Showing 75001 words to 78000 words out of 113548 words

Chapter 26 - DANA SANI BY AMNAH EL YAQOUB .pdf

may be shi zaka iya fada masa gaskya,"
bata Dade da hawa saman ba suka sauko tare da daddy

Daddy yace "ahmad me yake faruwa tsakanin da iyalinka"
Ahmad yace "daddy itace tace nasake ta, kuma namata abinda ta nema,"

daddy yace "kuma shine kasaketa har saki uku, haba ahmad kamar qaramin yaro? Ina ka taba
gani kai tsaye anyi haka?"
Ahmad yace "daddy kayi hakuri,"
daddy yace "sai maganar magani

Metayima da har zaka dauki mummunan mataki irin haka? Kokuma kai Dan ance bazaka haihu
ba, shine itama kace bari ka maida ta haka ku zama daya?"

Maganar ta masa ciwo nan da nan yafara hawaye yace "daddy kayi hakuri"

Daddy yace "a a ni ahmad kafi karfina, tunda nayima aure ka nuna min ban isa dakai ba,
shikkenan kaje duniya ce" ν ½νΉ†ν ΌνΏ»

Mamy hakima tace
" haba alhaji, ai ka tsaya kaji abinda yaron nan zai fada ko?
My son yimana bayani me yake faruwa?"
Ahmad yana hawaye yace " daddy Dan Allah kayi hakuri kayafemin, banyi haka Dan inci
mutuncinka ba, kayafemin daddy, insha Allah haka bazata sake faruwa ba

Daddy laila itace tasa min magani cikin drinks din dakina Gaba daya, nasha.. Har hakan yasa
nayiwa... Kuka yasa yakasa qarasa maganar, yace daddy laila nita zalunta, kawai nima ramawa

nayi, tabawa walaya magani tasamin nasha, tahir shine ya dubani a dalilin maganin ne yasa
nima bazan iya haihuwa ba, har sai andorani Akan magani

Idan dukanta nace zanyi bazan huce ba, shiyasa nabi shawarar zuciyata nima nayi Mata abinda
tayimin

Wannan dalilin ne yasa nakori walaya daga gidan nan, Amma kayi hakuri daddy, kabawa
mahaifin ta hakuri, yayafemin,"

Daddy yasauke numfashi yace" tokai waye yafadama duk wannan abubuwan? "
Ahmad yace" wallahi daddy da kunne na naji tana fadawa qawarta awaya," daddy yace

" shikkenan tashi kaje"
Ahmad kan kujera yakoma ya zauna shima yayi shiru

Daddy yadau waya yakira alhaji bukhar yayi masa bayanin komai, tare da neman yafiyarsa,
alhaji bukhar yace "wallahi karka damu, duk mahaifiyar tace take dorata Akan turbar banza,
nima nace karsu kuskura suzomin gida, nagaji da halaiyarsu alhaji,"

Daddy yace "a a alhaji ba za'a yi haka ba," nande daddy yayi ta tausarsa sannan sukai sallama

Daddy yafadawa su momy yanda sukai da mahaifin laila, nan momy tace " to alhmdlh tunda an
samu an fahinci Juna, kai kuma karka sake irin wannan

Dan anyi ma Abu kace kaima saika Rama, daka barta da halin ta ma, dakanta zatayi DANA
SANI
Kaga yanzu ba musan abinda mahaifiyarta zatayi ba, dakayi mana bayani tun farko da tuni an
warware matsalar cikin kwanciyar hankali"

Ahmad aransa yace ainagama warware matsala �


Cikin sanyin murya yace
" kuyi hakuri,"

wayarsa ya janyo yakira Abba yafada masa sun sauka lafiya, Abba yace a gaida baby

Momy ce tace" alhaji namanta ban fada makaba, munyi jika fa," alhaji yace" ko sauda ce
tasamu ciki? "
Momy tace " a a ahmad ne de yayi 'ya, "


