Showing 24001 words to 27000 words out of 49670 words

Chapter 9 - HAMDAH Book 2 Complete Free By Rasheedat Director .pdf


idan taje gidan matar tarika mata wulakanci da gani-gani shi yasa ma shekaran ta 7 bataje ba...

Hawayen fuskata na share kana nace
"To mama sai kin dawo Allah ya kiyaye hanya amma Mama ki dawo da wuri dan Allah".
tace
"Insha'allahu zan dawo da wuri HAMDAH kwana biyu zanyi da yar dar Allah zanje naga yanayin
zaman gurin in yaso ma zan saida gonana da yake can sai na dawo na kama mana gida a nan
ko kuma na kama mana a can Yola sai na dawo na É—auke ku sai mu koma".
nace
"To Mama Allah ya kai mu ya kiyaye miki hanya"
ta amsa da Amin Amin.

Da azahar É—in muka fita yi wa mama rakiya ni da Zainabu har bakin hanya muka kai ta yayin da
take rike da Nasmah,
da tun dawowar ta daga niman gida Æ´ar ta nanne mata sai da ta goye ta,
sai da muka tari mai abun hawa kafin ta miko min ita,
kana ta karɓi Naseem tana yi masa wasa shi ko sai wage mata baki yake,
duk yaran sai dariya suke mata itako sai wasa take musu,har sai da mai abun hawa yayi
magana kana ta miko min Naseem,
kuka ya saka yana zillo alamun zaije gurin ta,
murmushi tayi tare da lakata kuma tun sa tace
"Mai gidan ka zauna zanje nadawo yanzu bazan daÉ—e ba zanje na nimo sadaki na kawo maka".
dariya ya saka kamar wan da yasan me aka ce,

Zainabu tace
"Ai kam kine mo da yawa dan yanzu mata suke bawa maza sadaki".
Mama tace
"Ai kam".
kana ta shige abun hawa muna É—agawa juna hannu yayin da hawaye ke zuba a ido na,
muka juya muka koma gida...!★



Mommyn Twins ce



Ranar a zauren malam Musa yakuma kwana ya bar mana É—akin,
washegari haka na wuni sukuku bani kaÉ—ai ba hatta Naseem da Nasmah idan ka kallesu kasan
sunyi kewar Mama,duk da kuwa Zainabu tana jan su ajiki tana yi musu wasa,
Malam Musa kuwa yana iya bakin kokarin sa ya kawo mana abinci sosai Zainabu ta girka
mana....
yau kwana biyu kenan da tafiyar mama inata murna da zuba idon ganin dawowar ta dan nasan
yanzu kam tana hanya,
ganin bakina yakasa rufuwa Zainabu tayi ta zolaya ta tana yi min dariya.
murmushi nayi nace
"Ai in sha Allahu yau zata dawo".
Ido nayita kurawa hanya dan ganin isowar Mama har yamma shiru babu wani labari,
wasa-wasa har dare yayi zuwa lokacin kam shiru na zauna cikin damuwa jikina yagama
mutuwa.
har dare yayi nisa sosai nan ne na cire raina da dawowar mama a yau na sa a raina wata kila
sai gobe zata dawo.
goben ma haka shiru yanzu kam hankali na yakai kololuwa wajen tashi,
ba abun da ke damuna kaÉ—ai ba kenan,
duba da gidan da nake zaune duk da Ni basa nuna min wani hali ko kaÉ—an,
Amma bana jin daÉ—i badun komai ba,
sabo da ganin shi mai gidan da gidan sa a zaune yake kwana gashi yanzu yanayin damina
kusan kullum sai anyi ruwa ga sanyi haka akan taburma take kwana acikin zauren.
gaba É—a hankali ya ninku wajen tashi,
ace mai gida da gidan sa a zaure yake kwana zauren ma kan taburma ga sanyi.

