Showing 21001 words to 24000 words out of 49670 words
Chapter 8 - HAMDAH Book 2 Complete Free By Rasheedat Director .pdf
Malam Musa yace
"Ayya to Allah yataimaka yaune kwanan su uku ko? yakamata a musu huɗuba gashi kuma har
yanzu bai samu isowa ba".
da sauri Mama tace
"Haka ne kuma inaga zuwan sa kam ma zai kai har bayan suna ai ko baza'a jira har sai yazo ba
za'a yi musu huɗu ba,
Malam ayi musu huɗu ba kawai, yoo yaushe za'a zauna zaman jiran sa".
Malam musa yace
"To babu damuwa, shin yafaɗi sunan daza a sa ma yaranne?".
mama
tace "Eh". takalleni tare da faɗin
"Yayama sunan daya faɗa miki?".
shiru nayi kaina a kasa,
sai da mama ta kuma mai-maita
tan bayar kana nace
"Idris da Aysha"
tabbas babu sunan da ya dace da yaran face sunan Abbu da Inna, sun nuna min so da kauna
da kuma gata. bakuma zan taɓa mancewa da su a rayuwa taba.
Malam Musa yace "Masha Allah yara zasuci manyan suna".
gyara rukon baby boy din dake hannusa yayi kana yazura hannunsa cikin aljuhu yaciro dabino,
Nan yayi Masa huɗuba da suna Idris kamar yadda addini yakoyar,
kana ya mikawa Mama shi yace
"Allah yaraya Idris bisa Sunnah".
Mama tace "Amin".
ta kwantar da shi ta dauko baby girl din ta Mika masa Nan ita ma yayi mata huɗuba,
kana yamikawa Mama tare da fadin
"Allah yaraya Aysha".
Mama takuma amsawa da Amin Amin,tare da masa godiya.
Nan yayi Mana sallama yatafi.....
Mama ta dubeni da murmushi dason gusar min da damuwar da take hangoshi kan fuska ta, ta
kalli yaran tana faɗin
"Masha Allah kinwa Inna takwara ne ko wa kanki?".
ta faɗa tana murmushi,
ido na tsurawa babyn kana nace
"Wa Inna nayiwa takwara kamar yadda nima naci sunan ta".
dariya Mama tayi tare da lakata hancin babyn tana faɗin
"Kaga Aysha ɗiyar Aysha kakar Aysha uban giji yaraya ku da imani,
to me za'a rika kiran su yanzu kuma?".
tafaɗa tana duba na fuska ɗauke da murmushi.
shiru naɗan yi alamar nazari zuwa can nace
" *NASEEM DA NASMAH*"
baki Mama ta washe tana faɗin
"Iye Ah gaskiya sunan yayi kama dasu".
yanzu kam sai da mama tasani murmushi idanuna a kan yaran ina duba kamar da tace sunan
yayi da su....★
Yau Zainabu da kanta takawo mana abincin dare da kuɗi naira dubu 5.
nan take cewa Mama malam Musa ne yabata rance,
ranar da tazo niman kuɗine tayi wa malam ɗin magana ko yana dashi,
yace
Wlh baya dashi sai yau ya samu shine yabata takawo.
Mama tayi ta mata godiya tace dan Allah tayi masa godiya kuma in sha Allahu zata biya da
hannunta da yar dar Allah.
Nan da nan kuwa takai ragowar kuɗin da ake binsu a asibitin.
Washegari da safe aka sallame mu....
ranar da muka dawo gida a ranar mama tafara awara,na tausaya mata kwarai,
ranar sai da nayi kuka dan nasan dan ni ta fara sana'ar a yau wan da yakama ta ace hutawa
take da ɗawai niyar asibitin da ko baccin kirki batayi, sai gashi muna shiga gida tasoma wani ai
kin...
ana gobe suna da yamma bayan Mama tayi wa yaran wanka muna zaune ina cin abinci,
Mama na goye da Nasmah yayin da Naseem ke rike a hannunta tanata jijjiga shi, Mama ta
dube ni tace
"Wannan mai gidan fa in baiji motsi a bakin sa ba baya gane wa".
fuska na kwaɓe nace
"Mama yanzu fa suka sha".