Nan suka bashi labarin komai, daddy yace

" a a to akirata mana naganta," ahmad yana murmushin Jin dadi yanda iyayansa suka karbi
baby hannu bibiyu, yatashi da kansa yaje Dakin, lokacin har ansa Mata kayan shan iska ya
dauko ta akafadarsa kamar wata jaririya, mamy cikin kasa kasa da murya tace "hajia aikuma
munga ta kanmu Akan wannan yarinya," ν Ύν΄£
momy tace "um zamusha kallo kam, kamar akansa aka fara," ν Ύν΄£

daddy yana jinsu baice musu komai ba, kawai de yayi murmushi

Ahmad har gaban daddy yaje, ya dora masa baby Akan cinyarsa, yace
" daddy ga jikar taka, ina Santa daddy, wallahi ko iyayen ta banajin sunkaini Santa "ν ½νΈ³ν ½νΉ†ν ΌνΏ»

Gaba daya iyayen nasa suka hada ido cikin mamaki
Momy tace "aikam gashinan nagani, nina rasama ya akai suka baka yarinya, kamar wanda ka
musu asiri" ν Ύν΄£


Ahmad cikin shagwaba yace "kai momy"

Mamy hakima tace "to yanzu my son Naka shagwabar zamuji kona yar taka?" ν Ύν΄£
Sunkuyar da kansa yayi yana Sosa qeya

Daddy yace" ya sunan jikar tawa,"

baby tace" sunana baby"
Daddy yace "baby sunanki me dadi, Amma fadamin daya sunan, ai baby ba suna bane,"

tace "Izdihar"
Yace "to Allah yamiki albarka kinji,"

tace "to kaima haka" ν Ύν΄£

Gaba dayansu sukasa daria

Daddy yace "kina Zuwa school ko?" Tace " ina Zuwa a nursery 5 nake,"


Abba yace "a a masha Allah, da wanne suna ake kiranki a school dinku?"

Tace " Izdihar mu'az"

Daddy yace "gaskya ne, Amma daga yau kin koma Izdihar Ahmad muhd marzuk"

Ahmad dayake kallansu dadi yakeji kamar me


** *** **


"Nafeesa tun dazu nake kiranki Amma kinqi daga wayata, meyasa?"


"K'B atunani na, mun riga da mun Gama magana dakai,"
Kb yace " hakane, dama zan tafi Nigeria ne shine nace yakamata inji muryarki kuma inyi miki
sallama,"

feenah tace "ah "mabrouk" (congrats )
Allah yakiyaye hanya ya tsare "
Kb yace" nafeesa kinqi ni de, "
Feenah tace" Kb nafadama dalili aiko,"

yace" hakane, saboda ina Dan gidan Dan siyasa bakya sona," feenah tace
" haka yake, kuma Dan Allah kadena kirana, nariga da na zabi mijin da zan aura
Ahalin yanzu ma, cikin satin nan, ake tunanin saka mana rana, "

Kb yace" mukhtar ko? "
Feenah tace" ya akai ka sani? "

Kb yayi murmushi yace
" tayaya kike tunanin bazan San komai nakiba bayan ina kaunar ki "
Feenah tace" ok ngd bye," takashe wayar bata jira amsarsa ba

Kb yace feenah kenan, kina tunanin zan barki ne cikin sauqi haka? Bazai iyu ba!


** *** **


Ranar talata, iyayen mukhtar sukaje gidansu feenah, ba laifi anyi musu karba ta mutunci, inda
suka tsaida ranar bikin su bayan sun Gama karatu da wata biyu

Al'amarin ya yiwa wasu dadi, wasu kuma sabanin haka, tahir yaso ace yahadata da abokinsa
ahmad, husna ma hakan take

Yayin da kaka tace ita wannan al'amari baiyi Mata ba, saboda akwai tsohon saurayin nafi,
wanda ya kwanta Mata arai, shi taso nafi ta aura �

Saide bangaren ita feenah, abin yayi Mata dadi, tana ganin hakanne zaisa ta dena tunanin
mutumin dayaci amanarta

Amma a bangaren iyayen ta, sunfi kowa murna, suna Allah Allah ranar tazo suyi Mata auren,
saboda kada su sake maimaita DANA SANI irin wand sukai abaya






Mrs Usman ce ν ½νΆŠ
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

46


Salati yaci gaba da maimaita wa cikin ransa Zuwa wani lokaci
Kamar wanda aka tsikara yatashi cikin sauri yashiga mota Yabar gidan
Tashin motar da laila taji ne yasa cikin sauri ta Bude window ta leqa, tace "au shine ina jiran sa
zai shanyani yafita, zaizo yasameni ne,"
falo Takoma ta dora kafa daya kan daya


** *** **


"Hajiya yanzu ya zamuyi da yaran nan?"

