dameni baby,"

hannun ta ta dora Akan maqogaronta tace "anty kinji zuciyata tauri ne da ita" 橙提

Na kalleta naga inda hannun ta yake, batama San inane zuciyar ba,橙提

nadaura hannu na Akan maqogaron nace "um aikuwa zuciyar taki tauri ne da ita kamar ta
ubanki" 踫潤蕃踫董

Mama da futowarta kenan daga daki taji wannan firar tasu, cikin mamaki tace " nafeesa kinada
hankali kuwa?"






Mrs Usman ce 踫
[5/6, 3:32 PM] 儭DANGI DAYA儭: 潤摹DANA SANI 潤摹

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

43


Baby ma tazaro ido takama bakinta,踫cikin mamaki tace "da Abba kike?"
Mama ce taqaraso wajan da sauri, ta dakawa feenah harara, taja hannun baby sukabar wajan

Dafe kaina nayi da hannu na, oh ya Allah, meyasa na aikata haka? Yakamata indinga daidai ta
kaina Akan yarinyar nan

Tashi nayi natafi daki

Mama ta kalli izdihar tace "baby, idan anty tana hutawa kidena Zuwa wajan ta kinji?"
Baby tace "to mama, Amma ina Santa,"

mama tace "naji, naji baby nasan kina Santa, Amma kidena damunta kinji, oya dauki littafin ki,
kiyi karatu"


** *** **


"Gaskya my heart yakamata kazo mana hutu, yanzu fa watanka biyar," tahir yace "maman
mima, tunda nayi wata biyar ai kamar yaune zan dawo, ki qara hakuri, yakika ga autar
mama?Da fatan tazo lafiya,"

husna tace "lafiya kalau, takusa Zuwa minma," tahir yace "eh gaskiya kam yakamata, Allah
yakawo ta lafiya,"
husna tace "amin"


** *** **


"Mama zanje maqota mu gaisa na dawo,"

"to saikin dawo, ki gaishe su,"
baby tayi sauri tatashi, tana kade hannunta, zatabi bayan feenah,橙提

mama tace "zo nan izdihar, karkije aturaki titi da niyya mota ta kashe ki, �"
buta tadauka Zata shiga toilet, feenah ta girgiza kai kawai ta fita, izdihar naganin mama tashiga
toilet, tayi wuf tafice da gudu, 橙提
Nayi nisa atafiya, naji anjamin hijabi na, cikin murna tace
" yeee nataro ki, "
kallanta nayi da mamaki nace" ke meya futo dake daga gida? Ba mama tahanaki ba?" Kallo na
tayi, tana murmushi tace

" to ai inaso inbiki, Dan Allah zaki tafi Dani wajanki idan zaki koma inda kika zo?"
Feenah tace" nima inasan tafiya dake, Amma bazai iyu ba, kiyi hakuri kina Zuwa school kuma

gasu mama da Abba, da qawayen ki na school,"
cikin murna tace

" eh tona fasa binki, Amma de ina sonki"

Nima nace "ina sanki baby," tafiya mukaci Gaba dayi, nace "baby baki gaji bane? Oya zona
goyaki,"
tsugunna wa nayi tahau bayana, muka tafi, tace " sabuwar anty, kina goyani kullum, mama bata
goyani,"

nace "baby bakisan sunana bane?"
Tace "emana, ya sunanki?"
Nace "sunana baby nima, irin naki,"
tace "laaa ashema sunanmu daya,"

nace "keni bansan shirme sunana nafeesa," tace "nide baby zance," 橙提

nace "kina fada ina bige wannan bakin naki," daria tasa, ahaka mukaje unguwar kafin mudawo
tayi bacci, mama na falo taga mundawo, tace
" ashe ta biki," nace "eh mama, ai tayi bacci ma," mama tace " itama de batada zuciya,"

murmushi nayi kawai na kyale mama
Naje na kwantar da ita

Da daddare ina karanta novel awayata, nayi wanka nayi shirin bacci, saiga baby tazo da littafi
tace, "sabuwar anty inzo ki koyamin karatu?" Nace

" eh, zo ki zauna,"
ta zauna nafara yi mata, kuma sosai nafahinci yarinyar tanada kokari, nace "to yimin bayani,"

filla filla tafara yimin bayanin, nashagala ina kallanta, har muka Gama, nace "to ki tashi kije ki
kwanta,"

matsowa tayi jikina tace
" um um, sai anjima tukun," 橙提

nace "to karfa kimin bacci mama tazo tanata nemanki," tace "nifa anan zan dinga bacci, nabar
Dakin mama," 橙提

nace "a a baby yahaka,"

tace "Toni wajanki nakeso," tafadi haka kamar zatayi kuka, nace
" toyi shiru, kwanta,"

Maimakon ta kwanta Akan gadon, saita matso jikina ta kwanta, tace
" sabuwar anty,"

nace "baby kidena fadamin sunan nan,"
tace "to, taci Gaba da cewa kema kina sona ko?"