"To yaro shi ina ruwan sa ciki kawai yasa ni gama dai kiba shi yasha,
ga kawata ma na kan motsi".
Kamar na kurma ihu haka naji,
yanzu suka sha babu jimawa gashi yanzu wai suna nima,
cikin tura baki nace
"Allah kaɗan zan basu anjima kuma abasu kunu".
Mama tace
"Kunu kuma?".
nace "Eh". dariya tayi tace
"To shike nan yanzu dai ki basu susha".......
Washegari yakama ranar suna,
da sassafe Mama tayi min wanka kana tayiwa Nasmah da Naseem,
nashirya cikin doguwar riga ɗaya daga cikin kayana da nazo dashi tun wancan lokacin yaɗan
kasa min sabo da ciki sai na ajeshi bana sa shi, shi yana nan har yanzu da ɗan sabon tar sa.
ɗan ribar awara da tasamu na kwana biyu
da shi tayi cefane ta siyi shin kafa ta haɗa da sauran waken kosai suka girka abinci da Zainabu
da tun da safe tazo.
da rana makota suka shishshigo,
Mama mai yin biki ne tana da kokarin shiga wa mutane biki, duk wan da take yin biki da su
kowa sai da ya kawo mata rigar baby wasu na maza wasu na mata da omo da sabulu har da
man shafa wa.
Naseem yasamu kaya kala huɗu yayin da Nasmah ma tasamu kala huɗu.
da yamma kowa ya watse....
Bayan suna Mama tafara niman kuɗi ba kama hannun yaro domin biyan bashin da ake binta,
ba iya sana'ar awara da kosai kaɗai ta tsaya ba har da kayan miya tana sara tana siyar wa,
da duk wani abu na nasa'ar cikin gida da tasan zata sami riba a kansa tana siya ta siyar.
cikin yar dar Allah da ikon sa yadafa mata duk abun da zata taɓa na sana'a sai ta sami riba a
kansa...
ranar da muka yi arba'in ranar ta kai wa Zainabu da malam Musa kuɗin su,kamar yan da tayi
musu alkawarin bayan suna zata biya su takuma jajirce wajen nima har ta samu,
tayi ta musu godiya.....
Tun daga ranar hankalin ta ya kwanta ta kuma mai da hankalin ta wajen kula da Ni da kuma
ƴaƴana,
duk wani ribar da zata samu a kanmu yake kare wa.
yanzu nawar ke garau idan ka ganni bazaka ce CS aka min ba, nakan ji mutane da dama suna
cewa jikina mai kyau ne bana da kan jiki.....
Haka mukayi ta lallaɓa rayuwa nakuma daure da juriyar shayar da yaran,sai dai na rame kwarai
suko kamar hurasu ake, sunata girma da kuma kara wayo sosai,
lokacin da suka cika wata uku,
Mama ta haɗa musu garin kunu na alkama waken suya da gyaɗa,
nan ne naɗan sami sauki,
da shi muka cigaba da rainon su...
Ranar wata asabar..........!★
Mommyn twins ce
Ranar wata asabar hakan yayi dai-dai da watan su Naseem huɗu da sati biyu,
Zaune muke a tsakar gida, ina rike da Naseem a sakiyar kafafuna dan alokacin suke koyon
zama.
Mama na goye da Nasmah tana bacci, ita kuma tana ta ɗan aikace-aikacen ta.
Sallama mukaji daga bakin kofa da karfi, ba Mama kaɗai ba hatta ni sai da naji wani irin
muguwar faɗuwar gaba dajin muryar mai sallamar,
yau kusan sati ɗaya kenan Alhaji Mamman sai yayi sallama a gidan kullum sai yazo maganar
kuɗin hayar sa, wan da yanzu ya ninku yazama na shekara biyu da rabi.