Momy tace "hakuri zai bata mana hajiya, su sasanta kansu, shikuma zan sanarwa alhaji
matsalar ko wata qasar ne saiya shirya yaje su dora shi Akan magani,"

mamy hakima tace
" hakane, Amma wannan yarinya sai tayi DANA SANI
kizo ki tsaya a kanmu Dan cin mutunci kamar bamu haifeki ba,"
Momy tace" toya zamuyi hajiya alhaji nede duk ya janyo wannan matsalar"

** *** **


Yana tuqi ya dauko wayarsa yakira tahir, yace " tahir kazo gidanka kasameni inajiranka yanzu
akwai matsala,"

yana fadar haka ya kashe wayar
Tahir yace "to akwai matsala kenan duk yanda akai laila taqi hakura" ,
shima yahada yanasa yanasa yayi hanyar gida

Yana Zuwa gidan tahir maigadi yabude masa, yayi parking ya zauna acikin motar ko budewa
baiyi ba, kansa ya dora Akan sitiyari sai a wannan lokacin wani kuka mai ciwo yazo masa, shi
kadai yanata kuka, rayuwa kenan shikuma haka tasa rayuwar take, a duniya bazaiji dadin zama
da mace ba, ashe duk wannan bala'in daya shiga sanadin laila ne, tasan itace ta sashi a
wannan halin Amma itace take cewa bazata iya zama dashi ba, wai shine Dan shaye shaye,
hawaye ya share yace "tabbas laila sai kinyi DANA SANI"

qonqwasa glass din motar yayi, ahmad yabude masa, yashigo, ya kalli ahmad da idonsa yayi
jajir, yace "nawan me yake faruwa ne?"

Ahmad yace tahir " laila ce"

Sai hawaye
Tahir yace "bangane ba,? Meka ke nufi?"
Ahmad yace " tahir laila ta cuceni, ta azabtar Dani, kuma wallahi yanda ta illa ta ni, saita fadawa
aya zaqin ta"
Ahmad yafadawa tahir komai, yaci gaba da fadin " ashe itace tasa na dawo maci Amana a idon
yar mutane, har Yau nafeesa takasa fahimta ta, tahir laila ce tasa nakasa mallakar abinda
nakeso, tasa nayiwa rayuwar feenah illa, nasan cewa duk mijin dazata aura ayanxu, bazai ga
darajar taba, dole inci Gaba da neman feenah tahir inroqeta tayafemin in kuma aure ta,"
tahir yace
"innalillahi wa inna ilaihir raju'un
Abu kamar almara
Lailah!"
Yafadi haka cikin mamaki

Ahmad yace "wallahi tahir kaji abinda yake faruwa, yanzu haka batasan ma nabar gidanba,"
tahir yace
" yanzu menene abin yi? Ahmad kayi hakuri Dan Allah, haka Allah yaqaddaroma Naka rayuwar,
karkaje kadaki yar mutane kayi Mata illah"
Ahmad yace "bazan yi Mata komaiba tahir, Amma tabbas nasan sai tayi DANA SANI Akan
abinda tamin"

Tahir ya rungume shi, yana aikin rarrashi
Ahmad yace " wallahi ni tsoro ma take bani,ν Ύν΄£ν Ύν΄£ Mata kaidin su yafi karfin tunanin mutum,"

tahir yace "a a to yanzu buya zakayi kenan?"

Ahmad baisan lokacin daya saki daria ba, yace
" ni inbuyawa mace?" Tahir ma daria yayi yace
" Tome zakayi?" Ahmad yace "kawai idan natuna da abubuwan data haddasa a dalilin wannan
shan wannan maganin kawai sai inji Gaba daya tsoron mace ma ya shigeni,"

tahir yace "gaskya ne kayi hakuri ahmad hakika laila ta cutar dakai, Amma inama fatan samun
mace ta gari,"

ahmad yace "inaaaa, ainida kula wata mace sai ranar da Allah ya nufa,"

tahir yace "har feenah?"

