Showing 3001 words to 6000 words out of 49670 words

Chapter 2 - HAMDAH Book 2 Complete Free By Rasheedat Director .pdf

da kake faɗa kuwa?".
Abba ya gyara zama kana yace
"To me yafaru da wannan yanke hukunci haka? An san aure abune mai rai wata kila karshen
rayuwar sa kenan, shikuma cikin taya akayi yazamo ba naka ba tana da wani mijin bayan
kaine??".
Abba yafaɗa yana duban sa dason jin ba'asi dan shi kan sa yashiga ɗimuwa matuka...

Kafafun sa ya tanƙwashe kana yayi kasa da kansa yace
"Kayi hakuri Abba da abun da zan faɗa".
da sauri na ɗago kai na yayin da naji kukan ya tsaya cak na zuba masa ido babu ko kiftawa.
sai ya kuma yin kasa da kansa kana yacigaba da faɗin
"Lokacin da nayi tafi
naje nayi wata 1 ranar da na bar garin nan tana cikin yanayin rashin sarki,ranar da na dawo
kuma na tadda ta bata da lafiya bayan da na kai ta asibiti kuma likita ya tabbatar da tana ɗauke
da cikin wata ɗaya gatanan kuma ita shai da ce".
Yafaɗa yana nuna Ni da hannu.
Salati goggo Hauwa ta farka tace
"Amma lallai SALEEM a gaishe ka sabo da haka zakace ka haramta kan ka da ita sannan kuma
ciki ba naka ba? zancen banza kenan mata nawa suke da ciki kuma suna jinin al'ada ai ba akan
ta aka soma ba in ba ka sani ba kasani".
Maganar sa ce yasa goggo Hauwa yin shiru da nata maganar cikin ɗinbin mamaki kowa ke
kallon sa
yayin da shiko ya karkata hankalin sa gurin Abba da son bashi amsar tambayar da yakuma yi
mishi yanzu kan cewa da yayi mishi "Dalilin ka kenan?".
kan sa ya girgiza kana yace
"Bayan tafiya ta akwai wani wan da yake zuwa gurin ta ɗazu ma ai katan gida na suka tabbatar
min da haka".
wani irin zabura su Ummi suka yi suka haɗa baki wajen cewa
"Wani yake zuwa gurin ta??".
Abba kam hular kansa ya cire yashiga yin fifita da shi,niko ido na daɗa kura masa kamar tv...

Zaman sa ya gyara kana yasoma sanar musu duk abun da baba Mai gadi da Habu mai shara
da Sani direver suka sanar masa, kana ya ɗaura da ganin da Na'ima tace tayi mana a kan gado
da wan da Habu shima yace yagani.
salati parlour'n ya kaure da shi tuni hawaye yashiga wanke fuskar Ummi,
cikin takai ci Abba ya dube ni yana faɗin
"Abun da zaki saka mana da shi kenan ki ɓata mana family kin tozarta shi tozarci mafi muni me
kika nema kika rasa a rayu HAMDAH me muka gaza miki wacce gatace bamu baki ba sakayyar
da zaki yi mana kenan!".
kai narika girgizawa hawaye na zuba a idona na buɗe baki zanyi magana Abba ya daka min
tsawa.
kana ya dubi Ya SALEEM yace
"Tashi ka kaje hukuncin da ka yanke shine dai-dai ta haramta a gare ka kuwa tabbas".
a sannu ya mike yafita da sauri na mike tsaye kamar mai tashin aljanu na bi bayan sa kafin na
iso shi har ya isa farfajiyar gida da gudu nasha gaban san sa na ruko hannunsa na ɗaura kan
cikina cikin muryar kuka da fizgar numfashi na da nake ji kamar zai ɗauke, ina kallon fuskarsa
nace "Ya SALEEM Ya SALEEM wlh abun da ke cikin kinan nan naka ne kai ne uban sa, wlh babu
wani na mijin da ya taɓa rike koda bakin mayafi nane bare har ya sanni ƴa mace bayan kai Ya
SALEEM ɗan kane cikin kane wlh babu wani wan da yake zuwa guri na".

fizge hannunsa yayi kana ya dube ni da kyau yace
"Kada ki sake dan ganta abun da ke cikin ki da Ni ni ba uban sa bane, ke kinsan uban sa ai jeki
haifa ki kai masa abunsa in yaso ki kashe shi tun a ciki tun kafin ya fito duniya a san halin da
kike ciki, asan wacece ke mutum a fuska kawai,
In dai irin wannan ɗan ne zai zamo nawa har abada bana so!".
yana kaiwa nan ya juya yashige motar sa yafice a gidan..