takuma sana diyyar mune hakan ya faru kula da Ni da ƴaƴana shi ya hana ta ajewa Alhaji
Mamman kuɗin hayar sa,
yunkurin mikewa nashiga yi jin yacigaba da kwaɗa sallamar ba ko kakkautawa,
kafin na mike ma ya sako kansa cikin gidan yashigo,
yana faɗin
"Fasuma kinsan dai ba gidan mijin ki bane ba,kuma bamu haɗa kuɗi da ni da shi mun siya ba,
sannan kuma koda ace ma mun haɗa kuɗi da ni da shi mun siya,
kinsan dai yanzu yariga da ya mutu kuma dole a cire min nawa a ciki,
bare kuma gida gida nane ba nashi ba ko bulo ɗaya bai ɗaura a kan gidan nan ba,
bare ki zauna kice kina cin gadon sa,
dan haka kifita min a gida yau babu afuwa babu rangwami,
kifita min a gida yau zan saka ƴan haya acikin gida na,
gasu nan ma munzo tare da su,
ina bukatan kuɗi dan sabo da kuɗi na tara kafin na gina gidan,
ga ƴan haya nan mun iso da su ga kayan su can a moto dan haka ki fita kibasu ɗaki."
yakaraso ciki yana muzurai tare da cigaba da faɗin
"Ganan masu shiga gida sun iso ke kaɗai suke jira kifita kibasu ɗaki,
dan yanzu ɗakunan gida nasune su sun iya biyan kuɗin haka,
sannan kuma
bawai na bar miki kuɗin haya da na ke binki na shekara biyu da rabi bane ba,
ina binki bashin su kuma zaki nimo kibiya ni kaya na babu rangwami acikin watannan zaki biya
ni in baki bada ta daɗi ba zaki biya a hannun hukuma."
Cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa na ɗago Naseem dake hannuna na goya shi,
na mike tsaye yayin da Mama tarika haɗe hannayen ta biyu cikin matukar tashin hankali tace
"Dan Allah Yaya kayi hakuri insha'allahu ina nan ina kan tara maka kuɗin nan kayi hakuri dan
Allah kasan dai yanzu abubuwan sai a hankali,dan Allah
kayi hakuri in sha'Allah zan haɗa maka kuɗin acikin ƴan kwana kin nan,
kakara yimin afuwa".
cikin ɗaga murya Alhaji Mamman yace
"Dakata dan Allah Ni kin ishe ni kullum ke kenan maganar ki ayi miki afuwa ayi miki rangwami,
wai shin kan kuɗin nan in da rangwami da afuwa ake tarashi zai taru ne,
in dai da akwai rangwami acikin tara dukiya da zai taru ne?
nifa kuɗi kawai nake bukata,
shi kuma nake son tarawa,
kin san ta yan da akayi na tara kuɗi na siyi gidan?,
nifa kuɗi kawai nake bukata,
in da ace kin fita tuntini a gidan nan da na tabbata na tara kuɗin da yafi abin da ake tunani dan
haka ni kifita min agida kawai babu wani rangwami."
fuskarsa yajuya ta bakin kofa ya ɗaga murya yana faɗin
"Kushigo da kayan Bismillah ga gidan kushigo da su".
kofar da yake kallon na zubawa ido in da naga shima ya fuskanta yana maganar,
wasu mata da ƴan matasa ne suka fara shigo wa da kaya,
suka ta shigowa da shi suna ajiye wa...
Hannu mama ta kuma haɗawa tana cigaba da rokon sa da haɗa sa da Allah da yi masa
magiyar in sha Allahu zata biya sa kuɗin a cikin watannan,
yace
"Dai na haɗa ni da Allah ki cuce ni,
na dai faɗa miki babu bulo ɗaya da mijin ki ya ɗaura kan ginin gidan nan,
nariga da na gama magana yanzu bani da hannu acikin wannan gidan na nariga da na bada
hayan shi,na karɓi kuɗin sa dan haka fita ki basu gida yanzu nasu ne".
yajuya yaso ma tafiya yana cigaba da faɗin
"Kuɗi na da nake bin ki bawai na bar miki bane kuɗina yana nan a kanki kuma zaki biya ni,
na baki sati biyu ki biyani kuɗi na idan ba haka ba sai nayi miki rashin Mutun cin da baki tunani,
kin san ni a kan kuɗi ko uban waye ma zan iya masa rashin mutunci ko shi mijin naki da muke
uba ɗaya bai isa yaci kuɗi na ba tun da bashi ya nemo min ba."
yayi waje yana cigaba da zazzage bala'i.
