Showing 9001 words to 12000 words out of 49670 words
Chapter 4 - HAMDAH Book 2 Complete Free By Rasheedat Director .pdf
nabi bayan ta, ɗayan ɗakin da ke jire da nata ta nuna min
tace
"Shiga nan ɗakin ki kwanta na gyara miki gurin kwan ciya".
nace to,tana tsaye sai da taga nashi ga kafin ta wuce taje ta kulle kofar gida tadawo tashige
ɗakin ta.
bin ɗakin nayi da kallo,katifa ce a kasa da kaɗan yafi taburma kauri,sai wasu kayaki da kullin
buhunhuna a gefe,sai dai ɗakin a share tsaf yake babu ko datti.
a sannu na aje akwati na gefe na zauna kan katifar na janyo pillow da aka naɗe shi cikin
tsummar zani akayi masa riga da shi,na gyara na kwanta na rufe jikina da hijabi na,
numfashi na sauke lokacin da nakai hakarkari na kan shinfiɗi da sunan kwanciya,rabon da na
kwanta irin haka yau kwana uku, Allah mai girma yau gani acikin wata rayuwa,
saman ɗakin nabi da ido wan da kwano ne kawai rufin sa babu ko silim.
Allah ke nan mai iko mai yin yan da yaso da rayuwar ɗan adam,yau nice kwance cikin ɗakin da
babu gado bare wadaceccen katifa babu hasken wutan lantarki bare AC.
a tunanina kwanciyar da nayi zan sami yin ramuwar baccin da ban yishi ba na kwanaki uku
amma me sai naji babu ko ɗigon bacci a ido na,tunani damuwa kunci su suko addabi zuciya ta
haka na ta kuka sai daf asuba bacci yasamu nasarar sace ni....★
washegari da safe ina zaune cikin ɗakin tashigo
ɗauke da kwano da kofi ta dire shi gaba na, hannuna da nayi tagumi da shi na zare kana na
gaishe ta ta amsa tace
"Ki karya sai kiyi wanka ga ruwa can na kai miki banɗaki bari nagama suya sai mu tafi".
to kawai nace. ta fita na janyo kwano da kofin ɗumamen tuwo ne da kunu mai zafi saman murfin
kofin kuma awara ne da kosai suma sai turiri suke.
ina gama karya wan na sako hijabi nafito, tana zaune cikin kitchen tana ta suya yayin
yara suka zagaye ta sunata mika kuɗi tana zuba musu,har da matasa ma sunata shigo wa siya.
a sannu na shige bayin na ɗau tsawon lokaci ina wanke jikina da nake jin nauyin datti a fatata.
koda na fito daga wankan akwa tina na buɗe na ciro doguwar riga na material na saka,ina gama
sa kayan nazau na kan katifa.
can da jimawa ta shigo da mayafi a kan ta ta dube ni tace
"Taso mu tafi yau wa menene sunan unguwar taku?".
kasa nayi da kai da jikin hawaye ya cika min ido,jin ta kuma mai maita tan bayar sai na ɗago
nace
"Ni ba agarin nan nake ba zuwa nayi kuma ni bansan kowa a cikin garin nan ba"...
Da mamaki take kallo na cike da mamaki ta zauna kan ɗaya daga cikin ɗaurin buhun dake cikin
ɗakin, ta dube ni da kyau kana tace
"Tanan kika ɓullo kuma?".
kai na jinjina kana
nace "Wlh ni ba ƴar garinnan bace,ban taɓa sanin saba".
kwalla da suka zubo min na share kana nacigaba
"Kada ki mai dani gidan mu domin Abba na yace in nesan ta da su idan na dawo yace bai yafe
min ba, bana kuma son ta sana diyya ta naza mo silar barin Ummi na gidan mu,na gwammace
nayita yawo cikin duniyar nan har rayuwa ta takare na koma ga mahaliccina".
shiru nayi sakamakon muryata da ta sarke sabo da kuka.
ido Mama mai awara tazuba min,niko a hankali nashiga jan shashsheka.