Dur kushewa nayi a gurin ina wani irin kuka mai tsuma rai, na daɗe durkushe jin jiri na fisgata
na mike da kyar na koma parlour in da su Ummi suke har lokacin Ummi na hawaye sai dai ta
kasa furta ko da kalma ɗaya ce, goggo Hauwa da Aunty Halima sunyi jugum.
ina saka kafata cikin parlour'n Abba ya takatar da ni da faɗin
"Kada ki sake ki tako cikin parlour'n nan maza ki tafi kiyi nesa da mu domin zama da irin ki
acikin family tamkar rugujewar ahali ce,
kisani idan zuciya ta tabuga to kece sila kuma bazan taɓa yafe miki ba,bana kaunar nakuma
buɗe idanuna na ganki fita min a gida kitafi duk inda zakije amma ki sani ban yarda kije gidan
ɗaya daga cikin dangi naba har in dangi nane fita min a gida nace!".
yafaɗa cikin karaji baya nashiga ja inajin maganar Abba tamkar saukar ruwan dalma a zuciya
ta.
mikewa Ummi tayi hawaye taf idon ta tace
"Ina zataje Abba'n Fauzan ka bata lasisin shiga duniya kenan? bata da in da yafi nan in kuma
kace ta tafi to sai dai mutafi tare".
Ummi ta nufo ni tana cigaba da faɗin
"Ɗiyar ka mace zaka jefawa duniya sai dai in mutafi tare".
cikin fushi Abba yace
"Fatima idan kika fita daga cikin parlour'n nan to ki tabbata nayafe ki".
ido na waro cikin tsananin tashin hankali nashiga girgiza kai da karfi nace
"Ummi dan Allah dan Allah karki fita Ummi ki koma na rokeki Abba kayi hakuri ni zan tafi".
ganin tana ta daɗa matsoni yasani tahowa da gudu na rungume ta cikin muryar kuka nacigaba
da faɗin
"Ummi ki koma dan Allah karki fita".
sai kuma na zame jikina da sauri na saka hannuna biyu na share hawaye na nakuma kai hannu
kan fuskar ta nashare mata hawaye tare da yin wani murmushi ina duban ta yayin da wasu
zafafan hawaye suka zubo min nace
"Ummi duk inda nake a faɗin duniyar nan ko a muce ko a raye addu'ar ki itace zata zame min
garkuwa in nazamo silar fitar ki a gidan nan bazan taɓa yafewa kai na ba".
Najuya na dubi su goggo Hauwa da tuni suma hawaye yagama wanke musu fuska na haɗe
hannaye na biyu nace
"Dan Allah goggo Hauwa Aunty Halima kada kubar Ummi na ta fita dan Allah".
da sauri na juya nafita a cikin parlour'n na ɗau jakata dana yar dashi a tsakar gidan da sauri na
nufi kofar fita ina waige ko Ummi na biyo ni.
sauri na rika yi har na fita daga layin mu.......!★