Bayan sa Mama tabi tana cigaba da haɗa shi da Allah har kofar gida ta bishi,shi ko yaja garen
sa yahaye babur ɗin sa yayi gaba.
suko mutanen da yazo da su sai shigo wa da kaya suke suna jibgeshi a tsakar gida,
tuni hawaye yafara sauka a ido na, muna tsaye cirko-cirko har suka gama shigo da kayan.
matan suka dubi Mama sukace
"To mun gama shigo da kaya yazu shirya shi cikin ɗaki ga gurin yafara rufa wa kar ruwa ya
sauko ya jika mana kaya."
da sauri Mama ta dubi matar batare da tace komai ba,
Hannuna Mama tarike tana faɗin
"Zo mu fitar da kayan".
cikin zubda kwalla nace
"Mama idan muka fitar da kayan ina zamu kai?".
tace
"Allah bazai hanamu in da zamu kai ba."
Haka mukayi ta fito da kayan mu nuna kai shi can waje kofar gida,
tas muka fito da kayan muka jibgeshi waje duk da dama bawani kayan kirki bane.
muna tsaye a kofar gidan Zainabu ta iso mu hankali tashe tana faɗin
"Mama mai awara yanzun nan yaro yazo yace min yaga kuna ta fitar da kaya,
wasu kuma suna shigar wa ciki, Mama da ma tashi zakiyi shine baki faɗa mana ba?."
Murmushin yake mama tayi kana tace
"A'a mai gidan ne yazuba ƴan haya aciki shiyasa muke tashi muma tashin yanzu ne yasa memu
bawai tuntini da ma da shi bane".
Ido Zainabu ta waro tare da buga kirji tace
"Ya zuba ƴan haya a cikin gidan bayan da wasu masu hayan aciki,
ban taɓa ganin haka ba,
ba'a taɓa ɗaga ɗan haya rana a saka batare da an bashi lokaci ba sai an bashi kwanaki ya
kama gidan da zai zauna kafin a ɗaga shi,
ba irin wannan ɗagawar babu sanar wa ba,
to yanzu ina zakuje Mama kuna da wani gidan da kuka kama ne?".
Mama tace
"Ko ɗaya yanzu dai zamu ni mi wani gidan hayan da zamu zauna".
"Gaskiya kam amma wallahi bai kyauta ba ai ba haka ake yi ba ba'a taɓa ɗaga mai zaman haya
haka lokaci guda ba,
sai dai a baka lokaci ka kama wani gidan hayan sai ka tashi ba irin haka lokaci guda ba".
Mama kam murmushin karfin hali yacigaba da yi,
Niko hawaye ne kaɗai ke zuba a ido na naka iya furta komai.
Zanabu tace
"Mama ku tattaro kayan kizo muje ga guri yafara rufawa hadari yana kan taso wa".
ta sun kuya tana tattaro kayan tare da cigaba da faɗin
"Kuyi sauri kada ruwa yasau, ko kuzo muje kutara su a zauren gidan mu kafin ku sami wani
gidan".
Mama tace
"To Zainabu".
nan muka shiga kwashe kayan muna kaiwa gidan Zainabu a zauren gidan ta muka tara kayan
gaba ɗaya sannan muka shige ɗakin ta dan lokacin tuni ruwa ya sauko...
Tun da aka fara ruwan nan bai tsaya ba har yamma,
har Malam Musa yadawo yazo yasa memu a gidan,
koda yaji labarin bai ji daɗi ba kwarai yace Alhaji Mamman bai kyau ta ba bahaka ake yi ba,sai
dai yasan waye Alhaji Mamman karamin ai kin sa ne yin hakan.
Yacewa Mama bari a ɗauke ruwa zai fita yake yataya ta niman gida ko Allah zai sa a samu a
yammacin,.
Mama tace ita ma ɗin ruwan take jira yaɗau ke tafita niman gida.
