Showing 12001 words to 15000 words out of 49670 words

Chapter 5 - HAMDAH Book 2 Complete Free By Rasheedat Director .pdf

ake yi wani sa'in ma mudu ɗaya da rabi,kosai kuwa yanzu mudu ɗaya
ne,kuma fa duk wannan siyan kayan abin cin da aka faɗa a asibitin ne yake cinye kuɗin,Ni dai
Allah Mama ki bar siya haka ai naci da yawa ma fiye da yan da suka faɗa tun da sunce kwai
ɗaya ma naci ya wadatar,kifi kuwa ko na ɗari ne ba sai lallai an siyi hantan ba".
tace
"Tafi can me kika sani so kike kizo haihuwa kirasa jini sai an yi faman niman jini ko,ai waɗan
nan abubuwan da kike cin sune zasu tai maka wajen kara miki jini, ko kin zubda jini gun
haihuwa ma baza a sami wata matsala ba dan akwai jinin a jikin ki sosai".
kai na jinjina.
waje tayi tana cigaba da faɗin

"Yo menene amfanin niman kuɗin da baza'a magance damuwa ba lafiya ai yafi kuɗi".
juyawa nayi na koma ciki ina saka yadda zanyi na hanata kashe kuɗin nan da yawa dan yanzu
jarin da muka dogara dashi ɗin ma yafara yin kasa idan ya karye gaba ɗaya wace madafar
zamu dafa...


Acan kasar India lokacin da Ya Masa'ud yasa mi labarin abun da ya faru,bakara min girgiza da
tashin hankali ya shiga ba,cikin matukar tashin hankali yabaro kasar yatoho Nigeria,yayi kuka
da hawayen sa da yazo ya iske Abba yakori HAMDAH ba'a masan in da take ba kuma yahana
a nimo ta. lokacin yayi yunkurin nimota Abba yace kada ya soma,bai dai bi na Abba'n ba, ya baza cigiya
cikin garin Bauchi sai dai ba'a sami wani alamar da ya nuna tana cikin garin ba.
su Aunty Rafee'at
sunyi yunkurin kiran su Abbu da suke can kasa mai tsarki su sanar musu,
Ummi tace kada su sanar musu su barsu suyi iba dan su cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da
lumana.
kullum Ummi na kan sallaya tana yiwa ɗiyar tata addu'a da fatan samin kariyar Allah agare ta
aduk in da take a faɗin duniyar nan....

....★



After 1 month



Yau da wuri na dawo daga awu dan da sassafe Mama ta tashe ni na shirya ta rakani har cikin
asibitin kafin ta dawo, lokacin da muka isa asibitin mutum uku na samu a gabana.
na shigo gida na tadda Mama tana ta suyan awara masu siya sun zagaye ta,
ɗaki na wuce na tuɓe hijabi na na aje laidar agwaluma da na siya da ɗarin da Mama ta bani
tace ko zan ga wani abun da nake so na siya,
kana nafito.
in da take na isa nayi mata sannu da ai ki tace
"Har kin dawo da wuri haka an yi miki awun kuwa?".
nace "Eh ai yau mutum uku ne a gaba na".
tace "Ai yafi kaje da wuri ka dawo da wuri wani watan ma da wuri zamu tafi".
kofin kunun tsamiya mai ɗumi ta miko min da alama bata jima da dama shiba,
ta tsamo kosai cikin mai tazuba cikin kwano shima ta miko min na amsa, zan zauna kan kujera
tace
"A'a ɗauko taburma ki shin fiɗa kimike kafafun ki".
nace to.