dakyau ta zuba min ido cikin alhini tace
"Ke ko ƴar nan wani irin mummunar laifi kika ai kata haka,har mahaifin ki yayi fushi da ke irin
haka?".
kai nashiga girgizawa cikin muryar kuka nashi faɗin
"Wlh Allah ban ai kata abun da suka faɗa ba, kuma wlh Allah cikin nan nasa ne".
na karasa cikin kuka sosai,
cikin tsananin mamaki tamai da idanunn ta kan cikina dana ɗaura hannu kansa,kana ta mike
tadawo kusa da ni ta zauna tare da jan hijabi na ta zuba wa cikina ido,
kana tace
"Ba shakka ga ciki nan wanene mai cikin? yanzu ƴar nan wannan abu kika ai kata akan yaya
iyayen ki bazasuyi fushi dake irin haka ba ciki ciki".
tafaɗa tana tafa hannu.
kai nashiga girgiza wa
nace "Wlh ban ai kata zina ba cikin nan na Ya SALEEM ne".
hannuna ta ruko cikin rashin fahim ta tace
"Waye shi ɗin ta ya akayi yayi miki ciki to in ba zina ba menene?? kiyiyo ciki a waje kice ba zina
kika yi ba to menene sunan shi??".
ta jero min tanbayo yin ida nunta a kai na cike da fargaba da son jin ba'asi.
wasu hawaye masu zafi da kuna na share kana a sannu nashiga bata labarin rayuwa ta,tun
daga san da nafara sanin koni waye, har abun da yafaru dani yafito dani daga gida har kuma
yau da nake zaune a gaban ta.
kuka sosai nake har numfashi na yana fizga abun da yafaru da rasuwar Inna yadawo min sabo
fil a zuciya,cikin muryar shashsheka nace
"Allah ka kashe ni nahuta,kaɗauki rayuwa ta ko zuciya ta zata sami sassauci!!!!".
numfashi ta sauke cike da tsananin alhini da al'ajab.
Tace "Akul kidai na faɗan haka babu kyau Allah yafiki son kanki, yakan jarabci mutum dan
yagwada imanin sa,
hakika mahai fin ki ya yanke hukunci cikin fushi sai dai duk wan da hakan yazo masa rana a
saka dole yaji babu daɗe,shi kuma mijin ki ya kama ta yayi tunani ko da a ce hakan yafaru da
gaske aure yabashi,amma tun da yace bai amin ce ba bai kuma karɓi cikin ba to shi kenan,
ƴaƴa nawa suka rayu batare da uba ba, Allah sauke ki lafiya yataya ki rukon abun da zaki
haifa,su kuma waɗan da sukayi ruwa sukayi saki wajen ganin sun ɓata aure, Allah yanuna
musu buwayar sa da izzar sa na kwatar wa wanda aka zalinta hakkinsa tun anan duniya,
zaki zauna tare da ni a nan har zuwa lokacin da zuciyar mahaifin ki zai sassauto daga fushin da
yayi."
Nan tarika yi min nasiha takuma nuna matukar tausayar ta gare ni,har sai da taga na dai na
kukan.
nan take faɗa min ita ɗaya ce a gidan mijinta ya rasu tun da daɗe wa,
ƴaƴan ta uku sai dai tun suna kanana suka rasu dukan su.
Duk da halin da nake ciki amma na tausaya mata dajin bata da ɗaya.
Batabar ɗakin ba har sai da taga na dai na kukan gaba ɗaya.
can an jima ta kuma dawowa tace na fito tsakar gida zama Ni kaɗai zai daɗa kara min damu
wa...
tun daga ranar Mama ketason gusar min da damuwa ta, sai dai banajin har na mutu damuwa
da ɗacin dake raina zai yaye gaba ɗaya.