Ahmad yace "kadena saka feenah alayin sauran mata, saboda ita din ta banbanta dasu, Amma
hakika zamana da laila yaqare"

Tahir zaiyi magana ahmad yace "please tahir karka cemin komai please, gobe zan tafi zaria in
dauko baby"
Tahir cikin mamaki yace
" Dan Allah?,
Wai kana nufin har an wuce wajan?"
Ahmad yace "sa wasa, kaga fitamin a mota, zan wuce gida," ν Ύν΄£

tahir yace "to masu mota, Babu inda zanje, kafata kafarka, Dan nasan bazakayi wa laila hukunci
mai sauqi ba,"

ahmad yace "ka yarda Dani tahir babu abinda zanyi Mata,"

tahir yace "toshkn Allah yakiyaye"

Yafita yashiga gida, aransa yana tunanin qaidi irin na wasu matan

Ahmad bai wuce gidaba, kai tsaye wani chemist ya wuce, yayi musu bayanin irin maganin
dayake so, aka bashi, yashiga mota, bai wuce gidanba kawai yawo ya wuce, sai dare yakoma
gida

Yana Zuwa gida yaga laila afalo, wata tsanarta tasake shigar sa, wuceta yayi zai shiga daki,
tace

" jimana,"
ya juyo ba tare daya tanka mataba, tace
" kasan me nake jira ai
"bani"

tafadi haka gamida miqa masa hannu, ahmad yadawo ya zauna kusa da ita, yace " laila,
banasan rigima, kiyi hakuri mana ko?"
Laila tace " inaaaa bazai iyuba, bazan iya zama da juya ba,"

ahmad yace " toshkn naji zan baki takardar ki, Amma kibari sai gobe, yanzu banda nutsuwar
dazan iya rubutu kinga ne?" Yana fadar haka yashiga daki, ya kulle, kan kadonsa yafada, ya
riqe kansa dayake sara masa, yace" innalillahi, wannan wacce irin qaddara ce, Allah ya
baiyanamin feenah "
Washe gari da safe ya shirya, cikin qananun kaya, milk din Riga daga gefenta wajan hannun
anyi sirikin baqi, sai baqin wando jeans, agogo ne ahannunsa gucci, sai qamshin turare yake,
yayi masifar kyau, yan futowa falo, dining ya kallah, yanda ya Zata kuwa haka yagani, wayam
Laila ta futo cikin shiri itama, tace "dama kai nake jira ahmad,"

Ahmad ya kalleta yace "to zauna ina Zuwa,"

Kitchen yashiga ya dauko flask yadau cup ya tsiyaya ruwan zafin, yahada tea mai kyauri, ya
zauna afalo yanasha, ya cewa laila " jeki dauko takarda da biro,"

laila cikin sauri ta tashi, ta dauko daga tsaye ta miqa masa yakarba,
Saida yagama shan tea, sannan yajuyo ya fuskance ta, yace " laila, kinga Allah bayasan saki,
ya halatta manashi Amma kuma bayaso, kinga yanzu zaria zanje anbani yarinya saboda haka
zan dauko ta inkawo miki ita, saiki riqeta," ν Ύν΄£

laila tace "ahmad me kace?"
Ahmad yace "shikkenan yi hakuri, ina Zuwa, nasan bakici komai ba, kibari kisha ko ruwa ne
zuciyarki tayi sanyi saimu qarasa maganar,"

yatashi yashiga dakinsa ba tare daya jira amsar ta ba

Yana tashi laila tace " tab ni zan yima riqon yarinya, lalle, to ai nakama banajin zan riqesu bare
na wani"

Yana shiga dakinsa, maganin daya siyo jiya yadauko, yaciro guda hudu,ν ½νΈ³ν ½νΉ†ν ΌνΏ» yadauko
coca-cola yazuba acikin glass cup, yasa spoon yajuya, sannan yakawo Mata falo
Yace "gashi"

, Babu kunya laila ta karba takafa kai ta shanye, ahmad ya zauna yace "to yanzu me kika yanke

laila?"
Cikin fishi tace "kai nagaji da wannan renin wayon, bazan iya zama dakai ba, kuma bazan iya
riqema daba, Dan haka kasakeni cc