Ko da tagama suya kan taburman da na shimfiɗa tazo ta zauna cinikin da tayi ta zube su kasa
muka soma kirgawa,muka cire kuɗin komai da akayi amfani da shi, cikin murnar ganin yau an
sami riba har dubu ɗaya da ɗari biyar baki na washe nace
"Kai gaskiya yau kam an sami riba har dubu da ɗari biyar".
murmushi tayi tace
"Ai kam yau alhamdulillah bari na fita nayiyo mana cefani".
da sauri nace
"Yauwa Mama yau ni dai bana jin sha'awar hantar nan gara kifi ma kiyi mana irin miyar waken
suyar da ranar kika yi manan nan sai asa kifin kawai a ciki".
Nafaɗi hakan ne dan nasan tana fita ribar da aka samun zai kare wajen yin cefanen girkin da
take yi min wai na karin jini har sai ta taɓa uwar kuɗin ma.
tace
"To shike nan sai ayi shi tun da kina so".
sallamar da akayi ne yasa mu ɗagowa dukan mu,
Wani saurayi ne mai suna Sagir dake layin unguwar, kusan kullum sai ya shigo siyan awara,
da ai kowa yake a siya masa amma yanzu da kansa yake shiga cikin gidan ya siya,
idan ya shigo yarika bina da kallo kenan idan na gana haka sai na shige ɗaki.
karaso wa in da muke yayi yana faɗin
"Mama ban shigo da wuri ba Allah dai yasa an ajiye min".
murmushi Mama tayi tace
"Ai kuwa yau Sagiru gaba ɗaya na mance da ma HAMDAH ce ke tuna min waɗan da ake ajiye
musu ai kuwa yau ban ajiye wa kowa ba na man ce gaba ɗaya dan ita mai tunin bata nan bata
jima da shigo wa ba,
Sai dai kuyi hakuri sai na dare kenan".
tsayuwar sa ya gyara tare da dubana yace
"Shine yau baki tunawa Mama ba ai da kafin ki fita kin tuna mata da ta ajiye min kinga dai yanzu
laifin kine".
"Laifi na kuma?".
yace "Eh ai kece baki tuna mata ba".
Mama tace
"To an jima kam zata yi min tuni sai na ajiye maka".
yace
"Yauwa to Allah yakai mu".
Sai kuma ya ɗan sosai bayar keyan sa ya dube ni kana ya mai da duban sa kan Mama yace
"Mama zaki bani wan nan ɗiyar taki mai rashin tunin nan".
da sauri na ɗago jin abun da yafaɗa, Mama ko cewa tayi
"Wa wai HAMDAH kake faɗa?".
tafaɗa tana duban mu duka da shi.
yace
"Eh ita" Mama tayi murmushi tare da faɗin
"To ai matar aure ce kai baka ganta da ciki ba haihuwa tazo dan mijin ta soja ne kaga bazai
yiwu ta haihu a can ba shiyasa tazo gida".
Ido ya waro tare da buɗe baki da mamaki yakai hannu yarufe bakin yana faɗin

"Matar soja Innalillahi wlh ban taɓa luraba sai yau duk shigo war da nake,wai Allah ya rufa min
asiri da kafata ta ɓalle sabo da sallen kwaɗo inayi ana zuba min bulala,a gafar ceni wlh rashin
sani ne ki tai make Ni kada ki faɗawa yallaɓoi,
wlh Ni sai yau naga cikin ni duk gani na da ita ban taɓa lura da cikin ba".
yakarashe maganar yana dubana da haɗe hannayen sa guri guda alamun roko.
Murmushi nayi dan kullum idan ya shigo da hijabi a jikina kuma azaune yake sami na,nasan shi
yasa bazai ga cikin ba.
yace
"Um bari na tafi wata kila ma tsautsayin wahala ne yashi go da ni,amma da zanyi ido biyu da
jarumin sojan nan da na jinjina masa dan ya iya zaɓe kwarai,ko da zai sani sallen kwaɗo sau
goma sabo da na tayashi murna".
Mama tace
"Ah to gara dai ka tafi".
"Ai natafi ma". yayi waje yana dariya....★


A can cikin garin birnin Bauchi'n Yakubu kuwa,
A halin ABDULLAHI TURAKI na hango motocin su suna fitowa daga cikin airport,motocine guda
uku suke tafiya a jere, cikin mota na biyu wan da yakasan ce shine na tsakiya a ciki na hango
su Abbu da Mamie, fuskokin su ɗauke da farin cikin ganin su a kasar su kuma garin su........!★