Yau kwanan mama biyar da tafi babu alamar ta.
da safe na nufi zaure in da kayan mu yake naÉ—auki akwati na da nazo da shi tuntini na haÉ—a
kayana kala biyar wan da tuntini da ma da su nazo naketa sawa har yanzu sun gama tsufa sun
koÉ—e wasu ma har sun yayyaye sai da aka bisu da É—in ki,
na haÉ—a kayan cikin akwati,
na É—au ki kayan Naseem da Nasmah wan da suka samu a suna kala hurhuÉ—u sai kuma wan da

Mama tasiya tun kan na haihu na haÉ—a su cikin akwatin,
da É—an sauran kayan bukata,
nayi musu wanka nima nayi,
Zainabu tazuba min ido ganin inata shiri kana tace
"Naga kina ta shiri da haÉ—a kaya wai ina zaki ne haka da kaya?".
nayi murmushi tare da duban ta nace
"Zan bi Mama ne dan har yanzu gashi bata dawo ba".
Zainabu tace
"To ke da zaki jirata batace kijirata ba".
nakuma murmushi tare da faÉ—in
"Eh tace na jira ta amma har yanzu bata dawo ba kawai zan bita can É—in".
shiru Zainabu tayi kana tace
"To shi kenan amma Ni inaga da kin daÉ—a kara hakuri ki jirata".
nace
"A'a zan bita kawai".
tace to shike nan.

Bayan nagama kimsa yaran na É—auki Nasmah na goya na saka hijabi na kuÉ—in da mama ta tani
na ciro sannan na É—auki Naseem a hannu,
Zainabu ta roko min akwati na har bakin hanya ta raka ni,
na hau abun hawa zuwa tasha ina isa
Na shiga motar YOLA........

Acan cikin garin Bauchi'n Yakubu kuwa zaune Ummi take akan sallaya..........!★



Kuyi hakuri dan Allah wlh sabar sauri ko editing ban yi ba😫



Mommyn twins ce



Wani sassanyan kuka Ummi ta sake dai-dai lokacin da ta sallamar da sallar nafilar da take,
ta É—aga hannayen ta biyu tana kwararo addu'a yayin da hawaye ke sauka a idon ta,
tun ranar da HAMDAH tasa kafa ta fita agidan kullum Ummi acikin kuka take.
badare barana ko da yaushe acikin yimata addu'a take tana nina mata kariyar Allah a duk inda
take.
Wani sassanyar kuka mai matukar taɓa zuciya Ummi takuma sakewa lokacin da take jaddada
rokon ta ga mahaliccin mu.
yayin da muryar ta ke fita haÉ—e da sautin kuka.

Fauzan da yanzu shigo War sa cikin É—akin da sauri ya isa in da take yadurkusa gaban ta tare
da kifa fuskar sa kan cinyar ta,sai ya saki kuka yana faÉ—in
"Ummi dan Allah ki daina kuka Ummi kullum sai kinyi kuka Ummi ki dai na kuka".
yafaÉ—a cikin matukar damuwa da ganin halin da mahaiyar tasa kullum take ciki,
kansa ta shafa da hannunta É—aya yayin da ta É—ago hannunta guda tashiga share hawayen
fuskar ta.
a hankali tace
"Taso Fauzan yi shiru na dai na kukan".
tafaÉ—a cikin sansanin karfin hali da son danne zuciyar ta da ke wani irin muguwar bugawa,
Aduk san da ta nuna da HAMDAH irin yanayin da take shiga kenan sai dai na yau ya ninka na
ko yaushe.
yau bugun zuciya ne mai haÉ—e da É—inbin tsoro.
da sauri ta kai hannunta ta dafe kirjin ta tare da furta
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un".
da karfi cikin tsananin jin tsoron da ya lulluɓe ta..

cikin rawar murya mai haÉ—e da tsoro tacigaba da faÉ—in
"Ya Allah ka kare baiwar ka aduk in da take a duk halin da take ciki,ya Allah kafini sanin inda
take kakare ta da kariyar ka."
Kuka sosai Ummi tafashe dashi ta rungume Fauzan da shima yakara sau tin kukan sa,
kuka sosai Ummi take tamkar karamar yarin ya kuka.
cikin Muryar kuka Fauzan yake cewa
"Ummi kin ce Aunty HAMDAH zata dawo kullum haka kike faÉ—a gashi har yanzu bata dawo
ba,Ummi yaushe Aunty HAMDAH zata dawo?".
hawayen fuskarta tashi ga share wa yayin da take kokarin sai da hawayen da kuma kukan tace
"Ko bata dawo ba Allah zai kare ta a duk inda take a duk halin da take ciki, shine mai kariya
buwayar sa ya isa ko ina".
taÉ—ago Fauzan tashare masa hawayen fuskarsa kana taci gaba da faÉ—in
"Yi shiru kaji a duk inda take tana cikin kariyar uban giji".....