Sai dai nakan yi iya bakin kokari na wajen ganin na ɓoye damuwa ta ganin tana nuna kulawa da
son ganin na kwantar da hankali na,na sawa zuciya ta salama.
nakan faki idon ta a duk san da zuciya ta tatuno min da abun da yafaru sai na shiga bayi nata
kuka har sai naji zuciya ta taɗan sami sassauci, haka ma idan natuno da Ummi na ko wani hali
take ciki yanzu,nan ma bayin nake shiga nayi kuka na.
mama
bata taɓa barina na nazauna a ɗaki ni kaɗai,da zarar taga nashiga ɗaki naɗan ɓata lokaci zata
leko tace na fito,
wani sa'in ko makota zata shiga sai tace nazo muje.
idan aka ganmu tare a ka tan bayeta wacece Ni sai tace ƴar kanin tane tazo daga garin su
Yola..
....★
Da misalin ƙarfe 4 na yamma zaune muke a tsakar gida,
ina surfe wa mama waken kosan gobe,
Ita kuma tana wanke waken awara,
yanzu tare muke yin ai kin kosai da awar duk da hanani yi datake,wani sa'in ma Ni nake soya
mata tun idan naji hayaki kai na da ido na suyi ta ciwo har yanzu na saba,wani sa'in kuma ita
zata rika suyan Ni kuma na rika zubawa masu siya.
Juye waken mama tayi cikin robar kai markaɗe ta mike tana faɗin
"Yau baza ayi awarar dare ba gaskiya jiya dukan mu bamu yi bacci da wuri ba gashi yau da
safen ma bamu huta ba,yanzu daya kamata ace hutu muke gamu gaban wake,kullum ai kin
kenan kuɗi kuma ba taruwa yake ba".
Jinjina kai nayi Allah sarki Mama kullum haka take faɗa wai sai dai mukare a gindin wuta amma
bamu aje wani ribar kirki,bayan da ribar muke ci musha da sauran bukatu.
Murmushi nayi nace
"Mama ayi kawai tun da an sa har Da waken yau,kuma anjima zaki ga anata shiga nima".
tace "To shike nan ai badun an jikan bakam gaskiya da mun huta yau".......!★
Mommyn twins ce
Tun waye war garin yau nake jin tashin zuciya da warin magani a jiki na,
yau kwana huɗu kenan nake ta fama da irin wannan yanayin,sai dai nayau yafi na sauran
kwanakin, shiga na bayi sau uku kenan inata wanke jikina wai ko dun zan dai jin warin da kuma
tashin zuciyar,
amma sai ji nake kamar karuwa yake.
Sabulun da Mama ta siya min mai kamshi wan da tun ɗazu shi naketa wanke jikina da shi na
kuma ɗau kawa yanzu na fito tsakar gida,
yawun da ke kunshe a bakina naje can gefe na zubar,
fuska na yamutsa jin zuciya ta naci gaba da tashi kamar zanyi amai,
Mama dake jajjagen kayan miyar abincin rana ta dube ni da kyau tace
"Ya dai HAMDAH".
"Bako mai Mama".
nafaɗa ina daɗa yamusa fuskar,
ganin yan da nake ta zubda yawu yasa mama bani goro tace nasa a baki na zai ɗan rage min
yawun.
boket nakuma cikawa da ruwa na shiga bayi nayita mulke jikina da sabulun sai da na kusa karar
da salun kafin na fito,bawai kodun na dai na jin abun da nake jin ba sai dai dun gajiyar da nayi.
ina shiga ɗaki nayi wurgi da sabulun na sulale sakiyar ɗakin na zauna,
kai na na dafe jin yadda aman ke ta kokarin tahowa,sai juya kai nake.
da sauri na janyo akwati na na buɗe cikin hanzari nakifa fuskata cikin akwatin ina shaƙar ɗan
guntun kamshin turaren Ya SALEEM,daya zauna ciki sabo da kayana da ke ciki sai kamshin
yazauna jikin akwatin duk da na wanke kayan cikin yafi akirga amma yar yanzu akwatin yana
ɗauke da ragowar kamshin, duk da bawani kamshi mai yawa bane sai naja numfashi sosai
nake jiyo kamshin.