Mommyn twins ce



Cike parlour'n yake tam da ƴan uwa da abokan arziki,
kowa sai juya tsara bar da aka basa yake cike da jin daɗi.
Mamie bin cikin parlour'n da mutanen cikin tayi da kallo a karo na ba adadi,
yau kwana biyu ke nan da dawowar su amma bataga HAMDAH acikin masu zuwa yi musu
sannu da dawowa ba,ko a airport kuwa da a kaje tarar su ba ta cikin waɗan da suka je tarar
tasu,bata kawo komai a ranta ba dan tasan iyanzu kam cikin yakara girma ko shi zai hanata,sin
tiri kan hanya. Bayan sallar Isha Ya SALEEM yashigo cikin bedroom ɗin Mamie tana zaune tana warewa ƴan
uwan ta na kan gari waɗan da bata basu tsaraba,
a hankali yakara so cikin ɗakin yazau na kan kujerar da ke cikin ɗakin tare da gai da Mamie,
ta amsa tana faɗin
"Har yanzu baka tafi gida ba".
cikin yana yin nan nasa kamar an sashi dole yin maganar ko kuma mai jin bacci yace
"Eh yanzu zan tafi na shigo nayi miki sallama ne".
tace "Gara kam ka tafi yanzu haka HAMDAH na can tsoro duk ya ishe ta ga Halima ma naga
bata koma ba tace min anan zata kwana".

wani irin bugawa kirjin sa yayi da karfi jin an ambaci sunan ta.
shi har ga Allah ma ya mancewa da wata mai suna HAMDAH in ba yanzu da Mamie ta faɗa ba,
tun ranar da suka rabu ya goge sunan ta cikin zuciyar sa baya kaunar yaji wani ya ambaci
sunan ta,
sai kuwa akayi sa'a a cikin gidan sa uwar gidan tasa wato Na'ima tayi ruwa tayi saki wajen
ganin babu wan da yakuma tuno ta bare har arika ambaton sunan ta,dan hakan shine kaɗai zai
tai maka wajen ganin ya daɗa mancewa da ita na har abada,
kamar yan da bokan ta yasar mata tatafi bazata kuma waigowa ba
sai dai ma takuma yin nisa da su.
yanzu kuma ba wani zuwa family House ɗin su yake sosai ba,kuma ko da yaje ɗin ma gaisu wa
ce kaɗai suke yi yatafi.
da karfi-karfi haka zuciyar sa ke bugawa,har sai da yakai hannu ya dafe dai-dai saitin kirjin sa.

Mamie ta janyo wani ɗan madaidaiciya akwati tabuɗe, dogayen riguna ne da gyale da sauran
su zafafa sai gefen cikin akwatin kayan baby ne wanda mace da na miji zasu iya sawa.
murmushi tayi tare da faɗin
"Ga tsara bar ta dana mai gidan dan Ni wa mai gida na tsiya bawa kishiya ba,Abbu ne yayi
wahalar siyowa kishiya".
tayi maganar fuska ɗauke da murmushi cike da so da kaunar jikan ta da take saran fitowar sa
duniya ko mace ko na miji.
ta cigaba da faɗin
"Da zan baka kakai mata amma dai bari na bari idan tazo sai ta haɗa dana gun Abbu'n ku ta tafi
da
shi tun da shi har yanzu bai buɗe jakar saba".

Har lokacin hannunsa na dafe kan kirjin sa a hankali ya mike,batare da yace komai ba yafita,
bayan sa Mamie tabi da kallo bata kawo komai a ranta ba dan tasan halin ɗan nata sarai
miskilanci a jinin sa yake.
yana dai-dai ta zaman sa cikin mota yaja gajeren tsaki jin har lokacin zuciyar sa bata fasa
bugawa ba,a haka ya koma gida..
Washegari Mamie tayi ta zuba ido ganin zuwan HAMDAH amma shiru har yamma.
A ɓangaren Abbu ma ranar sai da ya tanbayi Mamie wai shin HAMDAH tazo ta karɓi tsara bar
tane bata karɓi na amaryar sa ba.
Nan Mamie ke ce masa ai ko sannu da dawowa bata zo musu ba amma dai tasan jikin ne
yasoma nauyi...