Tun da muka fara tafiya nakejin wani irin yanayi a jikina,
sai dai na kasa fassara kalar yanayin da nake jin kaina ciki,
ina dai zaune cikin matar shiru yayin da Nasmah ke goye a bayana har lokacin Naseem kuma
na rike a hannuna,
duk kanin su bacci suke,
daÉ—a gara rukon Naseem nayi kana na zuba wa titi ido.
sosai motar ke sharara gudu kan hanya sai dai nayi mamakin ganin tulin tafiyar da mukayi mai
nisar gaske wai har lokacin bamu iso garin Yola ba,
tashin tun sassafe gamuna har bayan azahar a kan hanya duk da kuwa gudun da motar take.
tun fasinjojin da ke cikin motar suna hira har kowa yayi tsit sabo da nisar tafiyar.
karfe uku da rabi dai-dai muka isa wani gari in da direba yagyara fakin a gefen titi,

numfashi na sauke tare da yiwa Allah godiya a raina nake faÉ—in
"Kai wannan gari akwai nisa har sai yanzu muka iso gaskiya wannan Yola'n akwai shi da nisa".
bankai ga idda maganar zucin da nake ba najiyo maganar direba yana faÉ—in
"To nifa iyaka na nan garin bazan karasa can Yola ba waÉ—an da zasu wuce zasu yi gaba sai su
sauka su tari wata motar anan".
Ido na waro da mamaki nace
"Au bamu iso Yola'n bane?".
wata matar da ke gefe na tace
"Eh ai bamu iso Yola ba tukun me mukayi ai da sauran tafiya".
"Ikon Allah".
nafaÉ—a a fili kana na buÉ—e marfin motar na fito, direban ya sauke mana kayan mu,
a hankali na koma gefen titi kan wani itace na zauna ina rungume da Naseem daya farka yana
shirin yin kuka,
gyara zama ta nayi da kyau nabuÉ—e jakata na ciro gorar kunu da na É—ura musu,
nabashi yasha kana na kunce Nasmah da naji ita ma tana motsi na bata itama tasha,kana na
kara musu da nono, sai da na tabbatar sun koshi sannan na mike na mai da Nasmah na goya
ta na É—auki Naseem...
wata mota ce tasharo kwana daga can dagodu sosai
sai kuma ta rage gudun dai-dai san da tazo daf da Ni taÉ—an gotani kaÉ—an sai ta tsaya.

Direban dake tuka motar yazoge glass É—in motar yaleko ni kana yace
"Tafiya ne?".
Kai na gyaÉ—a masa kana nace
"Eh". yace "Wani gari".
nace "Yola".
"Ok shigo ai wannan motar Yola can na nufa yanzu".
da sauri na gyara rikon Naseem nasun kuya na janyo akwati na,
da saurin sa yafito daga cikin motar ya karɓi akwatin yabuɗe but yasaka kana yabuɗe min gidan
baya nashiga kana ya mai da murfin yarufe yakoma mazaunin sa kana yaja motar muka soma
tafiya.
mamaki ne yakama Ni lokacin da naga Ni É—aya ce cikin motar babu kowa babu ko fasinja acikin
motar.
abun da tadaÉ—a bani mamaki ma shine motar batayi kama da na fasinja ba,ban kuma lura da
hakan ba sai da nashiga motar.
lafiyayyiyar mota ce irin na shiga kawai. shiru nayi ina bin motar da kallo motace mai kyau
tabbas batayi kama da motar É—iban fasinja ba.
wani irin tsalle zuciya ta tayi dai-dai lokacin Naseem da Nasmah suka zabura lokaci guda suka
kankame ni Naseem dake rike a hannuna yajuya kansa tare da kife fuskar sa a kirjina sai ya
shiga sauke numfashi,
leka fuskar sa nayi sai naga yana bacci,
Saukar numfashin Nasmah nakeji a bayana itama a hankali.
Idanuna na lumshe tare da kuma buÉ—e su,
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un"