A hankali narika sauke numfashi jin aman na lafawa,sai dai har lokacin ban fasa jin warin
maganin ba,najima fuska ta na kife cikin akwatin,sai dai har lokacin ina jin warin maganin,
a sannu na mike cike da takaici da kuma tausaya wa kai na dan nasan in kwana zanyi ina
shaƙar kamshin turaren sa kaɗai bazai gusar min da abun da nake jiba,
kamshin sa kamshin dake fita daga cikin jikinsa shi nake so shine kaɗai mai iya fidda ni cikin
wannan hali,
wasu zafafan hawaye ne suka tsiraro min kan fuska nakai hannu na share,
a sannu nayi kasa da hannuna zuwa kan cikina da sai motsawa abun cikin yake na shafa,
baya nayi na jingina bayana da jikin garu tare da rumtse idanuna,yayin da zuciya ta ke wani irin
matsanancin zafi da kuna,
idanuna nakuma rumtse wa da karfi cikin zubda kwalla da ɗacin zuciya nashiga faɗin.
"Shine uban ka yace bashi bane yakore ni bayan yasan jikin sa kaɗai nake shiga na dai na jin
warin magani ko tashin zuciya,yasa Abba ya koreni ya nesanta ni da Ummi na da ƴan uwa
na,yace kai ba jinin sa bane kada nasake danganta ka dashi,haka zaka fito duniya baka da uba
kahaɗu da hantarar mutane waɗan da zasu rika yi maka kallon shege,ina ma da ace Inna ta
tana nan da idan na haife ka wa ita zan bawa, na tabbata bazata taɓa bari duniya suyi maka
kallon shege ba,na tabbata soyayyar da take min bazata taɓa kin jina ba ko da ya kasan ce
shegen ne, na tabbata..na tabbata...na tabbata.."
kukane ya kwace min sai nayi saurin kai hannuna kan baki na na toshe tare da sakin kuka mara
sauti.
Muryar Mama naji tana tahowa ɗakin haɗe da kiran sunana,
da sauri nayi kokarin sai da kukan nashare hawaye na cikin hanzari, buɗu labule tayi tana faɗin
"HAMDAH mekike yi ne acikin ɗakin tun ɗazu ko bacci kike ne??".
shiru tayi da maganar nata tare da zuba min ido daga bakin kofar kana tace
"Au abun da kika zauna yi kenan? har sai yaushe zaki sanya wa zuciyar ki salama HAMDAH?,
ko badun ni ba kodun abun cikin ki kya fauwala wa Allah komai dan tsira da rayuwar ki wajen
haihuwa,idan fa kika cigaba da sawa zuciyar ki damuwa da yawan ta tuno abun da ya faru ya
kuma wuce ke zaki cutar da kanki, do min kuwa yanzu cututtuka sunyi yawa,ba a son mai lalura
irin naku ta yawaita shiga damuwa,sai ya iya yin sana diyyar ta ko na abun da zata hai fa agurin
haihuwa".
da sauri nashiga girgiza kai cikin son ɓoye damuwa ta nace
"Mama bafa kukan nake ba har yanzu Ban dai na jin aman bane,kuma yaki fitowa sai dai narika
jin tashin zuciya sosai".
shiru tayi idanunta a kai na kana tace
"To shike nan na ɗau ka ai kukan kika shigo yi,sa kaya kizo na dama miki kudun tsami wata kila
yasa ki dai na jin aman".
To nace,ta saki labulen ta juya dan zuwa dama kunun.
A hankali na sun kuya naɗau kaya nasoma sawa.
Ina gama wa na haye kan sallaya dan dama da al'wala ta na gabarar da sallar azahar kana
nafito,
Na tadda har ta dama min kunun garin dawa da ruwan tsamiya sai tashi da kamshin kayan yaji
yake,
a gefen ta bisa taburma na zauna tamika min kofin kunun,
na amsa nakai kofin bakina a sannu na soma sha,
a sannu cikin ikon Allah narika jin warin maganin da nake jin nan naraguwa,ina gama shan
kunun ta miko min gauta a cikin farin laida tace
"Tun da goron bai miki ba ki gwada cin gautar wata kila shi ya miki,
gobe Litinin idan Allah ya kai mu zaki fara zuwa awu nan cikin asibitin unguwar nan,gashi anata
faɗakar wa a gidajen rediyo yakama ta kifara zuwa dan yana da amfani kwarai."