Ahmad baiyi wata wata ba, yadau paper yafara rubutu, har zaisa saki daya, cikin ransa yace
kai! Ai kuma daddy yanasan auren nan,ν Ύν΄£ zai iya cewa namaidata, Dan haka yarubuta Mata
saki uku yabata, ya miqe yace
"to ni zan wuce, yarinyar da akaban ma ta isheni rayuwa, baizama lalle saina haihu ba, kekuma
tunda kinaso to kya samu awajan mijin dazaki aura,"

yana fadar haka yayi waje,
Motar sa yashiga yanaji kamar ansauke masa wani nauyi akansa, cikin nishadi yake tuqinsa
zaije yaga baby


** *** **


" Mama kisamin da wannan teddy dinma,"

mama tace" baby Amma naga alama so kike ki barni ko? "ν Ύν΄£

Izdihar tace" mama ai uncle dinma yana sona,"

mama girgiza kai tayi, aranta tace" ina miki maganar kanki, kinamin maganar yana sanki,"ν Ύν΄£

baby tace " to mama yaqi Zuwa ma, yaushe zaizo ne?"ν ½νΈ³

Mama tace"ai zaizo baby," Izdihar tace

" to mama kirashi awaya," mama tace
" wallahi idan bakimin shiru ba, saina bigeki."ν Ύν΄£ ν Ύν΄£


Dataga de mama Zata iya dukanta nan da nan tayi shiru,

12:26 yashigo Garin, kai tsaye gidan yashiga, da sallamar sa, baby najin sallamar sa ta taho da
gudu ta rungume shi, Riga ce ajikinta pink color, marar hannu, sai qasan rigar ansa net yayi
hawa hawa, tayi kyau sosai, anyi Mata fakin da gashinta, idan ka kalleta saika sake waigawa

Qansa aqasa ya tsugunna yagaida mama, suka gaisa sosai, mama aranta tace wannan yaro
shide akwai kunya 🙈 babu ruwansa, Abba aka kira awaya, yana Zuwa basuyi wata wataba,
sukai sallama dakowa suka dau hanyar kano, Izdihar sai bye bye take musu ta window, da yar

babynta ahannun ta,
Sunyi nisa atafia baby tace "uncle, kuma yaushe zan dawo wajansu mama?"

Ahmad cikin ransa yace tofa!
Kallanta yayi yace "baby ba yanzu zaki dawoba, Amma de zan dinga kawoki kina ganinsu
kinji?"
Baby tace "to dawa zan dinga wasa? Da anty?"

Ahmad yace "emana, dasu maryam dani,"

baby tace "yeee harda kai uncle? Ashe kaima zakana goyani kamar sabuwar anty?" ν ½νΈ³

Ahmad cikin ko in kula yace "sosai ma,"

tanata zuba masa surutu, har sukai nisa ahanya
Daga nan tayi bacci


** *** **


"Oh me yake damuna ne?"

Cigaba tayi dahada kayanta, saida tagama tas, sannan ta janyo Jakarta ta futo,

"oh ya Allah tafadi haka da karfi,"
ta tsugunna awajan, runtse ido tafara tana lashe lips dinta, maigadi yana hangota yataho da
sauri yana tambyarta hajiya lafiya kuwa? Laila ta dago ta kalleshi, tuni ya rikide yakoma Mata
ahmad, janyo shi tayi jikinta,ν ½νΉ†ν ΌνΏ»
cikin sauri ya fizge tare da fadin "subhanallah"
Yayi part din su hajiya da sauri yasanar musu abinda yake faruwa, dukansu suka futo, ga
ma'aikata sunata kallansu
Laila ta tashi dakyar Zata sake ruqo maigadi, duk wajan kamar almara suka hada baki wajan
fadin "lahaula wala quwata!!!" ν Ύν΄£

Mamy hakima tace "laila me yake damunki haka?"

Laila ta nunata da hannu tace "babu ruwan ki,"

tasake yin kan maigadi, mom ce tayi sauri tace
wa driver ya dauko mota akaita asbiti
Mamy hakima bata daddara ba, ta ruqota tace "yi hakuri kawo jakar amaida ciki,"

laila tasake nunata da hannu 👉🏻kamar yar maye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login