nafurta kan laɓɓana batare da nasan da fitowar sa ba.
yayin da yanayin da nake jinsa a tun motar farko da na rika ji ya karu matuka,
sai dai har lokacin nakasa gane kalar yanayin.
haka mukayi ta tafiya yayin da tsalle da bugawar da zuciya ta take ke karuwa a kowani
dakika,jin zuciyata nacigaba da azalzala ta sai nashiga nanata kalmar
Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un.
tafiya muke tafiya mai nisar gaske nayi mamakin ganin garin Yola da irin wannan nisar wajen
karfe 6 muna kan hanya can muka iso wata kungurmin daji danake hangosa daga nan kan
hanya.
a sannu direban yaÉ—an sakai ta godun da yake yafaka motar a gefen titi sakamakon kiran da ya
shigo wayar sa,
yajuyo ya kalleni yace
"Bari na amsa waya ina zuwa".
jiki a sanyaye nace masa "To".
ya sauka da sauri ya mai da murfin ya rufe, yaÉ—a masa can gefe yana wayar,
gabaki ɗaya hankali yakuma mummunar tashi tsoro mai firgitarwa ya lulluɓe ni, bugu da kari
ganin yanayin da Naseem da Nasmah suke ciki duk da bacci suke amma sai zabura suke suna
kankame ni.
daÉ—a kankame Æ´aÆ´ana nayi ina ambaton sunan Allah,
magana yake yana kallon motar a hankali nakai hannuna nayi kasa da glass É—in gefen da nake
a hankali batare da na saukar dashi duba.
naÉ—an maso jikin kofar na kasa kunnena..

A hankali nake jiyo sautin maganar sa duk da bana fahimtar abun da yake faÉ—a
sai dai yanayin iska dake kaÉ—a wa yana É—an É—ibo maganar zuwa inda nake.
"Yes oga yaukam nayi babban kamu wata yarin yace da Æ´aÆ´a biyu a ajiye min kuÉ—i na ayi musu
kyakkyawar ajjiya ina zuwa a damka min su,
ina faÉ—a maka rai uku da babba da yara kananu guda ku a dana min kuÉ—i na kawai munkusa
isowa,ina faÉ—a maka yarin ya ce gatanan inaga budurwa ce da yara guda biyu ai yau kam fitar
sa'a nayi, haba oga ai kai ma kuɗin da zaka karɓa akan su bana wasa bane jinin su ma kaɗai
makudan kuÉ—i ne bare sauran sassan jiki". wani irin masifaffen tsalle zuciyata tayi tamkar zata faso kirji na ta fito,
da karfi na dafe kirji na yayin da kai na yayi wani irin mummunar sarawa,
jikina yaɗauki ɓari kamar mazari kallon mutumin nake cikin matukar firgita da masifaffen tsoro.
Naseem na kuma rungume wa da karfi a kirjina,
cikin matsanancin tsoro hawaye yafara sauka a idona,
a hankali na masa ɗaya ɓarin hannun na rawa naɗaura jikin murfin motar na buɗe a hankali,
nazuro kafafuna waje namike,
na mai da marfin a hankali har lokacin yana tsaye yabaiwa motar baya yana ta kan wayar,
cikin sanÉ—a narika tafiya ahankali-ahankali narika tafiya na gangara gefen titi nashiga cikin dajin
dake gefen titin a hankali cikin sanÉ—ar narika shiga cikin dajin.
ina shiga cikin dajin narika gudu ina kankame da Naseem gudu nake babu ko kakkautawa da
iya kafina ban kuma sanin inda nake jifa kafata cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa,

gudun nake da iya karfina na sai da na isa gindin wata ƙatuwar bishiya kafin natsaya a gun na
rakuɓe jikin bishiyar,
ina mai da numfashi,
muryar mutumin najiyo daga can yana faÉ—in
"Ke ina kike ina kika shiga?".
cikin wani irin kaɗuwa da firgici nadaɗa rungume Naseem na rakuɓe sosai ajikin bishiyar, jikina
na cirawa...