kallon cikin tayi kana taci gaba da faɗin
"An ya kuwa HAMDAH lissafin cikin nan dai-dai kika yi?, cikin wata huɗu kamar cikin wata shida
ko bakwai,cikin fari da irin wannan girma haka kuma cikin fari bai fiye girma ba".
murmushi nayi nace
"Allah Mama dai-dai nake lissafin kinga lokacin da aka kai ni asibiti watan sa ɗaya ne dai-dai,
yanzu kuma an kara wata uku kenan bayan wancan wata ɗayan kin ga wata huɗun kenan".
baki mama tarike tace
"Iye har kin rike lissafin dalla-dalla ikon Allah zamani da ƴaƴan cikin ta".
dariya nayi cike dajin kunya narufe fuskata da tafin hannuna.
ranar gauta da kunun tsamiya na wuni sha cikin yardar Allah kuwa naji sassaucin abun da nake
ji.
Washegari da sassafe ina kwance Mama tashigo ta tadani tace natashi na shirya natafi asibiti
yin bukin,
bayan nayi wanka na shirya tare da ita muka tafi asibitin,ita tayi ta zirga-zirga da cuku-cuku ina
zaune sai dai abun da yakama dole sai nayi da kai na nake binta muje.
Sai wajen karfe 1 muka gama komai har da awun,
Kasan cewar yau ɗin Monday ne hakan kuwa yayi dai-dai da yau ne ranar awun masu cikin
fari,dan haka ya zamo ranar zuwa awo na kenan duk bayan wata ɗaya.
A gajiye muka shigo gida ga yunwa,
kitchen na shiga na ɗauko kofin ragowar kunun tsamiya ta da mama ta dama min da safe kafin
mutafi,
na fito tsakar gida gindin ɗan bishiyan tsada da muke zama musha iska na zauna kan taburman
data shin fiɗa,
ita kuma ɗumamen tuwo ta zubo tazo tazau na tana ci muna ɗan taɓa hira,har ta kammala,
lai dar magunguna da aka bamu a gun awu tajanyo ta fiddo da magungunar,
da sauri na kawar da kai na ganin maganin kaɗai yasa naji zuciya ta yaso ma tashi,
"Karbi maza ki haɗiye kin ji abun da suka ce kada ayi wasa da shan kwayar yana taimako
sosai,bari ma na tashi naje na nimo miki ƴan abubuwan da suka ce kirika ci wake kam muna da
shi,karɓa kisha na tashi".
juyowa nayi jin abun da take faɗa ji nayi kamar na zandara ihu, maganin ta mika min tare da
miko min ruwa tana cigaba da faɗin
"Karɓi mana kada su sha iska".
amsar maganin nayi ban da ruwan nace
"Ni da kunu zan sha bazan iya sha da ruwa ba".
tace "To sha dashi ɗin".
da kyar na haɗiye da kunun ma jin yana kokarin dawowa da sauri naɗau agwaluma da ta siya
min a asibitin naso ma tsotsa da sauri.
ta mike tana faɗin
"Bari naje gurin mai kayan miyar can na haɗo cefani".
kai kawai na gyaɗa mata tafita.
Baya na na jikina da jikin bishyar da nake zaune a gindinta,a hankali naci gaba da shan
agwalumar,
Ina zaune agun har ta dawo da cefane niki-niki a talakance,
nayi mamakin ganin har da hanta a cikin cefanen,
batare da ɓata lokaci ba ta haɗa min gwaten wake da hanta da ganyen ogu. kamar yan da
ma'aikatan asibiti suka faɗa...
duk bayan kwana biyu Mama zata siyo kifi ko hanta ko kwai ta sarrafa min shi,
lurar da nafara yi jarin awara da kosai yafara yin kasa nasan ba komai bane ya kawo hakan sai
waɗan nan kayan cime-cimen da take girka min,
wani ranar da zata je yin cefanen har takai bakin kofa nabiyo ta da sauri nace
"Mama ki bar kashe kuɗin nan haka kwanakin baya awara mudu huɗu ake yi kosai mudu biyu,
amma yanzu mudu biyu