Mommyn twins ce




Sauri nake kamar zan tashi sama duk da nafita daga layin unguwar amma hankali na bai
kwanta ba,tafiyar nake ina ta waige-waige,sai gani nake kamar Ummi zata biyo ni.
tafiyar kawai nake batare da nasan in da zani ba kokuma sanin in da na nufa ba.
Karar ababen hawa da naji ya karaɗe ko ta ina shine ya dawo dani cikin hayyaci na,nayi
mamakin ganin in da nake
Duk da kuwa tazarar dake sakanin unguwar mu da in da nake yanzu
wato winte.
Gefen titi na zame nashiga cikin mutanen da nagansu zazzau ne kan bence wasu ko nata
harkokin gaban su.yayin da zuciya ta keta azalzala ta ji nake idan naci gaba da jan numfashi
acikin garinnan tabbas zuwa anjima numfashi'n kwacewa zaiyi yatafi abun sa.
maganar da naji kusa da nine yasani ɗagowa wani ɗan yuniyon ne tsaye a kanmu yana faɗin
"Yauwa motar ku yanzu kam yacika kowa ya kawo kuɗin sa".
gafen da nake ya kalla kana yace
"Ƴan mata ke ma a wannan motar kike?".
tsintar kaina nayi da gyaɗa masa kai,yace
"To kawo kuɗin ki mota ta cika".
idanuna na mai da kan akwatin da ke gaba na tabbas nasan bana da ko sisi dan ban fita da ko
biyar daga gida ba, hasali ma babu abun da na iya ɗauka in ba wannan akwatin ba,ganin
yanata amsar kuɗin mutane sai na kai hannuna kan zip ɗin bayan akwatin ina ɗan wasa da shi
a raina nake faɗin "To ko ince masa yakarɓi akwatin a bakin kuɗin motar ne, Ni har da kayan cikin ma in dai zasu
ɗauke Ni suraba ni da garin nan".
yadda nake wasa da zip ɗin sai yana ɗan zugewa da mamaki nakurawa aljuhun jakar ido ganin
bakin kuɗi ya baiyana, da sauri na idda zuge zip ɗin nazaro kuɗin ina juyashi a hannuna naira
dubu biyu sabbi dar.
tunanin ta yadda akayi kuɗin yashigo cikin a kwatin nake,
nan take na tuno lokacin rasuwar Inna ina zaune a cikin bedroom ɗin Ummi taciro kuɗi cikin
wardrobe zatayi aika kasuwa daga cikin kuɗaɗen dubu biyu suka zubo,nakwashe ina mika mata
tafita da sauri tana faɗin na ajiye bari tazo,a lokacin kuwa kasan cewar ina zaune ne kusa da
akwatin sai naja zip ɗin a kwatin nasaka ciki kan cewar in tashigo zan cire na bata,gaba ɗaya
nagama mance wa a she dai ban bata ba..

Numfashi na sauke a hankali na furta
"Alhamdulillah".

dai-dai lokacin kuwa ɗan yuniyon ɗin yake faɗin
"Kawo nake".
duka kuɗin na mika masa sai naga ya zare dubu ɗaya yakai hannu aljuhu yazaro ɗari biyu sai
ya haɗa da dubu ɗayan nan ya mika min dubu ɗaya da ɗari biyu kenan.
karɓa nayi ina juya kuɗin a hannuna "Wato kuɗin motar garin da zasu ɗari takwas kenan?".
nayi tan bayar a raina,
ganin duk wan da yabada kuɗi sai ya shige cikin motar dake gaban mu sai nima na mike
nashige cikin motar ina rungume da akwatina.
Ina alla-alla motar ta tashi duk da kuwa bansan motar wani gari zata ba ban kuma da mu da
duk inda zaije ba ni dai burina nafita a cikin garin nan, bana kaunar na buɗe idanuna nakuma
ganina cikin garin bana kaunar narika shakar iskar garin naji na tsani garin gaba ɗayan ta.
numfashi na sauke tare da yin hamdala lokacin da motar ta hau kan titin taɗau hanyar fita daga
cikin garin......★