Gidan malam Musa ɗaki ɗaya ne tak a gidan shine kuma wan da suke zaune da matar sa a ciki.
dan haka zaure yako ma yaje ya zauna yabar mu acikin ɗakin,
gaba ki ɗaya Mama a takuri take ganin mai gidan yako ma zaure ya bar mana ɗakin.
wasa-wasa ruwan nan bai ɗauke ba sai daf magriba,
dan haka Malam Musa yace
Abar niman gidan sai gobe tun da yanzu dare yariga da yayi,
a zaure yakwana yabar mana ɗakin...
Washegari da sassafe Mama tafita neman gidan da zamu koma bata dawo ba sai wajen azahar,
tadawo gaba ɗaya a galabaice,
a ɓangaren Malam Musa shima bai jima da dawowa daga niman gidan ba,
Muna zaune a ɗaki
Zainabu ke tambayar Mama Allah yasa anyi sa a an sami gidan.
numfashi mama ta sauke cike da ɗinbin damuwa tace
"Wallahi nagama iya yawo na ban sami gida dai-dai da kuɗin hannuna ba duk gidan da naje
niman hayar sa gaba ɗaya sun fi karfin kuɗin hannuna,
azaman yanzu kuma gaskiya masu rangwami sunyi karan ci".
kai Zainabu ta girgiza cike da tausayawa kana tace
"Gaskiya kam yanzu rayuwa tayi tsada Allah yayi mana magani".
Amin muka amsa dashi,
gaba ki ɗaya jikina yagama yin sanyi.
Mama ta mike ta nufi zaure in da kayan mu yake can,ganin ta ɓata lokaci bata dawo ba sai na
mike na bi bayan ta,
ganin ta nayi tana shirya kaya cikin ɗan kari min jaka gaba ki ɗaya hankalin ta a tashe,
ta dube ni tare da faɗin
"Zanje garin mu HAMDAH kamar dai yan da na taɓa baki labari ni ƴar Yola ne aure ne ya kawo
ni nan,
yanzu rabona da Yola shekara 7 kenan zanje ni na dawo in sha Allahu kwana biyu zanyi na
dawo,
zan tafi mana da wasu kayayyakin mu zanje na duba kalar yanayin zaman can idan naje nasa
mu matsuguni,duk da dai dama muna da gidan gado kamar yadda na taɓa baki labari yanzu dai
zanje na duba acikin gidan gadon mu idan akwai ɗakin da zamu zauna,
zan dawo nazo na ɗau keki mukoma,
kwana biyu kacal zanyi na dawo sai na ɗauke ki mu koma tare".
ta ciro kuɗi naira dubu biyu da ɗari biyar ta mika min
tace
"Ga wannan ki rike a gurin ki ko zaki bukaci wani abun,
kin ga suma nan basu da karfin da zasu iya ɗawai niyar ku duka duk da bawai jimawa zanyi ba
kwana biyu ne ka cal,
Amma ki rike zai iya yi muku amfani,ko zaki ga abun da kike so ko su Naseem da Nasmah sai ki
siya musu".
numfashi na sauke
jiki a sanyaye dan Mama ta taɓa bani labarin family'n su
Su biyu ne agun mahaifin su ita da wanta na miji,
lokacin auren ta yayan ta baiso auren da wan da take so ba dan lokacin mahaifinsu ya rasu a
haka dai akayi auren sam baya so,
shi yasa ko taje gidan ma bata jin daɗi shi yasa takan daɗe bataje gidan ba dan ko taje ma baya
sauraran ta,
ko da mijin ta yarasu taje amma yaki yabata fuska tazau na agidan,
sai dai ta alakan ta hakan dan gidan nasa ne yanzu sabo da shi yaci gadon gidan,
abun tun yaranta har yanzu tana ta kan fama,
har yakai ga yanzu shi yayan nata yarasu sai dai matar sa ta ari abun ta yafawa kanta,
ta kanainaye gidan tace gida natane da ƴaƴan ta dan haka babu wan da ya isa ya zauna mata a
gida.
dan a lokacin da mahaifin su Mama ya rasu yayan ta shi aka basa gadon gidan in da ita aka
bata
gadon gonar mahaifin su...