Bayan sallar magriba,
da sauri Masa'ud yabi bayan Abbu suka shiga gida tare, a parlour suka zauna in da suka tadda
Mamie nan zaune,zama Masa'ud ya gyara dan yau yasha alwashin faɗa wa su Abbu abinda ke
faruwa duk da Ummi tace kada wani ya sanar musu sai sun daɗa hutawa sosai.
a cewar sa wani hutu yarage musu bayan ƴar uwar su ba a san halin da take ciki ba.
"Abbu Mamie".
Masa'ud ya kira sunan su yana duban su,a kusan tare suka amsa yayin da suka mai da

hankalin su kan shi.
Zaman sa ya daɗa gyarawa kana ya nisa yasoma magana,
"Abbu kunsan abun da ke faruwa kuwa?".
A tare suka haɗa baki wajen cewa
"Meke faruwa?".
"Assalamualaikum"
gaba ɗayan su suka juyo jin muryar Aunty Rafee'at tana sallama,suka amsa mata,ta karaso ciki
ta sami guri ta zauna tare da gaishe su in da Masa'ud ya gai data.
Mamie tace
"Unguwar dare bakya bari gari ya waye ba".
Hmm. kawai tace dan batajin abun da ke tafi da ita zata iya barin sa sai gobe, kwanaki arba'in
da suka shuɗe tayi sune cikin kunci da tashin hankali,
Dr Farooq ma yayi-yayi da ita kan tabari gari yawaye tace a'a yau kam bazata bari maganar
yakuma kwana ba,a son ta ma tun ranar da suka dawo Nigeria taso faɗa musu Ummi ce ta
hana ta,tun da har yau sun yi kwana uku da dawowa bataga amfanin rashin faɗa musun ba
gara su ma susanin. Masa'ud na ganin yanayin ta yasan abun da yazo faɗawa su Abbu shi ya kawo ta,
yace
"Aunty Rafee'at yanzu da ma zan faɗa wa su Abbu kenan".
da mamaki iyayen nasu ke kallon su Mamie da tun ɗazu da Masa'ud yace sunsan abun da ke
faruwa taji gaban kirjin ta ya yanke.
tace
"Wai me ke faruwa ne kam?".
tayi tambayar cikin yanayin fara shiga damuwa da fargaba.
A sannu Aunty Rafee'at tashiga basu labarin abun da ya faru tun daga farko har da korar da
Abba yayi wa HAMDAH.

Kamar a mafarki haka suke jin zancen nata,
Mamie kam salati tashiga rafkawa tana tafa hannu yayin da hawaye yafara sauka a idon ta,
Cikin sananin tashin hankali da kunar rai Abbu yaɗaga wayar sa yakira Abba batare da ya amsa
sallamar da yake masa ba yace yazo yan zunnan,
yana kashewa yakira lambar Ya SALEEM,
a ɓangaren Ya SALEEM ɗin kuwa yana zaune cikin bedroom ɗin sa Na'ima na gefen sa like da
shi,
ganin mai kiran nasa a irin wannan lokacin sai da ta ɗan girgiza,
yana ɗaga kiran
yace
"Duk abun da kake kabari kazo yanzu ina niman ka".
Abbu ya faɗa cikin fusatacciyar murya,
da sauri YA SALEEM ya mike ya ɗau makullin motar sa yafita,
A ɓangaren Na'ima kuwa kasa zaune tayi tarika zagawa cikin ɗakin dan duk abin da Abbu
yafaɗa taji, tsoron ta ɗaya kada akan maganar yarin yar nan Abbu yayi masa irin wannan kiran,
"Cabɗi jan lallai kuwa da sakel".

tafaɗa a fili.