★★★


A nan cikin garin Bauchi kuwa,
kan kace me labarin abun da ya faru yakaraɗe ƴan uwa,
su Aunty Jaleela duk sun taho gidan cikin tashin hankali,
Aunty Rafee'at da yanzu isowar su ita da Dr Farooq ko jiran ya dai-dai ta parking batayi ba tafito
cikin tsananin tashin hankali tanufi ciki.
Nan ta iske ƴan gidan dukan su zaune cikin parlour'n Ummi har da wasu ƴan uwan su,
da sauri tashigo cikin parlour'n cikin muguwar tashin hankali tana faɗin
"Ummi ina HAMDAH tatafi ina tasani batasan ko ina ba".
Ummi da har lokacin kwalla basu dai na zuba a idon taba takai hannu ta share wasu zafafan
hawaye,bata iya ce komai ba
sai kwallar da ta cigaba da sharewa.
cikin share kwalla goggo Hauwa tace
"Tatafi bamu san in da ta tafi ba".
tafaɗa tana sharce hanci.
Kuka Aunty Rafee'at ta sake da karfi cikin muryar kuka sosai tace
"Wlh cikin Ya SALEEM ne wlh cikin sane wlh na shaida HAMDAH bazata taɓa ai kata abun da
ake zargin ta ai kata ba".
da sauri
tayi gun Dr Farooq da yanzu yashigo tariko hannunsa tare da faɗin
"Wlh Allah cikin nan na Ya SALEEM ne Abba'n Adeel kai shai da ne".
sai kuma tasaki hannunsa tayi gun goggo Hauwa tace
"Goggo Hauwa kema shai da ce Ya SALEEM shine mutum na farko da ya taɓa sanin ta ɗiya
mace,wlh na rantse HAMDAH bata ai kata abun da ake zargi ba wlh sharri a ke mata".
takarasa maganar cikin shashsheka..
Aunty Jaleela ma nagefen Ummi takasa cewa komai sai kwallar da take ta share wa,
parlour'n yayi shiru cike da jimami da sautin kukan Aunty Rafee'at......★

Ido na zuba wa hanyar da bansan na wani gari bane,duk tafiyar da motar yake gani nake baya
sauri,
munyi tafiyar da yakai na a wa 2,wata matar da take gefe na tabuɗe murya tace
"Direba nakusa sauka ni a Narkuta zan sauka".
direban ya amsa mata da to.
tafiya kaɗan muka kara muka iso wani gari mai kyau da tsaruwa a dai-dai farkon shiga garin
motar ta tsaya direban yace
"Mun iso masu sauka a Narkuta".
kasan cewar Ni ina ta bakin kofa ne yasa dole sai da na sauka kafin matar tafita,
maganar direban naji a sama
"Ƴan mata kema a nan zaki sauka ne".
firgigit na dawo daga tunani da natafi sai kawai na sinci kai na da gyaɗa masa kai,
"No wahala"
yafaɗa tare da jan motar sa yayi gaba.

ido na baza kan titin kowa na ta harkokin gaban sa,
a sannu na masa gefe kan wani kwalbati da ya kasan ce hanyar shiga wani layi na zau na, tare
da aje akwati na a gabana,
yayin da masu a dai-dai ta da mashina suke ta tsayuwa suna tan bayana ina zani,wasu nace
musu babu wasu kuma nayi musu shiru.
najima sosai zaune a gurin.
Har guri yafara rufawa yayin da ababen hawa suka yawaita kowa yana kokarin konawa gida,
Ina nan zaune a kan kwalbatin,
shafa cikina da naji yana ɗan motsa wa nayi yanzu kam naji ina jin yunwa akasin ɗazu da
banajin ko ɗigon yunwa,duk da wunin yau bansa ko ruwa a baki na ba, dan ko breakfast banyi
ba.
a hankali na mike nanufi gurin wata mai sai da abinci da nake hango ta can gefen titin,kuɗi na
mika mata nace
"Abani abinci".
sai kuma na dubawa kuɗin da nake mika mata ido da mamaki ganin naira ɗari biyu ne bayan
nasan dubu ɗaya da ɗari biyu ne a hannuna,
waige-waigen gefe da gefe na nayi ko dubu ɗayan yafaɗi kasa ne amma babu ko alamar sa.
maganar
matar naji tana faɗin
"Babu abincin 200".
nace "To abani drink".
ta miko min gora na amsa na juya a hankali hanyar da na bi nabaza ido ko zanga kuɗin amma
har na'isa in da akwatina yake babu alamar sa,
kurɓa uku zuwa huɗu nayi wa drink ɗin sai naji cikina na murɗa ni sai na rufe gorar,
A sannu na ɗago jin karar mota ta tsaya daf da Ni dai-dai lokacin aka zuge glass ɗin motar
kasa, wani matashi ne zaune a cikin motar sai busa sigari yake,yayin da wani ke zaune a gefen