Kallanta nayi nace," sosai ma baby, ina sonki, kamar cikin duniyar nan baki daya,"

murmushi tasaki bata sake magana ba, bacci yadauketa

After 1 week
Nagama shirya kayana tsaf, nace " to mama zan tafi, Abba saina dawo,"

Abba yace" to mama na idan kinje ki gaida su husna," nace" to zasuji Abba, "
Jakata na dauka, aikuwa baby tasa kuka tariqe jakar
," Allah Abba zan bita, nide bazata tafi tabarni ba,"

Abba yace" ke izdihar, banasan shirme kinji ko, idan kin bita makarantar fa? "
Nima idona yayi ja, Inason tafiya da ita, acikin raina, to naga su mama basu ce intafi da ita ba,
Na dago kai nace" to Abba kabarta mutafi," Abba yace" mamana school dinta fa?" Nace
" zan shiga makarantar inyi musu bayani", mama tana kallanmu tace "nide nafeesa karki dauki
yar nan kinga babu idonmu ki cutar da ita," 橙提

nace "mama wallahi Babu abinda zai faru," tace "Toshiknn"
Aikuwa aka hada mana kayanmu awata jakar, dole Abba ne yace shi zaije school din ya nema
Mata alfarma
Amota haka taita bani labarin school dinsu, gidan husna direct muka sauka, ummi sai nan nan
take damu, Gaba daya bangarenta muka dawo, sai dare muke komawa part din husna, washe
gari agidan kaka muka wuni, nida baby dasu mima
Har mijinta tahadani dashi mun gaisa, yace shima yaso yana gida nazo, Zahra ma takawo min
ziyara, haka muka wuni muna bawa anty husna firar Sudan
Munje gidan kala ma, mun wuni, aysha anata shirin biki, mai gyaran jiki tanata fama, wani
watan za'a sha biki

Duk wani wajan yawo da wasan yara babu inda bankai baby ba, muyi ta pictures nida ita, muna
wanka zan zare ta mu shiga gari, mune gidan zoo, mune Park, sosai munsha yawo,
Nima na kaiwa Zahra ziyara nida baby, haka tabawa baby sweet sosai, har su pictures sunyi
dasu video sunata shirmansu
Satin mu daya a kano muka dawo gida

Cikin sati biyun danayi agida, sosai muka shaqu da baby, bana iya bacci ba tare dana jita ajikina
ba, pictures, videos duk haka nake yi Mata da wayata, wani kuma muyi tare, mun shaqu sosai,

kuma mun saba, ahaka har sati biyu na tacika, nafara shirin komawa makaranta
Ranar dazan koma, saida aka yiwa baby wayo tatafi school sannan muka tafi kano, nahadu da
Zahra muka tafi airport, ina kuka mukai sallama dasu mama da husna dasuka rakoni
Kuka na daya baby, bansan yaya zataji ba idan taga bana nan

Muna sauka kuwa nakira su mama nace musu mun sauka, tacemin ga baby nan tana zazzabi,
tun rana take kuka, taga bana nan, ni kaina kuka nasawa mama, tace" to yanzu kukan zakiyi
kokuma so kike nima ki karyamin zuciya, ga yarinya babu lafiya", haka mama taita min fada har
mukai sallama

** *** **


After 1month, alhmdlh nafara karatuna cikin kwanciyar hankali, kusan kullum sainaji muryar
'yata nakejin dadi,橙提
wani lokacin ina karatu, haka nake bari, sainaji muryar ta sannan zanci Gaba da karatun, Allah
Allah nake ingama karatun nan in koma kusa da yata, inde ina missing dinta videos dinta nake
kallah kokuma in kalli pictures dinta, haka mukhtar ma, har pictures dinta natura masa


** *** **


I V yake ta rabawa abokansa na office, yana cewa "wallahi wata yata ce, za'a yi bikinta wannan
weekend din, Dan Allah ku daure kuje"
Ahmad yafuto cikin sauri yana waya, zai fita daga company, Ammu ya karasa suka gaisa, ya
miqa masa iv din shima yace "yallabai ina gayyatarka Zuwa wajan bikin wata yata da za'a yi,"
ahmad ya karbi iv din yace "hassan ko itace wadda kadauko daga school kwanaki?"