Cikin gaggawa Abba ya iso sashin wan nasa do min amsa kiran sa, Abbu
ko zama bai bari Abbu yayi ba ya shiga nuna sa da yatsa yana faɗin
"Me ka ai kata kenan me kayi kenan Idris??
da hankalin ka da girman ka da tunanin ka zaka yanke mata irin wannan hukuncin,
menene amfani da ribar yin hakan ka jefata duniya da kan ka,
akan wani dalilin ka mara tushe da asali,
wani gurin da yafi nan ka bata acan ɗin da ka turatan?,
wani irin rashin imani ne hakan kai kana kwance a makwanci mai kyau kaci mai kyau kasha mai
kyau ita tana can awani duniyar da kai kan ka baka sani ba,baka kuma damu da duk halin da
zata shiga ba,a kan dalilin da baka da tabbacin sa!!".
Sosai Abbu ke yiwa Abba faɗa tamkar zai rufe shi da duka cikin tsananin ɓacin rai.
Ya SALEEM da yanzu shigo warsa ganin yan da Abbu keyiwa Abba yasa shi karaso wa cikin
parlour'n jiki a sanyaye,
da sauri Mamie da tunɗazu take ta sharar kwalla tamike tashi dukan kafaɗar sa tana faɗin
"Yanzu a bun da ka ai kata ke nan SALEEM abun da ka ai kata kenan kai ɗin ka kamata da kan
ka da wani acikin gidan kan?
shine har zaka sake ta?
shekaran ta nawa a cikin gidan sai yanzu zata kawo wani cikin gidan".
cikin muryar kuka sosai take maganar tana dukan kafaɗar sa.
hayaniyar da Ummi taji nafita sosai cikin side ɗin Mamie yasata fita da sauri tanufi side ɗin dan
ganin meke faruwa haka a cikin daren nan,
a tsakar gida ta haɗu da su goggo Hauwa da Aunty Halima suma jin hayaniyar ce tafito dasu
daga sashin Inna da sukayi masau ki can,da sauri sukayi cikin side ɗin hankali tashe jiyo
muryar Mamie tana magana cikin muryar kuka.

Suna shiga da sauri Ummi tayi gun Mamie daketa bugun kafaɗar SALEEM shi ko na tsaye ya
dukar da kan sa kasa,
hannu Mamie Ummi tarike tana faɗin
"A'a Mamie'n Nusaiba menene haka me yasa hakan?".
Mamie tace
"Kyale ni Ummi'n Fauzan idan baije yanemo taba bazan taɓa yafe masa ba,a ina ka ganta da
wani kataɓa kamata tana cin amanar auren ka ko ta hanyar magana da wani ko a waya ce??!,
kyale ni Ummi'n Fauzan sai ya faɗa min yaushe yataɓa kamata tana cin amanar auren sa".
sakin hannunta Ummi tayi kamo na Ya SALEEM da kansa ke sun kuye har lokacin yana jin
zuciyar sa nawani irin tafarfasa,
ta jashi gefe.
su goggo Hauwa kam tsayuwa sukayi suna kallon yan da Abbu ke yiwa Abba faɗa kamar zai
rufe shi da duka.

Rai ɓace Abbu ya juyo gun Ya SALEEM yana wasa masa wani irin mugun kallo,
ganin haka yasa Ummi haɗe hannayen ta biyu tace

"Dan Allah Yaya..."
hannu ya ɗaga mata batare da ya bari ta faɗi abun da zatace ba cikin fusatacciyar murya ya
dubi Ya SALEEM yace
"Kai ka ɗaura wa kanka aure da ita da zaka kwance?
yau nayi da nasanin haɗaka aure da ita nayi nadamar abun da nafaɗawa mahaifiya ta cewa kai
zaka rike mata jika da gaskiya da amana,
yau nayi nadamar faɗar hakan nayi nadamar saurin yar da da hankalin ka da nayi,
da nasani da tun wancan lokacin nacikawa Inna burinta na haɗa auren HAMDAH da Masa'ud,
ban yi tunanin kiyayyar da kake mata yakai nan ba, bayan ka saketa
kakuma bita da mummunar kazafi!!".
rumtse idanunsa yayi yana jin kansa naci gaba da yi masa mugun sara zuciyar sa na tafarfasa
yana jin maganganun iyayen nasa tamkar saukar aradu.
Abbu yaci gaba
"Ka kira ma ai katan gidan ka da duk wani mai hannu a kan maganar yanzu-yanzun nan suzo
ina neman su!!!".
yakarashe maganar cikin tsawa da karaji sosai..


A can cikin gidan SALEEM kuwa lokacin da sakon kiran Abbu ya'isa gare su wasu daga cikin
ma'aikatan gidan da ka gansu kasan suna cikin yanayin tsoro da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login