sa,kai na na kawar da sauri jin hayakin sigarin yana isoni, matashin ya dubi abokin tafiyar nasa
yace
"Maye wannan fa ta haɗu musala zata rage mana dare sosai".
Kai ya gyaɗa cikin cakewa da kayan mayen da yake ta shaka.
matashin ya dubeni yace
"Ya ƴanmata shigo muje mana mubaki masau ki muhuta kihuta sosai".
yafaɗa yana latso laɓɓan sa,
nan take maganganu Inna da tarika yimin lokacin tana kwance a gadon asibiti suka fara yimin
yawo a ƙwaƙwalwa ta.
rumtse idonuna nayi da karfi,sai na
kuma kawar da kai na batare da nako kalle in da suke ba bare na furta wani abun.
ɗayan dake zaune gefen mai zaman banza yaleko tare da ɗaga murya yace
"Zazzafa ce fa nawa za'a biya ki?".
nan ma banko juyo ba dan na fahimci ƴan iska ne inajin ɗayan yana faɗin
"Muje gaba akwai irin su, biyu zamu ɗiba dan mu huta sosai".
ɗayan kuma yace
"Ta haɗu fa duk da tana cikin hijabi".
"Shiyasa take taja mana aji manya masu zaren take so muje kawai".
haka sukayi ta magan ganunsu sukaja motar su sukayi gaba.
numfashi na sauke tare da cigaba da ambaton sunan Allah azuciya ta da nake,
tafiyar su dakamar 5mn wata mota takuma tsayuwa gefe na wannan karon sai da naji gaban
kirji na ya faɗi,da sauri na juyo jin muryar wan da yake cikin matar
"Shigo na sauke ki a gida mana da alama dai kin rasa abun hawa ne".
saurayi ne shima sai dai baiyi kama da irin waɗan can da suka wucen ba yana zaune cikin
kamala, murmushi yayi min kana yakuma faɗin
"Naga kin jima zaune a nan da alama dai jira kike azo daga gida a ɗauke ki in bazaki damu ba
muje na sau keki a gidan".
da sauri na girgiza kaina tare da faɗin
"A'a Nagode kaje kawai".
kai ya jinjina yadube ni da kyau tare da faɗin
"To in ma bazaki shiga motata ba to ina mai baki shawara daki nimi mai abun hawa kihau ki tafi
gida".
murmushi yayi cikin maganar da yake kana yaci gaba
"Duk wani wanda yagan ki zaune a nan to zai yi miki kallo irin kallon da waɗan can samarin da
suka yi miki yanzu suka wuce,gashi dai duk mai tunani idan ya ganki bakiyi kama da irin mata
masu tallen kansu ba duk da dai basa da kama,
bai kamata kici gaba da jira a kan wannan hanyar ba dan yana da haɗari sosai,
akwai matasa marasa ɗa'a su basa jiran amincewar mace ko kotaso ko kar taso zasu ɗauke ta
da karfi su kai ta ɗaki su kulle idan suka gama kwanakin da zasu yi dake suje su yasar da ke,a
irin wannan lokaci suke fitowa, babu kuma wan da ya isa ya dakatar da su domin ƴaƴan manya
ne,zai fi miki kyau kitari abin hawa kitafi gida". ido na waro ina kallon sa har yakai karshen maganar yayin da tsoro ya lulluɓeni sai nashiga
gyaɗa masa masa kai,shiko murmushi yakuma kana yace

"Ko za'a bani aron number?".
mikewa tsaye nayi
cike da jin tsoron da ya ɗarsa min a zuciya na bashi baya ina ta ɗan kalle-kalle.
ina jin sa yakuma maimaita tan bayar sa ganin bani da niyyar amsa shi sai yaja motar sa yayi
gaba.

ido na kurawa cikin layin da nake tsaye a mashigar sa, matasa da magidan ta kowa yana ta
haramar tafiya masallaci sallar magriba. Da sauri na sunkuya na janyo akwati na nasoma
takawa cikin layin da sauri sosai dan ba karamin tsorata nayi da jin abun da mutumin nan
yafaɗa min ba,sai dai ina soma tafiyar naji cikina yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login