Ina jin Muryar sa yana ta matsowa in da nake daga in da nake ɓoye ina kallonsa ya gangaro har
yazo kusa da ni yana ta waige-waige yana cigaba da faÉ—in,
ke Ina kike. numfashi nane yasoma yin sama-sama tamkar zai fice a jiki, ganin sa daf da Ni.
dubana nakai kan Naseem da ya buÉ—e ido yana kokarin yin kuka kai nashiga girgiza masa tare
da É—aura hannuna kan bakin sa narufe da karfi.
mutumin
ya É—au lokaci agun yana dube-dube kana yayi tsaki tare da faÉ—in
"Kash ga samu ga rashi taya ma akayi har tafita ban ganta ba".
yakuma jan dogon tsaki yajuya yakoma gon motar sa.
ina ganin haka nakuma sa gudu narika kusawa cikin dajin, gudu ne irin na ceton rai ko ina ce
rayuka,
bana ko ganin gabana.
ga lokacin tuni guri yasoma yin duhu sai dai hasken farin wata daya haske ko ina...

Tuntuɓe nayi da wata katuwar kututture da bansan tana gaba na ba,nayi luuu zan faɗi sai nayi
baya tangal-tangal kaÉ—an yarage na faÉ—i da baya,
Naseem ya suɓuce a hannuna yafaɗi kasa timm,bayan da nayi kuwa hakan yayi sana diyyar
kan Nasmah ya garu da jikin wata bishiyar dake baya na,
a tare suka saki kuka Naseem kam tun da yasaki wani irin kara mai karfi tun da yasaki karan
nan bai kuma yin motsi ba.
cikin tsananin firgici da tashin hankali nayi kasa naÉ—a go
Naseem da ko matsi bayayi na rungume shi a jikina da karfi nashiga girgiza shi da kiran sunan
sa,
"Naseem Naseem Naseem katashi dan Allah katashi katashi Naseem".
narika faÉ—a ina girgiza shi da kiran sunan shi amma ko motsi baiyi ba,
cikin rasa abin yi na zube kasa ina cigaba da girgiza shi,
babu ko alamar nunfashi tare da shi, hankali na yakuma mummunar tashi ga Nasmah sai
zandara ihu take.
wani kuka nasake da karfi ina girgiza shi da karfi,
É—ankwalin kai na na ciro nashiga fifita shi ina kiran sunan shi,
nan ma shiru rungume sa nayi da karfi ina faÉ—in
"Naseem ka tashi dan Allah kada ka mutu, ka kabuÉ—e idon ka dan Allah Naseem kada ka mutu
Naseem Naseemmmmmmm".
NafaÉ—a da karfi cikin muryar kuka...

Duk yan da nayi ta jijjiga shi da kiran sunan sa da kuma yi masa fifita yana nan a inda yake
babu numfashi a jikin sa,nayi ta kuka kamar raina zai fita ina kankame dashi,kamar an zabure
Ni na É—agosa da sauri na shin fiÉ—a shi a kasa na mike da sauri nashiga duba gefe da gefe na ko
zan ga ruwa na yayya fa masa ko Allah zai sa ya tashi, bazan mance ba ɗan goggo Hauwa yataɓa yin irin yan da Naseem yayi sai dai shi ba faɗuwa
yayi ba rashin lafiya yake sai numfashin sa yaÉ—auke lokacin sun zo gidan Inna sai naga Inna ta
É—ibo ruwa tayi ta yayyafa masa sai ya farfaÉ—o numfashin sa ya dawo.
da gudu nayi gaba narika É—an zaga gurin babu alamar ruwa agurin,
da gudu na dawo in da yake na É—ago shi
nashiga hura masa iskar bakina a fuskar sa, narika hurawa ina kiran sunan shi.
mun kai minti 30 agurin ina abu É—aya babu kuma sauyi,
da sauri nasaka bakina kan bakin sa narika hura masa iska da karfi,
wani nannauyar numfashi ya sauke tare da sakin kuka mai karfi ya kankame Ni,
nima kukan na kuma fashewa da shi na rungume shi ina faÉ—in
"Alhamdulillh Allah na gode maka".
da sauri na kunce Nasmah da take ta kuka tun É—azu na haÉ—e su duk na rungume.
nayita rarrashin su sai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login