Ammu yace "a a ya'uwarta cede,"
ahmad yace "Toshiknn insha Allah zanyi kokari inzo nima,"

daga haka yayi waje


** *** **


"Izdihar karfa kiyi wani wajan, wanka kawai zanyi inzo mutafi, kinga abbanki yaji ma da shirya
wa,"
baby tace "to mama"
Yar babynta ta dauka, tafara yimata kitso, tanata waqa, har mama ta futo, cikin shiri, izdihar ta

kallah duk tabata kwalliyar ta, janyota tayi tagyara Mata, taqara gyara Mata parking din gashin
ta, sosai idan ka kalleta zakace yar turawa ce, kwata kwata bazakace tanajin wani yare hausa
ba, Riga da wando ne ajikinta ja, tayi kyau sosai yarinyar kamar ka sace ta kagudu
Mama nagama komai, suka dau hanya
Gidan kala suka sauka, anan suka tarda su husna da yan biyunta harda ummi
Anata hidimar biki, husna na wajan amare anata shirya amarya 橙提

Karfe biyu daidai aka daura auren aysha da angonta nasir,akofar gidansu,
izdihar na Zuwa wajansu mama da mima, nan suka fara wasa, Ana wasa rimi rimi, anan ta nuna
halin nata na tsokana, 橙提橙提
mama da mima suka biyo ta da gudu, suna saisun Rama
Tafita waje da gudu

Suna tsaye shida abokan ango sunata gaida shi, kasancewar sa sanannan mutum, sai
murmushi yake, yaci manyan kaya cikin farin yadi mai tsada

Kawai yaji anbigeshi, kuma anriqe masa kafa anacewa
"boyeni, boyeni," 橙提

juyowar dazaiyi yaganta, gabansa yayi mugun faduwa, tsananin kamar dasuke da itane yasa
cikin rawar murya Ahmad yace "MY FEENAH"






Mrs usman ce 踫
[5/6, 3:32 PM] 儭DANGI DAYA儭: 潤摹DANA SANI 潤摹

Writing by Amnah el yaqoub


Dubun godia gareki, yanda kike bibiyar novel dina, nima ina tare dake, kyautar wannan page
izuwa Garki
@RESPECTABLE



45


Tahir yaci gaba dacewa, "Amma hakan bawani matsala bane, idan muka dora shi Akan magani

insha Allah za'a samu abinda akeso"
Ahmad shiru kawai yayi yana kallan tahir
Laila nagama Jin wannan batun tasaki tsaki, fuuuu ta tashi tafice daga office din har tana
bigewa da kujera Amma ko juyowa batayi ba

Ahmad ya sunkunyar da kansa, tahir yayi shiru,shi kansa ya rasa da wanne kalma zaiyi amfani
da ita wajan bawa aminin nasa hakuri, saboda haka yatashi daga kujerar dayake kai, yadawo
ya tsaya agefen ahmad yafara bubbuga bayansa alamun rarrashi,

ahmad yadago kansa cike da damuwa yace
"meyasa tahir? Meyasa?" Nan danan qwalla ta cika idonsa

Tahir idansa yakada yayi jajir, yace. "Ahmad kayi hakuri mana,ni dakai duk dayane ahmad, kaga
karkasa damuwa aranka, akan abinda yafaru, ni inde haihuwa ce wallahi nahakura ahmad
kadauki su mama, nabaka su, inde Akan yara ne zaka daga hankalin ka, nina hakura, banaso
ka sake shiga cikin damuwa ahmad, tunda kasan abinda yake damunka, ba'a San kacika tunani
"

Ahmad ya kalleshi yace
" tahir tabbas abin da ciwo, Amma Babu komai, damuwa ta daya tahir meyasa baka sanar Dani
hakanba tunda farko?"
Tahir yace" ahmad tayaya zan tabbatar da abinda nake tunani bayan bakada aure alokacin?
Ni kaina hasashe nake a wancan lokacin
Ashe abinda nake tunani zai zama gaskiya, kaga yanzu tashi muje mu lallaba madam mu bata
hakuri "
Ahmad yace" tahir yi zaman ka, kabarta kawai idan nakoma gidan zamu tattauna nida ita,ni
fishinta bai wani dameni ba, saboda bana kaunar ta, ni badan kada nayiwa Allah butulci ba,
danace gara ma da bazan iya haihuwar ba, dade inhada jini na da laila,saboda banga tarbiya
awajanta ba bare yaran dazamu haifa su samu, sannan tahir kabar maganar su mama, kaimafa
su kenan awajanka tahir, ummi tanasan yaran Sosai saboda me ni zan dauke muku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login